Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Raka’o’i Biyu Kafin Sallar Juma’a

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamualaikum malam barka da warhaka malam mene ne hukuncin yin raka'o'i biyu kafin sallar juma,a Allah ya jikan mahaifa ya saka ma gidan aljannah bissalam

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumun salamu warahamatullah,

Game da yin raka’o’i biyu kafin sallar Juma’a, akwai bambanci tsakanin raka’o’in na fila da ake yi kafin Juma’a, da kuma abin da wasu suke kira sunnah kafin Juma’a kamar yadda ake yin raka’o’in rawatib kafin azahar.

Abin da ya tabba ta shi ne cewa babu wani hadisi sahihi da ya tabba tar da cewa Annabi ﷺ ya kasance yana yin raka’o’i biyu na musamman a matsayin sunnah mai ƙayyadadden lokaci kafin Juma’a, kamar raka’o’in sunnah na kafin azahar. Saboda haka, bai dace mutum ya ɗauki raka’o’i biyu kafin Juma’a a matsayin sunnah mu’akkadah mai ƙayyadadden adadi ba.

Amma idan mutum ya shiga masallaci kafin liman ya fito ko kafin huduba, ya halatta ya yi na fila raka’a biyu ko fiye da haka gwargwadon yadda Allah Ya sauƙaƙa masa. Wannan yana cikin sallolin na fila na gaba ɗaya, kuma musamman akwai Tahiyyatul Masjid idan mutum ya shiga masallaci.

Dalili shi ne hadisin Jabir رضي الله عنه cewa Annabi ﷺ ya ce

«إِذَا جَاءَ أَحَدُكُمْ يَوْمَ الْجُمُعَةِ وَالإِمَامُ يَخْطُبُ فَلْيَرْكَعْ رَكْعَتَيْنِ وَلْيَتَجَوَّزْ فِيهِمَا»

Ma’ana: “Idan ɗayanku ya zo ranar Juma’a alhali liman yana huduba, to ya yi raka’a biyu, kuma ya taƙaita su.”(Bukhari da Muslim)

Wannan hadisin yana nuna mana cewa idan mutum ya shiga masallaci ranar Juma’a ko da liman ya fara huduba, zai iya yin raka’o’i biyu na Tahiyyatul Masjid, sannan ya zauna ya saurari huduba.

Haka kuma Annabi ﷺ ya ce

«بَيْنَ كُلِّ أَذَانَيْنِ صَلَاةٌ»

Ma’ana: “Tsakanin kiran sallah biyu akwai sallah.” Sai ya ce: «لِمَنْ شَاءَ» — “ga wanda ya so.” (Bukhari da Muslim)

Saboda haka, idan mutum ya zo masallaci kafin Juma’a, yana iya yin raka’o’i biyu na na fila, ko ya yi fiye da haka, ba tare da ya yi imanin cewa akwai takamaiman raka’o’i biyu da Annabi ﷺ ya kebanta da su kafin Juma’a ba.

Saboda haka, yin raka’o’i biyu kafin Juma’a ba haramun bane. Idan an yi su a matsayin na fila ko Tahiyyatul Masjid, abu ne mai kyau kuma yana da asali. Abin da ya kamata a kiyaye shi ne kada a ce akwai sunnah ta musamman tabba tacciya ta raka’o’i biyu kafin Juma’a wadda Annabi ﷺ ya kasance yana yin ta a kai a kai kamar sunnah kafin zuhr.

Kuma idan liman ya hau mimbar ya fara huduba, bai kamata mutum ya shagaltu da wata na fila ba sai abin da hadisin Jabir ya kebance na raka’o’in Tahiyyatul Masjid guda biyu, sannan ya zauna ya saurari huduba cikin nutsuwa.

Allah Ya taimake mu wajen bin Sunnah da fahimtarta daidai, Ya karɓi ibadunmu, Ya gafarta mana kura-kuranmu, Ya jikan iyayenmu da rahama, Ya sanya su cikin Aljannatul Firdausi.

WALLAHU TA'ALA A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments