Kamar yadda muka ga abin da Aiman al-Zawahiriy, shugaban Al-Qa'ida ya fada a kan Sayyid Qutub, cewa; littatafansa su ne tartsatsin farko na wutar tunanin Ta'addanci a Duniya, su suka tunzura matasa, har suka kafirta shugabanni da talakawa, har suka shiga ta'addanci a kan al'umma, to yau kuma muna tare da ABU MUS'AB AL-SURIY, daya daga cikin Jagororin Al-Qa'ida, don mu ji irin masayin Sayyid Qutub a wajensa, da kuma irin experience dinsa game da littatafansa, da irin tasirin da Fikrorinsa suka yi a kansa.
Waye Abu Mus'ab al-Suriy?
Asalin sunansa Mustapha
Abdulkadir. A farko Memba ne a wata kungiya mai suna "الطليعة
المقاتلة للإخوان المسلمين", wacce take karkashin Kungiyar
Ikhwan, wacce wani mai suna "Marwan Hadeed" ya kafa a Syria don yakar
Gomnati, wanda shi ma ya tasirantu ne da Fikirar Sayyid Qutub ta yakar Gomnati,
a lokacin karatunsa a Misra.
Kuma shi Abu Mus'ab ya zama
cikin masu horar da mayakan Kungiyar Ikhwan a Jordan, wanda daga baya ya rabu
da Kungiyar ta Ikhwan, har daga karshe ya tsallaka zuwa Afghanistan, a can ya
shiga Kungiyar Al-Qa'ida.
Shi Abu Mus'ab ana daukarsa
cikin wadanda suka tasirantu matuka da littatafan Sayyid Qutub da na Abdallah
Azzam. Wanda har ya zama cikin "Munazzirun" na kungiyoyin
ta'addancin, wanda har ya rubuta littatafai a kan haka.
Ga irin abin da ya fada a
kan Sayyid Qutub da Littatafansa:
((رائد
الفكر الجهادي في العصر الحديث بلا منازع والذي يعود لأفكاره ميلاد منهج التفكير
ونظريات الحركة في (التيار الجهادي المعاصر) كان بلا شك الأستاذ الشهيد المعلم
(سيد قطب) رحمه الله.
الذي
ابتدأ حياته أديبا شاعرا و باحثا ناقدا لامعا. وعاش نضوج الفكر خلال الحقبة
الصاخبة الحرجة من تاريخ مصر المعاصر خلال الأربعينات والخمسينات والستينات، وهي
زوال الملكية وثورة الضباط الأحرار. واحتلال فلسطين والعدوان على مصر. واحتك عن
قرب بالإخوان المسلمين وتأثر بحركتهم...
فقد
ضم كتابه الفريد (في ظلال القرآن) - وهو تفسير حركي لآيات القرآن الكريم في ضوء ما
نقله المفسرون من الآثار - خلاصة النظريات الحركية للفكر الجهادي المعاصر، وخلاصة
ما أراد سيد طرحه من مفاهيم. وكان كتابه (معالم في الطريق) هو الأهم على صغر حجمه،
وحوى خلاصة ذلك الفكر و طروحاته الجهادية الانقلابية الثورية. وكونت مكتبته
الواسعة - من الكتب الاخرى من مثل كتاب (خصائص التصور الإسلامي) و(هذا الدين)
و(جاهلية القرن العشرين) وغيره - منهجا متكاملا لفكر جهادي حركي معاصر يناسب تلك
المرحلة)).
دعوة
المقاومة الإسلامية العالمية (ص: 692)
"Jagoran tunanin Jihadi
a wannan zamani, ba tare da jayayya ba, wanda haifar da Manhajin Tunani da
Nazarin Harka a "Kungiyoyin Jihadin Zamani" yake komawa ga
Fikrorinsa, ba shakka ya kasance shi ne USTAZ SHAHIDI, MALAMI, "SAYYID
QUTUB" (RH).
Sayyid Qutub wanda ya fara
rayuwarsa a matsayin Masanin Adabin Larabci, Mawaki, Mai bincike, Mai naqadi
mai kwazo. Ya rayu cikin nunan tunani, a zamani na hayaniya mai wahala a
Tarihin Misra, a tsakanin 40s, 50s, 60s, lokacin gushewar tsarin mulki na sarauta,
da tawayen jami'an soja "Free Officers Movement (Egypt)", da mamaye
Falasdinu, da kuma ta'addanci a kan Misra. Sai kuma ya yi gogayya ta kusa da
Kungiyar Ikhwan, ya tasirantu da harkarsu (Gwagwarmayarsu)...
Hakika fitaccen Littafin
Sayyid Qutub wanda babu ya shi (Fi Zilalil Qur'ani) - Tafsiri ne na harka
(gwagwarmaya) ga Ayoyin Alkur'ani Mai girma, bisa hasken abin da ya ciro daga
Malaman Tafsiri na Athaar -, littafin ya tara "khulasa" na nazarorin
Gwagwarmaya na Fikrar Jihadi a wannan zamani. Da "khulasar" abin da
Sayyid ya so ya yada na ra'ayoyi. Kuma littafinsa "Ma'alim fid
Dareeq" ya kasance littafi mafi muhimmanci duk da karancinsa. Littafin ya
tattara "khulasa" ta waccar Fikra, da ra'ayoyinsa da littatafansa na
Jihadi, na juyin Mulki da Juyin juya hali. Littatafansa gaba daya - da sauran
littatafan irin su (خصائص التصور الإسلامي)
da (هذا الدين) da (جاهلية
القرن العشرين) - sai suka gina cikakken Manhaji ga
Fikrar Jihadi na Gwagwarmayar zamani, wanda ya dace da wancan lokaci)).
To jama'a, kun ji dai abin
da jagororin Kungiyoyin Ta'addancin suke fada, na yadda suke daukar Fikrorinsu
daga Sayyid Qutub a cikin littatafansa.
Saboda haka, ko shakka babu,
Fikrorin Sayyid Qutub su ne tushe na Kungiyoyin Ta'addanci a wannan zamani. Tun
daga kan Al-Qa'ida, Da'ish da ire - irensu, har zuwa kan Boko Haram.
Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
07 September, 2021
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.