Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa Da ƙasa Na kwanaki biyu Kan ‘Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa A Yau’ da Hukumar Gidan Tarihi ta jihar Katsina ta shirya tare da haɗin guiwar Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua Katsina a ranakun 25-26 ga watan Yuni, 2013 a babban ɗakin taron jami’ar.
Daga
Umar Aliyu Bunza
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
Lambar Waya: 07063532532, 08095750999
Ƙibďau: aliyubunzaumar@yahoo.com
Tsakure
Al’ummar Hausawa, al’umma ce da ta kasance bisa tsarin
al’adu da ɗabi’u na gari tun kafin cuɗanyarta da Turawan Mishan. Da Turawan
suka shigo garuruwan Hausawa suka ga al’adunsu da ɗabi’unsu, suka burge su, sai
suka yi rubuce-rubuce kansu da ma rayuwar Hausawa gaba ɗaya. Haka al’adu da ɗabi’un
Hausawa suka kasance abin yabawa har zuwa baya-bayan mulkin mallaka suka gurɓace,
wasu al’adu da ɗabi’un na gari ma suka ɓata. A wannan maƙala na duba al’adu da ɗabi’un
na Hausawa ne daga rubuce-rubucen Turawan, sannan na duba yadda suka gurɓata
daga zamanin mulkin mallaka zuwa yau.
1.0
GABATARWA
Al’ada kalma ce da take nufin hanyar rayuwar al’umma. Al’ummar Hausawa ta
kasance bisa al’adu na gari tun kafin shigowar Turawan Mishan ƙasar Hausa.
Wannan ya sanya lokacin da Turawan suka yi cuɗanya da Hausawa sai al’adun
Hausawa suka burge su har suka yi rubuce-rubuce kansu domin amfanin sauran
Turawan duniya. Haka rayuwar Hausawa ta ci gaba har zuwa lokacin da Turawan
Ingila suka yi wa ƙasar Hausa mulkin mallaka. Tun wannan lokaci al’adun Hausawa
suka gurɓata har zuwa yau da wasu al’adun suka ɓata, aka maye gurbinsu da wasu
miyagun al’adun. Manufata a wannan maƙala ita ce, duba wasu al’adun Hausawa da
Turawan Mishan suka taras a wancan lokaci, suka kuma taskace su a littattafansu
na adabi, sannan da duba yadda suka gurɓata a yau. Na fara da duba al’adun
Hausawa gabanin Mishan da kuma bayan shigowar Mishan da duba yadda al’adun suka
gurɓata daga lokacin kafa mulkin mallaka zuwa yau. Daga ƙarshe na kawo
sakamakon bincike da kammalawa da manazarta.
2.1
AL’ADUN HAUSAWA GABANIN SHIGOWAR MISHAN
Al’umma Hausawa al’umma ce da ta daɗe da wanzuwa a bayan ƙasa. Faɗar lokacin da
al’ummar ta fara wanzuwa abu ne mai wuya sai dai ƙiyastawa kawai. Al’ada wadda
Bunza (2006: ɗɗɗii), ya ba ta ma’ana da cewa ‘Al’ada tana nufin dukkanin
rayuwar ɗan Adam tun daga haihuwarsa har zuwa kabarinsa. A ko’ina mutum ya samu
kansa duk wata ɗabi’a da ya tashi da ita tun farkon rayuwa, ita ce al’adarsa da
za a yi masa hukunci a kai. Babu wata al’umma da za ta rayu a doron ƙasa face
tana da al’adar da take bi, kuma da ita ake iya rarrabe ta da wata da ba ita
ba.’ Al’ada sababbiyar hanyar rayuwar al’umma ce da ke tafiya kafaɗa-da-kafaɗa
da masu ita. Wannan ya sa al’adu da rayuwar Hausawa suka kasance suna tafiya
tare tun lokaci mai tsawo.
Tun kafin saduwar Mishan da Hausawa, al’adun Hausawa sun kasance nagartattu da
suka samar wa Hausawa yabo da ɗaukaka ga Turawa. A wancan lokaci al’adun
Hausawa sun kasance abin alfahari ga kowane Bahaushe. Wannan ya sa a ko’ina
Bahaushen wancan lokaci ya shiga ake mutunta shi, ake amincewa da shi har a ƙulla
alƙawarin amana da shi a kuma ba shi gaskiya. Al’adun ne suka toshe kowace kafa
da za ta ba kowane Bahaushe dama na ya zama lalatacce ko ya zama abin ƙi a
kowace irin mu’amala. Bunza (2011: 252), ya kasa al’adun Hausawa na wancan
lokaci zuwa gida bakwai. Idan aka yi la’akari da kason, za a ga cewa, ba shakka
gabanin shigowar Mishan a ƙasar Hausa, al’adun sun tanadi dukkan abin da mutum
yake buƙata na kyautata rayuwarsa. Wannan ya shafi zamantakewa da tsaro da ci
da kai da kyakkyawan shugabanci da sauransu. Ganin irin wannan tsarin al’adun
Hausawa na gari ya sa wasu Mishan suka yaba al’adun. Ga misali Likita Miller
wanda yake ɗaya daga cikin Ayarin Mishan Ga Hausawa na ƙungiyar CMS ya bayyana
Hausawa:
‘A matsayin maɗaukaka daga ‘yan uwansu na kudancin
ƙasa ta fuskar al’adu da halayen kirki da kuma halin zaman tare.’
(Crampton, 1975: 139).
Idan aka yi nazarin kalaman wannan ɗan Mishan za a ga cewa, bayanan na nuni ne
ga cewa, al’adun Hausawa a wancan lokaci sun kasance na gari wanda haka ya sa
Hausawa suka fifita kan sauran ƙabilu ta fuskar halayen kirki da kuma iya zama
da kowane mutum. Wannan ya nuna a zamantakewar Hausawa da kowace ƙabila a
wancan lokaci akwai amana da gaskiya da kariyar mutunci wanda duka kyakkyawan
tanadi ne na al’adunsu ya haifar da haka.
3.1
AL’ADUN HAUSAWA BAYAN ZUWAN MISHAN
Mishan ayarin Turawa ne da ya tunkari ƙasar Hausa da nufin yaɗa addinin
Kirista. Su waɗannan Turawa sun kasance a ƙarƙashin wasu ƙungiyoyi da aka kafa
kan wannan manufa ta yaɗa addinin a sassan duniya daban-daban. ƙungiyar Church
Missionary Society (CMS) ce ta fara ɗaukar alhakin tura jami’anta zuwa ƙasar
Hausa don wannan aiki.
Tun kafin shigowar jami’an Mishan cikin Hausawa, sun sami wasu bayanai game da
Hausawa ta hanyoyi daban-daban da kuma lokuta mabambanta. Ana hasashen Turawa
sun fara sanin wani abu game da Hausawa ne tun a wajajen ƙarni na sha shida. An
nuna cewa a wajajen shekarar 1535 ne aka sami wani Balarabe ɗan asalin Afrika
ta Arewa mai suna Al-Hassan ibni Muhammad Al-Wizaz Al-Fasi wanda ya sauya
sunansa zuwa Leo Africanus a lokacin da ya yi zaman kurkuku a ƙasar Italiya ya
rubuta littattafai guda bakwai cikin harshen Larabci inda ya bayar da labarin
tafiye-tafiyensa cikin daulolin Afrika. An fassara littattafan zuwa harshen
Ingilishi da wasu harsunan ƙasashen Turai. A cikin littafi na bakwai ne ya
bayyana ziyarar da ya kai ƙasar Borno da wasu dauloli na ƙasar Hausa a tsakanin
shekarar 1513 zuwa 1515. Ya nuna ƙasar Borno na da nasu harshen magana, sai dai
ƙasa ɗaya (da bai ambaci sunanta ba wadda ita ce ƙasar Hausa) ya nuna suna
amfani ne da harshen Gobir (Yahaya, 1988: 73 da Hair, 1994: 31).
Bayan bayanan wannan mutumin kuma, akwai wani bawa ɗan ƙasar Borno da wani
Balarabe ɗan ƙasar Tunis mai suna Abdurrahman wanda ya kai ziyarar jakadanci a ƙasar
Denmark ya je da shi. Shi wannan bawan ya ji harsunan Barbarci da Larabci da
Hausa. Daga wannan bawan ne wani ɗan ƙasar ta Denmark mai suna Niebuhr wanda ya
ji Larabci dalilin yawon da ya yi a cikin ƙasashen Larabawa a wajajen shekarar
1773, ya koyi Hausa har ya rubuta wasu kalmomin Hausa da ya ji daga wannan
bawan (Yahaya, 1988: 74 da Hair, 1994: 33). A ƙasar Ingila kuwa an fara samun
labarin ƙasar Hausa ne kai tsaye a cikin shekarar 1792 daga wani ɗan kasuwa
Balarabe mutumin Moroko (Morocco) mai suna El-Hajj Abd Salam Shebeni wanda ya
yi zuwa fatauci a Ingila. Shi wannan Balaraben ne ya gaya wa Sakataren ƙungiyar
Afrika ta London cewa akwai wata ƙasa da ake kira HOUSA a Afrika ta yamma, kuma
mutanen cikinta suna da ilimin rubutu da haruffan Larabci (Yahaya, 1988: 75 da
Hair, 1994: 34). Samuwar waɗannan bayanai ya sa Turawa suka shiga neman matakan
shigowa cikin wannan al’umma domin sanin rayuwarta don ganin yadda za a tatsi
arzikinta. Wannan ya sa gwamnatin Ingila ta tura ayari daban-daban na leƙen
asiri daga shekarar 1821-1896 don tara mata bayanai kan ƙasar Hausa (Batten,
1934:318-320 da Niɓen, 1955: 63-76).
Ta ɓangaren Turawan Mishan waɗanda ƙudurinsu shi ne yaɗa addinin Kirista kuwa,
fitacciyar ƙungiyar nan ta yaɗa addinin Kirista mai suna Church Missionary
Society (CMS) da ke da mazauninta a Ingila tuni ta fara tunanin yadda za ta
ratsa ƙasashen Afrika ciki kuwa har da ƙasar Hausa. Sai dai tun kafin ƙungiyar
ta shigo ƙasar Hausa, sai da ta fara tura wasu jami’anta a ƙasar Saliyo a
shekarar 1832 domin aikin yaɗa addinin Kirista da kuma fara nazarin al’adu da
harsunan al’ummun da aka tara a wurin domin ya zama sharar fage ga waɗanda za a
tura domin aikin yaɗa addinin Kirista can cikin ƙasashen mutanen. A wajen
wannan aikin ne ɗaya daga cikin jami’an mai suna James Feredrick Schon ya
karkata hankalinsa zuwa ga nazarin al’adun Hausawa ta hanyar harshensu da
adabinsu. Haka kuma tun a wannan aikin Schon ya fara bayyana ƙimar Hausawa ta
la’akari da girman harshensu da al’adunsu. Ya ce,
Idan aka yi batun muhimmanci, (harshen Hausa) ana iya ɗora shi a matsayin na
farko.... Zai iya buɗa ƙofa don hulɗa da ɗimbin mutane da kuma ƙasashe masu
yawa..... Ana iya danganta watsuwar harshen da yanayin kasuwancin da ya gudana
tsakanin Hausawan da sauran ƙasashe, (Ade-Ajayi, 1970: 357).
A wani wurin a cikin bayanin na Ade-Ajayi, (1970: 357), Schon ya ƙara bayyana
yadda ya fahimci girma da ƙimar harshen Hausa a tsakanin sauran harsunan, ya
ce:
Harshensu (na Hausa) ya tabbatar da fifikonsu a kan sauran harsunan ƙasashen
Afrika waɗanda nike da masaniya kansu. Harshen na da yalwar kalmomi; kuma
tsarin nahawunsa na da sauƙi da sha’awa, wanda shi ya sa yake da sauƙin
fahimta.
Idan aka yi la’akari da sha’awar Schon kan harshen Hausa da kuma yadda ya nuna ƙimar
harshen, wannan na nuna cewa ko al’adun Hausawa a wancan zamani nagartattu ne
kuma tsayayyu da ke iya ba Bahaushe kowane irin girma da kariya.
Bayan kammala aikin Schon a Saliyo, sai kuma a shekarar 1841, gwamnatin Ingila
ta shirya wani ayari don gano Kogin Neja da kuma tattara bayanai dangane da
al’ummun da suke zagaye da kogin. A wannan tafiya ƙungiyar CMS ta sami wakilcin
mutane biyu (Schon da Crowther) da aka yi aikin na watanni shida. A wannan
tafiya ce Schon ya sami damar saduwa da Hausawa masu yawa a ƙasashen da ke maƙwabtaka
da ƙasar Hausa, kuma inda al’adun Hausawa suka yi tasiri sosai kan al’ummun da
ke wuraren. A yawace-yawacen da Schon ya yi a wajajen Bida da nazarce-nazarcen
da ya yi na sa ido kan al’adun Hausawa ya sa ya ƙara faɗin wani abu kan Hausawa
kamar haka:
Hausawa da masu jin harshen suna nan a ko’ina daga yankin Idda; kuma a duk
lokacin da ka ƙara matsawa, haka za ka
ƙara ganin su a ko’ina...., (Ade-Ajayi, 1970: 120).
Da yake abin nema ya samu, da ƙare aikin gano Kogin Neja, a shekarar 1847 sai
Schon ya bar aikin yaɗa addini, ya koma Ingila ya zauna ya shiga rubuce-rubucen
littattafan Hausa. ɗaya daga cikin littattafan nasa mai suna littafin Magana
Hausa (1885) ya kasance kan al’adun Hausawa kawai ta hanyar adabin Hausa (
Schon 1885).
Akwai al’adun Hausawa masu yawa da Schon ya taskace a wannan littafi da suka haɗa
da yanayin hulɗa da shugabanni da tsarin cin abinci da magani da lamarin layya
da sana’o’i da sauransu. Ga misali, ‘tatsuniyar mutane uku sunansu Kusa da
Kwania da Gaba.’ A wannan tatsuniya an nuna Kusa mutum ne mai dukiya. Shi kuma
Kwania ba shi da dukiya mai yawa. Shi ko Gaba talaka ne, amma mai dabara da
wayo. Wata rana Kusa ya nuna wa abokansa (Kwania da Gaba) zai je wurin sarki
neman wata buƙata. Kwania ya ce masa ya tafi ya aikata. Kusa ya tafi wurin
Sarki, Sarki ya ce ba zai saurare shi yau ba, sai ya sake dawowa wata rana. Ya
dawo ya gaya wa abokansa. Gaba yana shiru bai ce ƙala ba. Can sai ya ce, zan ba
ku wata dabara ko da yake na san ba za ku ɗauka ba domin ni talaka ne. Kai Kusa
baƙo ne a garin nan, kana da dukiya, amma a nan ba ka bi hanyar da ta kamata ba
da ka tafi wurin Sarki da kanka, ba zai ba ka abin da kake so ba. Idan kana son
ka samu abu ga Sarki, ka tambayi manyan mutane na kusa gare shi. In sun ga
dabararka mai kyau ce, su gaya wa Sarki. Wannan tatsuniya ta nuna al’adar
Hausawa ta yanayin hulɗa da sarakuna. A nan Gaba ya nuna a al’adar Hausawa idan
ana neman abu ga Sarki, to ta gefen fadawa makusantan Sarki ake bi don samun
nasara ba wai kai tsaye ake zarcewa wajen sarki ba. A nan akwai sananniyar
al’adar Hausawa ta girmama shugaba da kuma tsari na musamman a zaman fada.
Shi kuma labari mai suna ‘Ragon laiya’ an taskace al’adar Hausawa ce ta saye da
tattalin ragon layya tun kafin lokacin Sallar layya ya yi da kuma irin al’adun
addini da Hausawa ke yi na wanke rago da kula da lafiyarsa har zuwa ranar layya
a yanke shi. Haka kuma an kawo wasu al’adu da Hausawa ke yi lokacin Sallah na
abinci da hawan Sallah da sauransu.
Shi ko labari mai take ‘Albasa magani ga sara machiji’ ya kawo bayanin wasu
al’du na maganin Hausawa ne guda biyu. Na farko amfani da albasa don kariyar
kai daga saran maciji da kuma yadda ake sarrafa ta don amaye dafi idan maciji
ya yi sara. Magani na biyu shi ne yadda ake amfani da kanwa don maganin ciwon
ciki.
Labarin ‘cin tuwo na Afrika abin na murna shi ke’ a cikinsa an taskace al’adun
Hausawa ne na tsarin zamantakewar iyali da kuma tarbiyyarsu ta cin abinci. A
wannan labari an kawo wasu al’adun Hausawa na cin abinci kamar ci tare da
jama’a da shimfiɗa tabarma ko buzu a ci a bisa, da haɗa hannun uwa da yara don
ta kula da yadda yara suke cin abinci da sauransu.
Ta fuskar al’adun sana’o’in gargajiya kuwa, an kawo al’adun jima da rini da
kamun kifi. An kawo cewa, a al’adar Bahaushe a wancan lokaci ana yin rini ta
hanyar gina rami mai zurfi kamar gaba huɗu ko biyar sannan a gyara cikinsa da
yumɓu. Idan ya bushe, sai a cika shi da ruwa sannan a jiƙa baba a sa ciki har
ya kusa cika ramin. Daga nan sai a ɗauki sanduna masu tsawo huɗu, a daka baba
har ya fara ja, sannan a rufe shi kamar kwanaki huɗu ko biyar, a buɗe ramin, a
wanke zane fari in mai datti ne, sannan a sa cikin marina.
Ita kuma sana’ar jima ana yin ta ta hanyar cika babbar tukunya da ruwa a zuba
tokar kara ko itace sai a dama tokar sannan a zuba bisa ga fatar da ke da
gashi. Daga nan a bar ta ta kwana ɗaya ko biyu sannan a fitar da fatar. Daga
nan sai a shimfiɗa fatar kan wani ice da ake kira majimi sannan a yi amfani da
wani icen mai suna ɗan majimi, sai mai jima ya durƙusa ya shiga yin jima ta
hanyar goga ɗan majimi ga gashin fatar. Sannu-sannu gashin zai fita ya bar
fatar. Daga nan sai a wanke fatar, a daka bagaruwa a zuba cikin tukunya a zuba
ruwa, sannan a tsoma fata ciki, a rufe ta kwana. Daga nan sai a fitar da fatar
a tafi a shanya ta. Idan ta bushe sai a shafa mata mai a ta murzar ta har ta yi
taushi. A lokacin da ake murzar ta idan tana kuka shi yake nuna bagaruwa ta
ishe ta. Idan kuwa aka murza ta aka ga ko’ina da taushi, shi ya nuna mai ya
ishe ta. Daga nan sai a tafi a yi jika ko walki.
Ita kuma sana’ar kamun kifi an nuna a al’adance ana yin ta ne da taru. Haka
kuma a wasu wurare suna kamun kifi ta hanyar shiga ruwa da goruna biyu
manya-manya da sanda ƙarama. Idan aka kama kifi babba sai a sa sanda a fashe
kansa.
Idan aka dubi yanayin da aka nuna ana gudanar da waɗannan al’adu za a ga cewa,
ko bayan zuwan Mishan, al’adun Hausawa suna nan bisa tsarinsu na inganci da
nagarta ba su garwaya da kowace irin baƙuwar al’ada ba balle su tashi daga
ainihin yadda aka san su ko su sauya launi ko siga ta yadda za su dabirta ɗan
gado ko Bahaushe idan ya gan su. Haka kuma bayanan al’adun ya kawo yadda al’adu
daban-daban suka tanadarwa Hausawan hanyoyin maganin matsalolinsu da samun ci
gaba a rayuwarsu.
Bayan samuwar wannan littafi da Turawa suka shafe shekaru 8 suna nazarin
al’adun Hausawa a cikinsa, sai kuma shekarar 1893 ƙungiyar CMS ta sake turo
wani jami’inta mai suna Charles Henry Robinson zuwa ƙasar Hausa. C. H. Robinson
ne ainihin ɗan Mishan na farko da ya yawaci sassan ƙasar Hausa har kuma ya
share shekaru uku (1893-1896) cikinta. A yawace-yawacen nasa, babban abin da ya
fi ɗauke masa hankali shi ne lamarin addinin Musulunci da karatu da neman ilimi
da ya mamaye ƙasar Hausa. Wannan ya sa Robinson ya bayyana abin da ya gani game
da rayuwar Hausawa kamar haka:
‘Baya ga Hausawa babu wata al’umma a Arewacin Ekwaito, haka ma a dukkanin faɗin
Afrika in ban da Masar da Abissina wadda ta rage harshenta a rubuce, ko kuma ta
yi wani hoɓɓasa don samar da adabi. Hausawa sun sarrafa tsarin baƙaƙen Larabci
suka rubuta waƙoƙi masu yawa nasu bayan ayyukan tarihi da na shari’ah’
(Robinsoon 1900: 179).
Idan aka yi la’akari da wannan bayani za a ga cewa, tun da al’ada ta haɗa
kowane abu na rayuwar al’umma, ke nan karatu da neman ilimi wani sababben abu
ne da ya yi kaka-gida a rayuwar Hausawa tun a wancan zamani. Ci gaban al’adun
Hausawan wancan lokaci ya sa har suka ƙirƙiri dabarar sarrafa baƙaƙen Larabci
su rubuta harshensu wanda kuma suna cikin kaɗan daga al’ummun Afrika da suka yi
wannan.
Bayan lamarin ilimi, Robinson ya nuna Hausawa sojoji ne kuma masu gaskiya da ƙarfi
wanda ke nuna al’adun Hausawa a wancan zamani kyawawa ne kuma suna bisa tsari
managarci da rashin samun gurɓata bale lalacewa. Ga abin da ya ce:
‘..kamfanin Royal Niger ya yi ɗaukar su (Hausawa) ‘yan sanda da sojoji tun kafa
shi. Taƙaice, aikin kamfanin ba zai gudana ya yi nasara ba tare da taimakonsu
ba. Ga alama an halicci Hausawa ne a matsayin sojoji. Ba shakka sun sami wannan
ɗaukaka ce ba don yaƙi ba kawai sai dai saboda fifikon halayya. Wannan fifikon
ya fito fili ne musamman lokacin da aka ɗauki Hausawa aikin ɗan sanda, lokacin
da ana Lagas. ɗan sanda ɗan ƙasa na kowace ƙabila an shaide shi da karɓar cin
hanci, wannan ya sa ba a dogara gare shi ga aikin gaggawa ko kuma kamo duk
wanda ya san yana sama gare shi. ɗan sanda Bahaushe farar fata sun tabbatar
yawanci ba ya karɓar cin hanci, kuma yana son nuna muhimmancinsa ta hanyar kamo
kowane mutum duk yadda ya yi masa lallami da daɗin baki da kawo uzuri. Waɗannan
ɗabi’u da kuma ƙarfin jiki (physical strength) na yi amanna su suka sa Bahaushe
ya zama tsayayyen soja. Yana daga abin da na lura da shi a lokacin da muke
tafiya zuwa cikin ƙasar Hausa, Bahaushe na iya ɗaukar riɓi biyu na kayan da
sauran ƙabilu ke ɗauka ya yi tafiya ba tare da gunaguni ba (Robinson, 1900:
25-28).
La’akari da wannan bayani, ya nuna ke nan a wancan lokaci, akwai wasu al’adu na
gari da suka sa Hausawa suka sami karɓuwa da fifiko ga Turawa fiye da kowace ƙabila
ta kusa ko nesa ga Hausawa. Ire-iren waɗannan al’adun sun haɗa da riƙon
gaskiya, amana, rashin tsoro, rashin cin hanci da kuma juriya. Wannan kuwa ya
faru ne saboda yawace-yawacen Mishan da zamansu cikin Hausawa bai sa Hausawa
suka rena al’adunsu balle su kalle su ƙauyanci ba. Haka kuma Mishan ba su sami
damar kafa wani abu da zai gurɓata tunanin Hausawa ba har ya shafi al’adunsu.
Shi kuma Reberan Brooke wanda yake shi ma ɗan Mishan ne a zaman da ya yi a
wajajen Lokoja, ya yi nazarin rayuwar Hausawan da ya yi hulɗa da su a wurin, ya
bayyana nasa ra’ayi game da rayuwarsu kamar haka:
‘Hausawa su ne mafi kyaun al’umma a Afrika a wajen hikima
za ka gan su masu son watsa zaman lafiya. Halinsu na nuna sanin
ya kamata ya kasance abin jan hankali (burgewa).
(Bunza, 1994: 266).
Shi ma Miller wanda shi ne ya jagoranci zaman Ayarin Mishan Ga Hausawa na ƙungiyar
CMS a cikin ƙasar Hausa, musamman a garin Zariya daga shekarar 1901 ya bayyana
Hausawa:
‘A matsayin maɗaukaka daga ‘yan uwansu na kudancin ƙasa ta fuskar al’adu
da halayen kirki da kuma halin zaman tare.’ (Crampton, 1975: 139).
Idan aka yi nazarin waɗannan bayanai da idon basira, za a tabbatar da cewa a
zamanin zuwan Turawan Mishan ƙasar Hausa, al’adun Hausawa sun kasance abin
sha’awa da yabawa wanda shi ya sa Turawan suka fifita darajar Hausawa kan
sauran ƙabilun da ke kusa da kuma nesa da Hausawa duk da irin takin saƙa da
suke yi da lamarin addinin Hausawa na Musulunci. Tilas tasa Turawan suka
tabbatar da cewa Hausawa ne amintattu kuma waɗanda ake iya dogara kan aikinsu
ga ƙwazo da rashin lalaci, balle raganci. Duk waɗannan sun samu ne saboda
kyakkyawan tanadi da al’adar Bahaushe ta yi masa na gaskiya da mazakuta da
kyawawan halaye da dauriya, kuma ba wani abu da ya gurɓata al’adar tasa.
4.1 KAFA
MULKIN MALLAKA ZUWA YAU: CI GABA KO CI BAYA
Mulkin mallaka wani tsarin mukin mamaya ne na ƙarfin soja da Turawan Ingila
suka yi wa Nijeriya. ƙasar Hausa ta kasance ɗaya daga cikin yankunan da irin
wannan tsarin ya samar wa koma baya a al’adunsu. Wannan ya faru ne ta yadda
jami’an mulkin mallaka suka sauya tunanin Hausawa, suka yaƙe su a ilmance.
Likita Miller a lokacin ganawarsa da Lugga a shekarar 1900 ya ba da shawarar
musanya hanyar karatun Hausawa ta Muhammadiya da ta boko domin ta haka ne masu
tasowa a gaba za su tashi da tunani irin na Kirista –Turawa a maimakon na cikin
adabin Musulmi wanda yake na addinin Musulunci (Miller 1936: 200-201). Idan aka
dubi wannan musanyawar za a ga cewa, wata hanya ce ta yaƙar tunanin Hausawa a
ilmance Miller ya kawo. Turawan na sane da cewa, tsarin karatun Muhammadiya
yana ƙunshe da hanyoyin tabbatar da al’adun Hausawa na gari waɗanda matuƙar aka
bar Hausawa kansu ba za a mulke su yadda ake so ba. Al’adun Turawa ba za su
shimfiɗu ba sai idan an shigo wa Hausawa da su ta hanyar ilimi. Da wannan aka ɗaga
darajar ilimin boko, aka takura na Muhammadiya. Ba shakka wannan musanyawar ta
taka rawa ƙwarai ta hanyar raunana al’adun Hausawa na gari na da can.
Idan aka dubi al’adun Hausawa da suka burge Mishan na wancan lokaci har suka faɗe
su a rubuce-rubucensu na adabi, za a ga cewa, da yawa daga cikinsu sun gurɓace,
wasu kuma sun ɓata ba ko kufansu.
Idan aka ɗauki al’adar cin abinci a taro yau da yawan garuruwan Hausawa wannan
al’ada ta mutu. Magidanta sukan ci abincinsu ne cikin gidajensu sai abin da ba
a rasa ba idan an yi baƙon kunya. Su ma yara a yau, iyaye ba su kula da su haɗa
su su ci abinci tare ba, a maimakon haka sai dai a sa wa kowane yaro abincinsa
a kwano daban. Batun kula da hannun da yaro ke cin abinci da shi an yi watsi da
wannan. Sai ka ga yaro na cin abinci da hannun hagu, idan ma wani ya yi magana,
sai ka ji uwa ta ce ‘Yarinta ne. Idan ya girma ai zai bari.’ Rusa irin wannan
al’ada ya kawo wa Hausawa rashin haɗin kai da jin kukan juna balle a taimaki
marashi.
Lamarin maganin gargajiya an illanta shi. Kanwa wadda a al’adance Hausawa sun
san ta karta’u ce ga ciwon ciki, a yau an nuna ita ke sa ciwon hawan jini. Irin
wannan suka ta raunana ilahirin magungunan gargajiyar Hausawa. Wa zai shafa
albasa a ƙafarsa idan zai yi tafiya da dare don kare kai daga maciji? Wa zai
sha kunun albasa don zubar da dafin maciji? Da yawa ‘yan yau ba su san da
wannan ba, balle tunanin jarrabawa ba. Wannan illantawa ta sa yau ƙasar Hausa
sai magungunan gargajiya na wasu ƙasashe kamar Sin ake tallatawa ko’ina waɗanda
wasu itacen ƙasar Hausa ne aka ɗauka, aka je da su can aka sarrafa.
Ita kuwa al’adar sayen dabbar layya da tattalinta tun da sauran lokaci da Schon
ya kawo a wannan littafi, tuni ta zama tsohon yayi. Hausawa masu yawa a yau sun
gwamnace su bari sai ranar jajibirin Salla su sayi dabba, ta kwana ɗaya a
hannunsu, su yanke wai don tsoron kiwo. Irin wannan ya sa a lokacin Sallar
layya kuɗin dabbobi ke tashin gwabron zabo. Ka ga mutum ya shiga kasuwa da kuɗi
masu yawa, amma sai a ga ya fito kasuwa da dabba kamar ta sadaka. Ta wannan
dalili ya sa wasu Musulmi a yau suke yanka dabbar da ba ta cika ingantattun
sharuɗɗan layya ba.
Sananniyar al’adar Hausawa ta riƙon sana’ar gado yau wannan an bar ta.
Sana’o’in gargajiya da suka burge Turawa a wancan lokaci kamar jima da rini da
su da sauransu al’amarinsu a yau sai ci baya yake yi. ‘Yan gado sai barin
sana’o’in suke yi suna komawa ga wasu don neman arziki marmaza. Su kuma masu
haye, suna shiga cikin sana’o’in babu shiri don ba naƙaltar al’adun sana’o’in.
Wannan yanayi ya kawo wa sana’o’in gurɓatar al’adunsu da kuma ci baya wanda ya
sa a yau ƙaramin abu kamar yuƙa an fi ganin ƙimar na ƙasashen waje.
Shi kuwa abin da ya ɗauke hankalin Robinson na addini da ilimin Hausawa, yau
zamani ya sa an bar Hausawa baya har ta kai yankin ƙasar Hausa ake yi wa burgar
kasancewa koma baya ta fuskar ilimi. Ta fuskar ƙwazo, jarunta, gaskiya da riƙon
amana da Robinson ya nuna Hausawa ne kan gaba, sai Hausawan yau kamar ba
jikokin na jiya ba ne. A yau har wasu ƙabilu da ba su kai Hausawa ba ke nunin
Hausawa da ɗan yatsa suna kira musu ci-ma-kwance marasa amfani, sai dai a tatsi
arzikin wasu a kai musu kawai. Kowane rashi gaskiya wanda Turawan suka nuna
babu shi ga Hausawa kamar cin hanci, rashawa, ƙarya, tsoro, butulci da uwa-uba ƙin
juna a yau sai Hausawa kawai. Irin wannan yanayi da zamanin mulkin mallakaya
jagorancin ɗinka wa Hausawa rigar ƙasƙanci suka sa ya ja musu kowane irin cin
kashi yi musu ake yi. Kowace shara a kansu ake zubarwa. Abin da ba a san
Hausawa da shi ba na sakin al’adunsu da rungumar baƙin al’adu ido rufe sai ga
shi yau ya ƙare kansu. A yau koma baya ga al’adun Hausawa na gari da Turawan
Mishan suka tabbatar a wancan zamani ba ƙarama ba ce, kuma ba wadda ake iya
shawo kanta ba ne kai tsaye cikin lokaci kaɗan ba.
5.1
SAKAMAKON BINCIKE
Binciken nan da aka gudanar don gano koma baya ga al’adun Hausawa da Mishan
suka taskace a rubuce-rubucensu ya gano wasu muhimman batutuwa kamar haka:
i) Kafin haɗuwar Mishan da Hausawa, al’adun Hausawa sun kasance masu kyau,
wanda kuma su ne suka yi wa Hausawa jagoranci ga zama sahun gaba ga samun yabo
ga Mishan.
ii) Shigowar Mishan ƙasar Hausa da hulɗarsu da Hausawa ba su yi wani tasiri ga
sauya tsare-tsaren al’adun Hausawa ba. Rashin tasirin kuwa ya kasance ne saboda
Mishan a wancan lokaci ba su sami kafa kowane abu da zai gurɓata tunanin
Hausawa ba, balle ya taɓa al’adunsu.
iii) Al’adun Hausawa sun fara gurɓata ne daga lokacin mulkin mallaka. Lamarin
mulkin mallaka ne ya shigo da abubuwa masu yawa da suka yaƙi tunanin Hausawa da
su har suka gurɓata al’adunsu. Karatun boko ne ya kasance kai na abubuwan da
suka gurɓata al’adun Hausawa.
iɓ)Tilas sai Hausawan yau sun riƙi al’adun na jiya za su sami ɗaukaka a
duniyarsu. Al’adun Hausawa da suka rayu kafin mulkin mallaka irin gaskiya,
mutunta juna, alƙawari, amana, riƙon sana’a da sauran halaye na gari ne suka sa
Mishan suka yaba waɗancan Hausawa. Ba shkka su ne za su sa a yaba Hausawan yau.
Wannan zai burge ku
https://www.amsoshi.com/2017/07/25/al%c6%99alami-ya-fi-takobi-nazarin-kaifin-al%c6%99alamin-malam-saadu-zungur-a-fagen-dagar-siyasar-nijeriya/
6.1
KAMMALAWA
Al’ada aba ce da ta shafi ɗaukacin rayuwar al’umma. Kamar yadda aka gabatar,
al’ummar Hausawa koda Turawan Mishan suka riske su sun same su da al’adu
nagartattu waɗanda su ne wannan maƙala ta nuna misalan wasu daga abin da
Turawan suka yi rubutu kansu. Al’adun sun ci gaba da zama na gari har zuwa
zamanin mulkin mallaka lokacin da zamani ya yi illa kan rayuwar Hausawa, ya gurɓata
al’adunsu. Haka wannan illar ta ci gaba kan rayuwar Hausawa har zuwa yau da
nason jiya na mulkin mallaka ya rage kan Hausawa. A taƙaice maƙalar ta tabbatar
da gurɓatar waɗancan al’adun a yau saboda illar zamani.
MANAZARTA
Ade-Ajayi J. F. (1970), Journal of the Reɓ. James Frederick Schon and Mr.
Samuel Crowther who accompanied the Eɗpedition up the Niger in 1841. Second
Edition. Frank Cass & co. Ltd., London
Ade-Ajayi, J. F. (1962), Christian Missions In Nigeria 1841-1891: The Making Of
A New Elite. Eraston, New York.
Aliyu, S. A. (2000), ‘‘Christian Missionaries and Hausa Literature in Nigeria,
1840- 1890: A Critical Eɓaluation.’’ A Cikin Mujallar Kano Studies New Series ɓol.1,No.1,
Jami’ar Bayero, Kano.
Amfani, A. A. (2011), ‘‘Hausa Da Hausawa: Jiya Da Yau Da Gobe.’’ Laccar da aka
gabatar a taron One Day Symposium on Hausa Language and Hausa People:
Yesterday, Today and Tomorrow. Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria.
Ayandele, E. A. (1979), Nigerian Historical Studies. Frank Cass & co. Ltd.,
London.
Bargery, G. P. (1933), A Hausa-English and English-Hausa ɓocabulary. Oɗford Uniɓersiry
Press, London.
Bargon Hikima Diwanin Waƙoƙin ɗangaladiman Wazirin Sakkwato Alƙali (Dr.)
Muhammadu Bello Giɗaɗawa (2006), Jami’ar Usmanu ɗanfodiyo, Sakkwato
Bunza, A. M. (2006), Gadon Feɗe Al’ada. Tiwal Nigeria LTD, Lagos.
Bunza, A. M. (2011), ‘‘ Al’adun Hausawa Jiya Da Yau: Ci Gaba Ko Lalacewa’’ A
cikin KADA Journal Of Liberal Arts ɓol. 5, No. 1 Faculty Of Arts, Kaduna State
University.
Bunza, A. M. (2012), ‘‘Ba A San Maci Tuwo Ba Sai Miya Ta ƙare’’ Takardar da aka
gabatar a taron ƙasa na huɗu (4) na ƙungiyar GIZAGO a Tsangayar Ilmukan Alƙur’ani
ta Marigayi Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo Abubakar III, ranar Lahadi, 30-12-
2012
Bunza. A. M. (2012), ‘‘Hausa A Faifan Nazari: Ana Barin Na Zaune Domin Na
Tsaye.’’ Takardar da aka gabatar a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar
Umaru Musa ‘Yar’aduwa, Katsina domin maraba da sababbin ɗaliban Sashen Hausa a ƙarƙashin
jagorancin Shugaban Sashe farfesa Sabir Salama ranar Alhamis 1 ga Maris, 2013.
Bunza, M. U. (1999), ‘‘Hausa Factor in Christian Proselytization Of Northern
Nigeria 1841- 1903.’’ A cikin Journal Of Hausa Studies Readings in Hausa
Language, Literature and Culcure ɓol 1, No 1. Sashen Koyar Da Hatsunan
Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Bunza, U. A. (2013), ‘‘Bauta Da Aikin Hajji Da Tasirinsu Ga Ginuwar Wani ɓangare
Na Adabin Hausa.’’ Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa na
farko da Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Bayero, Kano shirya daga ranar
14-16 ga Janairu, 2013.
Burns, A. (1969), History of Nigeria. Unwin Brothers Limited, London.
Crampton, E. P. T. (1976), Christianity In Northern Nigeria. Gaskiya
Corporation, Zaria
Crowder, M. (1962), Story of Nigeria. Faber, London
Dubagari Bello, M. (1984), ‘‘Tasirin Al’adun Hausawa A Kan Fulanin Jama’are.’’
Kundin digiri na farko, Jami’ar Usmanu ɗanfodiyo, Sakkwato.
Hair, P. E. (1994), The Early Study of the Nigerian Languages: Essays and
Bibliograpies. Cambridge University Press, London
ƙamusun Hausa (2006), Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Loɓejoy, P. E. (1983), Transformations in Slavery A History of Slaɓery in
Africa. Cambridge University Press, London
Mani, A. (1966), Zuwan Turawa Nijeriya Ta Arewa. NNPC, Zaria
Malumfashi, I. A. M. da Bunza, U. A. (2013), ‘‘Folklore, Missionaries and the
Colonialists in Northern Nigeria.’’ Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna
sani na ƙasa don karrama farfesa ɗandatti Abdulƙadir, Jami’ar Bayero Kano a
ranakun 2- 5 ga watan Afrilu, 2013.
Miller, W. R. (1936), Reflections of a Pioneer. CMS, London.
Miller, W. R. (1949), Walter Miller: An Autobiography. CMS, London
Miller, W. R. (1949), Haɓe We Failed In Nigeria? London and Redhill: United
Society For Christian Luterature Lutterworth Press.
Muhammad A. B. (1991), ‘‘Tasirin Zuwan Turawa Kan Sarautun Gargajiya Na ƙasar
Hausa: Tsokaci Kan Sarautar Kano.’’ Kundin Digiri na Biyu, Jami’ar Bayaro,
Kano.
Niɓen, C. R. (1955), Labarin Nijeriya. NORLA, Zaria.
Robinson, C. H. (1896), Specimens of Hausa literature. University Press,
Cambridge.
Robinson, C. H. (1897), Hausa or 1500 Miles. London.
Robinson, C. H. (1900), Nigeria Our Latest Protectorate. Negro Uniɓersities
Press, New York.
Schon, J. F. (1885) Magana Hausa Native Literature Provers, Tales, Fables and
Bisto Fragments in the Hausa Language. Society For Promoting Christian
Knowledge. North Umberland Avenue, London
Skinner, N. (1980), An Anthology of Hausa Literature. Zariya NNPC.
Yahaya, M. (1991), ‘‘Matsayin Sarautar Wawan Sarki A Fadar Sarkin Zazzau’’
Kundin digiri na farko, Jami’ar Usmanu ɗanfodiyo, Sakkwato.
Yahaya, Y. I. (1988) : Hausa A Rubuce : Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa.
NNPC, Zaria
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.