An ciro daga littafin:
BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)
Na
Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU
A
fannin ƙwadagon
kan intanet da ya shafi kimiyyar harshe, jarabawa nau’in aiki ne wanda ya shafi
aunawa da sanya maki ga ayyukan da waɗansu suka yi. Akan samu lokutan da kai
tsaye akan ba da aikin fassara domin jarabawa, misali idan za a ɗauki sababbin
ma’aikata Hausawa.[1] Yayin da mai fassara ya kammala fassara kalmomin jarabawa da aka ba
shi, to za a ba wa ƙwararre wanda zai duba sannan ya sanya maki.
A
waɗansu lokuta kuwa, ana iya ɗauko ɓangaren wani aiki mai yawa da aka gudanar a
tura shi domin dubawa da sanya maki. Wani abin lura shi ne, jarabawa a wannan
fannin ya bambanta da fannonin ilimi da matakan karatu da ake da su. Dalili
kuwa shi ne, a mafi yawan lokuta, dole ne mutum ya samu kashi casa’in da bakwai
a cikin ɗari (97%) kafin ya ci jarabawar. Da zarar ya yi ƙasa da haka, to za a ɗauke
shi a matsayin mai rauni.[2] Ƙa’idojin sun ci karo da
faɗin Hausawa cewa: “Ɗan’adam ajizi ne” ko “Ɗan’adam tara yake bai cika
goma ba.” Wani abin da ya ƙara bambanta su shi ne jerin ƙa’idojin abubuwan da ake
dubawa yayin jarabawar. Gudanar da aikin jarabawa yana iya kasancewa a kan wata
manhajar intanet, ko kuma a kan fayil ɗin Excel. A duba misali a cikin hoton da
yake ƙasa:
Hoto Na 4.5: Aikin jarabawa da aka turo cikin harshen Hausa
Madogara:
Saƙon imel daga kamfanin
fassara na ByLanguages
A
cikin wannan saƙon imel da aka turo, za a tarar da cewa kamfanin sun yi
jarabawa ne a sabon mai aikin fassara zuwa harshen Hausa. An turo fassarar
Hausar da ya yi a matsayin aiki domin a duba a saka mata maki.
Aikin
karatun bita yana matuƙar kama da na ‘gyaran rubutu.’ Bambancinsu shi ne,
karatun bita mataki ne da yake gaba da na gyaran rubutu. Ana yin sa ne bayan an
kammala gyara rubutu. A wannan gaɓar, abin da ake buƙata kawai shi ne dubawa da
tabbatar da babu tuntuɓen alƙalami ko ɗan jirkicewar tsarin rubutu. Akan daidaita
wuraren da kwamfuta take jirkita rubutun Hausa, misali “book” a matsayin
“boko.”
Kamfanin
Terra Translations sun bayyana cewa, tsarin fassara yana iya ƙunsar mataki biyu kawai
wato ‘fassara’ da ‘gyaran rubutu.’ Yana kuma iya ƙunsar matakai uku (3), wato
‘fassara’ da ‘gyaran rubutu’ da kuma ‘karatun bita.’ (Marco, 2022 SL. 1).
Karatun
bita ya kasance ɗaya daga cikin ƙwadagon kan intanet na ɓangaren kimiyyar harshe da suke
da ƙalubale
mai yawa. Dalili kuwa shi ne, akwai masu karɓar ayyukan Hausa da dama a kan
intanet waɗanda ba ƙwararru ba ne. Da yawa daga cikinsu ba ko Hausawa ba ne.
A sakamakon haka, mai karatun bita zai iya cin karo da ayyukan da suke tattare
da ɗimbin matsaloli. Matsalolin suna iya haɗawa da ƙa’idojin rubutu da ma
nahawun harshen kansa.[3]
Ƙirƙirar Rubutu (Content Creation)
Rubutu
ba ya yin kansa. Duk wani rubutu da aka gani a kan intanet (kafafen intanet) ko
a fuskar na’ura ko allunan tallace-tallace (da sauransu), to rubuta su aka yi.
Fagen ƙirƙirar rubutu yana da matuƙar faɗi. Kasuwarsa ta daɗe
tana ci a duniya. A matakin duniya, duk wani babban kamfani da zai iya zuwa ƙwaƙwalwar mutum, to lallai
wannan kamfani yana aiki da masu ƙirƙirar rubutu. Haƙƙinsu ne su samar da:
a. Bayanin
kamfani cikin salo mai jan hankali,
b. Tallace-tallacen
hajojin kamfanoni,
c. Bayanan
yadda ake sarrafawa ko amfani da kayayyakin kamfani,
d. Samar
da rubuce-rubucen da za su ɗaga darajarsu da ƙarfinsu a duniyar intanet
(online ranking), da makamantan waɗannan.
Ba
sosai ake samun aikin ƙirƙirar rubutun Hausa ba a kan intanet. Dalili kuwa shi ne,
yawancin kamfanoni da ma’aikatu da hukumomi suna bayar da ire-iren ayyukan nan
ne cikin harshen Ingilishi, ko wani babban harshen ƙasar da suke. Yayin da ake
son samar da na Hausa, to sukan bayar da aikin fassara ne, ko kuma fassara da ƙirƙira.[4]
Kamfanin Speak Your Language (SYL) sun bayyana ‘taƙaita kashe kuɗi’ a matsayin
ɗaya daga cikin amfanin fassara rubutu a maimakon ƙirƙirar sabo (Speak Your
Language (SYL), 2023 para 8-10).
[1] Yawanci kamfanonin ƙwadagon kan intanet da suka
shafi kimiyyar harshe sukan yi jarabawa kafin fara aiki da ‘yan ƙwadago.
[2] Ɗaya daga cikin ƙalubalen ayyukan ƙwadagon kan intanet da suka
shafi kimiyyar harshe shi ne, ana iya cewa tsarin bai yarda da batun “ɗan’adam
ajizi ne” ba.
[3] Wannan babban ƙalubale ne ga Hausawa,
musamman manazarta harshen Hausa. Idan ba su tashi domin amfani da damarmakin
da ake da su na ayyukan da suka shafi Hausa a kan intanet ba, wasu na daban za
su ci gaba da cin gajiyar damarmakin. Abu mafi muni shi ne samar da gurɓatattun
bayanai dangane da harshen.
[4] A baya an tattauna waɗannan a ƙarƙashin 4.1.1.2 da 4.1.1.4.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.