Ticker

6/recent/ticker-posts

Aminu Ladan ALA: Rama Cuta ba Laifi ne ba

Amma gane wanzami,
Mai biɗar mai jarfa,
Rama alkhairi ga mai cuta ba illa ne ba Alan waƙa.

Kar ka ruɗa ruɗaɗɗe,
Kar ka murɗa murɗaɗɗe,
Rama cuta ga macuci ba ille ne ba Alan waƙa.



Haƙuri yana da maauni ba za ka ɗauki raini ba,
Haƙuri yana da misali ba za ka ɗauki wasa ba,
Haƙuri yana da suriri ba za ka ɗauki zambo ba,
Ba ka zo da cuta ba ba hali na zambo ba,
Ba da tsigunagun ba,
Rama cuta ga macucinka ba illa ne ba.

Kar ka juya juyayye,
Kar ka rikkita rikitacce,
Maida alkhairi akan sharri ba tsoro ne ba.

Mun zamo madubin duban al’umma na ci gaba,
Mun zamo fitulun da ke hasken binne su ba wai ba,
Mun zamo abin sha’awar a gani a jib a fahar ne ba,
Kar ka fara yin zamba,
Kar mu koyi yin zamba,
Ba batu na tsoro ba,
Mu ake duba da alkhairi ba masu sharri ba.

Sara da sassaƙa ba zai hana gamji tofo ba,
Kainuwa dashen Allah ba shukawar mutane ba,
Tsiran da Allah ke so zai tsiro ba da lura ba,
Ba da kai ruwa gun ba,
Rabbi kai na sa gaba,
Ban nufi ga cuta ba,
Sama sassauci ga mai cuta ta ba tsoro ba.

Kar ka zagi zargagge,
Kar ka doke jemamme,
Kau da zambo ga mazambaci ba kasawa.

Haƙuri yana da faraga da ba ai wa ƙaidi ba,
Haƙuri yakan dafa dutse ya sha ba za ya ƙosa ba,
Haƙuri yana saka bawa ya hau abokanan gaba,
Ba a ma yi komai ba,
Ba ka ma ga komai ba,
Ba ka riske komai ba,
Mai da alkhairi ga mai sharri ba illa ne ba.

Ba zai zo da gwalli ba,
Shi ba jahilci ba ƙauna ce,
Ba ja-in-ja ai ba,
Ku ne madubin dubawa ai rayuwa baba,
Ba a fara komi ba,
Ba ka riske komi ba,
Ku zo mu yo tuba,
Yanzu anka sa ƙamba,
Taimako da idanunka ka ƙauna be ma ba.

Godiya nake a gurin Allah da ba za ta irgu ba,
Da ya ba ni abokanan hulɗa ba ‘yan ta’adda ba,
Ba ‘yan izan wuta ba ‘yan hikima ba ‘yan baranda ba,
Fantimoti ag gaba,
Da Maryam A. baba,
Ga Murja ‘yar baba,
Da fasihiya Fati Nijar mai hali babba.

www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments