Dan Jahamiyya ya ce: Ayoyi da Hadisan Siffofin Allah dukkansu "Majaz" ne ba Hakika ba.
Ahlus Sunna ya ce: Yaya za mu yi da wadannan Nassoshin Alkur'ani da Sunna da Maganganun Salaf masu yawa da suka zo suke tabbatar ma Allah wadannan Siffofi?
Dan Jahamiyya ya ce: Ai dole
a yi Tawilinsu, don a tsarkake Allah daga "Tajsimi" da
"Tashbihi".
Ahlus Sunna ya ce: Yanzu
kana nufin Zahirin Alkur'ani da Hadisan Annabi (saw) suna nuni ga
"Tajsimi" da "Tashbihi", alhali "Tajsimi" da
"Tashbihi" kafirci ne, don haka kenan Allah da Manzonsa a Alkur'ani
da Sunna sun bayyana mana abin da zahirinsa kafirci ne?
Dan Jahamiyya ya ce: Ai yin
magana da "Majaz" Uslubi ne na Fasahar Larabci, wato a yi magana da
lafazi amma ba zahirinsa ake nufi ba.
Ahlus Sunna ya ce: To amma
sai dai yawan wadannan Nassoshi, da yadda dalalarsu suka zo bisa nau'uka
daban-daban, yana tabbatarwa bisa yakini cewa; wadannan Siffofi tabbatattu ne
ga Allah Madaukakin Sarki, kuma Annabi (saw) da ya zo da su yana nufin a kudurce
zahirinsu.
Yanzu zai yiwu ya zama duka
Nassoshin da suka zo, a ce kowane Nassi a cikinsu Allah ba zahirin Nassin yake
nufi ba?
Zai yiwu a ce: abin da Allah
yake nufi shi ne ra'ayin masu kore wadannan Siffofi ga Allah, sai
tawile-tawilen da suka fada su zama su ne gaskiya, su ne abin da Allah yake
nufi?
Idan kuwa haka ne to dole a
samu wasu abubuwa guda uku munanana a tare da Allah wanda ya fadi Nassoshin ko
Annabi (saw) da ya zo da su:
1- Suka cikin ilimin wanda
ya fadi wadannan Nassoshi.
2- Suka cikin bayaninsa.
3- Suka cikin Nasiharsa.
Na farko: Wanda ya fadi
wadannan Nassoshi imma ya zama ya san cewa; gaskiya shi ne tawile-tawilen masu
kore Siffofin, ko kuma bai sani ba. To idan bai sani ba, wannan suka ne cikin
iliminsa.
Amma idan kuma ya san cewa:
gaskiya ita ce: kore Siffofin, da yin Tawilin Nassoshinsu, to imma ya zama zai
iya bayanin hakan wa mutane, ya tsarkake Allah daga "Tashbihi" da
"Tajsimi", ko kuma ya zama ba zai iya yin bayanin hakan ba. To idan
ba zai iya yin bayani ba, to hakan suka ne a fasaharsa da bayaninsa. Sai ya
zama 'Yan Falsafa da 'Yan Jahamiyya da Mu'utazila da yaransu Asha'ira sun fi
shi fasaha da iya bayani. Wannan kuwa kowa ya san cewa; maganar banza ce,
saboda Annabi (saw) ya fi kowa cikin mutane fasaha da iya bayanin gaskiya da
shiriya.
Amma idan kuma yana da ikon
yin bayani, amma sai ya ki yin bayani wa mutane, sai ya fada wa mutane sabanin
hakika, wato Allah ba shi da wadannan Siffofi, amma ya zo ya ce: Allah yana da
fiska, hannaye biyu, yana da ido, yana da kafa, kuma yana sama, yana saukowa
sama ta Duniya… to wannan suka ne cikin Nasiharsa, bai zama mai Nasiha ga
mutane ba. Alhali kowa ya san Annabi (saw) ya fi kowa cikin mutane Nasiha da
son shiriyar mutane. Shi ya sa Allah ya siffanta Manzanninsa da Nasiha da
bayani, Allah ya ce:
{وَمَا
أَرْسَلْنَا مِنْ رَسُولٍ إِلَّا بِلِسَانِ قَوْمِهِ لِيُبَيِّنَ لَهُمْ}
[إبراهيم: 4]
((Ba mu aiko wani Manzo ba
face da yaren mutanensa don ya yi musu bayani)).
Kuma ya ce:
{وَأَنْزَلْنَا
إِلَيْكَ الذِّكْرَ لِتُبَيِّنَ لِلنَّاسِ مَا نُزِّلَ إِلَيْهِمْ} [النحل: 44]
((Kuma mun saukar maka da
"Zikr" don ka yi bayani wa mutane abin da aka saukar gare su)).
Kuma Sahabbai sun yi shaidan
cewa lallai Annabi (saw) ya isar da dukkan Manzanci, ya yi musu bayanin komai
na Shiriya. Sun tabbatar ya yi musu Nasiha bai ha'ince su ya boye wani abu ba.
Babu wani alheri face ya yi musu bayaninsa, babu wani sharri face ya tsoratar
da su game da shi.
To idan tabbatar da zahirin
wadannan Nassoshin Siffofin Allah sharri ne da bata da kafirci me ya sa Annabi
(saw) bai bayyana wa al'ummarsa ya tsoratar da su a kan yin hakan ba?
To in dai Annabawa da
Manzanni suna da ilimi, kuma sun iya bayani, kuma su masu Nasiha ne ga
mutanensu, masu so musu alheri da shiriya ne, ta yaya za su bar mutane cikin
duhu da bata, su zo da Nassoshi masu nuna cewa: Allah yana da fiska, yana da
hannaye biyu, yana da kafa, yana da Sura da sauransu, alhali kuma Allah ba shi
da wadannan Siffofi, kuma tabbatar masa su "Tajsimi" da
"Tashbihi" ne?
Kuma idan Tawile-tawilen
Asha'ira su ne gaskiya, me ya sa Annabi (saw) ko Sahabbansa ba su yi mana
bayani ba, su ce: ga gaskiyan abin da ake nufi da Nassoshin?
Yanzu zai yiwu su wadannan
Malaman Asha'ira su zama sun fi Manzon Allah (saw) sanin Allah kenan, ko sun fi
shi iya bayanin gaskiya, ko sun fi shi son tsarkake Allah, sun fi shi son
shiryar da mutane, shi ya sa shi ya bai bayyana ba, su kuma suka bayyana?!
Dan Jahamiyya ya ce: Ai kai
Basalafe ne Mujassimi, ba za ka fahimci gaskiya ba, saboda Ibnu Taimiyya ya
bata maka tunani.
Ahlus Sunna ya ce: Ina binka
bashi fa Malam, dole ka zo ka ba ni amsoshin tambayoyina.
Dan Jahamiyya ya ce: Babu
wata amsa da zan ba ka, tafi ka ba ni wuri Mujassimi kawai.
Ahlus Sunna ya ce: Allah ya
shirye ka, ya sa ka dawo bin Alkur'ani da Sunna da Mazhabar magabata, ka bar
Mazhabar 'Yan Falsafa da Jahamiyya da yaransu; Mu'utazila da Asha'ira.
Ma'assalama..
Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
09 September, 2022
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.