Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Za a Iya Kashe Tsaka Da Ruwan Zafi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam da fatan an wayi gari lafiya? Shin mutum zai iya kashe tsaka da ruwan zafi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Tsaka dabba ce mai nau'in ƙadangare amma ba takai kadangare girma ba, kuma tafi rayuwa a cikin ɗakuna.

Ya halatta a kashe tsaka saboda illolinta ga lafiyar Ɗan Adam da kuma zamantakewar yau da kullum, kuma saboda Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kirata da suna "FASIQAR HALITTA". Kuma ya yi umurni da kasheta ta hanyar bugu ko sokewa da mashi.

Imamu Muslim ya ruwaito hadisi acikin Sahihinsa (hadisi na 2,238) ta hanyar Nana A'ishah (radhiyallahu anha) cewa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi umurni da kashe tsaka.

Hakanan acikin Sahihul Bukhariy hadisi na 3359 wanda aka ruwaito ta hanyar Ummu Shareek (radhiyallahu anha) ta ce "Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi umurni arika kashe tsaka ya ce "Domin ta kasance ita ce ta hura wutar nan (wacce kafirai sukayi nufin Qone Annabi Ibrahim da ita).

Addinin musulunci Addini ne mai tsafta da son zama lafiya, don haka ne ya shar'anta mana wasu ababe da suka halatta mutum ya kashe su daga ciki ma akwai wanda idan ka kashe kana samun lada, daga cikin waɗannan halittu akwai tsaka! Wacce Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kira ta da cewa lallaifa ita tsaka algun-guma ce wacce kuma Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya tabbatar mana da cewa lallaifa dukkan wanda ya kashe tsaka a duka guda ɗaya rak! To yana da lada ɗari (100).

Amma dangane da hukuncin kashe tsaka ko duk wani kwaro ko dabba ta hanyar amfani da ruwan zafi, wannan kam bai halatta ba, saboda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya hana yin amfani da wuta domin azabtar da wani abu ko kashewa. Shi kuwa ruwan zafi tamkar wutar ne.

Daga cikin hujjoji akwai hadisin Sayyiduna Abu Hurairah (radhiyallahu anhu) wanda Imamul Bukhariy ya ruwaito akan lamba ta 3016. Abu Huraira ya ce "Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce "BABU MAI YIN AZABA DA WUTA SAI ALLAH".

Sannan Imam Abu Dawud ya ruwaito hadisi acikin Sunanu nasa akan lamba (2675) cewa watarana Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yaga wani gidan tururuwa wanda wani daga cikin Sahabbai ya Qoneshi da wuta, sai ya ce "KADA WANI YA YI AZABA DA WUTA SAI UBANGIJIN WUTAR"

Don haka abin da ya yafi kyau kuma yafi daidai da addini shine duk abinda akayi umurni da kisansa, to ka kasheshi ba tare da amfani da wuta ko ruwan zafi ba. Misali kamar maciji, kunama, tsaka, kudin cizo, kwarkwata, rina, shanshani, cinnaka, da sauransu.

Yazo acikin wani hadisi wanda Imamun Nawawiy ya kawoshi a cikin Arba'una hadeethan Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce "IDAN ZAKUYI YANKA TO KU KYAUTATA YANKAN, HAKANAN IDAN ZAKUYI KISA KU KYAUTATA KISAN".

Domin korar tsaka a gida, ka nemi gishiri ka gauraya da garin tafarnuwa ko danyar tafarnuwa sai ka watsa a duk inda kake yawan ganin ta a gidanka, tsaka za ta bar wajen a cikin gaggawa.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments