𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, Malam.
Ina da tambaya, don Allah Allah ya gafarta,
Malam. A matsayina na namiji, idan ina cikin tafiya sai na haɗu da wasu mata a
hanya, shin ya halatta in yi musu sallama, ko kuwa akwai wani hukunci na
musamman game da yi wa mata sallama a irin wannan yanayi?
Don Allah, Malam, ina neman ƙarin bayani bisa koyarwar Musulunci.
Na gode. Allah ya saka da alheri.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuh.
Da farko dai Allah ya
umarcemu da yaɗa sallama a tsakanin
mu ya kuma wajabta mana mayar da sallama ga daukacin musulmai. Ya sanya sallama
ta zama wani abu dake yaɗa soyayya a tsakanin
muminai. Allah ya ce:
وَاِذَا
حُيِّيۡتُمۡ بِتَحِيَّةٍ فَحَيُّوۡا بِاَحۡسَنَ مِنۡهَاۤ اَوۡ رُدُّوۡهَا ؕ اِنَّ
اللّٰهَ كَانَ عَلٰى كُلِّ شَىۡءٍ حَسِيۡبًا
Kuma idan an gaishe
ku da wata gaisuwa, to, ku yi gaisuwa da abin da yake mafi kyau daga gare ta,
kõ kuwa ku mayar da ita. Kuma Allah Yã kasance a kan dukkan kõme Mai lissãfi.
(Surah: An-Nisaa, Ayat: 86).
An ruwaito Abu
Hurairah ya ce; Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) ya ce: bazaku shiga
aljannah ba har sai kun yi imani, baza kuyi imani ba har sai kunso junanku.
Shin bazan gaya muku wani abu ba wanda idan kun yi shi zakuso junanku?, Ku yaɗa sallama a
tsakaninku, zaku so junanku. (Muslim ne ya ruwaito shi a hadisi mai lamba 54).
Umarnin yaɗa sallama umarni ne
ga kowa (maza da mata) kuma ya shafi dukkan musulmai. Ya haɗa da maza suyiwa maza
sallama, mata suyiwa mata sallama, da sallama tsakanin muharraman juna. Anan an
shar'anta sallama a tsakanin wannan sashe ya yi sallama ga ɗayan sashen da aka
wajabta ma mayar da sallama.
Amma akwai hukuncin
da ya hana namiji yin sallama ga macen da ba muharramarsa ba idan yaji tsoron
aukuwar fitina a dalilin wannan sallama.
Babu laifi ga namiji
ya yiwa mace sallama batareda yin musabaha da ita ba, idan ita tsohuwa ce. Amma
bazai yiwa wacce ba tsohuwa ba sallama idan baida tabbacin rashin aukuwar
fitina. Wannan shine sharhin malamai Allah ya yi musu rahama.
An tambayi Imam Malik
shin za'a iya yiwa mace sallama? sai ya ce: "Idan tsohuwa ce banga
karhanci a sallamar ba, amma idan ba tsohuwa bace bana son haka"
Al-Zarƙaani ya yi bayanin
dalilin da ya sa imam malik ya ce baya son haka, a sharhinsa na Al-Muwatta:
Saboda yana tsoron fitina idan yaji muryarta idan zata mayar da sallama.
Acikin (Al-Adaab
al-Shar'iyyah 1/370) ance:
Ibn Muflih ya kawo
cewa Ibn Mansoor ya tambayi Imam Ahmad akan yiwa mata sallama sai ya ce: Idan matar
tsohuwa ce babu laifi.
Saalih (Ɗan Imam Ahmad) ya ce
na tambayi babana akan yiwa mata sallama sai ya ce: sallamar da ta shafi
tsofaffin mata babu laifi, amma waɗanda ba tsofaffi ba baza'a sa suyi magana ba
wajen mayar da sallama.
Al-Nawawi ya ce
acikin littafinsa mai suna Al-Adhkaar a shafi na 407) cewa: Sallamar mata ga
mata yan uwansu kamar sallamar maza ne ga maza. Idan macen kuma matarsa ce ko
baiwarsa ko muharramarsa, to kamar shi ne yake yin magana da wani namiji.
Saboda haka zasu yiwa juna sallama haka mayarwa.
Amma idan wata mace
ce daban kuma tanada kyau, kuma yana jin tsoron zata fitineshi, to shi bazai yi
mata sallama ba, idan kuma ya yi mata sallama, to bai halatta ta amsa masa ba.
Hakanan itama bazata yimasa sallama ba, idan ta yi masa bazai amsa mata ba,
idan ya amsa to ya yi makaruhi.
Idan akwai taron
mata, namiji zai iya yi musu sallama. Haka idan taron maza ne zasu iya yiwa
mace sallama matukar akwai yaƙinin cewa dasu da ita babu Wanda zai
fitinu.
An ruwaito daga Asma
bintu Yazeed (radiyallahu anhaa) ta ce; Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa
sallam) ya wuce ta wajenmu (Mata) sai ya yi mana sallama. (Abu Dawood, 5204).
Albani ya ingantashi a Saheeh Abi Dawuda.
Al-Haafiz ya ce
acikin Al-Fath: Akan halaccin sallama tsakanin mata da maza: Abinda ake nufi da
ya halatta shine idan babu tsoron fitina.
Al-Haleemi yana cewa
Saboda Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) Ma'asumi ne kuma an kiyaye
shi daga fitina. Duk wanda keda yaƙinin ya tsira daga
fitina, to zai iya yiwa mata sallama. Idan kuma akasin hakan ne, to ya tsare
kansa ya yi shiru.
An ruwaito
Al-Muhallab yana cewa: Ya halatta maza suyiwa mata sallama haka mata suyiwa
maza sallama idan babu fitina.
Domin Neman karin
bayani duba: (Ahkaam Al-Awrah wa'l-Nazar na Musaa'id ibn Ƙaasim al-Faalih.
WALLAHU TA'ALA A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.