Ticker

6/recent/ticker-posts

Abubuwan Da Suke Kawo Yawan Sakin Aure

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum malam ina kwana Ya aiki Allah ya taimaka. Dan Allah ina son sanin abubuwan da suke saka rabuwar aure, wato yawan sakin aure a wannan zamani?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Abubuwan da suke kawo yawan saki a wannan zamanin gaskiya suna da yawa, kuma wannan filin ba zai ise mu yin bayani sosai ba, amma ga kaɗan daga cikin su;

Da farko dai da macen da za a Aura, da shi Namijin da zai yi Auren kab sun ɗin bawai suna yin Auren domin Allah bane, ko tsakanin su da Allah da zuciya 1 tak ba, sai domin Sha'awa. Kuma idan kin haɗa neman Aure irin na da har zuwa yin Auren su da wadda ake yi a yanzu, za ki samu ba ɗaya bane, ko wannan kaɗai ya isa a samu yawan Saki, a yanzu hira da ake yi tsakanin saurayi da Budurwa wasu sai su fi shekara 5 suna soyayya, da can kuma bahaka bane, ya yi yawa ayi sati 2 ko wata 1 ko shekara 1 tak har an yi.

Sa'annan Namiji sai ki samu ya yaudari Yan mata sama da ukku ya sanya musu kunci da baƙin ciki har da iyayen su, sun ce sun bar shi da Allah sai ya zo ya Aure ki, shin kina ganin cewa ba za a samu Yawan Saki ba a dalilin haƙƙin waɗancan?

Haka ke ma mace sai a samu mace ta haɗa samari da yawa alhalin mutum 1 tak za ki Aura, toh waɗancan da kika sanya su cikin damuwa da baƙin ciki da tashin hankali wani a dalilin ki har wani ya mutu, sai yanzu kika yi Aure shin me kike tsammani? Shin Allah zai bar ki kuyi rayuwar jin dadi alhalin kin kuntatawa wasu? Kin ga dole ne a samu matsala ayi Saki, kuma da can bahaka bane.

Sa'annan Saurayi da Budurwa idan suna zance wasu ban da hirar batsa ba abun da suke faɗi, da can ba a san wannan ba, kuma hirar da can sai ki samu mace ta zo da ƙawar ta ko kanin ta, Namiji ya zo da abokin sa sai ki samu cewa har a gama hirar ita budurwar da za a Aura ba za ki taɓa jin muryar ta ba har a gama hirar, idan tayi magana kenan ki ji kalma 1, ga kunya sosai, shin yanzu haka ake yi?

Sa'annan hirar da can sai ki samu a tsakanin Namiji da mace za ki samu tazarar mita 2 ko 3, shin yanzu haka ake yi? Wani ya rumgune mace wai Hira suke yi a hakan, Wani fa kafin ya Auri mace babu irin tsiraicin jikin ta da bai taɓawa, wani har dakinsa ko hotel zai dauki Budurwar sa ya kai ta can, wani har zina sai sun yi, wadda ba zai yi zina ba sune waɗanda kawai za su tsaya a hirar batsa da iya taɓa ko ina a jikin mace da yin kiss nata, wani har farjin mace sai ya yi duk abun da zai yi da ita, kuma wai a hakan Aure za a yi, shin waɗanda suka saɓawa Allah irin wannan kina tsammanin za su zauna lafiya ba yawan Saki? Kin ga dole ne a samu yawan Saki domin an zubar da daraja da albarkan Auren.

Wani hira yake yi da Budurwar sa lokacin Sallah zai yi ko a jikin su, haka za a zo gurin biki Amarya a wannan ranar ba Sallah domin ana kauyawa Dance ko wani party nata da sauran su, shin ta yaya ba za a samu Yawan Saki ba, domin tun kafin ku zama ma'aurata kun gama saɓawa Allah kun fusata Allah, toh ya sheɗan ba zai shiga lamarin Auren ku ba? Wadda da can duk waɗannan abubuwan ba a yin su shiyasa sai Namiji ya yi shekara 50 da matan sa amma bai taɓa Buɗe bakin sa ya ce ya Saki matar sa ba, kuma idan kin kalla irin yadda suke yin rayuwar Auren su ba Boko ba Arabic, amma wallahi sai abun ya burge ki, ga kunya ga ladabi da biyayya ga soyayya mai kyau ba karya ba yaudara, toh shin yanzu hakane? Toh shiyasa dole ne a samu yawan Saki na ba gaira ba dalili, domin ba a san mahimmancin Auren ba.

Sa'annan mafi yawancin masu yin Aure a yanzu, waje ne kaɗai suka san darajar mace, da darajar Iyayen ta da na dangin ta, domin kawai yana son ya samu karɓuwa a gurin ita budurwar da kuma iyayen ta sabida a ba shi Auren ki, toh daga lokacin da ya samu daman Auren ki shikenan, daman a waje kike da daraja da ƙima har da iyayen ki, toh yanzu ya mallake kin ga shikenan sai yadda Allah Ya yi, daga lokacin ne sai ki samu bai ganin mutuncin iyayen ki, ke kanki ba ki isa kiyi magana ba ya dawo faɗa da zagi da cin mutuncin iyayen ki, toh irin wannan sai ki ga Saki na ta shiga a tsakanin ku ba gaira ba dalili, amma duk wadda ya san waɗannan abubuwan, toh kina iya samu ba wani yawan Saki, domin da an samu matsala iyayen ki za su yi masa magana zai saurare su zai yi amfani da maganar su kuma zai gyara kuskuren sa.

Azamanin da can ana neman Aure har su yi Auren suna yiwa Ubangijin su kekkyawar fahimta da zato mai kyau, amma na wannan zamanin bahaka suke ba daga kan matan har mazan ana yiwa Allah mummunar fahimta da zato, shiyasa kike ganin mace ko Namiji tun kafin su yi Aure sai ki ga sun tsara wa kansu iya Yaran da suke so da sunan wai iya su ya ise su domin suna ganin cewa iya waɗanda za iya tarbiyya ba da ilmi da iya daukar nauyin su kenan, sun manta cewa Allah Shi ke yin komai, toh mai irin wannan mummunar fahimta da zato ga Allah, ta yaya Allah ba zai sanya masa kunci da zafin rai ayi ta Saki ba?

Idan kin haɗa neman Auren da suna yi ne domin Allah da zuciya 1 tak, suna yin Auren su domin Allah kuma tsakanin su da Allah domin su taimaki rayuwar su, sai ki ga babu wani gwaji akan ko kowane irin cuta irin su HIV ko genotype da sauran ciwon, sa'annan idan mace ta zo haihuwa ba wani tiyata sai ki ga ta haihu, kuma sai ki ga an yi Auren sun zauna lafiya sai su Haifi Yara sama da 20 babu mai Sickler, sa'annan Allah Ya ba su ikon ilimantar da su, da tarbiyyar da su da daukar nauyin su, sabida dukkan su zuciyar su a tsarkake yake, sun yiwa Allah kekkyawar fahimta da zato Shi ne mai iko akan komai, kuma sun yi Auren su domin Allah ne bawai don biyan bukatar shi Namiji ko na macen ba, sa'annan har a fara neman Auren har ayi soyayya har a daura Auren babu karya a rayuwar Auren su balle a gurin biki.

Amma a wannan zamanin sai anyi gwajin komai na kowane irin cuta ne, daga farkon neman Auren har zuwa a daura, har zuwa ki zama matar shi ya zama mijin ki, Allah kaɗai Ya san iya karya da saɓawa Allah da za a yi na yi bayanin a sama, sa'annan idan an zo gurin bikin Auren ta, Allah kaɗai Ya san iya saɓa maSa da ake yi, ga karya wasu ma bashi ko kayan aro za su karɓo domin burge mutane a haka za a yi Auren, sa'annan sai a Haifi Yaro guda 2 ko 1 tak sai ya zama tashin hankali da bala'i gare su, daga nan ba natsuwa da kwanciyar hankali sai Saki, amma ki duba wancan na farko ba gwajin komai ba karya a rayuwar su, sai ayi Auren a zauna lafiya a Haifi Yara dayawa idan kin ga Yaran ba ki isa ki ce tarbiyyar su bai yi ba, wancan sai su yi shekara 20 ko saki 1 bai taɓa shiga tsakanin su ba, amma wannan kuma sai su yi wata 1 da yin Aure sai ki ji har an sake ta ta dawo gidan su, ko kuma ayi sati 1 tak da yin Auren a fara shiga tashin hankali har a fara yin Saki. Sabida ba a yi domin Allah ba kuma an sa karya a ciki.

Sa'annan, da macen da za tayi Aure da Namijin da zai Aure ta kab ba su san dokokin Aure ba, da za a ce ki ajiye Budurwa ki tambaye ta shin menene haƙƙin Allah a kanta na zaman ta matar Aure? Ba ta san su ba, menene haƙƙin mijin ta da na Yaran ta, ba ta san su ba, ibadar ta da sanin hukuncin jinin hailar ta kab daker za tayi miki bayani, sa'annan ki dawo gurin yadda za ta tsara tarbiyyar Yaran ta idan ta haihu kab daker za ta miki bayani, kuma wai a hakan Aure za tayi ta haihu, kuma wai a Hakan Auren za tayi ta zauna da ɗan Adam, toh don Allah wadda ba ta san waɗannan abubuwan ba ke kina ganin cewa, za ta iya zama da Namiji ba tare da an samu Saki ba? Amma da za ki tambaye ta style na Jima'i, ko ki tambaye ta maganin Infection da maganin gyaran jiki ko na karin ni'ima a farjin ta kab ta san su, amma ba ta san komai na zaman Aure ba, haka shi ma namijin da zai Aure ki, da za a tambaye shi waɗannan abubuwan kab ba zai kawo miki su ba, amma ya san maganin karfi maza kowane iri ne, Auren su ya kusa ba su neman ilmin zamantakewar Auren nasu amma kuma sun san maganin kawar da Sha'awa, wasu har BF suke kallo kafin su yi Aure domin kawai su iya style na jima'i kada a ji kunya.

Toh don Allah wadda ba zai san waɗannan abubuwan da suka wajaba a kansa ba, bai san dokokin Allah akan Saki ba, bai san darajar macen da yake Aure ba, bai san na Iyayen ta ba, bai san illa da azabar Allah da ke kansa idan ya kasa sauke waɗannan abubuwan da Allah Ya daura masa ba, bai san yadda zai bai Yaran sa tarbiyya ba, amma ya san hanyar da zai bi ya yi jima'i da mace, shin kina ganin wannan idan ya Aure ki zai zauna da ke ba Saki? Kin ga dole ne a samu Yawan Saki.

Shi Aure kamar mutum ya siya Moto ne, kin ga idan sai da kika siya motar ne za ki koyi yadda ake yin tuki, shin kafin ki iya motar don Allah ba za ki ji Ciwo ba? Shin kafin ki iya motar nan shi motar kansa ba zai lalace ba? Karshe ma sai ki ce ai daga motar ne bari ki siyar da shi ki siya wani, alhalin bawai daga motar bane daga ke ne sabida ba ki san mahimmancin motar ba, sa'annan ba ki iya tuka motar ba kika siyo shi, amma da a ce kin fara neman sanin mahimmancin motar fa? Ko kuma kin koyi yadda ake yin tuki kafin ki siya motar, kin ga komai zai zo miki da sauki, kuma za ki rike motar da mahimmanci sosai, toh haka rayuwar Aure yake, ita mace ita ne motar kin ga wadda ya Aure ki bai san darajar ki ba, sa'annan bai san ya zai gudunar da rayuwar Auren sa a kanki ba kawai suna dai ya yi Auren, amma bai san dokokin Aure ba, kin ga dole ne a samu yawan Saki ya shigo.

Amma da a ce da mace da Namiji idan Auren su ya kusa irin saura wata 3 sai a dauki hanyar zuwa gurin Malamai suna neman ilmin Addini akan rayuwar Auren da sanin dokokin Allah akan Aure da hukuncin Sa da hukuncin Saki da sauran abun da ya shafi Aure da haƙƙin mace, toh Wallahi Saki ba zai yawaita ba, amma mace ba ta Neman ilmin komai sai dai wai ta gyara farjin ta don kada ta je mijin ta ya raina ta, shi ma namiji ba ruwan sa da neman sanin dokokin Allah akan Aure, sai shan maganin karfin maza domin kada ya Aure ki a Daren farko ya ji kunya, toh don Allah masu irin waɗannan tunanin shin ta yaya Auren su zai jima? Kin ga dole ne a samu yawan saki ya shigo.

Sa'annan ana sa rayuwar karya, da rayuwar Yan Boko ko turawa, ba a aiki da abun da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya yi, a yanzu Bidi'ar da mata suke aikatawa da sunan Addini ko idan Auren su ya kusa, ko wannan kaɗai ya isa yawan saki ya shigo, yanzu kamar misalin irin yadda a yanzu ƙawayen Amarya da suke sauke Al Ƙur'ani kafin Bikin ta, a wanne Aya ko Hadisi aka Samo shi? Yin Walimar mata a ina aka samo shi? Idan an zo maganar al'adu irin su kauyawa da sauran su kab a ina aka samo su?

Sa'annan tun kafin ayi Auren Namiji ya gama Yankewa Allah hukuncin cewa shi iya Yara 2 kaɗai yake so a rayuwar sa, alhalin watakila Yaran da zai samu sun fi 10, amma yana gayawa Allah cewa shi fa Yara 2 kaɗai yake so, idan matar sa tayi Kuskuren haihuwar Yara zuwa ukku, shikenan daga wannan lokacin an fara samun matsala kenan zai daina kula da ita da yi mata komai, sai ya koma cutar da matar da Yaran ta domin ta haihu Yara har ukku, shin mai irin wannan halin ta yaya ba za a samu yawan Saki ba?

Sa'annan haka itama macen za ta ce ai ba za ta fara Haihu daga zuwan ta gidan miji ba, sai ta ga cewa ya rayuwar mijin yake gidan zama a gidan sa ko kuma ba na zaman a gidan sa ba, sa'annan ta ce sai sun more rayuwar su, ai sai ta more Budurcin ta kafin ta fara haihuwa, ko kuma tun kafin ayi Auren tana Yanke hukunci ma Allah cewa ba za haihu sosai ba domin kada ta tsufa, idan tayi rashin sa'a ta samu Namijin da shi kuma yana son haihuwa sosai, kin ga me aka yi? Idan an rashin sa'a daga nan sai a fara samun matsaloli sosai da tashin hankali har saki.

Toh shiyasa na ce miki wasu daga cikin masu yin Aure a yanzu bawai suna yin sa tsakanin su da Allah da zuciya ɗaya kamar yadda mutanen da suke yin nasu, kuma kab sun din su ba su neman ilmin zamantakewar Auren kamar yadda suke neman maganin biyan bukatar su na cire sha'awa.

Kin ga idan an nema ilmin toh dole ne akwai hakuri da juriya, dole ne za a ce sai mun yi koyi da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) domin kada a je a samu azabar Allah ko kuma a dalilin Auren mutum ya shiga wuta, toh amma ba a neman ilmin, ba a ma san sa ba, shin ta ina za a yi hakurin?

Kin ga ba hakuri ba juriya ba uzuri, wani akan ba ki sa masa Ruwa a buta sai ya ce ya Sake ki, kin ga idan akwai ilmin sani dokokin Allah dokar Auren, don Allah zai iya cewa ya Sake ki akan kawai ba ki sa Ruwa a buta ba?

Sabida haka indai za a tashi a nema ilmin Addini yadda za a bautawa Allah, za a nema ilmin Addini akan dokokin Allah da Ya shimfiɗa akan Aure, za a nema ilmin sanin Hukunce-Hukuncen Saki, za a nema ilmin sanin komai akan mace da rayuwar Aure, sani jinin hailar ta har zuwa biki, har janaba, sanin tarbiyyar Yaran su, sanin Haƙƙoƙin mace, sanin Haƙƙoƙin Yaran ta, sanin darajar iyayen ta, ya san yadda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da Sahabbai Suka yi rayuwar Auren su, duk waɗannan abubuwan kab a ce wadda zai Aure ki ya san su gaba ɗaya, a ce ke ma ta ɓangaren Namiji kin san komai akan waɗannan abubuwan, kin ga wannan ko ka da a ce za a samu matsaloli wallahi ba sosai ba, kai ni ina ganin ma indai an nema ilmin yadda ya dace kuma an yi koyi da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da Sahabbai wallahi karyar ayi Saki, idan kin yi Aure sai dai mutuwa ta raba ku.

Amma indai ba a san waɗannan ba, toh dole ne a tsinci kai cikin hatsarin Saki, ko Malami ne wadda ya san hukuncin Allah sai ki ga ya Auri mace amma kuma ana ta samun Yawan Saki tare da kuntatawa matar sa da Yaran sa, dalilin cewa bawai koyi da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yake yi ba, kuma dalilin cewa bai aiki da ilmin sa, domin shi ilmin mutum daban aiki da ilmin daban, sai ki samu jahili ya rike ki da mutunci, sai ki samu masanin Allah ya kuntatawa rayuwar ki, haka nan duk Bokon mutum indai babu Addinin Musulunci kuma bai san waɗannan abubuwan da muka ambata ba, toh dole ne a samu yawan Saki ya shigo, kuma an fi neman magani 90% akan neman sanin ya za a zauna da mace, ya za ki zauna da Namiji, Allah Ya tsare Ya shirya. wannan kaɗan daga cikin abubuwan da suke kawo yawan Saki kenan a yanzu.

WALLAHU A'ALAMU.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments