Adabin Baka A Cikin Littafin Zamanin Nan Namu

    Na
    Ahmad Garba

    3.2 SHARHIN JIGON WASA TA BIYU (‘YAR MASU GIDA)


    ‘Yar Masu Gida ita ce wasa ta biyu da ke cikin wannan littafi. Wasar ta fara daga shafi na (29) zuwa na (58). Wasar ‘Yar Masu Gida an tsara ta ne domin nuna illar talla ga ďiya mace. ‘Yar Masu Gida ďiya ce ga Malam Abdu. Shi kuma Malam Abdu wani dattijo ne da ya kasa ďaukar ďawainiyar ďiyarsa. Ya bar lalurin ‘Yar sa Gida ga mahaifiyarta wato Tagudu wadda take ďora mata tallar Ƙosai. Wata rana Malam Abdu ya so ya hana ta fita talla sai matarsa ta yi cikinsa da cewa:
    Tagudu:
    “Talla kam ta zama wajibi domin kuwa da tallar nan zan yi maki kayan ďaki da kuma kayan gara da kuma sauran kayan aurenki.”

    Tun daga wannar maganar Malam Abdu ya fita sha’anin ‘Yar Masu Gida ta ci gaba da tallace-tallacenta.
    Sarkin Samari:
    “Ga dai ‘yar masu gida can wata kwalluwar yarinya ce an fito talla cikin yara suna gaďa.”

    A nan ana so ne a nuna cewa ga ‘Yar Masu Gida can ta fito zuwa talla, inda za ta haďu da sauran yara da sauran da samarin gari. Wannan kuwa da tilastawar iyayenta – musamman uwa ita Tagudu, da ta yi tsayin daka wai sai ďiyarta ta yi talla wai don idan ta tashi aurar da ita ta samu abin yi mata gara. ‘Yar Masu Gida yarinya ce mai hankali mai natsuwa kuma kullum tana cikin gida ba ta fita ko’ina sai in fita ta zama tilas to wannan kam sai ta fita.
    Amma:
    “Yar Masu Gida manya ga ta can ta kama hanya da kayan tallanta niƘi-niƘi ta nufi cikin gari ga kuma sarkin samarin garin can, kusan yana murmushi kiranta zai sa a yi” (shafi, 30).

    Tun daga nan an fara samun matsala da wata irin gagarumar illa, wadda ko ga ta da ďaukar kayan talla niƘi-niƘi, har da shigowa cikin gari, ko da ma Hausawa na cewa: “Sare-saren hauka zubar da yawa.” ‘Yar Masu Gida dai ta fara kama hanyar lalacewa:
    Sarkin Samari:
    “‘Yar Masu Gida, yau kuma shige mu kai tsaye za a yi da kayan Ƙosan, abin har ta kai mu da a sha ruwan tsuntsaye ne! Laifin ne muka yi ko kuma kuďin Ƙosan ne yau kika ga ba mu da su? Haka fa kika zo nan kika shige mu kai tsaye, wajen ‘yan teloli, ko waigowa nan ba ki yi ba.”

    ‘Yar Masu Gida dai ta shiga kasuwa kuma ta fara haďuwa da Sarkin Samari har dai ya kasa haƘuri yau kam sai da ya yi mata magana. Ya gwada Ita kuma ta amsa masa da cewa Ai na ga rainin wayonku ne na ga ya yi yawa saboda idan mutum ya kawo maku talla, maimakon ku saye sai ku tsaya kuna damun sa da wasu surutai marasa kan gado. Shi kuma wani mai suna Tanko anƘi ya `yarmasu gida.
    Tanko:
    “Mhm ‘Yar Masu GidaSarki! Mun ji a ajiye mana na kobo biyar kan shimfiďarmu gobe kuma in kin kewayo kya same ni nan da kuďinki.”

    ‘Yar Masu Gida:
    “To ba ga ta ba kun fara aikin naku! Ga shi nan kuma in na zo, a ce sai gobe da ma samarin garin nan taurin bashi ke gare ku.”

    Bala:
    “‘Yar Masu Gida kin ajiye mini nawa Ƙosan na kobo huďu a rumfarmu, kusa da kokon nan da na saya ina jiran ki, kin safa sharatun ne.”

    Wannan ya nuna yadda ta ke ta shan da mutanen kasuwa da na cikin gari wato samarin gari a lokacin da take tallar Ƙosai, duka dai samarin sun kwashe Ƙosai ba shi.
    ‘Yar Masu Gida:
    “‘Yar Masu Gida ke ta zagayewa cikin kasuwa, rumfa-rumfa, tana tallan Ƙosai wannan ya ja, wancan ya ja. Wani cinikin kuďi hannu, wani bashi, amma na bashin ya fi yawa. Wani ma ba za a biya ba har abada. In ta hana, a ce mata budurwar Ƙauye.”

    A nan an ga yadda samari da sauran mutanen kasuwa suke ta wasa da hankalin `Yar Masu gida har ta kai suna mata wani dubi na budurwar Ƙauye saboda tana magana a kan suna ďaukar Ƙosanta bashi. Wannan ya haďa ta da uwarta, domin in kuďin nan sun Ƃata. Tunaninta ya kai ya dawo, ta rasa abin da zai mata daďi. Su kuma Ƙawayenta ga su can sun gama sayar da abin sayarwarsu, suna gindin itaciya inda suke taruwa suna hira har da samarin garin. `yar Masu gida to zo ta zauna ta ce:
    “Wash! Ni ‘Yar Masu Gida. Ita da ta zuba mini Ƙosan kobo hamsin cur ga samarin garin nan duk sun ďauke bashi, ko kobo talatin Ƙwarara ban Ƙulla ba. Ga kuwa Ƙanwata, wadda muke ‘yan uba, yau samarinta juye suka yi mata Ƙosan da ta ďauka na kobo talatin ne kawai, amma saurayin nan da ya yi mata juye kobo sittin cur ya watsa mata. Ƙosan kuwa ya yi sadaka da shi. Duk ranar nan da muka sha, suna can suna ta taďinsu da ita. Wannan saurayi nata da zuciya yake” (shafi, 32).

    Idan ‘Yar Masu Gida ta shiga tunanin yadda za ta haďu da mahaifiyarta da kuma yadda za su kwashe saboda ta aza mata kayan kwabo hamsin amma duk ta bari samari sun kwashe Ƙosai sun bar ta da kwabo talatin. Ita ko ‘yar uwarta ga ta can saurayinta ya saye kayan Ƙosan duka. Kayan na kwabo talatin ne, amma ya ba ta kwabo sittin. Idan aka yi la’akari da wannan za a iya cewa, ita wannan Ƙanwar ta sanadiyyar talla ta lalace har ta saba da samari kuma sun saba ba ta kuďi. Ita ko ‘Yar Masu Gida ba ta da wanda zai ba ta bare ta je ya yi mata juye, amma sanadiyar abokantaka da wata mai suna Rakiya, wannan yarinyar har ta fara amsar shawarar da take ba ta.
    Rakiya:
    “Allah ya sa ga ki! ‘Yar Masu Gida ashe ba ki da wayo? Ke ba ki da saurayi ne? to ba ki tambayarsa ki ce masa ya cika miki, kuďin Ƙosanki ya Ƃace? In ce ko ke ba ki san yadda ake yi ba ne? Ƙe mu ko wani abin kwaďayi muke son saye Ƙarya muke yi wa saurayi mu ce masa kuďinmu sun bace ya cika mana sakarai marar wayo.”

    Ita Rakiya budurwa ce da ta saba da samari. Da ta fi damuwar ‘Yar Masu Gida sai ta ba ta wannan shawara. To sai dai! ‘Yar Masu Gida ba ta ďauki wannan shawarar Rakiya ba. Ta dawo gida, sai mahaifiyarta ta karƂi tiren Ƙosan. Ta lissafa ta ga ba su cika ba, sai ta ce mata:
    Tagudu:
    ‘Yar Masu Gida kobo talatin na gani ina sauran kobo ashirin ďin?”

    ‘Yar Masu Gida:
    “Inna ai na ba samari bashi ne waďansu kuďin kuma sun Ƃata ne, ‘yan Ƙosai ya yi yawa ne ai kasuwar kuma waďansu sai da na yi uku kobo na samu san nan na samu na sayar da shi.”

    Tagudu:
    “Laa, yau Allah ya nuna mini lalatacciyar yarinya maras hankali maras zuciya. In sayi wakena na kobo talatin cikin tsadan nan, in hana idona barci cikin dare ina haƘilo, ga kuďin mai, ga na itace in zuba miki Ƙosan kobo hamsin, na wajen kobo tara sa’annan ki kawo mini wata tsiya wai kobo talatin ba kunya ba tsoro, har da iya faďa mini wai kin bayar bashi ne, wani kuma kin sayar, uku kwabo! Kuďin waken fitar, sauran wahalata su mai da itace da hana idanuna barci duk sun tafi a faďuwa! In ce ko ke kasuwar taki daban ce? Ga ‘Yar Mai-ďaki-da-shiraya Ƙaramar yarinya ce na kobo 25 uwarta ta sanya mata, amma kobo hamsin ta zo gidan nan da su. Kai Allah wadan naka ya lalace. Watau ke ce mujiya, sarkin baƘin jini, wadda ba ta da samari ko? Duk garin nan babu sauran budurwa a fage kamarki kyanki da girmanki duka sun zama na banza tun da ba ki da samarin kirki. Ko ‘yar lalatatta kike, kin sami uwar banza, da za ta yi miki haƘilo ke da mutanen banzan da kika ba bashi. Lalle ba ki san tsiyata ba tukuna! Ko abincin gidan nan ba ki ci fita tun da girma da arziki, duk inda kuďina suk shiga, ki samo mini abina. Lalatatta, raƂa-dannin ‘yan mata. Ƃace mini da gani daga nan! In kuwa kika gidan nan ba tare da kuďin nan ba, sai na yanke ki da wuƘar Ƙarfe. Haihuwar takaici haihuwar rage jini!” (shafi, 34).

    Wannan shi ne ya haifar da sanadiyyar lalacewar ‘Yar Masu Gida ta lalace har ta kai ba ta kwana gida, kuma ta ci kuďin, wancan, ta ci na wannan. Daga Ƙarshe har sai da uwarta duk abin da ta ta sai da shi saboda ta biya mutane bashin abin da ‘Yar Masu Gida ta ci ga hannun jama’a. Daga nan ta haďa da sarkin samari.
    Sarkin Samari:
    “Wata sabon gani! Wace ce haka kamar ‘Yar Masu Gida a garin nan? Allah ya nuna mana Annabi. Ke ce yau a dandali? Lalle wannan sarauta tawa ta yi kwarjinin gaske, har manyan ‘yam mata kamar su ‘Yar Masu Gida suna cikin naďina. Ai sai mu koma gindin itaciyar can ga kujerata ga taki, ki yi kallo. Amma yanzu tun da kika zo na tuƂe ta na naďa ki.

    ‘Yar Masu Gida fa ta yi niyyar ta Ƙi dukan abin da Sarkin Samarin ya tambaye ta, amma ta tuna da abin da Ƙawayenta suka gaya mata da kuma irin abin da uwarta ta nuna mata, ta gani lalle ne ta karƂi gaďar Sarkin Samari idan tana son zuciyarta ta kwanta wajen uwarta. Ta Gudu. Uwar ta yi mata korar tsiya domin kuďinta ga shi kuma ta gamu da Sarkin Samari mutumin da ta san shi sabo da mugun toshinsa.

    3.3 NADEWA


    A nan ne wannan babi ya zo Ƙarshe, babin ya Ƙunshi taƘaitaccen sharhi wasannin littafin Zamanin Nan Namu. Babin ya fara da kawo taƘaitaccen tarihin marubucin wato Shu’aibu MaƘarfi. Daga nan ne aka yi sharhin wasar farko ta Malam Maidala’ilu da kuma wasa ta biyu ta ‘Yar Masu Gida. Idan aka yi nazarin wannan wasar, sai a fahimci cewa, haƘiƘa malam Shu’aibu MaƘarfi yana ƘoƘarin nuna illar talla ne ga ďiya mace. Ya nuna dalilin talla ne ‘Yar Masu Gida ta fara buďe ido da maza har kwana ďakin samari.
    Wani abu da wasar ta kawo shi ne mai gida koyaushe ya ďauki lalurar gidansa. Bai dace barin mace da lalurar gida ba domin haka ke sa mata su yi amfani da azawa ďiyansu mata talla domin samun abin ďaukar lalurorinsu. Irin wannan sakaci na wasu maza ne ya sa mahaifiyar ‘Yar Masu Gida ta aza wa ‘Yar Masu Gida talla domin lalurorin ďiyar kan wuyanta suke.
    www.amsoshi.com

    1 comment:

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.