4.4.1
Kasuwannin Hadahadar Kuɗin Intanet
Kamar yadda ake da kasuwannin hadahadar
nau’o’in kayayyaki daban-daban a duniyar zahiri, haka abin yake a duniyar
intanet. A intanet, akwai manyan kasuwannin hadahadar kuɗin intanet. Kasuwannin
suna da tsarinsu da ƙa’idojinsu. Sukan kasance
cikin na’urori a tsarin kafafen intanet da manhajoji.
Yawanci akan gina su a tsarin da ake kira
“mutum zuwa mutum” (Peer-to-peer (P2P)). Wannan tsari ne da yake ba wa masu
kasuwanci damar gudanar da cinikayya kai tsaye a tsakaninsu. Bugu da ƙari, ana killacewa da adana kuɗaɗe da kadarorin ‘yan
kasuwa tare da ba su cikakken tsaro ta hanyar amfani da fasahar da ake kira bulokcen
(blockchain).
Fasahar Bulokcen tana taka rawa sosai a
fannin gudanar da harƙallolin kuɗi cikin tsaro
tare da adana tarihinsu. Tsari ne wanda ya kauce wa takunkumin bi ta hannun
wasu (misali bankuna) wanda yake gudana cikin sigar ƙeƙe-da-ƙeƙe tsakanin ‘yan kasuwa da
kwastomomi. Ya kuma kasance ƙashin bayan hadahadar
kuɗaɗen intenet, waɗanda su ma alƙibla ce da kasuwancin
duniya ta dosa a yau.[1]
Fitattun kasuwannin hadahadar kuɗaɗen intanet
sun haɗa da:
a. Binance – (https://www.binance.com/)
b. Crypto – (https://crypto.com/)
c. Gate – (https://www.gate.io/)
d. KUCOIN – (https://www.kucoin.com/)
e. OKX – (https://www.okx.com/)
f. Paxful – (https://www.paxful.com)
4.4.2
Nau’o’in Hadahadar Kuɗin Intanet
Akwai manyan nau’o’in hadahadar kuɗaɗen
intanet guda biyu waɗanda Hausawa sukan shiga. Su ne (a) masu uwar kuɗi da (b)
marasa uwar kuɗi. An samar da waɗannan rabe-rabe ta la’akari da amfani ko
rashin amfani da uwar kuɗi a cikin kasuwancin. A taƙaice ke nan, akwai waɗanda suke buƙatar uwar kuɗi kafin gudanar da su. Akwai kuma waɗanda ba
sa buƙata. A ƙasa an kawo bayanai game da
waɗannan nau’o’in hadahadar kuɗaɗen intanet.
Wannan nau’i ne na hadahadar kuɗin intanet
wanda yake buƙatar uwar kuɗi kafin gudanarwa. Yana matuƙar buƙatar ƙwarewa da naƙaltar yanayin kasuwa. Yana
iya zuwa da babbar hasara yayin da aka yi sake ko aka saɓa ƙa’idojin hadahadar. Wani abu kuma shi ne, dole ne mai
gudanar da irin wannan nau’in hadahadar kuɗin intanet ya kasance yana bibiyar
sauye-sauyen da suke faruwa a kasuwanni. Dole ne kuma ya riƙa sabunta iliminsa game da sababbin ƙa’idoji da matakan hadahadar, wanda hakan yakan kasance ƙalubale ga Hausawa masu yawa.[2]
Shi ma wannan nau’in hadahadar kuɗaɗen
intanet ya rabu zuwa gida biyu kamar haka:
(a) Kasuwanci (Trading) (Proof
of Work (PoW)
(b) Kulle Kuɗi (Farming/Yield
Farming/Liquidity Farming/staking (proof of stake PoS))
4.4.2.1.1 Kasuwanci (Trading)
An tattauna ma’anar kasuwanci a ƙarƙashin 2.1 a babi na
biyu. Ta la’akari da bayanan Tanko (2000 sh. 35) da Gummi (2014 sh. 77) da
Abdullahi (2021 sh. 2), ana iya cewa kasuwancin kuɗin intanet fasaha ne
na saye da sayarwa ko musanyen kuɗaɗen intanet domin samun riba, ta hanyar bin
matakai da dabarun da suka haɗa da gano wurin sayen kaya cikin sauƙin farashi da amfani da dabaru da ilimin sanin kasuwa da
lokacin da sayar da hajar zai fi kawo riba.
Kasuwancin kuɗaɗen intanet ya shafi saye da
sayar da kuɗaɗen tamkar dai yadda Hausawa da sauran al’ummomi suke gudanar da
kasuwancin canjin kuɗaɗen ƙasashe a duniyar zahiri.
Wani abin burgewa shi ne, ya zuwa yanzu, kuɗaɗen intanet an yi su ne kawai
domin su kasance a duniyar intanet. Ba a kallon su ko a taɓa su. Haka kuma,
kasuwannin da ake kasuwancinsu duk a kafafen intanet suke. Babu buƙatar a je kasuwa a duniyar zahiri domin gudanar da
kasuwancin.
A irin wannan kasuwancin ne za a samu
Bahaushe ya je kasuwar da ba a kallon ta a zahiri (kasuwar kan intanet), ya yi
ciniki tare da mutumin da bai san shi ba, kuma bai san a inda yake ba a duniya,
sannan ya sayi abin da ba zai taɓa kallon sa a duniyar zahiri ba ballantana ya
taɓa shi (kuɗi ko kadarar intanet).
4.4.2.1.1.1 Ire-Iren
Kasuwancin Kuɗin
Intanet
Kasuwancin kuɗin intanet bai kasance cikin
salo ku siga ɗaya ba. Yana da bambance-bambance masu yawa. Waɗansu daga cikin
bambance-bambancen sun samu ne sakamakon nau’in jarin da ‘yan kasuwan suke
amfani da su. Wasu kuwa sun samu ne sakamakon bambanci tsakanin kasuwannin.
Haka kuma, akan samu bambanci ta fuskar dabarar gudanar da kasuwancin, kamar
abin da ya shafi lokacin sayen kaya da lokacin sayarwa.
Ana iya raba kasuwancin kuɗin intanet waɗanda
Hausawa sukan shiga zuwa manyan rukunoni guda huɗu kamar haka:
a. Kasuwancin kuɗi-hannu
b. Bashi mai ‘yanci
c. Bashi mai takunkumi
d. Dauwamammiyar kadarar
intanet
Kowanne daga cikin waɗannan yana da tsarinsa
da ƙa’idojin gudanar da shi. Haka kuma, Bahaushe
ɗankasuwa yana iya gudanar da nau’o’in kasuwanci sama da ɗaya. Hasali ma, a
rana ɗaya mutum yana iya ziyartar kasuwannin hadahadar kuɗin intanet
daban-daban domin gudanar da kasuwanci.
A ƙasa an kawo bayanan
waɗannan nau’o’in kasuwancin kuɗin intanet.
4.4.2.1.1.1.1 Kasuwancin
Kuɗi-Hanu
(Spot Trading)
Kamar yadda sunan ya nuna, wannan nau’in
kasuwancin kuɗin intanet ne wanda yake buƙatar jari a hannu yayin
gudanarwa. Yana da tsari irin wanda Hausawa suke yi wa kirari da: “Hannun
kuturu da makaho.” Zubinsa yana da matuƙar kama da na saye da sayar
da hajoji a duniyar zahiri.
Wani ƙarin abin sha’awa dangane
da kasuwancin kuɗin intanet na kuɗi-hannu shi ne, mai sayarwa yana da
damarmakin saita akawun ɗinsa ta yadda akawun ɗin zai gudanar da abubuwa da
dama ko da mai shi ba ya kan intanet a wannan lokaci. Misalan abubuwan da zai
iya saitawa sun haɗa da:
1. Saita Farashin Saye: Ɗankasuwa yana iya sanya kuɗi a lalitar akawun ɗinsa
sannan ya saita akawun ɗin da cewa, da zarar nau’in kuɗin intanet kaza (misali
Bitcoin) ya sauƙo zuwa farashi kaza (misali naira miliyan
ashirin da tara), to ya saya masa. Yayin da aka yi wannan saitin, da zarar
farashin Bitcoin ya sauƙo zuwa wannan farashi, to
kwamfuta za ta saya wa ɗankasuwan adadin Bitcoin da ya saita.
2. Saita Farashin Sayarwa: Ɗankasuwa yana iya saita cewa, da zarar farashin kuɗin abu
kaza (misali Tether) ya kai kaza (misali miliyan uku) to kwamfuta ta sayar masa
kai tsaye. Ko da ba ya kan intanet a wannan lokaci, kwamfuta za ta sayar idan
aka cimma wannan farashi.
Bambancin wannan nau’in kasuwancin kuɗin
intanet da sauran shi ne, kuɗin da ɗankasuwa yake da shi, shi ne kaɗai adadin
kadarar intanet da zai iya saya. A ɓangare ɗaya kuwa, iya kaɗarar intanet da
yake da ita, ita kaɗai zai iya sayarwa.
Yana da kyau a fahimci cewa, kasuwannin
hadahadar kuɗaɗen intanet akan samar musu tsaro mai aminci domin bayar da
kariya ga ‘yankasuwa. Duk Bahaushen da aka damfara ko aka yi wa sata, to haƙiƙa ya yi sakaci ne, ko kuma
ya shiga harkar ba tare da wadataccen ilimi ba. A ƙasa an kawo misalan matakan da za a iya cin karo da su
yayin gudanar da wata harƙallar kasuwancin kuɗin
intanet a kasuwar duniyar baɗini:
1. Mai sayar da kuɗin intanet
zai baje hajarsa tare da zayyana farashin hajar. A ɓangare ɗaya kuwa, zai
zayyana nau’o’in hanyoyin da za a iya biyansa.[3]
2. Mai sayen kuɗin intanet zai
duba farashin da ya gamsu da shi, sannan ya tura buƙatar ƙulla harƙallar kasuwanci.
3. Da zarar ya tura adadin
kaya da yake so, sannan su biyun suka nuna cewa ciniki ya faɗa, to na’urar
kasuwar za ta kulle adadin hajar da ake buƙata daga akawun ɗin mai hajar tun kafin a tura masa kuɗin
kayan.[4]
4. Mai sayen kaya zai tura
kuɗi tare da shaidar biya cikin hanyoyi da matakan da suka keɓanta ga kasuwar.
Daga nan zai danna alamar cewa ya biya kuɗin kaya a jikin harƙallar da suka ƙulla.
5. Mai sayar da kaya zai duba
ya tabbatar da kuɗi sun cika, sannan ya danna alamar bayar da tabbacin cewa
lallai an biya shi.
6. Masu kasuwar za su tura
kaya (wanda suka riga suka kulle kamar yadda aka zayyana a sama a lamba ta 3)
zuwa ga akawun ɗin wanda ya saya bayan sun cire kuɗin aikinsu (wanda yake
daidai da kuɗin kasuwa a duniyar zahiri).
Idan wata jayayya ta shigo dangane da wannan
harƙallar kasuwanci, to jami’in kasuwar zai buɗe
tattaunawa ta musamman. Zauren zai haɗa jami’in da kuma masu taƙaddamar, a inda kowa zai gabatar da hujjojinsa. Aikata
rashin gaskiya a kasuwannin hadahadar kuɗaɗen intanet yana kai ga an kulle
akawun ɗin mutum (mai aikata rashin gaskiyar). Hakan zai iya janyo masa babbar
hasara. Wannan ma ƙalubale ne ga Hausawa
kasancewar cikin harshen Ingilishi ake gudanarwa.
4.4.2.1.1.1.2 Kasuwancin
Bashi Mai ‘Yanci (Margin Trading)
Wannan ɗaya ne daga nau’o’in kasuwancin kuɗin
intanet da Hausawa sukan shiga wanda yake buƙatar uwar kuɗi. Bugu da ƙari, ɗan kasuwa yana da damar samun bashin kuɗi domin
gudanar da kasuwanci. Wannan nau’in bashi ya kasance mai ‘yanci ne saboda wanda
ya karɓe shi yana da ‘yancin gudanar da kasuwancin da ya ga dama, kuma a
lokacin da ya ga dama.
Kasuwa ce take ba da wannan bashi. Kowace
kasuwar hadahadar kuɗin intanet tana da tsarinta da ƙa’idojinta na bayar da irin wannan bashin.[5] Wata muhimmiyar ƙa’ida ita ce, dole ne ya kasance ɗankasuwa yana da
waɗansu kuɗaɗe a cikin lalitar akawun ɗinsa kafin a ba shi bashi. Bayan wannan,
akan yi la’akari da tarihin yanayin hulɗar kasuwancin ɗankasuwa wajen ba shi
bashi. A kasuwar Binance, ɗankasuwa yana iya samun aron kuɗin da ya kai kaso
ɗari da ashirin da biyar (125%) na uwar kuɗin da yake da shi.
Da farko ɗankasuwa zai sanya kuɗaɗensa a
matsayin kafin alƙalami (security deposit). Daga nan za a ara
masa kuɗin da zai iya kasuwanci da shi a cikin kasuwar. Wannan zai ba shi damar
samun riba mai kauri. Misali, wanda ya shiga da naira dubu ɗari (N100,000)
kaɗai, idan ya ci ribar 10%, to ribar za ta kasance dubu goma (N10,000) kawai.
Idan kuwa ya shiga da dubu ɗari biyu da ashirin da biyar (N225,000)[6] ne, to ribar 10% ɗinsa za ta kasance dubu
ashirin da biyu da ɗari biyar (N22,500).
Ɗankasuwan da ya karɓi
wannan nau’in bashin kuɗi yana da damar gudanar da kasuwanci iri biyu. Sun
kasance kamar haka:
A. Saya (Long Position
(Buying)):
Yayin da mutum ya sayi kadarar intanet da kuɗin da aka ba shi rance, sai
darajar kaya ya tashi, to zai sayar ya samu riba. Ɗankasuwa yana iya karɓar bashi a daidai lokacin da alƙaluma suka nuna cewa kayan da zai saya ya gama araha,
sannan zai fara tashi ba da jimawa ba.[7]
B. Sayarwa (Short Position
(Selling)):
Ana irin wannan tsarin ne yayin da ake tunanin farashi zai yi ƙasa. Yayin da aka ba wa ɗankasuwa kuɗin intanet (misali
Dogs biyu (2)), to zai sayar. Da zarar farashi ya yi ƙasa (kamar yadda ya yi hasashe), hakan na nufin zai iya
sayen kuɗin intanet ɗin da suka fi adadin waɗanda aka ba shi bashi. Da zarar ya
saye su, zai mayar da waɗanda ya karɓi bashi, shi kuma ya riƙe sauran.[8]
Babban ƙalubalen wannan wannan nau’in
kasuwanci shi ne, da zarar hasara ta samu wanda ya karɓi bashi yadda har ta kai
abin da aka yi hasarar ya kai adadin kafin alƙalamin da ya sanya, to kai tsaye na’urar masu kasuwar za
ta sayar da wannan kadara ta mayar da kuɗinta. Shi kuwa zai tashi ba shi da
tsuntsu ba shi da tarko. Misali a nan shi ne, idan ɗan kasuwa ya sanya
kafin alƙalami na naira ɗari (₦100), sai aka ba shi
kashi ɗari da ashirin da biyar (125%), to zai shiga kasuwa da naira ɗari biyu
da ashirin da biyar ke nan (₦225). Idan har farashin abin da ya saya ya faɗi da
darajar da ta kai ta naira ɗari (₦100), to hakan yana nufin kafin alƙalamin da ya sanya ya tafi, saura bashin da aka ba shi
kawai. A daidai wannan lokaci, na’ura za ta sayar da kayan nan take. Kuɗin da
za a sayar ke nan zai kama naira ɗari da ashirin da biyar (₦125), wanda shi ne
daidai kuɗin da aka ba shi bashi. Don haka masu kasuwa za su ɗauki abinsu. Shi
kuma ya tashi a tutar babu ke nan.
Ɗaukar bashi da yawa yana
tafe da riba da kuma haɗari. Idan aka samu riba, to za a sha romo. Yayin da
faɗuwa ta auku kuwa, tana iya kai ga laƙume kafin alƙalami da mutum ya sanya. Ya kasance tamkar nau’o’in
kasuwancin da Hausawa suke yi wa laƙabi da “gwari.”
4.4.2.1.1.1.3 Kasuwancin
Bashi Mai Takunkumi (Futures Trading)
Wannan ma nau’in kasuwanci ne da ya ƙunshi karɓar bashi. Yana matuƙar kama da wanda aka tattauna a baya a ƙarƙashin 4.4.2.1.1.1.2, wato Bashi
Mai ‘Yanci. Babban bambancinsu shi ne, ɗankasuwar da ya karɓi nau’in wancan
bashin yana da damar gudanar da kasuwanci a duk lokacin da ya so. Shi kuwa
wannan nau’in bashi, akwai ƙa’idar lokacin da za a iya
gudanar da kasuwancin.
Bashi Mai Takunkumi nau’in bashi ne da ake
karɓa domin a aiwatar da wani taƙamaiman kasuwanci a wani
takamaimai lokaci. Ɗankasuwa zai yi hasashe ne
bisa ilimin sauyin farashin kasuwa. Idan sayen kaya zai yi ya ajiye domin
sayarwa a nan gaba, zai saita wani lokaci a wata rana da yake hasashen zuwa
lokacin farashin zai yi daraja sosai. Da zarar lokacin ya yi, na’ura za ta sayar
da kayan ko da ɗankasuwan ba ya kan intanet. Idan sayan kaya zai yi kuwa, yana
iya saita lokacin da yake hasashen farashi zai sauƙa sosai. Da zarar lokaci ya yi, to na’ura za ta saya
masa. Daga nan sai batun sayarwa a lokacin da farashi ya sake tashi.[9]
Wannan ma babban ƙalubale ne ga Hausawa. Za a iya lura da cewa, akwai
kasada sosai a cikin wannan nau’in bashi. Waɗanda za su iya cin gajiyarsa kawai
su ne waɗanda suka naƙalci alƙaluman da suke haifar da hawa da sauƙar farashin kayayyaki a kasuwannin duniyar kuɗin intanet.
4.4.2.1.1.1.4 Kasuwancin
Dauwamammiyar Kadarar Intanet (NFT Trading)
NFT[10] nau’in kadarar kan intanet ce da ta bambanta
da sauran kadarorin ko kuɗaɗen kan intanet. Tsarinta daban ne kasancewar kowace
guda tana cin gashin kanta ne. Ba a iya sauya ta da wani nau’in kuɗin intanet
ko kadarar intanet. Wani abu kuma da NFT shi ne, kowanne nau’in kadara guda ɗaya
ake samu. Ba kamar sauran nau’o’in kadarorin intanet ba ne da ake iya samun
nau’i ɗaya cikin adadi mai yawa. Misali, binciken Lee (2024) ya tabbatar da
cewa, an tanadi kimanin Pi da suka kai biliyan ɗari (biliyan 100).
Dauwamammiyar Kadarar Intanet tana zuwa cikin
sigogin da suka haɗa da:
a. Zane
b. Tsofaffin kayayyaki
c. Gidajen duniyar intanet
d. Kayayykin cikin wasannin
kan intanet
e. Abubuwan duniyar zahiri da
duniyar intanet
Ana amfani da kuɗin intanet wajen saye da
sayar da su. Hausawa ba su cika gudanar da wannan nau’in kasuwanci ba. Bugu da ƙari, ya fara zama tsohon yayi kasancewar hadahadar
kuɗaɗen intanet ta fara ɓoye shi. Duk da haka, dama ce ga Hausawa wacce za su
iya shiga a dama da su.[11] Ya sayar da shi a cikin watan Maris na
shekarar 2021.[12]
Hoto Na 4.15: Dauwamammiyar Kadarar
Intanet
Madogara: Conti & John (2023)
Za a iya lura da cewa, hoto na 4.15 da aka
kawo a sama, zane ne kawai na wani abu da yake kama da biri. Wani abin burgewa
da mamaki shi ne yadda kadarorin NFT suke da tsada. Akwai wanda ya sayar da
hoton kakansa a kan kuɗin intanet da darajarsa ta kai miliyan ɗaya da dubu ɗari
biyar a kuɗin Nijeriya (₦1,500,000).[13] Jack Dorsey wanda ya kasance shugaban
kamfanin Twitter (Twitter, Inc) daga shekara ta 2015 zuwa 2021, ya sayar da
rubutunsa na farko a kan kafar Twitter a matsayin Dauwamammiyar Kadarar
Intanet. Ya sayar a kan farashin dalar Amurka miliyan biyu da dubu ɗari tara
($2,900,000).[14]
Hoto Na 4.16: Dauwamammiyar Kadarar
Intanet Daga Rubutun Jack Dorsey a Kan Kafar Twitter
Madogara: Locke (2021)
Kamar dai kasuwancin duniyar zahiri, akwai buƙatar Hausawa su naƙalci dabarun kasuwanci
yayin fara gudanar da hadahadar kuɗaɗen duniyar intanet. Hasali ma, ana buƙatar bincike da karance-karance dangane da hadahadar
kuɗaɗen duniyar intanet sama da yadda ake buƙata a kasuwannin duniyar zahiri. Hakan ya zama wajibi
kasancewar yadda a kullum ake samun sauye-sauyen ƙa’idojin gudanar da kasuwancin kuɗaɗen intanet.
Yana da matuƙar fa’ida Bahaushe ya nazarci ciki da wajen hulɗar, ba
wai ya faɗa mata ido rufe ba. Yawancin Hausawa waɗanda suke kukan tafka hasara
sun shiga ne ba tare da wani ilimi ba, wato abin da Hausawa sukan ce “kama
ra’aitan nasa.” A koyaushe masu hadahadar kuɗin intanet sukan
amsa tambayoyi makamantan waɗannan kafin su faɗa kasuwanci:
a. Shin wane nau’in kaya zan
saya?
b. Shin yanzu ne ya dace in
sayi kaya la’akari da alƙaluman kasuwa?
c. Shin yanzu ne ya dace in
sayar da kaya la’akari da alƙaluman kasuwa?
d. Shin wane nau’in kasuwanci
ya kamata in yi?
e. Shin a wace kasuwa ya
kamata in yi hulɗar kasuwancin?
f. Shin wane farashi zan saka
ko a kan wane farashi zan nemi kaya?
g. Shin ta wace hanyar biyan
kuɗi za a biya ni, ko kuma ta wace hanyar biyan kuɗi zan biya?
Akwai wasu muhimman dabarun hadahadar kuɗaɗen
intanet. Su ne kamar haka:
1. Kasuwancin Fakafaka (Scalping)
Wannan dabarar kasuwancin kuɗin intanet ce a
inda ɗan kasuwa yake sayen kaya sannan ya sayar cikin ƙanƙanin lokaci. Nau’in
kasuwanci ne da Hausawa suke yi wa kirari da “sha yanzu, magani yanzu.” Mai
gudanar da wannan nau’in kasuwanci yana bin ƙaramar riba tare da guje wa yin hasara. Kwatakwata wannan
nau’in kasuwancin ba ya haura mintuna kafin a kammala shi. Ma’ana dai, ana
farawa ne sannan a kammala shi cikin mintuna ƙalilan.[15]
2. Kasuwancin Rana (Day Trading)
Kamar yadda sunan ya nuna, dabarar kasuwancin
kuɗin intanet ce da ake farawa sannan a kammala cikin rana ɗaya. Ɗankasuwa yana iya sayen kaya da safe, sannan ya yi ta
bibiyar tashin farashi. Zuwa dare (ko kafin nan) zai iya sayarwa musamman
saboda tsoron kada kasuwa ta juye cikin dare ya samu hasara alhali ba ya kusa
(yana bacci). Yawanci ana farawa da kammala wannan nau’in kasuwanci cikin
mintuna zuwa awowi kaɗan.
3. Kasuwancin Bin Hawa Da Sauƙar Farashi (Swing Trading)
Wannan dabarar kasuwanci ce da ake amfani da ƙididdigar sauƙa da tashin farashi a
kasuwanni daga kwamfuta. Akan gano lokacin da ya fi dacewa a shiga kasuwa ko a
fita ta la’akari da alƙaluman giraf daga kwamfutar
da take karantar motsin hawa da sauƙan farashin kayayyaki.
Yawanci akan ɗauki ‘yan kwanaki kafin a kammala wannan nau’in kasuwanci (daga
lokacin da aka sayi kaya zuwa lokacin da za a sayar).
Hoto Na 4.17: Giraf Ɗin Hawa Da Sauƙar Farashi a Kasuwannin
Kuɗaɗen Intanet
Madogara: Mitchell (2024)
A hoto na 4.17 da yake sama, za a iya lura da
alamar hawa da sauƙar farashi. Wannan shi ne
yake nuna Koriyar Kasuwa da kuma Jar Kasuwa (kamar yadda aka
bayyana a ƙarƙashin 4.4.2.1.1.1.2).
Fahimtar yadda ake amfani da alamomi da alƙaluman yana buƙatar ilimi na musamman.
4. Kasuwancin Doguwar Ajiya (Position
Trading)
Wannan dabara ce ta kasuwancin kuɗin intanet
inda ɗankasuwa yake ajiye kadarar da ya saya na wani lokaci mai tsawo (misali
watanni ko shekaru) kafin sayarwa. Lamarin yana kama da yadda Hausawa sukan
sayi wata kadara su ajiye ta na tsawon lokaci a duniyar zahiri.
5. Kasuwancin Bin Kasuwanni (Arbitrage
Trading)
Wannan nau’i ne na dabarar kasuwancin kuɗin
intanet wadda ta shafi sayen kadara a wata kasuwa tare da sayar da ita a wata
kasuwa ta daban domin samun riba. Lamarin yana kama da yadda Hausawa sukan yi
fatauci ko gudanar da kasuwancin bin kasuwanni a duniyar zahiri. Mai gudanar da
wannan nau’in kasuwanci zai yi la’akari da bambancin farashin da yake tsakanin
kasuwanni. Daga nan sai ya sayi kadara a kasuwar da take da sauƙin farashi sannan ya yi saurin kai ta kasuwar da take da
tsada domin sayar da ita. Masu kasuwancin kuɗi a hannu (spot trading) sun fi
amfani da wannan dabarar kasuwanci.
4.4.2.1.2 Noman Kuɗi (Farming)[16]
Ana yi wa wannan nau’in hadahadar kuɗin
intanet taken “Shaidar Bayar Da Gudummawa” wato “Proof of Stake (PoS)” a
Ingilishi. Kalmar ‘farming’ tana da fassarar ‘noma’ a harshen
Hausa. Abin da yake faruwa a irin wannan hadahadar kuɗin intanet makamancin
wanda yake faruwa ne a harkar noma a duniyar zahiri. Masu noman kuɗi a kan
intanet sukan kulle waɗansu kuɗaɗe na tsawon wani lokaci tare da hasashen cewa
zuwa lokacin za su samu riba a kan kuɗaɗen da suka kulle. Abin ya yi kama da yadda
Hausawa suke shuka amfanin gona kaɗan sannan su girbi amfani mai yawa. A. Sani
(keɓantacciyar tattaunawa, 7 ga watan Nuwamba 2024) ya bayar da misalan noman
kuɗi aka dama da Hausawa kamar haka:
a. Cetus (https://www.cetus.zone)
b. OKX Yield Aggregator (https://www.okx.com)
c. PancakeSwap (https://pancakeswap.finance)
d. Raydium (https://raydium.io)
e. SUN.io (https://sun.io)
f. Uniswap (https://uniswap.org)
[1] Domin samun cikakkun bayanai game da
bulokcen (blockchain), ana iya duba Xu et al. (2019).
[2] M.M. Manga (keɓantacciyar tattaunawa, 18 ga
watan Satumba 2024)
[3] Wannan ya shafi bankuna ko waɗansu hanyoyin
biyan kuɗi na kan intanet da za su bayar da dama ga mai sayen kaya ya tura kuɗi
zuwa ga mai sayarwa.
[4] Hikimar yin hakan ita ce, babu yadda za a
yi mai sayar da kaya ya damfari mai saye. Misali, idan ba a kulle hajar ba, mai
sayar da kaya yana iya tunanin ƙin tura kayan bayan an tura
masa kuɗi.
[5] Wannan yana ɗaya daga cikin ƙalubalen hadahadar kadarorin intanet. Dole ne ɗankasuwa
ya riƙa karantawa da bibiyar sauye-sauyen da ake
samu a tsakanin kasuwanni. Ba zai iya dogaro da bayanan wata kasuwa domin ya
gudanar da kasuwanci a wata kasuwar ta daban ba.
[6] Bayan an ba shi bashin kaso ɗari da ashirin
da biyar (125%) na uwar kuɗinsa
[7] Tashin kayayyaki a kasuwannin kuɗin intanet
shi ake kira da Koriyar Kasuwa (Green Market). Yayin da farashin
kayayyaki suka yi ƙasa kuwa, shi ake kira Jar
Kasuwa (Red Market).
[8] Sake sayen kaya da ɗankasuwa yake yi bayan
ya sayar, shi ake kira buy back a Ingilishi (wato dai sake saye).
[9] Domin ƙarin bayani, ana iya duba
Bajpai (2024).
[10] NFT yana nufin Non-Fungible Token, wato
kadarorin da ba za a iya maimaita su ko maye gurbinsu ba.
[11] Domin samun ƙarin bayani, ana iya duba Cuban (2024) da Sharma (2024).
[12] Domin samun cikakken bayani, ana iya duba
Locke (2021).
[13] An samu wannan bayani daga F. M. Bande,
(keɓantacciyar tattaunawa, 10 ga watan Maris 2024). An tantance shi ta hanyar
kallon makamantan labaran a kan intanet.
[14] A kuɗin Nijeriya a watan Oktobar shekarar
2024 (lokacin da dala ɗaya ta kai naira dubu ɗaya da ɗari bakwai), wannan
adadin kuɗi a cikin naira zai kama biliyan huɗu da miliyan ɗari tara da da
talatin (₦4,930,000,000).
[15] An kawo cikakken bayanin wannan dabarar
kasuwanci a kasuwar FXOpen. A duba FXOpen (2024).
[16] Bayan Farming, wannan nau’in
kasuwanci yana da sunaye da suka haɗa da “Yield Farming” da “Liquidity Farming”
da “Staking.”
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.