𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Shin haila yana iya zama sau biyu (2) a wata ko sau ɗaya (1) a shekara tare da hujja? Aiki ne (assignment) aka ba mu.
SHIN
HAILA YANA IYA ZAMA SAU 2 A WATA KO SAU 1 A SHEKARA?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa
AlaikisSalaam Wa Rahmatullah;
Eh, sosai ma kuwa akwai irin waɗannan matan, amma ba kowacce mace ce take yin haka ba. Akwai wadda ita jinin hailar ta a shekara sau 1 tak take yi ko sau 2 a shekara 1 tak. Wannan malamai sun
tafi akan hakan, sa'annan akwai wata macen ita a wata 1 tana yin Jinin Hailar
ta sau 2 ne, har Shari'a ya ce musu, idan sun zo iddar su za su yi wata 2 ne
kacal sun gama iddar su a maimakon su yi wata 3.
Wadda
ita kuma a shekara sau 1 tak take yin jini hailar ta ko sau 2, ita kuma suka ce
dole ne za ta zauna na Shekara 3 ko 2 kafin za ta gama iddar ta wannan haka
hukuncin yake matukar haka halittar zuwan jinin hailar ta yake.
A
gurin wasu Malaman kuma mace ba ta yin Jinin Haila a wata 1 sau biyu. Domin
Hadisi ya inganta daga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) Yake cewa,
larura ce da Allah Ya saukar wa Ya'yan Adamu a kowanne wata.
Sai
dai abin da bincike ya tabbatar shine wata m`cen tana yin Jinin Hailar ta a
farkon wata, da kuma karshen Wata sau 2 a cikin wata 1. Wanda yake kenan a
cikin wata biyu tana iya yin Jinin hailar ta sau Ukku kenan. Wanda Hakan ya
nuna cewa mai irin wannan Jinin al'adar, za ta iya gama iddar Sakin ta bayan
rabuwar ta da Mijin ta a cikin wata biyu kaɗai a maimakon wata Ukku kamar yadda bayani ya
gabata a sama.
Malamai
suka ce duk wadda Jini ya zo mata a cikin wata 1 sau biyu, matukar ba farkon
wata da karshen wata bane. Toh dole wannan Jinin daya al'ada ne, ɗayan kuma na Cuta ne.
Amma akwai matan da su suna yin jini a shekara 1 sau biyu, wasu kuma sau 1 ne. Bayanin ya gabata a sama. Akwai wadda kuma a cikin wata 1 jinin yana iya tsallake mata ba tare da ta ga hailar ta ba. Wannan kuma wani abu ne a hannun
Allah, yana yin hakan ne a bisa wata hikima ta sa.
Sabida
haka, indai kin tabbatar da cewa ke tun farkon fara yin jinin haila a rayuwar
ki ai a wata 1 kina yin jinin hailar ki Sau 2 ne a maimakon sau 1, toh idan an
Sake ki sai kiyi tsarki ukku, wato misalin a wannan watan jinin ya zo ya gama
yin kwanakin sa ya dauke, toh kin yi 1 kenan, idan a karshen watan jinin ya
sake zuwa ya yi iya kwanakin sa ya ɗauke, kin ga kin yi biyu a cikin wata 1, yanzu
saura miki tsarki 1 ki gama iddar ki, toh idan wani watan ya kama jinin hailar
ya zo ya yi iya kwanakin sa ya dauke kika yi wanka, shikenan yanzu kin gama
tsarki ukku da Allah Ya ce ayi, don haka kin gama iddar ki.
Idan kuma macen da take yin jinin hailar ta sau 1 a wata ne, toh ita kuma za ta yi jinin na wata uku ne, idan kuma a shekara 1 sau 1 ko 2 kike yin jinin hailar ki, toh wannan aiki ya same ki dole ne za ki zauna ba aure har sai wannan jinin ya zo ya dauke, kin yi haka har sau uku kafin iddar ki ta kare.
Idan
kuma kin yi family planning, toh wannan hukuncin yana chanzawa domin duk wadda
tayi family planning jinin hailar ta na iya rikicewa, sabida haka hukuncin su
na iya chanzawa matukar jinin hailar ta baya saiti.
Idan
kuma mace bata yin jinin haila, sabida ta girma ta dena yin jinin haila a
yanzu, ko kuma karamar Yarinya ce wadda ba ta fara yin jinin haila ba a rayuwar
ta, toh waɗannan mata
guda 2 su kuma aka ce za su lissafa iya wata Ukku ne kaɗai shikenan sun gama iddar su, sabida haka sai a
mayar da hankali domin kowacce da hukuncin ta, kuma kafin ki aikata abu
yakamata kiyi tambaya bawai sai bayan an aikata za a yi tambayar ba.
Allah
Shine Masani.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.