Kafin zuwan Musulinci a ƙasar Hausa, alummar Hausawa cikin duhun kai take. Ba su da ilimin addini kuma ba tsarin rayuwa ba a tunanin abin da za a fada mai kyau ko maras kyau. A cikin wannan hali na rayuwa babu abin yi sai maguzanci, watau bori, tsafi da camfe-camfe bautawa iskoki da dodanni da suke yi a wannan lokaci ya sa ake samun kalmomin da ke nuna magazanci a cikin karin magananunsu. Misalan karin maganganun da aka samu kafin zuwan Musulunci sun haɗa da:
1. Ƙarya ta ƙare bori ya kashe boka.
2. Agwagwa ba ruwanki da tsafi.
3. Ba’a bori da sanyin guiwa.
4. Bori É—aya suke yi wa tsafi.
5. Ginginbodi kingin girka.
6. Lahadi ga arna fashi.
7. Na samu gafara gun dodo.
8. Ranar tsafi bunsuru ka kudi.
2 Sun ba da kai, bori ya hau
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.