Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Aka Tilasta Wa Ya Kashe Wani

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu Alaikum Malam Khamis muna godiya da fadakarwa. gaskiya ina matukar jin dadin wannan group Mai albarka. Malam Khamis, Allah Ubangiji ya saka maka da alkhairee. Tambayata a nan ita ce; Mene ne Hukuncin wanda aka tilastawa ko aka yi wa barazanar kisa domin ya kashe wani mutum?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

A cewar Shari'a ta Musulunci (Fikhu), wanda aka tilastawa ko aka yi wa barazanar kisa domin ya kashe wani mutum, ba ya da halascin ya kashe shi. Idan aka tilasta masa har ya kashe mutumin, mafi yawan malamai (kamar Malikiyya da Shafi'iyya) sun tafi a kan cewa za a yi masa hukuncin kisa (Ƙisas) shi ma, da kuma wanda ya ba da umarnin (mai tilastawar), domin shi ma ya aikata kisan da gangan.

Wasu daga cikin malaman Hana fiyya sunce hukuncin kisas zai rataya ne a wuyan wanda ya tilasta shi (umarni), amma duk da haka wanda ya aikata ɗin yana da laifi a gaban Allah idan bai yi hakuri ya ki kashe shi ba.

Malamai sun haɗu a kan cewa rayuwar wani ba ta da sauki ko wani fifiko a kan ta wani, don haka ba a halasta mutum ya ceci ransa ta hanyar kashe wani maras laifi ba. Hakika Allah maɗaukakin Sarki Ya ce

وَمَنۡ يَّقۡتُلۡ مُؤۡمِنًا مُّتَعَمِّدًا فَجَزَآؤُهٗ جَهَـنَّمُ خَالِدًا فِيۡهَا وَغَضِبَ اللّٰهُ عَلَيۡهِ وَلَعَنَهٗ وَاَعَدَّ لَهٗ عَذَابًا عَظِيۡمًا‏ 

Kuma wanda ya kashe wani mũmini da ganganci, to, sakamakonsa wutar Jahannama, yana madawwami a cikinta kuma Allah Ya yi fushi a kansa, kuma Ya la'ane shi, kuma Ya yi masa tattalin azaba mai girma. (Suratun Nisaa Aya ta 93).

Ya zo a cikin Bukhari da Muslim, lafazin muslim daka Abiy Bakrata Allah yakara yarda da shi ya ce: Na ji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi wasallam) yana cewa: Idan musulmai guda biyu suka fuskanci juna da takubbansu suna faɗa, da wanda aka kashe da wanda ya yi kisan dukkansu 'yan wuta ne, sai Sahabbai Sukace: Wanda Aka kashe fa? sai Annabi ya ce: Shi ma da ya samu dama shi ne zai kashe ɗan'uwansa.

Abisa wannan hukuncin musulmi ya fuskanci ɗan'uwansa da makami ya kashe shi laifi ne mai girman gaske da nassin Alƙur'ani da Sunnah, duk wanda ya aikata haka zai shiga wuta.

Bai halatta farwa mutum ka kashe shi ba da hujjar cewa tirsasa maka akayi, oganka ne a aikin damara na kaki, ko sarki ko waninsa.

Ibnul Arabi Ya ce: Babu Saɓani tsakanin Al'umma idan aka tirsasawa mutum akan kisan kai, cewa bai halatta Agareshi ya fanshi kansa da kashe wanda akace ya kashe ɗin ba, wajibi ne ya yi hakuri akan bala'inda yasameshi. Ma'ana ba zai kashe wanda aka tirsasashi ya kashe ba, sai dai shi ya yi hakuri akashe shi kawai (shi ne masifa da bala'inda ya sameshi).

Wanda kuma bai yarda akashe shi ba sai ya kashe wanda aka tilasta masa ya kashe, to yana da zunubin kisan kai, za a zartar masa da hukuncin kisasi (shi ma za a kashe shi).

Imamu shafi'i Allah yajikansa a cikin luttafinsa AL'UMMU.

Da'ace wanda akayiwa Umarni ya yi kisa yana sane, cewa ogansa ko sarkin da ya umarceshi da ya yi kisan yasan akan zalunci ne za ayi kisan, to wanda yasashi kisan za ayiwa kisasi, su duka sun yi tarayya akan zunubin kisan kai abisa zalunci. Amma idan baisan akan zalunci aka sashi kisan ba, zunubi da kisasi yana kan wanda yasashi kisan matukar, kisan bana shari'a bane.

Imamun Nawawi a cikin Sharhin Muslim Ya ce: Kasancewar mai kisa da wanda aka kashe, abune da shari'a ta zo da shi, cewa dukkansu suna wuta.

Amma tunda ka riga ka aikata kisan cikin rashin sani, to saika rufawa kanka asiri ka cigaba da neman gafara da tuba awajan Allah da kara dagewa akan ayyukan kwa rai, sadaka, kyautatawa iyaye, sada zumunci taimakon marayu. Allah zai karbi tubanka ya yafe maka laifin kisan kai da kayi.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments