Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Babu Laifi In Roki Allah Ya Canza Min Wani Mijin?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu alaikum. Malam barka da war haka ni ce da mijina muna tare tin yana halin Babu. Na yi hakuri a kan hakan yanzu ya samu arziki. Amma baya ba mu abincin kirki na yi na yi amma ya ƙi yarda, ga shi ba ya iya sauke nauyin shi na aure. Abubuwan suna da yawa. To shi ne nake addu'ar Allah ya yacanja min wani mijin. Shin hakan lefi ne?? Domin nace ya sake ni amma yaki yin sakin.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullah.

Haramun ne mace ta nemi saki daga wajen mijinta ba tare da wani laifin da girmansa yakai Ayi hakan ba. Duk da cewa kuma ga laifukan nan kin ambacesu kamar haka

1. RASHIN ABINCI: Wannan babban laifi ne wanda shi kaɗai ma zai iya haddasa Ƙunci ayana yin zaman aure. Idan hakan tana faruwa ne sanadiyyar shi ma bashi da shi, to shike nan. Amma in dai yana da halin da zai wadataku da abincin Amma ya ki ya baku saboda rowa, to tabbas ya shiga cikin laifi. Domin Allah yana cewa

لِيُنۡفِقۡ ذُوۡ سَعَةٍ مِّنۡ سَعَتِهٖؕ وَمَنۡ قُدِرَ عَلَيۡهِ رِزۡقُهٗ فَلۡيُنۡفِقۡ مِمَّاۤ اٰتٰٮهُ اللّٰهُؕ لَا يُكَلِّفُ اللّٰهُ نَفۡسًا اِلَّا مَاۤ اٰتٰٮهَاؕ سَيَجۡعَلُ اللّٰهُ بَعۡدَ عُسۡرٍ يُّسۡرًا

Sai mawadaci ya ciyar daga wadatarsa kuma wanda aka ƙuntata masa arzikinsa, to, sai ya ciyar daga abin da Allah Ya ba shi. Allah ba Ya kallafa wa wani rai face abin da Ya ba shi. Allah zai sanya sauƙi a bayan tsanani. (Surah: At-Talaaƙ, Ayat: 7).

Hakkin ciyarwa yana daga cikin wajibabun hakkokin dake kan kowanne mai iyali. Idan aka rasashi tare da cewa mijin yana da iko amma bai bayar ba, to mace tana da damar daukaka maganar zuwa ga iyaye ko waliyyai domin su yi wa mijin nata magana a samu mafita.

2. RASHIN GAMSARWA: Shi kuma wannan yana da alaƙah ne da yana yin halitta ko lafiyar namiji. Wani namijin lafiyarsa kalau sai dai yana yin halittarsa ne shi bashi da karfin sha'awa ko bukatar iyali. To irin wadannan mazajen idan suka haɗu da mace wacce ita kuma tana da tsananin bukata, akan samu gagarumar matsala ta wannan ɓangaren.

Wani kuma watakil rashin lafiya gareshi kamar basur, ko ciwon sugar (DIABATES) Ko hawan jini mai tsanani. Da farko yana iya sauke wannan hakkin, Amma daga baya jin ya ya sameshi.

To idan mijin naki yana cikin kashin farko, zama za kuyi atsakaninku ku tsara yadda za ku shawo kan matsalar. Misali mai tsananin bukata sai ya saukaka, shi kuma marar bukata sosai sai ya kara kokari gwargwadon yadda zai sauke hakkin dake kansa.

Idan kuma wani ciwon ke damunsa, ki bashi lokaci ya nemi magani, idan kina da damar taimaka masa akan hakan sai kiyi.

Batun abinci kuma ki sanar da magaba tansa ko naki su yi masa magana. Idan ya gyara shike nan. Idan kuma bai gyara ba tunda maganar tana gaban magaba ta sai ki jira hukuncin da za su yanke.

Ina ganin in shaAllahu wannan shawarar za ta fi samar miki da mafita mai kyau fiye da waccen tunanin naki.

Kowanne namijin da kike hange ko kike fatan samun irinsa, to shi ma fa yana da nasa matsalolin kuma yana da nasa halayen masu kyau da marassa kyau. Watakil ma naki mijin ya fi shi kirki. Gara dai kiyi hakuri kiyi fatan Allah ya gyara miki naki mijin.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments