Ticker

6/recent/ticker-posts

Surkulle a Maganin Gargajiya Ta Fuskar Ayyukan Bokaye

Citation: Balarabe Zulyadaini & Baba Mohammed Shehu (2017). Surkulle A Maganin Gargajiya Ta Fuskar Ayyukan Bokaye. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 5. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660

SURKULLE A MAGANIN GARGAJIYA TA FUSKAR AYYUKAN BOKAYE

Na

Balarabe Zulyadaini

Da

Baba Mohammed Shehu

TSAKURE

Wannan bincike mai taken: Nazarin Gamayyar Surkulle da Magungunan Gargajiya ta fuskar Ayyukan Bokaye, ya yi magana ne kan gamayyar surkulle cikin maganin gargajiya. Tattare da haka, an yi bitar ayyukan masana da manazarta da suka haɗa da: Bunza (2006), Almajir (2009) Ruƙayya (2006) da sauransu. Sannan an yi amfani da hanyar hirar baki da baki da bokaye don jin ta bakinsu ko ra’ayoyinsu domin samo bayanai waɗanda yawansu ya kai gomasha takwas (18) maza da mata da aka yi hira da su. Wannan bincike ya fito da yadda bokaye ke gudanar da ayyukansu ne na haɗa surkulle da magani a yankin Guddiri. Wato an gano yadda bokayen ke warkar da cututtuka daban-daban ta hanyar tsarma surkulle cikin magunguna da suka haɗa da ciwon jiki da ƙunar wuta da gyambo da targaɗe da sossokiya da sauransu.

ABSTRACT

This research entitled: The incantation forces in Traditional Medicine given by Hausa 1uack doctors. The works of scholars were however reviewed. These include: Bunza (2006), Almajir (2009), Ruƙayya (2006) and the like. The method of data collection used was face to face interview conducted with 18 informants both male and female. The data presented and analyzed which discusses the findings where the incantations recorded; this believed to be mixed with traditional medicine by Hausa Native sorcerers (quack doctors) in Guddiri area to cure: Body pain, wound, fracture, cancer and so on.

GABATARWA

Surkulle da magani suna daga cikin al´adun Hausawa waɗanda ake amfani da su, a saboda haka ne ma wasu manazarta suka yi wa waɗannan al´adu (musamman surkulle) kallo ta fuskoki da dama wato akwai masu aiwatar da ko sarrafa su da ma waɗanda suka mayar da su sana´a (Bunza 2006). Wannan aiki za a yi ƙoƙori ne a yi magana kan surkulle cikin maganin gargajiya ta fuskar ayyukan bokaye.

Bokaye suna ɗaya daga cikin nau´in masu yin surkulle da kuma bayar da magunguna a ƙasar Hausa. Kusan ma a iya cewa su ne likitocin ƙasar Hausa kafin zuwan baƙin al´ummomi ƙasar Hausa (Rukayya, 2006: 23).

A wannan bincike, an yi amfani da hanyar gudanar da bincike ta yin hirarraki da bokaye da kuma masana magungunan gargajiya domin jin ra´ayoyinsu wajen fito da wannan aiki.

Haka kuma don samun sahihan bayanai, na yi hira da mutane masu rukunin shekaru ashirin zuwa ɗari waɗanda yawansu ya kai goma sha takwas (18) dukkansu a yankin Guddiri.

MA´ANAR BOKAYE

Bokaye dai wasu mutane ne da suka rungumi sana´ar bayar da magungunan gargajiya ga mutane, domin warkar da wasu cututtuka ko kuma biyan bukatun mutane kuma mutane suna zuwa wajensu don samun biyan bukatu. Haka kuma bokanci al´ada ne ko sana´a ce wadda Hausawa ke yi suna bayyana abubuwan gaibu, wato faɗin yadda wani abu ya kasance kafin ya faru ko kuma ba da maganin ciwo da sunan iskoki ko makarai (Alhassan, 1982).

YADDA AKE GANE BOKAYE

Bisa tsari irin na al´ada, bokaye akan iya gane su ta waɗansu siffofi.Waɗannan siffofi a hannu guda, da su ake iya bambance bokayen da sauran mutane masu sana´o´i takwarorinsu.

Saka hular saƙi baƙa ko fara.

Sanya riga ´yar shara bunjuma da wando tsala.

Izga da suke sakawa a hula (a jikin hular) sukan yi mata ado da wuri.

Rataya layu iri-iri (manya da ƙanana)

Suna riƙe ko rataya zabirar magani akwai butar duma da sukan rataya a jikin zabirar.

Riƙe butar duma ta musamman (don iskoki ko yin siddabaru)

Suna sanya warki, wanda aka yi wa ado da wuri an saka masa ƙararrawa.

Sanya riga fara da baƙa a haɗe wuri guda a ranar Juma´a.

Shafa turare a kowane lokaci.

Amfani da goro farare da jajaye da kwalbar turaren wuta da ƙaramin gatari mai tsini a kafaɗunsu da barandami da kuma ƙaramar wuƙa.

Sanya guru. Shi gurun akwai mai maɗauri wanda sukan ɗaura a mara ko sakawa a ɗaki.

YADDA BOKAYE KE GANE CUTUTTUKA

Bokaye suna da hanyoyi da suke bi su gane cututtuka da ke damun mutane.Waɗannan hanyoyi sun danganta ne da yanayin ciwo, sannan hanyoyin gane ciwo na bambanta daga boka zuwa boka.Wato kowane boka da irin tasa dabarar da yake bi ya gane ciwo (Adamu, 1998).

Bokaye na gane wasu cututtuka ga jikin marar lafiya ta hanyar bayanin da majiyaci ya yi ko waɗanda ke tare da marar lafiyan (kamar iyayen yara jarirai ko miji, ko mata,) ke bayyanawa ga bokaye.Ta irin wannan hanya boka na iya gane irin cutar da take damun mutane.Ire-iren cuttutuka da bokaye ke warkarwa akwai: Ciwon jiki, kunar wuta sossokiya, daji ko sabara ciwon kai da sauransu.

Wasu bokayen na gane cututtuka ne ta hanyar duban gurbi ko wurin da cuta take. Ire-iren waɗannan cututtuka akwai; ƙunar wuta, ƙuraje, makero da sauransu.

Bokaye na gane ciwo ta hanyar amfani da iskoki. Ire-iren waɗannan cututtuka sun haɗa da: Shan inna, taɓin hankali, matsalar haihuwa da sauransu.

Wata hanyar da bokayen ke bi su gano ciwo ita ce taɓa wurin da ciwo yake. Ire-iren cututtukan su ne; ciwon ɓalli-ɓalli, ko kumburin wani sashe na jiki da sauransu.

YADDA BOKAYE KE SAMUN MAGUNGUNAN GARGAJIYA

Bokaye suna bin hanyoyi daban-daban domin samun magungunan garga- jiya. Ga ciwon da ba a san kansa ba, bokaye na ɗiban saiwoyin itatuwa ne. Haka kuma bokayen suna amfani da ganyayen itatuwa, wasu kuma sassake-sassake ne na itatuwa suke ɗiba, wasu kuma saiwoyi, ko sassake, ko ganyen ne suke haɗawa da surkulle. Wani lokacin kuma surkullen kansa yana iya zama magani.(Bunza, 2006: 246).

MA´ANAR SURKULLE

Masana daban-daban sun bayyana ma´ana da kuma asalin surkulle.

Bunza (2006) ya bayyana kalmar surkulle da cewa asalin surkulle daga Hausawa ta fito, wato kalma ce wadda take da tushe guda biyu: ´Sur´ da ´kulle´. Tushen ´sur´ ya yo daidai da tushen kalmar ´surutu´ wanda a ganin wasu, surkulle kan ɗauki ma´anar surutu. Sannan gaɓoɓin ´ƙulle´ waɗanda suka yi daidai da ƙulli na magani da ake yi na gargajiya don warkar da ciwo.

Haka kuma Ruƙayya (2006) da ta ambato Bunza (1988) ya bayyana ma´anar surkulle da cewa:

Surkulle shi ne shirya wasu zantuka da ba su da ma´ana, ba su da kai bare gindi kuma ga su da wuyar hardacewa. Ko an san sha´anin sihiri, sukan ce idan ba a iya waɗannan surkulle ba zai yi ba.

Haka nan, Adamu (1992) ya bayyana ma´anar surkulle da cewa:

´´Surkulle wasu jerin maganganu ne a sassarƙe da ake ƙirƙirar su cikin Hausa da Larabci da Baubauci. A cakuɗe ake karanta su da nufin bayyana wasu abubuwan mamaki don cimma biyan bukata´´.

A ta fuskar tarihi, wasu masana suna bayyana cewa surkulle daga al´ummar Filani aka samo shi (Bunza 2008) da Shehu 2002).

Bokaye a bisa tsarin sana´arsu ta bayar da maganguna, ba su taƙaita a kan bayar da magani kaɗai ba, cikin al´amuransu na sana´ar bokanci, suna yin karance-karance da sunan addu´o´i wannan kuma shi ya sa za a iya kiransa da sunan surkulle.

Kasancewar ayyukan bokaye ayyuka ne na magance cututtuka na ɓoye da kuma na sarari wannan ya sa suke surkulle suke kuma haɗawa da ´yan jiƙe-jiƙe na ganyaye, saiwoyi da sassake; wuri guda domin su warkar da marar lafiya.

2.1. SURKULLEN CUTUTTUKA A MAGANIN GARGAJIYA

A wannan kashi kuma za a duba ne a gano yadda al’amarin surkulle da magungunan gargajiya ke haɗuwa wuri guda domin samar da waraka ga cututtuka.

Wani abin lura a nan shi ne surkulle a karin kansa tumbin giwa ne. Yana iya shiga cikin fannoni da dama, sai dai in ba a yi dogon nazari da bincike ba. Haka kuma surkulle wani danƙo ne ko a ce wani maganaɗisun magungunan gargajiya ne. Haka kuma shi surkulle da baki bokaye ke aiwatar da shi. Kuma shi mazugin turara magunguna da bokaye ke bayarwa wato surkulle ke ƙara sa masu karɓar magani daga wurin bokaye su yi imani da yawancin magunguna da ake ba su. Surkulle a wajen bokaye da wasu daga cikin masu ba da magani shi ne gindin magani.

Haka kuma a wannan kashi, zan yi bayani kan yadda bokaye ke gwama surkulle cikin magungunan ta nau’o‘in magungunan cututtuka daban-daban na jiki waɗanda ake kamuwa da su, da waɗanda suke na rauni ko haɗari da na ciki da na fatar jiki da na sihiri ga mutane da sauransu.

Bokaye suna surkulle ne a lokacin ɗiban magani, wasu wajen sarrafa maganin, wasu wajen aiwatar da magani, wasu wajen neman wata buƙata, sannan wasu surkullen kuma ana tsarma su wajen warware wani asiri. (Bunza, 2006).

2.1.1 SURKULLE CIKIN MAGANIN CIWON JIKI

Ciwon jiki ciwo ne da ke samun nau’in mutane maza da mata manya da kuma yara. Wato ciwo ne akasari da yake samun mutum ta hanyar aikata wani aiki na ƙarfi kamar faskare, ko tonon rami, ko daka da sussuka da sauransu. Haka kuma ciwon jiki yana faruwa a sakamakon wasu cututtuka da ka iya samun mutum kamar su zazzaɓi (na cizon sauro) ko mura da sauransu.

Bokaye suna yin surkulle da akan haɗa waɗansu magunguna. Haɗa wannan magani da karatu na surkulle yana matsayin wani sinadari ne da zai ba da damar maganin ciwon jiki ya yi saurin aiki. Maganin ciwon jiki da bokaye ke sarrafawa shi ne:

Haɗi: A sassaka faaruu

Tafarnuwaa

Saiwar sanya

Saiwar sabara

Cittaa

Idan aka sami waɗannan itatuwa da tsirrai, za a haɗa su wuri guda. Gabannin su bushe sai a daka su gaba ɗaya lokaci guda. A lokacin da ake daka su sai a karanta surkulle da zai gabata. Daga nan kuma sai a zuba ruwa a ɓararraka su a tukunya.

Awo: Babba a ba shi rabin ƙaramin kofi sau ɗaya a rana. Yaro kuma cikin ƙaramin cokali sau ɗaya.

Wani abin lura a nan shi ne mai jin ciwo ga jiki babba ko yaro, zai sha magani ne a sau ɗaya, sai kuma lokacin da ya sake gamuwa da wani ciwon jiki sai ya sake zuwa a ba shi irin wannan magni haɗe da karatun surkulle.

Karatun surkulle da bokaye ke yi na haɗawa da magani shi ne kamar haka:

Dabò-dabò, dabà-dabò

Zâi daakà, ràbaa mù dà

Gàjiyàr jìkii,

Dabàr ragàbaa, sànnu dà kŷautaa,

Ciiwoo tàfi, kòomaa bar sakatar,

Naakà nakèe neemaa dà alheeriì.

Surkulle da ya gabata surkulle ne da bokaye ke yi yayin da suka gama tattara dukkan saiwoyi da sassake na magani. Haka kuma wannan surkulle bokaye na yin sa ne a lokacin da suke haɗa magani da suka samo. Wannan surkulle yana da dangantaka da jiki a wurin da aka ce ciwon “t̀afi koomaa” da kuma “ràbaa mù dà gàjiyàr jìki”. Yin haka yana ƙara wa magani ƙarfi. Haka kuma ana bayyana wa iska ne da taimakonsa na samun sauƙin ciwon jiki. Kalmar “alheri” ita ce kaɗai take ta aro daga Larabci. Sauran kalmomi ba kamar “zui”, dabo-dabò”, “dabà-dabò”, da “dàbar ragàbaa” kalmomi ne na kambama aljani. Haka nan ‘dabar ragabaa su ma kalmomi ne da ke nuna yabo ga aljan. Sannan ‘Zui’ kalma ce ta sunan aljanin.

Ta fuskar shigar wani harshe za a ga cewa, babu tasirin wani harshe a surkullen. Dukkan kalmomin na harshen Hausa ne.

2.1.2 SURKULLE CIKIN MAGANIN GARGAJIYA NA ƘUNAR WUTA

Ciwon ƙunar wuta ciwo ne da ake gamuwa da shi a sakamakon haɗarin gobarar gida ko ta wani abin hawa kamar mota ko mashin ko jirgin sama ko na ƙasa ko garwashin wuta da dai sauransu. Irin wannan ciwo na ƙunar wuta, ciwo ne mai haɗarin gaske sau tari mutum yakan rasa ransa ma gaba ɗaya.

Ta fuskar magani da ake haɗawa da surkulle akwai:

Haɗi:   saiwar kuükaa

Kaucin gamjii

Sassaken gabaaruwaa

Lokacin da aka sami waɗannan nau’o’in itatuwa uku, za a bari su bushe, sai a daka su, su yi laushi. Daga nan kuma sai a karanta addu’ar surkulle da ta gabata sau bakwai (7) a zaune kan kujera ko wani abin zama. Idan aka gama karanta surkullen sai kuma a saka dukkan garin maganin cikin kwano, a zuba ruwa a kai ya sami kamar minti goma (10) a dinga sha da shafe wurin da ya ƙuna.

Awo: Babba cikin rabin kofi sau biyu a rana tsawon mako ɗaya zuwa biyu. Yaro kuma rabin ƙaramin ludayi sau biyu a rana tsawon mako ɗaya zuwa biyu.[1]

Ta fuskar shafawa kuwa:

Babba a shafa a gurbin da ƙunar take sau biyu safe da yamma. Yaro kuma a shafi gurbin da ƙunar take sau biyu a rana. Dukkansu tsawon mako biyu zuwa uku.

Bisa wannan mataki na surkulle da magani, wani boka da aka yi hira da shi, an bayyana mani cewa wannan surkulle da magani da suke bayarwa, magani ne da ya taƙaita ga ciwon da ya samu ta hanyar ƙunar wuta mai ci ne kaɗai.

A irin wannan ciwo na ƙunar wuta, bokaye suna karatu na surkulle su haɗa da magani na gargajiya da ya gabata wuri guda domin warkar da marar lafiya. Surkulle da bokaye ke karantawa, karatu ne da suke yi a lokacin da suke sarrafa maganin. Surkullen shi ne kamar haka:

Tamar tamàrii sâu baa kà kutum àikâu,

kaanà kàsàncee dà aikìi nasaraa,

sai dà gafarùl kaimaakà sûr.

Surkulle da ya gabata bokaye suna karanta shi ne sau bakwai a daidai lokacin da ƙunar wutar ya sake zagayowa. Manufa ga aikin bokaye ba za a yi wa marar lafiya magani da za a haɗa da karatun surkulle ba sai bayan awa ashirin da huɗu.

Ta lura da ɗaiɗaikun jimlolin da wannan surkulle ya ƙunsa, za a ga surkullen yana nuna magani da aka haɗa sai da surkullen ake so su yi amfani ko aiki ga ciwon ƙunar ta samu ga jiki. Surkullen ya ƙunshi kalmomi kusan guda huɗu muhimmai. Wato ‘àikâu’ da ‘kàsànce’ da ‘aikì’ da kuma ‘nàsarà’, dukkansu suna nuna fatan tabbatuwar aikin surkulle da magani da aka tsarma ne. kalmar ‘nasaraa’ kalma ce daga Larabci da ke nufin samun sa’a ko dace. Sannan ‘kàsànce da aikì’ na nufin maganin ya yi aiki ko amfani ga ciwon ƙunar wuta.

2.1.3 SURKULLE CIKIN MAGANIN GYAMBO

Gyambo ciwo ne wanda ake samunsa a sakamakon rauni da ake gamuwa da shi ko dai ta hanyar yankuwa da wuƙa, ko kwalba ko wani ƙarfe, ko kuma wani ƙurji da ya gagara warkewa. Wato a dunƙule gyambo daɗaɗɗen ciwo ne da ake ganinsa a zahiri a hannu ko a ƙafa ko a wani ɓangare na jikin mutum ko dabba da sauransu.

Magani da za a haɗa da addu’ar surkulle shi ne:

Haɗi: Saiwar gamjii

Kimbaa

Ararraɓii

Saiwar saabaraa

Yayin da aka sami waɗannan itatuwa sai a haɗa su waje ɗaya, a daka su duka, a dinga barbaɗawa a kan gyambo. Idan an zo gabanin a barbaɗa maganin, sai a yi karatun surkulle, a yi humraa wato a hura garin maganin bayan kowane karatu. Ana yin karatun a sau tara ranar Laraba lokacin fitowar rana da kuma daidai lokacin faɗuwarta; a kowace Laraba. Wato ana karatun surkulle a shan magani ko amfani da magani. Lokacin da aka zo barbaɗa maganin, boka yakan umarci marar lafiya ya ɗaga kai ya kalli sama ne.

A irin wannan ciwo na gyambo, surkulle da bokaye suke ƙirƙira wanda suke haɗawa da magani domin samar da warakar irin wannan ciwo, shi ne kamar haka:

Sàgànaani sàgàntami kâi duwà,

Kâi duwà idòo dùbi samà sufùlum màkà sha,

kù bar manà yà zo sù mairo kù daafàa masà yâu ɗaya.

A wannan surkulle da ya gabata, bokan da aka yi hira da shi ya bayyana mani cewa kalmomin da aka maimaita na ‘saganaanii’ ‘sagantamii’ kalmomi ne na girmamawa ga iskan da ake so ya ba da magani. Wato ana nufin babba ɗan babba ne. Kalmomin ‘kai duwa’ ana fassara ko gabatar da marar lafiyan ne wato kamar a ce ga mabuƙaci. ‘Idoo duubi sama’ yana da alaƙa da ciwon da kae neman warkarwa saboda da ma an ce yayin saka maganin, ana so a kalli sama.

2.1.4 SURKULLE CIKIN MAGANIN TARGAƊE:

Abin da ake nufi da targaɗe shi ne nau’in ciwo ne wanda yake faruwa ko samun mutum a sakamakon buguwa ko haɗari da wata gaɓa ta jiki ke samun illa ga ƙashin jiki na yatsun hannu ko na ƙafa.

Maganin da za a haɗa da karatu na surkulle da zai zo nan gaba shi ne kamar haka:

Haɗi: Man shaanuu

Ruwan kaaɗaa

Faskara-saawuu

Haka kuma lokacin da aka samu waɗannan abubuwa da suka gabata, sai a haɗa su wuri guda a ɓararraka. Yayinda suke ɓararraka ne za a tsaya a daidai murhu, a karanta addu’ar surkulle ana tofawa cikin ruwa mai tafasa. Daga nan sai a sauƙe a sake ɗebo manshanu a haɗa da faskara-sawu da ruwan kaɗa a dinga yin karatunn ana kuma tofawa kan targaɗen.

Ta la’akari da warakar wannan nau’i na ciwo, karatun surkulle da ake yi da magani wanda bokaye ke gaurayawa domin warkar da mai irin wannan ciwo a nan shi ne:

Tùrgui mùrgui

Gàjeer̂e nà dòodoo

Maagànii zaa nà baayar.

La’akari da surkulle da ya gabata, za a ga kalmar ‘Turgui’ ana nufin targaɗe ne. an dai sami naso ne a kalmar targaɗe; inda aka saƙala mata wasalin ‘u’ da kuma wasalin ‘ui’ a ƙarshenta. Haka kuma a kalmar ‘murgui’ ita kuma kalma ce mai ma’anar matsawa, wato irin matsa wurin da aka yi targaɗen yayin gyaran (ciwon) targaɗe ake nufi.

Kasancewar wannan surkulle ne na aiwatar da magani, a nan ana nuna ko nufin dodo yana da taimako, sannan ya ba da maganin, ya kuma yi aiki. Haka nan, babu tasirin wani harshe, duka kalmomin Hausa ne tsantsa a cikin surkullen.

2.1.5 SURKULLE CIKIN MAGANIN SOSSOKIYA (MAKUIƁIYA)

Sossokiya ko makuiɓiya ciwo ne da ke samun mutum cikin lokaci guda da zai ji ɓangaren gefen cikinsa na zogi kamar ana caccaka masa allura.

Dangane da irin wannan ciwo, akwai surkulle da kuma magani da bokaye ke bai wa marar lafiya ya yi amfani da su ya rabu da wannan ciwo cikin lokaci ƙanƙani.

Magani da za a haɗa surkullen da shi, shi ne:

Haɗi:   Saiwar raawayaa

Minjiryaa

Ruwaa sai a haɗa su a daka da ruwa.

Surkulle da suke haɗa maganin gargajiyar da shi kuma a nan shi ne kamar haka:

Fùru fùmtumà sàkàr ni

Baa ni dà nauyii,

Sarafàr safari sarsar.

Surkulle da ya gabata, surkulle ne da ake yin sa bayan an gama tattara maganin. Za a yi surkullen yayin da ake daka saiwar rawaya da kuma minjiriyar.

Awo: Babba: Cikin cokali babba ɗaiɗai sau uku a rana tsawon kwana biyu. Yaro kuma cokali ƙarami sau biyu a rana tsawon kwana biyu.

La’akari da surkulle da ya gabata dukkansa yana ƙunshe ne da kalmomin Hausa. Kalmar ‘fùru’ da ta ‘fùmtumà’ suna da alaƙa da ciwon ne, wato ana kamanta yanayin yadda zafin ciwon yake. Sannan akwai luguden bakin ‘F’ da na ‘S’ cikin wannan surkulle. Sannan jimlar “baa ni da nauyi” na nufin marar lafiya ba kowa ba ne, an fi shi ƙarfi wato wani abu mai kama da ƙanƙantar da kai don neman biyan buƙata.

2.1.6 SURKULLE CIKIN MAGANIN GARGAJIYA NA BASIR:

Basir ciwo ne da yake nau’i biyu. Akwai na ciki, akwai kuma mai tsirowa a dubura. Basir na ciki shi ne wanda marar lafiya zai dinga yawan kasala; idan ya kwanta ba zai so tashi ba. Haka nan ana yin kashi wanda yake kamar zawo-zawo, atuni-atuni. Basir mai tsiro kuma shi ne wanda ake samun tumullar nama da za ta tsira a bakin duburar mutum; wani lokaci yakan zama kamar ƙwayar gero wani lokaci kuma kamar tsawon rabin yatsar mutum.

Haka nan magani da za a haɗa yana maganin basir mai tsiro ne (na ciki).

Magani da za a haɗa surkullen shi ne kamar haka:

Haɗi: Saiwar saabaraa

Sassaken ƙiryaa

Sassaken tauraa

Juudan ƙasaa (gaɗakuukaa)

Za a haɗa su a daka, a mayar da su gari sai kuma a jiƙa da ruwa mai tsabta. Sassake da saiwa da aka ambata kowanne ana yi masa surkulle yayin da za a ɗiba.

Awo: Babba rabin kofi (ƙarami) sau biyu a rana na tsawon mako uku.

Mai irin wannan nau’i na basir shi kuma kashinsa yakan fito a ɗan motse. Wani lokaci kuma da kauri yake kuma da wahala yake fita. Surkulle da bokaye ke yi su haɗa da magani shi ne kamar haka:

Matambàmbàrin taɓàr bàkaa

Zân ɗiibàa dà saǹinkù sâi

Wata raanaa ìdan naa daawoo.

Wannan surkulle ne da a ke yi na ɗiban magani da ake so a haɗa tare da maganin da ya gabata domin warkar da marar lafiya, mai fama da ciwon basir. Wannan surkulle kamar yadda muka zanta da wata mai ba da maganin gargajiya ta bayyana cewa magani da surkullen za su yi amfani ga maganin basir mai tsiro da na ciki.

Haka kuma wannan surkulle (da ya gabata), kamar yadda wani boka ya bayyana mani yana nuna cewa sai an ambaci wani abu da suke kira `ƙwanƙwa ƙofa` wato sai an ambata da cewa za a ɗiba. Sannan ambaton ‘sai wata rana idan na dawo’ yana nufin ko da an dawo wata rana ba sai an ce ‘zan ɗiba da saninku’ ba. Haka kuma jimlar ‘matambambàrin taɓàr bàkaa’ yana da alaƙa da ciwon basir. Wato kalmar ‘matambambarin’ wani nau’in yabo ne da kambamawa ya zuwa ga iskokin ko iskan da ake neman amfanin saiwa da saƙe-saƙin da za a haɗa. Saboda a ganin ko bayanin da bokayen suka yi, sun bayyana cewa cutar basir tana da alaƙa da baƙaƙen iskoki ne domin ciwo ne mai wuyar warkewa a jikin marar lafiyar.

2.1.7 SURKULLE CIKIN MAGANIN DAJI (SABARA)

Sabara ciwo ne da idan ya kama mutum za a ga ƙuraje ƙanana sun feso masa a wani sashe na jiki misali kamar ƙafa, ko hannu ko baya ko kai da dai sauran sassan jiki. Haka nan, wannan ciwo, ciwo ne da yake yawan fitar da ruwa da kuma ƙaiƙayi. Bokayen da aka yi hira da su na wannan yanki na Guddiri, sun bayyana cewa ciwon daji (sabara) ba ya buƙatar yin allurar asibitin zamani.

Magani da za a haɗa da surkulle shi ne:

Haɗi: Ararraɓii

Manshaanuu

Gishirin balmaa

Ganyen kanyaa

Ruwaa

Idan aka sami waɗannan itatuwa da ƙaya, sai a haɗa su a daka. Daga nan, sai a raba su kashi biyu, kashi ɗaya a saka ruwa kaɗan a gauraya a dinga shafa wa wurin da ciwon yake. Kashi na biyun kuma za a zuba ruwa kamar rabin matsakaiciyar butar alwala (ta duma), a bari ya tsumu, daga nan sai a ba wa marar lafiya ya dinga sha.

Awo: Babba da yaro duka za a ba su rabin ƙaramin kofi sau ɗaya a rana tsawon kwana uku.

Bokaye suna yin surkulle, su haɗa da maganin gargajiya da aka ambata domin warkar da ciwon daji. Surkulle da bokaye ke haɗawa da maganin da ya gabata shi ne kamar haka:

Kùuna kàbàsin dafàrân,

Kà buusù jumuràl jàbaalì,

Daajìi sauƙar haràb.

Wannan surkulle kamar yadda aka zanta da wani boka ya bayyana mani a hirar da na yi da shi a ranar 7 ga Maris 2017, cewa surkulle ne da za a yi yayin da za a sha maganin da aka haɗa.

Wannan surkulle za mu ga yana da tasiri sosai a haɗa maganin warkar da cutar daji. Za a ga kalmar ‘Daajìi’ da kuma ‘Sauƙar’. Kalmar ‘daajì’ ta farko ana riya cewa daga cikin wasu magungunan da za a haɗa akwai waɗanda a daji ake samo su. ‘Sauƙàr harabi’ na nufin samuwar nasara ga warkewa daga cutar daji da ake neman waraka.

Wani abin dubawa ga wannan surkulle, za a ga maimaicin wasu sautuka kamar sautukan ‘k’ da ‘j’ na kalmomin ‘kuunà kàbàsin’ da kuma ‘jumuràl jàbaalì’. Haka kuma kalmar ‘jàbaalì’, kalmar aro ce daga harshen Larabci wadda take nufin dutse. Sauran kalmomin ba su da wata ma’ana ta karan kansu. A dunƙule dai surkullen yana nufin ciwo ya fita daga gurbin da yake ya koma daji.

2.1.8 SULKULLE CIKIN MAGANIN KUMBURIN MARAINA:

Ciwon kumburin maraina wani nau’in ciwo ne da mutum yake gamuwa da shi a sakamakon cin wani abu ko shan ruwa marar tsabta. Haka kuma kumburin maraina na faruwa a sakamakon canjin yanayi da jikin ɗan’Adam bai saba da shi ba, wanda a tattare da haka fatar jikin maraina kan gamu da irin wannan kumburi. A wata fuskar kuma kumburin maraina na samuwa ne a dalilin mayawuya.

Maganin gargajiya da za a haɗa da surkulle shi ne kamar haka:

Haɗi: Itaacen tsaamiyaa

Itaacen fatsi-fatsi

Itaacen hannu, a haɗa su a dandaƙa su tare, a zuba a ruwa a dinga sha.

Yayin da aka sami haɗin itatuwa da suka gabata (a sama) an bi dukkan matakan haɗawa, a lokacin da ake haɗa itatuwa ne za a yi karatu na surkulle za a kawo nan gaba.

Awo: Babba, rabin ƙaramin kofi sau ɗaya a rana, na tsawon kwana uku zuwa biyar. Yaro kuma ɗaya bisa uku (1/3) na kofi sau ɗaya a rana tsawon kwana uku.

Akwai nau’in surkulle da ake yi wanda ake haɗawa da maganin gargajiya da ya gabata kamar haka:

Dam dà kafaa dàamaa manì

nà shaa àlbarkar hàlìttuu.

Wannan surkulle ne da bokaye ke yi domin sarrafa maganin da za a yi amfani da shi wajen warakar ciwon kumburin maraina. Wato kalmar daamaa da mani yana nufin aiwatar maganin. Kalmar albarka kuma tana nufin halittu da ke raye a doron ƙasa.

KAMMALAWA

Wannan bincike da aka gudanar ya fito da wani fanni na al´adar Bahaushe na haɗa mabambantan al´adu guda biyu wato surkulle da magani a ta fuskar yadda bokaye ke gauraya su wuri guda su samar da warakar cututtaka.

A bisa ga wannan, za mu ga binciken ya fito da yadda bokayen suke gauraya ire-iren surkulle da magunguna iri daban-daban waɗanda za a samu warakar ciwo ko cututtuka. A ciki, an bayyana yadda ake harhaɗa surkulle da magani a warkar da cututtukan da suka haɗa da: ciwon jiki da kunar wuta da gyambo da targade da basir da sauransu.

Haka kuma a wannan bincike an bayyana yadda ake gauraya kalmomin harsuna daban-daban waɗanda suka haɗa da na harshen Hausa da Larabci da kuma Filatanci a yayin da ake ƙulla surkulle a haɗa shi da maganin da bokayen ke bayarwa a yankin Guddiri.

MANAZARTA

Abraham, R. C. (1946). Dictionary of Hausa Language London, Hodder and Stoughton.

Abubakar, R. U. (2006). Camfi da Surkullen Masu bayar da Magunguna a

ƙasar Hausa, kundin Digiri na ɗaya, Jami´ar Bayero Kano.

Adamu, M. T (1998). Asalin Magungunan Hausawa da ire-irensu. Kano ɗan Sarkin Kura Publishers l.t.d.

Al-Hassan, H. da Wasu, (1982). Zaman Hausawa, Bugu na Biyu, Babu Maɗaba‘a

Almajir, T. S. (2009). Surkulle: Yanaye-Yanayensa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa, Cikin Himma Journal of Contemporary Hausa Studies Vol. I NO: I Department of Nigerian Languages Umaru Musa ´Yar´aduwa University, Katsina.

Bunza, A. M (1998). Surkulle. Takarda da aka gabatar A Taron Ƙara wa Juna sani . Jami ´ar Usumanu Ɗanfodiyo, Sokoto.

Bunza, A. M. (2006). Gadon Feɗe Al´ada, Lagos Nigeria, Tiwal Nigeria Limited

Jinju, M. H. (1990) Maganin Gargajiya na Afirika Tare da Maida Karfi A Kan Nazarin Itatuwan Magani na Hausa da Warkewa, Zaria, Gaskiya Corporation Limited.

Suleiman, U. F. (2000). Muhimman Bayanai a kan Asiran Aljanu, Sokoto, Al´amin Press Kofar Atiku.

Shehu, B.M. (2002), ´´Surkullen Mata Kundin Digirin Farko, Sashen Nazarin Harsuna da Kimiyyarsu, Jami´ar Maiduguri.

Shehu, B. M (2013). Tasirin Surkulle Cikin Magungunan Gargajiya na                                      Hausawa, kundin digiri na biyu. Sashen Nazarin Harsuna Da Kimiyyarsu, Jami’ar Maiduguri.



 Yobe Journal - Volume 5

Post a Comment

0 Comments