𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaekum warahmatullah wabarkatuh. Malam fatan ka wayi gari lafiya malam ina chikin matsala babba ina neman addur ku malam. Ni ce na kasance ina son yin aure tun ina da shekara 15 zuwa 16 sai mahaifina ya hanani. Duk wanda ya zo da niyyar aure ya hana wai makaranta zan yi na yi ta hakuri har lokaci yaja Kuma malam babban abin da yake damuna ba duk bukatuna yake yimin ba kawai sai na haɗu dawani ya yaudareni ya kusanceni muka aikata haramun SUBHANALLAH ya tafi ya kyaleni ana haka na haɗu dawani zai aureni na kaishi wajen mahaifina amma ya ce a'a ba yanzu ba na yi na yi na hakura amma saurayin nan ya nuna min babana zai yarda muka shaku sosai har yakai na fada masa ni ba budurwa bace amma ya ƙi ji yaki gani wai shi ahakan ma ba zai chanja ra'ayinsa ba. Ni kuma na amince ashe shi ma zina ta kawoshi shike nan daga ranar rayuwata ta dawo ko yaushe ina aikata zina kowa kawai ya zo ya ban yan chanji na amsa ya yi zina Da ni ya tafi Kuma sai na yi hakan na dawo ina kuka ina dana sani. Amma ba zai Hana gobe na kara aikatawa ba, SUBHANALLAH. Yanzu ina son na yi tuban har abada tuban da ba zan sake komawa ruwa ba. malam ina bukatan addu'a da Kuma shawarwarin masu kyau a taimaka Dan Allah ina cikin damuwa ina son nazama ta wannan ɓangaren na fi karfin zuciyata.
HUKUNCIN MAHAIFIN DA
YAƘI AURAR DA 'YARSA HAR TA YI ZINA
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis salam wa
rahmatullahi wa barakatuhu
Hakika kin aikata
kuskure mai girma wanda ban da shirka da kisan kai, babu zunubin da ya fi shi
girma. Shiyasa Allah Ya ce
وَلَا
تَقۡرَبُوا۟ ٱلزِّنَىٰۤۖ إِنَّهُۥ كَانَ فَـٰحِشَةࣰ وَسَاۤءَ سَبِیلࣰا
"KADA KU KUSANCI ZINA. HAKIKA ITA (ZINA)
TA KASANCE ALFASHA CE KUMA HANYAR MUMMUNA CE". (Surah Al-Israa’i: 32).
Kuma Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi Wa Sallam) Ya ce "MAI ZINA BA ZAI YI ZINA A LOKACIN DA
YAKE ZINA ALHALI YANA MUMINI". (Wato ana zare musu imani a san da suke
aikata zina).
Kuma lokacin da ya je
isra'i Ya ce Ya ga wasu mutane Mazaje da Mataye ana gana musu mummunar azaba da
wuta. Wutar tana shiga ta ƙasan su suna ta kururuwa amma ba'a
raga musu. Suna cikin wani kurkuku kamar tanderu ko rijiyar wuta. Mala'ika
Jibreelu ya ce maSa "Waɗannan Mazajen da Matayen ai Mazina ta ne".
Shi kuwa mahaifin ki
kuskuren sa a bayyane yake a fili. Domin kuwa shi ya janyo miki afkawa cikin
wannan kuskure. Da ace ya aurar da ke tun da farko watakil da kin samu kamewa
da runtse idanun ki da baki afka cikin zina ba.
Sabida haka wallahi
ya zama wajibi iyaye masu irin wannan ra'ayin su ji tsoron Allah su dena. Domin
wajibin su ne su aurar da yarin ya da zarar ta isa auren kuma ta samu manemi
kamar yadda magaba ta suka Sunnanta mana cewa ku aurar da 'ya'ya Mata yana daga
cikin abubuwan da Addini yake umurnin ayi cikin gaggawa. A cikin Mausau'ah ta
Ibnu Abid Dunya, Juz'i na 8 shafi na 50 ya kawo maganar Imam Ƙatadah (rah) wanda ya
ce "Duk mahaifin da 'yar sa ta isa aure amma bai aurar da ita ba, har ta
je ta aikata alfasha, toh shi ma yana da laifi a ciki".
Ki sani cewa duk da
girman laifin ki amma afuwar Allah da rahmar Sa ta fi shi girma. Kuma Allah mai
gafara ne, kuma mai karɓar tuba ne. Kuma Yana
mutukar murna da bayin Sa masu tuba gare Shi. sai dai kada kiyi tubar da za ki
sake komawa gidan jiya domin kin ji an ce Allah Yana amsar tubar Bayin Sa,
akwai tuban da Allah baYa amsa.
Allahu Subhanahu Wa
Ta'ala Ya ce
قُلْ
يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ أَسْرَفُوا عَلَىٰ أَنْفُسِهِمْ لَا تَقْنَطُوا مِنْ
رَحْمَةِ اللَّهِ ۚ إِنَّ اللَّهَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ جَمِيعًا ۚ إِنَّهُ هُوَ
الْغَفُورُ الرَّحِيمُ
"KA CE YA KU
BAYI NA WAƊANDA SUKA AIKATA 'BARNA BISA KAWUNAN SU! KADA KU FIDDA
TSAMMANI DAGA RAHMAR ALLAH. HAKIKA ALLAH YANA YAFE ZUNUBAI BAKI ƊAYA, HAKIKA SHI SHI
NE MAI GAFARA MAI JINƘAI". (Suratul zumar:l Aya ta 53).
Ina baki shawarar
cewa ki bi waɗannan hanyoyin domin
samun cikakkiyar tuba irin wacce Allah Yake so;
1. Ki yi nadama sosai
bisa miyagun ayyukan ki na baya. ki tsani Namiji in dai Mazinaci ne shi,
sa'annan Zinar kanta ki tsane ta sosai a zuciyar ki, wato ko da wasa kada ki taɓa yarda ki sake
aikata wannan.
2. Ki dauki alkawari
tsakanin ki da Allah cewa har abada ba za ki sake aikata Zina a rayuwar ki ba,
duk karfin sha'awar ki ko nawa namiji zai ba ki ko me za a mallaka miki kiyi
alkawarin cewa ba za ki sake aikata wannan ba har abada, ko jikin ki wani zai
taɓa ba za ki bari ba.
3. Ki gujewa duk wani
sababi ko dalilin da zai iya sanya ki komawa cikin wannan laifin aikata Zina a
rayuwar ki. Wannan ya haɗa da Ƙauracewa samari ko Ƙawayen da kika tabba
tar suna aikata irin wannan laifin. Kuma kada ki sake sanar da wani saurayi
cewa kin taɓa aikata zina, kada
ki kuskura ki sanarwa kowa ki bar abun daga ke sai Allah, idan kin yi sahihin
tuba shike nan.
4. Ki chanza duk wani
tsarin rayuwar ki, ki shiga Islamiyya ki Ƙaro ilimin Addini. Ki
chanza tsarin dressing ɗin ki kada ki rika
sanya suturar da za ta janyo hankalin maza zuwa gare ki. kuma ki yi istibra'i
domin ƙara tabba tar da tsarkin mahaifar ki da kubuta daga abin
da ya gaba ta. Ki yawaita karatun Alƙur'ani da na filolin
dare da rana da niyyar neman kusanci da mahaliccin ki.
5. Ki sani cewa Allah
Yana tare da ke a duk inda kike, kuma Shi ne Ya fi cancanta ki ji ƙunyar Sa, ki ji
nauyin Sa gurin ki cire tsiraicin jikin ki ga Namiji ya yi Zina da ke, ki
nisanci saɓa maSa. Ki sani cewa
mutuwa tana nan tafe kuma Alkiyama tana tafe babu koƙwanto a cikin ta dole
ne sai kin mutu, ki tuna cewa idan kin mutu a yau me za ki gaya wa Ubangijin
ki.
Don haka ki tanaɗi keƙƙyawan guzuri domin
neman da cewa da rahmar Allah, ki yawaita sadaƙah, sada zumunci da
neman gafarar Ubangijin ki domin samun kankarewar zunuban ki. Ki mayar da
hankalin ki sosai wajen gyaran hayayen ki da dabi'un ki, ki sani cewa babu inda
rayuwar nan za ta kai ki sai hallaka, ki tuna wannan abun a ranki? yanzu
misalin masu yin Zina da ke, don Allah da ace ke Yar su ne, ko ƙanwar su, ko Yar uwar
su, shin za su yarda wani ya yi Zina da ita?.
Amma meyasa ke akan
kuɗi ko akan iphone 17
pro max ko akan wani abun duniya ki tsaya kina bayar da jikin ki ga Namiji ya
yi Zina da ke haka kawai don ki samu abun duniya 😭 ko don ki cire
Sha'awar ki wai sabida an ƙi aurar da ke? haba Yar uwa wallahi da
ace kin san irin girman darajar da Allah Ya ba ki wallahi ko tafin hannun ki ba
ki isa ki budewa Namiji ya kalla ba idan ba Mijin ki ba, balle wai har ki je ki
buɗe masa ƙafafun
ki ya ga tsiraicin jikin ki kuma ya yi Zina da ke ya ba ki abun da kike so, ki
ji tsoron Allah kuma kiyi gaggawar tuba kamar yadda na yi miki bayani a sama in
Sha Allah Allah zai amsa tubar ki matukar kin yi Sahihin tuba.
Kuma irin wannan
rayuwar a yanzu ba Yan mata ba, ba matan Aure ba har da zaurawa, toh kowacce ki
shirya makomar ki da abun da za ki tarar a Lahirar ki, a nan duniya kan kin ji
daɗin ki kin more
rayuwar ki kuma kin samu abun da kike so, toh azabar Allah da uƙubar sa na jiran ki,
kin ga babu amfanin jin dadin rayuwar ki da kika yi.
Kuma iyayen Yara kullum
muna kira akan ku ji tsoron Allah, ku rika Aurar da Yaran ku a lokacin da suka
kai yin Aure ba gwaninta bane wai ku Yar uwar ku ai sai ta yi degree ko
master's kafin ta yi aure, za ku sama mata abun da kuke son ta samu amma kuma
ba ku da amsar da za ku gaya wa Ubangijin ku, kuma ba za ta je Lahira a tambaye
ta certificate na degree ko professor ba, saboda haka ku ji tsoron Allah idan
kun Aurar da su akan lokacin su kun huta, idan kun ƙi toh kowa ya shirya
karɓan hukuncin Allah, ai
dazun kun ji mun karanta a littafin zadud-zajeuni, kowa sai Allah Ya tambaye
shi idan kunne ya ji jiki ya tsira. Allah Ya sa mu dace Allah Ya shiga gafarta
mana ba ki ɗaya.
WALLAHU A'ALAMU.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.