Ticker

6/recent/ticker-posts

Yawan Tunanin Mutuwa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu Alaikum, malam dafatan anwuni, lafiya. Malam, dan Allah a temaka mun da addu'a da zanna yi. Wallahi na fi wata huɗu kullum nazauna. Sai Ina tunanin mutuwa, kona mutu gashi ansani arami. Haka dai da sauransu kulum in gari yawaye. Sai in yi tunanin ba zan Kara wuni a duniya ba. Na gode

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Walaikumus salamam Warahmatalahi wabarkatahu

Abin da kake fuskanta na yawan tunanin mutuwa kullum har tsawon wata huɗu yana da matuƙar nauyi, kuma yana iya kasancewa alama ce ta matsananciyar damuwa (anxiety) ko ɓacin rai (depression). Irin wannan tsoron da fargabar cewa ba za ka kai ga ƙarshen rana ba yana addabar zuciya, amma yana da kyau ka sani cewa ba kai kaɗai ke fuskantar wannan kalubale ba.

Wannan tunanin ba wai yana nufin gaskiya ne za ka mutu ba; kawai damuwa ce ta yi maka yawa a zuciya kuma tana buƙatar kulawa.

Duk yadda kakai da jin daɗin rayuwarka dole watarana mutuwa sai ta ziyarceka, ka shirya ko baka shirya mata ba. Lallai mutuwa wata aba ce da babu makawa sai ta auku ga duk wanda ke raye, kuma kowa ya sani dole ne zai mutu. Bawa ya kasance cikin yawan tunawa da ita wannan mai yanke jin daɗi abu ne mai fa'ida matuƙa ta fuskar rayuwar ɗan Adam.

Ita mutuwar nan dole ce amma ba kowa ne yake son ta ba, saboda tunanin abin da zai tarar a inda zai je, amma kuma tsoronsa da ita ba ya tasirin komai wajen risƙar sa gare shi.

Ash-Sheikh Muhammad Swalih Al-Munajjir (Rahimahullah) yana cewa a cikin littafinsa Zhahiratu Dha'aful Iyman

(ﻭﻣﻦ ﺃﻛﺜﺮ ﺫﻛﺮ ﺍﻟﻤﻮﺕ ﺃﻛﺮﻡ ﺑﺜﻼﺛﺔ ﺃﺷﻴﺎﺀ : ﺗﻌﺠﻴﻞ ﺍﻟﺘﻮﺑﺔ، ﻭﻗﻨﺎﻋﺔ ﺍﻟﻘﻠﺐ، ﻭﻧﺸﺎﻁ ﺍﻟﻌﺒﺎﺩﺓ . ﻭﻣﻦ ﻧﺴﻲ ﺍﻟﻤﻮﺕ ﻋﻮﻗﺐ ﺑﺜﻼﺛﺔ ﺃﺷﻴﺎﺀ : ﺗﺴﻮﻳﻒ ﺍﻟﺘﻮﺑﺔ، ﻭﺗﺮﻙ ﺍﻟﺮﺿﺎ ﺑﺎﻟﻜﻔﺎﻑ، ﻭﺍﻟﺘﻜﺎﺳﻞ ﻓﻲ ﺍﻟﻌﺒﺎﺩﺓ ..)

MA'ANA: (Duk wanda ya yawaita tuna mutuwa za a karrama shi da abubuwa uku:

1. Gaggauta tuba.

2. Wadatar zuci.

3. Nishaɗi a ibada.

Kuma duk wanda ya manta da mutuwa za a yi masa uƙuba da abubuwa uku

1. Jinkirta tuba.

2. Rashin yarda da kaɗan.

3. Kasala a cikin ibada.

Duba: Zhahiratu Dha'aful Iman, Shafi na: 56-57.

Waɗannan sune fa'idojin yawan tuna mutuwa, da kuma uƙubar mantawa da ita.

"Koda yaushe ka dinga shagaltuwa da tuanin mutuwarka, da haka ne za ka sami cikakkiyar taƙawa da tsoron Allah, musammman a cikin sallarka, domin lallai duk wanda yake yawan tuna mutuwarsa, to lallai za kaganshi yana yawan taka-tsan-tsan wajen afkawa saɓon ubangiji"

"Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam , Ya ce: ka dinga tinawa da mutuwa a cikin sallarka, domin lallai idan mutum yana tunawa da mutuwa a cikin sallarsa, to zaifi yin ƙoƙari wajen ya ga ya yi ta da kyau, (ya inganta ta)"

Albaniy, Sahih Al-Jam'i : {849}

Kullum ka zamto cewa akwai tsarin tunawa da mutuwa a cikin jerin kundin tunaninka na yau-da-kullum, domin lallai ita mutuwa abâce wacce take buƙatar a shirya mata kafin zuwanta, kuma ita ba ta gaza zuwa gurin wanda wa'adinsa ya cika, ko da kuwa ya kasance a cikin katanga mai kewaye da shi ne.

Hanyar mafi kyau ta magance wannan matsalar ita ce yawaita addu'o'i, ambaton Allah (Zikiri), da kuma neman kariya daga shaiɗan.

Allah ya tabba tar da mu akan tafarkin shiriya.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments