𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Allah yakarama malam lafiya da Nisan kwana me albarka. Tambayana malàm wanda ya yi zunubi babu niyya ko sha'awa, sannan a lokacin zuciyansa ya ki abun yana jin damuwa, mene ne hukuncinsa idan ya rasa mafita. Shin mene ne hukuncin Hakan? Allah ya saka da alkhairi 🙏
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis salam wa
rahmatulLahi wa barakatuhu.
Tambayar taki tana da
harahen damo. Za ta iya nufin mutumin da aka tilastashi har ya aikata wani
zunubi, ko kuma mutumin da halin matsatsin rayuwa ya kaishi zuwa ga aikata ayyukan
saɓo. Allah shi ne
masanin hali da rayuwar bayinsa, kuma yasan abin da suka aikata afili ko aɓoye da kuma dalilansu
na yin hakan.
A Musulunci, hukuncin
mutumin da ya fada cikin zunubi saboda matsin lamba, tursasawa, ko rashin
mafita ya dogara ne akan irin yana yin da yake ciki da kuma nau'in zunubin.
Idan mutum ya tsinci
kansa a yana yi na yunwa, rashin lafiya, ko hadari na mutuwa inda babu wata
mafita face aikata wani abu da aka haramta (kamar cin mushe ko satar abinci don
kar ya mutu) wannan babu laifi akansa. Halal ne gare shi ya aikata abin da zai
tseratar da rayuwarsa, amma iya gwargwadon abin da zai tseratar da shi kawai, ba
tare da ketare iyaka ba.
Idan dai halin rayuwa
ko tilasci suka zamto sun kai mutum zuwa ga aikata wani aikin zunubi, to babu
laifi ko zunubi akan abin da mutum ya aikata ba tare da niyya (ganganci), zaɓi, ko sha'awa ba, musamman
idan zuciyarsa ta ki abun kuma yake jin damuwa. Wannan damuwar da mutum yake ji
a zuciyarsa tana nuna alamun ingancin imaninsa.
Allah yana yafewa bawansa
mutukar dai shi bawan bai ɗauki wannan amatsayin uzurinsa na yin zunubin a ko yaushe
ba, wato wajibi ne mutum ya nemawa kansa mafita, kada ya zauna ahaka, kada ya
saba da aikata wannan abun har ma ya dawo yana yinsa kuma da gangan.
A cikin Alkur'ani mai
girma, Allah ya ce
وَ لَيۡسَ عَلَيۡكُمۡ
جُنَاحٌ فِيۡمَاۤ اَخۡطَاۡ تُمۡ بِهٖۙ وَلٰكِنۡ مَّا تَعَمَّدَتۡ قُلُوۡبُكُمۡ ؕ
وَكَانَ اللّٰهُ غَفُوۡرًا رَّحِيۡمًا
Kuma babu laifi a
gare ku ga abin da kuka yi kuskure da shi, kuma amma (akwai laifi) ga abin da
zukatanku suka ganganta, kuma Allah Ya kasance Mai gafara, Mai jin ƙai.
Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce "Hakika saboda Ni, Allah ya yafe wa
al'ummata abin da suka aikatashi cikin kuskure, da wanda suka yishi cikin
mantuwa, da kuma abin da aka tilastasu akansa". (Ibnu Maajah da Baihaƙiy suka ruwaitoshi).
Malamai da yawa sun
yi magana game da ma'anoni da bayanan da wannan hadisin ke kunshe da shi. Daga
cikin abin da suka faɗa sunce lallai duk
wanda ya aikata wani aikin saɓon Allah bisa tilastawa daga waninsa, to babu laifi
akansa. Sai dai laifin yana kan wannan da ya tilastashi ɗin.
Akwai wasu manyan
zunubai da malamai suka ce babu halacci ko tursasawa a cikinsu, ko da rayuwar
mutum tana cikin hatsari
1. KISAN KAI: Ba ya
halatta mutum ya kashe wani domin a tseratar da tasa rayuwar. Wanda aka
tilastashi domin ya kashe wani ko wasu, kuma ya aikata kisan kai ɗin, to lallai sai
anyi masa haddi da shi da wanda ya tilasta masa ɗin. Saɓanin sauran laifuka.
2. ZINA: Malamai da
dama sun tafi akan cewa tursasawa ba ta halatta maza su yi zina ba. Amma matar
da wani ya tilasta mata ya yi zina da ita ta hanyar fyaɗe, to wannan babu
laifin zina a kanta. Laifin yana kan wanda ya tilasta mata ɗin.
Abubuwan da ya kamata
mutum ya yi idan ya faɗa cikin wannan yana
yi
1. NEMAN GAFARA
(ISTIGFARI): Ko da yana yin ya ba ka damar aikata hakan, yawaita istigfari yana
wanke dukkan wani datti na zuciya.
2. TUBA NA GASKIYA:
Kudiri niyyar cewa idan ka fita daga wannan matsin lambar ba za ka sake komawa
ba.
3. KIYAYE HAKKIN
WASU: Idan matsin lambar ya sa ka cutar da dukiyar wani (kamar sata don abinci),
kana da alhakin biyan sa idan ka sami iko nan gaba.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.