Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Zuwa Wajen Mai Duba Taurari Domin Sanin Dacewar Aure

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh. Mallam, mene ne hukuncin mace ko namiji ya je wajen mai duba taurari ko boka domin ya duba ya ce su biyun sun dace da juna ko kuma ba su dace ba wajen yin aure?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'aikumus Salam Warahmatullahi Wabarakatuh.

A Musulunci, ba ya halatta mace ko namiji ya je wajen mai duba taurari, boka, ko mai yin hasashen dacewa da rashin dacewa ta hanyar taurari domin ya ce ko mutane sun dace su yi aure ko ba su dace ba.

Dalili kuwa shine ilimin gaibu na Allah ne shi kaɗai.

 قُل لَّا يَعْلَمُ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ الْغَيْبَ إِلَّا اللَّهُ

Kace: Babu wanda yake cikin sammai da ƙasa da yasan gaibu sai Allah. (Suratun-Namli).

Annabi (Sallallahu ya ce:

 مَن أَتَى عَرَّافًا فَسَأَلَهُ عَنْ شَيْءٍ لَمْ تُقْبَلْ لَهُ صَلَاةٌ أَرْبَعِينَ لَيْلَةً

Wanda ya je wajen mai duba ya tambaye shi wani abu, ba za a karɓi sallarsa na kwana arba’in ba. (Sahih Muslim).

Zuwa wajan irin wadannan mutane na saka mutum ya rasa imaninsa baki ɗaya. Saboda haka, dacewar aure ba a tantance ta da taurari ba. Ana duba addini, halayya, amana da sauran abubuwan da Shari'a ta yarda da su, sannan a yi Istikhara da neman shawara.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments