Header Ads Widget

Request to place your ads here.

Kanu

6/random/ticker-posts

Tauhidi A Bakin Makadan Baka Na Hausa

Daga


Umar Aliyu Bunza
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
07063532532, 07014529336, 08095750999
aliyubunzaumar@yahoo.com


Yuni, 20141.0 Gabatarwa


Tauhidi shi ne kaďaita Allah Ta’ala da bauta tare da amincewa da dukkanin abin da ya jingina wa kansa na sunaye da siffofi da ayyuka. Tauhidi ne abu na farko da ke tabbatar da kasancewar mutum Musulmi. Kaďaita Allah (tauhidi) shi ne ginshiƘi na farko mai Ƙarfi da addinin Musulunci yake kansa. Don a kaďaita shi (Allah) ne ya aiko Annabawa da manzanni masu yawa daga zamanin Annabi Adamu (AS) zuwa Annabi Muhammadu (S A W). Bayan tauhidi sai sauran ayyukan ibada kamar Sallah da Azumi da Zakkah da Hajji da sauran al’amurran zamantakewa.
Al’ummar Hausawa mutane ne da suka kasance Musulmi, kuma masu riƘo da tauhidi cikin kowane lamari nasu. Wannan ya sa kowane abu ya faru mai kyau ko maras kyau, Bahaushe kan danganta kasancewar abin daga Allah (S W T). MawaƘan baka wani rukuni ne cikin Hausawa da ke da cikakken tasirin Musulunci cikin rayuwarsu. Wannan tasirin ya kasance wani muhimmin abu har cikin waƘoƘinsu. Kasancewar tauhidi ginshiƘi babba cikin rayuwar Musulmi, ya sa mawaƘan bakan suke tsarma tauhidi cikin waƘoƘin. Suna yin haka ne saboda wani lokaci su yi wa al’umma wa’azi da faďakarwa. Wani lokaci kuma suna yi saboda tasirin Musulunci da kuma Ƙarfin imaninsu ga kasancewar Allah mai iko kan komai da kowa, kuma mai aikata abin da ya so, da kuma kasancewar Allah abin dogara da neman biyan buƘata da kuma kariya.
Manufata a wannan maƘala ita ce nazarin tauhidi da ke Ƙunshe cikin wasu ďiyan waƘoƘin mawaƘan baka na Hausa. Duk da yake daga cikin waƘoƘi ne zan duba tauhidi, na kauce wa kawo ma’anar waƘa da tarihinta domin wasu masana da manazarta (Ɗangambo, 1981 da 2007 daYahya, 1997 da Gusau, 1993 da 1996 da Ibrahim, 1983 da Isma’ila, 1998 da Lere, 1987 da Gumel, 1992 da sauransu) sun riga sun yi rubuce-rubuce kan wannan. Don haka wannan maƘalar ta fara da duba tauhidi.

2.1 Ma’anar Tauhidi


Sanin ma’anar tauhidi abu ne mai muhimmmanci ga kowane Musulmi. Idan Musulmi suka san tauhidi, suka kuma kiyaye shi, zai zama mataki na farko na kiyaye tanade-tanaden Ubangijinsu da kuma bauta masa bisa haƘiƘa. Wannan ya sa wasu masana lamurran Musulunci suka dubi matsayin tauhidi a Musulunci da kuma Ƙunshiyarsa suka fito da ma’anoni daban-daban gwargwadon fahimtarsu. Ga kaďan daga cikinsu. A cewar Wazirin Kano (1980: 8):

“Tauhidi shi ne tabbatar da samuwar zati, Ƙadiri, mai siffofin kamala, tsarkakakke daga kowace irin tawaya da kowace irin naƘasa wanda bai yi kama da komi ba, kuma babu wani abu da ya yi kama da shi ta kowace fuska da kowane hali”

A taƘaice, idan aka yi la’akari da wannan ma’ana ana iya cewa tauhidi shi ne tabbatar da samuwar Allah Maďaukakin Sarki mai kowa mai komai tare da bauta masa shi kaďai ba tare da tarayya da komai ba a cikin kowane nau’i na bauta masa ba da kuma sakankancewa ga samun sakamako ga yi masa bauta da kuma azaba ga yi masa tarayya a bauta.

3.1 Rabe-Raben Tauhidi A Musulunci


Tauhidi ya mamaye dukkan rayuwar Musulmi wanda hasali ma shi ne Ƙofar da ake shiga addinin Musulunci daga gare ta. Wasu malaman Musulunci kamar Asimina (1980) ya karkasa tauhidi zuwa gida uku kamar haka:
i) Tauhidur-Rububiyyat (kaďaita Allah da ayyuka) wanda shi ne tauhidin kaďaita Allah da ayyuka misalin halitta, da azirtawa, da rayuwa, da kashewa, da juyar da al’amurra, da kawar da cuta, da makamancin waďannan. Wannan nau’in haƘiƘa kafirai sun yi iƘirarinsa tun bisa lokacin manzon Allah (SAW) amma bai shigar da su cikin Musulunci ba.
ii) Tauhidul-uluhiyyat (kaďaita Allah da bauta) shi ne na kaďaita Allah da bauta misalin, addu’a, da yanka, da alwashi, da neman taimako, da neman tsari da wanin waďannan. Wannan nau’i na tauhidi shi ne wannan da kafirai suka yi musun shi, kuma jayayya ta kasance a cikin shi take tsakanin mazanni da al’ummunsu tun daga Nuhu amincin Allah ya tabbata gare shi har zuwa ga Annabibimmu Muhammadu sallalahu alaihi wasallam.
iii) Tauhidul-Asma’u was-siffat. (kaďaita Allah da sunaye da siffofi) wannan na nufin miƘa wuya (imani) ga dukkan abin da ya tisgo (ya zo) a cikin AlƘur’ani mai girma da hadisai ingantattu na daga sunayen Allah da siffofinsa waďannan da ya siffanta kansa da su, ko manzonsa ya siffanta shi da su a kan haƘiƘan (tabbaci). Waďannan su ne muhimman kashe-kashen tauhidi da malaman Musulunci suka yake kansu.

4.1 Tauhidi A Bakin Makaďan Bakan Hausa


Tauhidi abu ne da ya zama ruwan dare cikin waƘoƘin makaďan Hausa saboda tasirin Musulunci a zukatansu. An yi ƘoƘarin kawo misalan tauhidi ta hanyar bijirowa da ďan waƘa da ake ganin akwai tauhidin a ciki tare da bayanin sa domin haƘa ta cim ma ruwa. Ga misali, Alhaji Musa ƊanƘwairo yakan sanya tauhidi a cikin waƘoƘinsa a wurare da dama. A waƘarsa ta Ado Bayero wadda ake yi wa amshi da ‘Barkak ku da taurin gaba, na yarda da Sarki Ado’ akwai tauhidi kamar haka:
‘Gaskiya na nan ga wurinta,
Mutane mu yarda da Allah,
Wanda duk yay yarda da Allah,
Ka san wannan bai taƂewa’

Al’amarin yarda da Allah, tauhidi ne da ya game duk kashe-kashen tauhidi. Wannan ďan waƘan ya game yarda da samuwar Allah, da kaďaita shi da bauta, da ayyuka da duk wani abin da ya Ƙunshi miƘa wuya ga Allah. Haka kuma, makaďin ya bayyana sakamakon duk wanda ya tsai da Ƙafa ga yarda da Allah a ďango na Ƙarshe na rashin taƂewa koyaushe.
A waƘarsa ta ‘Mai dubun nasara garnaƘaƘi Sardauna’ nan ma ƊanƘwairo ya shigo da tauhidi inda yake cewa:
‘Tun da Allah shi ya hukunci bawa nai,
Shi ka ba shi komai,
Kuma shi ka hana mai,
‘Yan uwa ku riƘa,
Ba Ƙarfi nai na ba,
Ƙarfin Allah ne’

Wannan ďan waƘa ya Ƙunshi tauhidi na kaďaita Allah da ayyuka. Hukunta kowane lamari ya wanzu, ya tabbata abu ne da ya kaďaita ga Allah kawai. A nan mawaƘin ya bayyana Allah a matsayin mai hukunta komai ta hanyar bai wa bawansa komai, ko hana mashi. Haka kuma ya nuna ko da mutum na da wani abu ya san ba Ƙarfinsa ya ba shi ba, sai dai Ƙarfin Allah wanda imani da haka tauhidi ne tsayayye, kuma ingantacce.
Bayan ƊanƘwairto, shi ma Narambaďa sanannen makaďi ne da ke amfani da salon wa’azi da faďakarwa a cikin waƘoƘinsa. Wannan ya sa al’amarin tauhidi ya zama abu mai sauƘin gani da yawanci ake tsinta cikin wasu waƘoƘinsa. Ga misali, a waƘarsa ta Sarkin Ɓurmin Moriki Muhammad, Narambaďa ya sanya al’amarin tauhidi a inda yake cewa:
‘Jahilci rashin sanin Allah,
Abu dai in ya taho,
Ga Allah aka mai sai’

Wannan ďan waƘa babu shakka ya bayyana al’amarin tauhidin kaďaita Allah da bauta ne. Mai da dukkan abin da ya zo ga Allah al’amari ne na kaďaita Allah da bauta ta hanyar imani da Ƙaddara mai kyau, ko maras kyau duka abu ne daga Allah.
A waƘar Gamda’are Sarkin Kudu Ali, nan ma Narambaďa cewa ya yi:
‘Batun Allah mu shi muka biya,
In Allah ya zaƂi abin da kash shukka,
Ka san shina hita.’
A cikin wannan ďan waƘa an samu tauhidin kaďaita Allah da ayyuka ta inda makaďin ya bayyana Allah a matsayin mai zaƂen abu da kuma tabbatar (fitar) da shi. Bayan wannan ma akwai kuma tauhidin nan na kaďaita Allah da siffofinsa. Hakan zai inganta ganin yadda makaďin ya bayyanar da bin maganar Allah wanda magana na cikin siffofin Allah Maďaukaki.
Shi ma Aliyu Ɗandawo fitaccen makaďin fada ne da ke ƘoƘarin fito da tasirin addininsa na Musulunci a cikin waƘoƘinsa da dama. Saboda haka, ba zai zama abin mamaki ba a ga lamarin tauhidi ya fito a cikin waƘoƘinsa. A waƘarsa ta Tukur Sarkin Yauri Aliyu Ɗandawo ya kawo lamarin tauhidi yana cewa:

‘Tukur ka yi don Allah,
Shi ka bari don Allah,
Halinka ba ďai da halin na yau ba tun can hwarko,
Abin da duy yas same shi bai cewa wani yay yi mai,
Ga Allah shi ka dogara,
Shi ko tuban mai,
Abin da duy yas samu shi tabbata,
Allah yan nuhwai shi tun farko.’
Ilimin tauhidi ne ya mamaye wannan ďan waƘa kuma ya Ƙunshi tauhidi na kaďaita Allah da bauta ne. Tun farko, ana iya fahimtar tauhidin ta inda mawaƘin ya bayyana duk abin da ya samu ba maganar wani ya yi sai dai ya mai da lamarin ga Allah. Ya kuma nuna cewa, Allah ne ya nufa tun farko hakan ya kasance. Haka lamarin tauhidin kaďaita Allah da bauta yake. Bawa ya san Allah yake hukunta masa komai, ba wani halitta daban ba.
A wani ďa na wannan waƘar ga yadda Aliyu Ɗandawo ya sake fito da tauhidi a inda yake cewa:
“Ka ga komi tsananin hwari,
kana ishe tohwahiya da kunnuwa na ďanya,
Cikin sarautar Allah ta rayu ba da ruwa ba,
Allah bai yi sarautad da za a koyo nai ba.”

Rayawa da kashewa abu ne da ke hannun Allah Maďaukakin Sarki. Allah yakan raya abin da ya ga dama koda kuwa a muhallin da ba a al’adanci rayuwar abin ba. Yakan kuma kashe abin da ya ga dama duk da irin tanade-tanaden da aka yi masa na ďorewar rayuwarsa. Yarda da haka ga mutum, tauhidi ne na kaďaita Allah da ayyukansa. Ke nan wannan ďan waƘa ya taro sha’anin tauhidin kaďaita Allah ne da ayyuka. Hakan ya tabbata ne bisa ga la’akari da yadda ya Ƙunshi al’amarin ikon Allah na raya wani tsiro ba tare da ruwa ba wanda ko shakka babu yana daga cikin ayyukan da Allah ya kaďaita a kansu. Idan fari ya tsananta, kowane tsiro na mutuwa, amma ita tunfafiya koyaushe tana ďanyar ta kamar babu fari. Wannan Ƙarfin iko na Allah ne kawai kamar dai yadda ya halicci Annabi Adamu (AS) ba uwa ba uba, ya kuma halicci Annabi Isah (AS) da uwa kawai ba uba.
Mamman Shata shi kuma makaďin jama’a ne da ya yi fice sosai a waƘar Hausa. Mamman Shata yakan sanya tauhidi a cikin waƘoƘinsa a wajen ƘoƘarin warware jigon waƘarsa. Ga misali, a waƘarsa ta Ado Bayero wadda ake yi wa amshi da ‘Ado na Kano Ɗan Abdu’ Yana cewa:
‘Ka ji birnin Kano har daji,
Allahu wanda ya yi ta,
Ado na Kano yab baiwa.’

A wanna wuri, ana iya fito da tauhidin nan na kaďaita Allah da ayyuka inda mawaƘin ya yi bayanin cewa, Allah ne Mahaliccin da ya halitta Kano, kuma shi ne mamallakin mulki mai ba da mulki da ya ba da sarautar Kanon ga Ado Bayero.
Wani makaďin jama’a da ake samun tauhidi cikin waƘoƘinsa shi ne Sani Ɗan-Indo. A waƘarsa ta ‘Mai mai da tasha sabuwa’ Ɗan-Indo cewa ya yi:
‘Sani nay yi tunani na sani,
Mai tunani na sani,
Shin wa ka baje ma wuri,
Allah ďai ka baje ma wuri.’

Tauhidin da yake Ƙunshe cikin wannan ďan waƘa shi ne tauhidin kaďaita Allah da ayyuka. Tauhidin zai tabbata ta kallon yadda makaďin ya bayyana Allah ne kaďai ke iya wa mutum wuri, ya ba shi dama ya yi abin da yake so. Yarda da wannan tauhidi ne tsayayye a addinin Musulunci. A wata waƘar tashi ta Garba Abu kuwa cewa ya yi:
‘Na ji abin mamaki a’a Garba Abu,
Ka ji abin tarihi a’a Garba Abu,
Wasu ‘ya ‘ya sun ce da Aljani nika aikin ga,
Wasu ‘ya ‘ya sun ce da malamai nika aikin ga,
Wasu ‘ya ‘ya sun ce da ilimi nika aikina,
Wasu ‘ya’ya sun ce da boka nika aikina,
Su san da komi Allah ya ce,
A yi shi don ya zan ba illa.’

Babu shakka, za a iya hango tauhidin nan na kaďaita Allah da ayyukansa a cikin wannan ďan waƘa. Al’amarin tauhidin zai iya tabbata ganin yadda mawaƘin ya miƘa lamarin fasaharsa ta w aƘa ga hukuncin Allah. Yarda da cewa, duk abin da Allah ya ce shi ke tabbata da kore kowane abu kan haka, tauhidi ne tabbatacce a Musulunci.
Bello Ɗan Sha-biyu na cikin makaďin Hausa da ke sanya lamarin tauhidi a waƘoƘinsa. Ga misali, a waƘarsa ta motar siyasa cewa ya yi:

‘To Allah shi ka canza mutum,
A in bai canza mutum ba,
Na san kowa ba ya canza shi.’

Lamarin canza mutum abu ne wanda ya taƘaita ga ikon Allah kawai. Yarda da haka abu ne da ke kyautata imanin Musulmi da kuma inganta tauhidinsa. Ke nan wannan ďan waƘa yana ďauke ne da tauhidin kaďaita Allah da ayyuka, inda makaďin ya tabbatar da Allah ne kaďai mai canza mutum. Allah ya kaďaita ga wannan domin shi ne muƘallabil Ƙulub kuma mudabbirul amri. Haka kuma duk wanda Allah bai canza ba, haƘiƘa ba wani wanda zai iya canza shi.
Shi kuma Ɗan’anace sanannen makaďin maza ne da ya yi fice sosai a Ƙasar Hausa musamman a waƘoƘinsa na dambe. Ɗan’anace mawaƘi ne da ke shigowa da tauhidi a cikin waƘoƘinsa musamman saboda tauhidi shi ne ginshiƘin addininsa na Musulunci. Ga misalan tauhidi a cikin wasu waƘoƘinsa.
‘Bismillahi Alhamdu,
Mun gode ma Allah
Kyawon ďan Musulmi
Ya san Allah guda na.’

Sanin Allah ďaya ne da sakakancewa kan haka shi ne Ƙololuwar tauhidi. Wannan ďan waƘa Ɗan’anace ya kawo tauhidin kaďaita Allah da sunayensa da siffofinsa ta inda ya bayyana ingantacciyar siffar nan ta Allah Guda (Ahad) wanda ba ya da abokin tarayya ta kowane gefe. Ɗan’anace har kuma ya bayyana cewa, yin imani da kasancewar Allah shi kaďai shi ne daidai ga ďan Musulmi. A wani ďan kuma Ɗan’anace na cewa:
‘To Allah shi ad da mutane,
Allah shi ad da iyawa,
Kuma Allah shi yay yi sarki,
Yay yi talakka,
Yay yi makafi, yay yi guragu,
Yay yi talakawa, yay yi matsaci.’

Babu shakka, wannan ďan waƘa ya ginu ne a kan tauhidin kaďaita Allah da ayyukansa ta la’akari da yadda makaďin ya bayyana Allah a matsayin Mahalicci, kuma mai cikakken ikon halitta abubuwan halitta daban-daban. Da ikonsa ya halitta mutane aji daban daban kamar sarakai da makafi da guragu da talakwa da sauransu.
Shi ma makaďa Muhammadu Gambo makaďin maza ne da ya yi fice musamman a waƘar Ƃarayi. Ko da ya ke makaďin Ƃarayi ne, akan sami tauhidi a cikin waƘoƘinsa wanda zai tabbatar muna da cewa, komai munin waƘa in dai daga bakin Musulmin Bahaushe ta fito, to ba za a rasa tsarmin lamarin tauhidi ba a cikin ta. Tasirin Musulunci a rayuwar Gambo ya sa wani lokaci yakan yi amfani da salon wa’azi da faďakarwa a waƘoƘinsa. Ga misali, a waƘarsa ta Inuwa Ɗan Maďaci, Gambo cewa ya yi:
‘Wanga ba wada Allah bai iya ba,
Ko mis same ka a filin duniyag ga,
Kak ka kuka da kowa wanga dangana,
HaliƘu Allah ke matsama.’

A nan Gambo ya fito ne da tauhidin kaďaita Allah da ayyuka ta inda ya bayyana Allah a matsayin mai ikon aikata komai. Haka kuma ya bayyana cewa,ba wani a faďin duniya da zai iya sa wani abu ya sami mutum face Allah kawai. Saboda haka, duk wani abin da ya sami mutum, ya dangana ya bar wa Allah kawai. Samuwar irin wannan tunani a zucci na tabbatar da kaďaita Allah da yarda da Ƙaddarorinsa. A wani baitin da ke cikin waƘar Jibirin Mugun Tsoho a gunduwoyin Ƙarshe da ke ďauke da mai da jawabin wata mata ga Ƃarawon da ke yi mata barazanar kashi, Gambo ya kawo tauhidi inda yake cewa,
……………………………….
‘In ya yi tunani sai ya dangana,
Don ba wani kuka za shi yi ba,
Ya ce haka Allah yah hukunta,
Kowa ajali nai na tahowa.’

A nan ma Gambo ya sake bayyana tauhidin kaďaita Allah da ayyukansa ne ta hanyar bayyana dangana da abin da Allah ya hukunta. MiƘa wuya da ga abin da Allah ya Ƙaddara ga bawa, tauhidi ne da ke kan kaďaita Allah da ayyukansa.
Shi kuma Amali Sububu makaďin sana’a ne da ya yi fice a waƘoƘin noma kuma wanda a cikin waƘoƘin yake sakaďa lamarin tauhidi. Ba wani abin mamaki ba ne ganin Amali Sububu na sanya tauhidi a waƘoƘinsa saboda akwai tasirin Musulunci tare da shi. Ga abin da ya ce a waƘarsa ta Isah Mai Kware mai amshi kamar haka:
‘Allah Ubangijinmu hiyayye mai sama,
Jabbaru Mai dare Mai rana HaliƘu,
Na gode mashi,
Da yai man lafiya,
Da hura ta yah haďa,
Sutura ta mai sama,
Kuďďina HaliƘu,
Mui ta zaman duniya,
Kahin lahira ta ce musu,
Ta amshe musu,
Jatau duniya,
Ba komi ba ce.’

Idan aka yi la’akari da abin da ke cikin wannan ďan waƘa, za a iya ciro nau’in tauhidi biyu a cikinsa. Na farko shi ne tauhidin nan na kaďaita Allah da sunayensa da siffofinsa inda makaďin ya jera siffofin Allah a ďangaye uku na farko. Daga nan kuma sai makaďin ya juya akalarsa zuwa ga fito da tauhidin nan na kaďaita Allah da ayyukansa inda makaďin ya bayyana Allah a matsayin mai baiwa ga kowane abu kamar ba da lafiya da abinci da arziki da sutura da sauransu. Ya kuma tabbatar wa Allah siffarsa mai halitta (haliƘi).
Haruna Uji shi kuma fitaccen makaďi ne a fagen sha’awa. Kasancewar sa Musulmi ya sa ake samun tauhidi a waƘoƘinsa. Ga misalin tauhidin a waƘarsa ta BaƘar Rama inda ya ce:
‘Komi da ka duba,
Sha’anin Allah ne,
Arziki da karatu,
Wannan nufin Allah ne,
Da dukiya da haƘuri.’

Idan aka yi nazarin abin da yake Ƙunshe a wannan ďan waƘa za a ga cewa Haruna Uji ya yi kawo tauhidin kaďaita Allah da ayyuka ne ta inda ya bayyana duk abin da mutum ya duba ya gani, ya san sha’anin Allah ne. Yarda da kasancewar komai cikin yarda da Ƙudurar Allah abu ne da ke tabbata tauhidin Musulmi. Allah cikin Ƙudurarsa ya halitta komai. Ba wani abu zai kasance idan ba da Ƙudurar Allah ba. Wannan kuwa ya haďa da dukiya, da karatu, da arziki da haƘuri da ma sauran abubuwan da bai kawo ba.
Da yake a nan ne aka cimma Ƙarshen misalan tauhidia cikin wasu waƘoƘin makaďan Hausa, ana iya cewa, misalan tauhidi da aka samu a rukunan waďannan makaďan sun yi ƘoƘarin fito da nau’o’in tauhidi wanda idan aka yi nazari za a ga ba tauhidi ne manufar, ko saƘon waƘoƘin ba, sai dai don kasancewar sa tauhidi abu ne wanda tun farko muka nuna yana tafiya da rayuwa gaba ďaya ya sa suka shigo das hi cikin waƘoƘin nasu. Wato abu ne mai wuya Musulmin mawaƘi Bahaushe ya buďe baki ya yi waƘa har ya Ƙare bai ambaci wani nau’i na tauhidi ba.

 

karanta wannan

https://www.amsoshi.com/2017/07/29/tarbiya-cikin-adabin-hausa-tsokaci-daga-karin-magana/

5.1 Kammalawa


Idan aka yi la’akari da misalai da bayanai da maƘala ta zo da su, za a ga cewa, lamarin tauhidi abu ne babba, kuma mai tasirin gaske cikin rayuwar Hausawa. Wannan ya kasance ne ganin cewa, ko da yake ana kallon waƘoƘin bakan Hausa matsayin sharholiya, kuma na raha, amma kuma sai ga shi ana tsintar batutuwan tauhidi masu yawa cikin waƘoƘin. Haka na Ƙara tabbatar da cewa, lamarin tauhidi ta kowace fuska aka dube shi, abu ne da ya yi kaka-gida cikin rayuwar mawaƘan bakan Hausa. Irin wannan kaka-gidan ta sa ko da ba don Musulunci kai tsaye suke shirya waƘoƘinsu ba, amma kuma tauhidi na shiga da fice da kuma giittawa cikin wasu ďiyan waƘoƘin nasu.

Manazarta


Altine, H. (1983), Aliyu Ɗandawo Da WaƘoƘinsa. Kundin Digiri na Farko, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato

Asimina, S. M. S (1989), Attauhidu WalfƘhu Wat-tajwid lil- Faslir Rabi’u Al- Ibtida’iyyat. Mahfulzatil-Wizaratil Ma’arif. Saudi Arabiya.

Bunza, U. A. (2001), TaƂa Kiďi TaƂa Karatu: Tauhidi A Bakin Makaďan Bakan Hausa. Kundin digiri na farko, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Bunza, U. A. (2013) Wa’azi A Bakin Gambo Dogo Mai Kalangu. Cikin Mujallar Makaďi A Mahangar Manazarta. Jerin takardun da aka gabatar a taron Ƙara wa juna sani kan tubar Muhammadu Gambo Mai Kalangu, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto. ISBN. No: 978-8082-02-5

Gumel, M. A. (1992), Tarbiyya Da Dangoginta A WaƘoƘin Makaďan baka Na Hausa. Kundin digiri na farko, Jami’ar Bayero, Kano..

Gusau, S. M. (1993), Jagoran Nazarin WaƘar Baka. Fisbas Media Services, Kaduna.

Gusau, S. M. (1996), Makaďa Da MawaƘa Na Hausa. Fisbas Media Services, Kaduna.

Gusau, S. M. (2014), WaƘar Baka Bahaushiya (The Hausa Oral Song). BUK Inaugural Lecture Series No 14. Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kono.

Ibrahim, M. S. (1983), Kowa Ya Sha Kiďa 1. Longman Nigeria Limited, Kaduna

Isma’ila, S. S. (1998), Shahararrun WaƘoƘin Makaďa Ibrahim Narambaďa Tubali (1875-1960). Kundin digiri na farko, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Lere, N. D. (1987), Wasu Jigogin WaƘar Baka. Kundin digiri na farko, Jami’ar Bayero, Kano.

Mahe, A. (1984), Ɗan’anace Da WaƘoƘinsa. Kundin digiri na farko, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Muhammad. A. W. (2000), Littafin Tauhidi. Ma’aikatar Kula da Harkokin Addinin Musulunci da WaƘafai da Wa’azi daShiryarwa daga Aljihun Cibiyar Ibrahim ibn Abdul Aziz al-Ibrahim ta Taimakon Al’umma, Saudi Arabiya.

Tsoho, M. Y. (2013), Tsabar Rashin Tausayi Da ƁurƂushin Tauhidi A WaƘoƘin Ɓarayi Na Gambo Mijin Kulu. Cikin Mujallar Makaďi A Mahangar Manazarta. Jerin takardun da aka gabatar a taron Ƙara wa juna sani kan tubar Muhammadu Gambo Mai Kalangu, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto. ISBN. No: 978-8082-02-5

Wazirin Kano. A. A. (1980), Tauhidi Mai Dalilai. NNPC, Zariya.

Yahya, A. B. (1997), Jigon Nazariin WaƘa. Fisbas Media Services, Kaduna.

Post a Comment

1 Comments

Rubuta tsokaci.