Ticker

6/recent/ticker-posts

Ciyar Da Mace Ba Shi Ne Yake Nuna Ka Sauke Hakkinta Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam, barka da safiya. Allah Ubangiji ya taimaka. Malam, ina da tambaya: Yau kimanin wata huɗu da 'yan kwanaki rrabona da mijina ya sadu da ni. Wallahi malam, tun kafin na haihu rabona da shi, yanzu kuma na haihu, yau wata huɗu da kwanaki. Ni ba ƙazama ba ce; ina gyara jikina, ina gyara ɗaki ciki da waje. Na tambaye shi me na yi masa ko baya gamsuwa da ni, sai ya ce a'a. Kuma wallahi malam, ko a da bai kai minti ɗaya yana kawowa, amma duk da haka ina haƙuri. Ta kai na faɗa wa ƙanin mahaifina, sai ya ce min ko babu abinci ne? Na ce akwai. Ta kai ina ce masa ya saƙe ni. Ga shi ba ya cin abincina, ina masa wankan kai da ruwan wanka sai ya ce ba ya so. Na rasa yadda zan yi, wallahi ni ba ƙazama ba ce, daidai gwargwado ina tsabta. Wallahi malam na gaji. Malam, ɗan Allah ka ba ni shawara. Na je asibiti an auna min hawan jini (BP), ya kai 170/90 mmHg, alhali tun da nake hawan jinina ba ya wuce 110/70 mmHg.

CIYAR DA MACE, BA SHI NE YAKE NUNA KA SAUKE HAƘƘINTA BA

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikis salaam:-

Ai dole ne Hawan Jini ya kama ki domin wannan cutarwa ce da Zalunci da kuma rashin sanin dokokin Allah na Aure, Kuma gaskiyar magana shi ne iyayen Mata da Maza duk ba ku yin Shari'ar da ya dace da abun da Allah da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) suka ce, Ciyar da Mace da Tufatar da ita ba shi ne manufar yin Aure ba, Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) Ya ce ku Auri Mata masu haihuwa domin na yi Alfahari da Yawan ku a ranar Alƙimaya, bai ce ku Auri matan da za ku rika ciyar da su da shayar da su shikenan sai Kun ga damar yin Jima'i da su ba, ba ku yin Shari'ar Adalci ga Yaran ku Mata Kuma wallahi sai Allah ya tambaye ku ko ba ku so.

Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) idan Mace ta kawo karar Mijin ta bawai cewa yake yi ai ba ki rasa Ci da Sha ba da Tufafin sawa ba, ko Kuma ya ce yana Ciyar da ke? Yana Shayar da ke? Yana Tufatar da ke? Yana miki komai? Ya ce ki je kiyi hakuri ki ci gaba da zama da shi a haka ba, wallahi Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ba irin wannan Shari'ar yake yiwa Mace ba. Dole ne a kira Mijin a kira Matar a haɗa su ayi musu Shari'ar gaskiya in gyara ne su gyara in rabuwa ne su rabu haka Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yake yi.

Amma wai iyayen Mata da Maza sai su ce ai ba ki rasa Ci da Sha ba don haka ki je ki ci gaba da yin hakuri da shi wannan Shari'ar Kuskure ne shiya sa dayawa wasu Matan suke yin Zina da Madigo domin ba a karba musu haƙƙin su Mijin baya Jin maganar kowa sai abun da zuciyar sa ya ce. Iyaye ku ji tsoron Allah domin sai Kun maimaita Shari'ar nan a gaban Allah ko ba ku so.

Kin ga irin wannan daman shiya sa muke cewa kullum idan Mace ta tashi yin Aure ta tsaya dakyau gurin zaben Miji wadda ya San Darajar ki, ya san Darajar na gaba da shi sa'annan yake Jin maganar na gaba da shi Kuma me tsoron Allah inda a ce irin wannan kika samu da Hawan Jini bai kama ki ba.

Duk yadda kika Kai ga son sa a waje kafin ya Aure ki indai kin fahimci baya Jin maganar kowa sai na zuciyar sa babu Tausayi ko tsoron Allah a Zuciyar sa toh rabuwa da shi ne yafi dacewa ga rayuwar ki domin in bahaka kina iya samun kanki a irin yadda yanzu kika samu kanki kuma ayi ta cewa kiyi hakuri tun da kina samun ci da Sha a gidan sa.

Idan Namiji yana da waɗanda suke taka masa Birki kuma yana da tsoron Allah a Zuciyar sa ya San Darajar ki yana tausayawa rayuwar ki ko halin da kike ciki, toh Mace ba ta Shan wahala sosai a gurin sa, amma in babu waɗannan a gurin Namiji toh Mace na Shan wahala a gurin sa kuma Babu yadda kika iya da shi sai dai hakuri ko rabuwa da shi.

Sabida haka shawara na farko shi ne ki Kara da yin Addu'a kamar yadda kike yi, ki Kara danne zuciyar ki da yin hakuri da juriya da jajircewa gurin cinye jarrabawar ki da Allah ya daura ki akai bawai Allah baya son ki ba, Allah yana son ki shiya sa ya haɗa ki da Miji wadda yake Zaluntar ki in kin iya jurewa da hakuri shikenan kin cinye jarrabawarki ki shiga Aljannah domin Allah yana tare da masu hakuri da juriya, ki dage da yin Addu'a sosai domin babu abun da ya gagari Ubangijin ki sa'annan ki bar wa Allah Zabin sa idan ci gaba da zama da shi Alkhairi ne ga rayuwar ki toh Allah ya shirye shi ya gane gaskiya ya dena cutar da rayuwar ki har damuwar sa ya sa kina fama da Ciwo, idan kuma ba Alkhairi bane Allah ya kawo Sanadin rabuwar ku kowa ya je Allah ya haɗa shi da Rabon sa.

Shin meya sa Mafi Yawancin Mata suke kamuwa da rashin lafiya Hawan Jini da sauran su musamman matan Aure? Amma Maza kina iya Tara Maza 10 daker ki samu Mai Hawan Jini 2 amma mata 10 wallahi sai an samu 5 ko dukka goman duk suna da matsalar Hawan Jini da wani ciwon, duk Sanadin zaman gidan, Haba Yan'uwana Maza wanne irin cutarwa ce da Zalunci ne haka?

Na biyu shi ne duk yadda za a yi ki je har gaban Waliyyin sa tare da hujjojinki ki sanar da shi komai kar ki ji tsoro ko kunyar gaya masa gaskiya domin gurin a gyaran Aure ko gyaran addinin babu wannan, kiyi masa Barazanar cewa ke kin gaji idan Mijin ki ba zai iya ba kawai a sa shi ya Sake ki, domin ba ki ga amfanin zaman ki a gidan ba a matsayin kina Mace, sai ki ja baki kiyi shiru ki ji me zai ce miki.

Waliyyin ki da Waliyyin sa sune haƙƙin Auren ku yake kan su Wanda a ranar Alƙimaya dole ne sai sun je gaban Allah sun yi bayanin wannan nauyin da aka daura musu, don haka in sun bari ana cutar da ke suka ja ba ki suka yi shiru ai dalilin su kina samun ci da Sha toh sai Allah ya tambaye su, sabida haka sune idan ana samun matsala irin wannan toh gurin su ake zuwa idan ta gagara ne sai a haɗa da iyayen ku da wasu Manyan daban. Sabida haka kiyi hakan ki je ki same shi ku yi magana.

Na uku, indai rashin Saduwa da ke zai je fa rayuwar ki cikin halaka na Zina ko Madigo ko biyawa kanki Bukata ko wani Saɓawa Allah toh gara Auren ku ya mutu Kun rabu kowa ya je Allah ya haɗa shi da Rabon sa a gaba, domin cewa wai ba ki rasa Ci da Sha da Tufafin Sawa ba, wannan ba shi ne hujjojin ba, idan gidan ku ai ana miki komai kuma wata kila Abinci ko abin Sha ko Tufafin Sawa da ake miki a gidan ku ba irin sa kike samu a yanzu ba amma sabida ki samu Rahmar Allah zuwa Aljannah kike zaune a gidan Mijin ki da Daɗi ba Daɗi duk kina hakuri, kenan wannan maganar na iyaye cewa ba ki rasa ci da Sha ba wallahi wannan ba hujja bane Kuma inda a ce haka Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) yake yiwa Mata Shari'a idan sun kawo karar Mijin su da ina ji yanzu ba wannan rayuwar ake Ciki ba. Iyaye ku ji tsoron Allah!!

Sabida haka indai kin bi duk matakan gyara ya ƙi sa'annan lafiyar sa ƙlau bawai bai da lafiya ba, Kai ko da a ce baida lafiya ne ai domin ya tausayawa rayuwar ki irin Kunci ko tashin hankali da za ki shiga yakamata ya yi ya tausayawa rayuwar ki ya tashi ya nema Magani domin ya sa miki Farin ciki akan abun da kike so indai a fannin Jima'i ne, amma ya ƙi sa'annan har gobe baya kusantar ki kuma wata kila lafiyar sa ƙlau yake, kin ga wannan ai Zalunci ne da rashin tausayawa rayuwar ki.

Idan bai da lafiya ne sai ayi masa uzurin cewa Bai da lafiya sai ya tashi ya nema Magani domin biya miki Bukatun ki, in kuma wani abun kika yi masa ya fito ya gaya miki sai ki gyara wannan shi ne rayuwar Aure mai tsafta bawai irin wannan Zaluncin ba.

Sabida haka indai kin bi matakan Shari'ar Musulunci na gyara ya ƙi ya gyara, toh mafitar ki ɗaya shi ne rabuwa da shi, domin Cewa ki ci ki Sha kullum kina tare da mijin ki baya miki komai, kuma haƙƙin sa ne ya sauke wannan, sa'annan lafiyar sa ƙlau amma sai ya ƙi kin ga duk hakurin ki wata rana akwai lokacin da hakurin ki zai kare ko shedan yafi Karfin zuciyar ki har ki aikata abun da ya Saɓawa Allah ki dawo kina nadamar hakan kin ga akan ki Saɓawa Allah gara Auren ya mutu.

Shiya sa dayawa wallahi wasu daga cikin matan Aure a yanzu wasu suke koma yin Zina wasu yin Madigo, sabida irin Zalunci da rashin Tausayi Mazajen su na ƙin yin Jima'i da su ba tare da wani hujja ba a gare su kawai don su kuntatawa rayuwar su ne, Mata dayawa sun zama Yan Iska dalilin Mazajen su.

Amma inda a ce kene za kiyi Kuskuren hana shi kanki a ce misalin kina fama da ko rashin lafiya ne ko kuma ba ki Jin za ki iya yin Jima'i da shi sabida wani abun da ya yi miki a ce ki yi sati 2 kin hana shi kanki, da nan kuma shi ne zai yi ta yawo da sunan ki a gaban duk wadda za su iya Yi miki magana ki ji su duk hanyar da zai bi zai bi domin ki dawo gare shi ya Rika yin Jima'i da ke, sa'annan kullum sai ya ja miki Aya da Hadisi. Amma ke wata 4 babu Jima'i kuma yana gari, sa'annan lafiyar sa ƙlau yake ƙin yin Jima'i da ke, wannan Zalunci ne da rashin Tausayi da cutarwa wallahi.

Idan ma wani laifin kika yi masa kamata ya yi ya gaya miki Kuskuren ki ya ce ki gyara wannan shi ne rayuwar Aure, idan Bai da lafiya ne a fannin Jima'i sai ya tashi ya nema Magani, amma bawai ya ƙi haɗa Shimfida tare da ke ba har wata 4 babu hujjar komai kawai don mugunta da kuntatawa, akwai wadda ma ita tafi wata 7 Mijin ta bai sadu da ita kuma suna gari ɗaya kawai ya tare a gidan Amaryar sa ya bar uwar gidan wata 7 sai dai kawai ya yi ta tura mata Abinci kamar Rago ya ajiye, duk wannan Zalunci ne da rashin Tausayi wallahi Kuma sai Allah ya tambaye su akan wannan Zaluncin.

Bayar da Abinci da abin Sha gurin kwana Tufafin Sawa Magani idan babu lafiya duk wannan Haƙƙin ne daga cikin Haƙƙoƙin Aure, toh amma ba shi ne zai zama hujjar cewa wai idan Mace tana samun su ai shikenan Namiji sai ya ga damar saduwa da ita ko kula ta ba, ke ma Yar Adam ce kina da Rai kina da Jini a jikin ki sa'annan Allah ya Sanya Sha'awa gare ki, Shi ma Namiji ai bawai ya Auro ki ya kawo ki gidan sa domin kawai ya yi ta ciyar da ke kamar Rago bane, yana Dinka miki Tufafin Sawa ba, babbar manufar yin Auren shi a kanki shi ne yin Jima'i da ke ki haifa masa Yara masu Albarka, domin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ma ya ce ku Auri mata masu haihuwa domin na yi Alfahari da Yawan ku a ranar Alƙimaya, meya sa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) bai ce ku Auri mata masu girki ba? kawai su Rika dafa maku Abinci Kuna ci Kuna Sha ba sa'annan kuna ciyar da su ba? Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya hana Auren Macen da ba ta haihuwa, kenan Jima'i ba Karamin abu bane da Namiji zai tsaya ya yi wata 4 ko 7 wani ma shekara 1 suna gida 1 gari ɗaya lafiyar sa ƙlau itama lafiyar ta ƙlau amma ya ƙi kusantar ta wallahi wannan Zalunci ne da cutarwa Allah zai tambaye ku.

Sabida haka indai ba zai gyara ba kuma kin bi duk hanyar da za ki bi domin ya gyara ya ƙi toh idan hakan zai sa ki koma Saɓawa Allah ko biyawa kanki Bukata, ko yin Zina, ko yin Madigo toh gara Auren ya mutu Hakan shi ne Mafi Alkhairi gare rayuwar ki.

Idan kuma zai gyara shikenan sai ya gyara ki ci gaba da yin hakuri da shi a hakan, idan Waliyyin sa ya gagara kina iya samun wani Malami a Anguwar ku ko inda yake zuwa Sallar Jam'i in yana zuwa Sallar kenan, sai ki samu limamin gurin kiyi masa bayani ya kira shi ya yi masa Nasiha ya tunatar da shi in Sha Allah in an yi da ce zai gyara.

In Kuma ya ƙi gyarawa kina zuwa gaban Alkali masanin Shari'ar Musulunci ya raba Auren ku domin kin yi iya Bakin Kokarin ki kamar yadda Shari'ar Musulunci ya ce ayi kin yi amma ya ƙi, sabida haka ki samu Alkali kiyi masa Bayanin komai shi ya San hukuncin da zai yi.

Idan Kuma kina ganin za ki iya yin hakuri da juriya ki danne zuciyar ki sa'annan rashin Jima'i da ke ba zai taɓa sa ki koma yin Zina ko Madigo ko biyawa kanki Bukata ba, toh shikenan sai ki ci gaba da yin hakuri da juriya da danne zuciyar ki, kawai ki bar shi da Allah ki Rika samun Ladan ki shi kuma yana deban Zunubi, idan bai nema Gafarar ki kin yafe masa ba toh zai je gaban Allah ya yiwa Allah bayani Azabar Allah na jiran sa ko baya so.

Sa'annan ki Rika tashi tsakiyar dare, kina yin Nafila, kina gayawa Allah damuwarki ki Yawaita yin Addu'oi har Allah ya ganar da shi In Sha Allah, Allah zai ganar da shi.

Idan kin yi haƙuri, kin jure, kin danne zuciyar ki. Allah yana tare da ke fiye da tunanin ki, amma wannan dai zalunci ne da rashin tausayi da rashin sanin dokokin auren da haƙƙin mace. Idan Kuma ba za ki iya ba toh fa gara an rabu yin hakan zai fi Alkhairi gare ki Ina fatan kin gane? Allah ya Kara miki hakuri da juriya ya kawo miki mafita a rayuwar ki.

WALLAHU A'ALAMU

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments