𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
ASSALAMU alaikum wa wabarakatuhu. malam, mene ne hukuncin madigo wato mace ta nemi yar'uwarta mace (lesbian) a Musulunci, domin abun ya zama ruwan dare a tsakanin mata
HUKUNCIN
MACE TA NEMI YAR'UWARTA MACE (MAƊIGO KO LESBIAN)
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
Salam Warahmatullahi Wabarakatuhu.
Maɗigo Shi Ne Mace Ta Nemi Yar Uwarta Mace. Wannan
Aiki Haramun Ne A Musulunci, Kuma Ya Saɓawa Tsarin Da Allah Ya Halicci Bayinsa Akai. Kuma yana daga cikin manyan zunubai ga tarin cututtukan da ake kamuwa da su a dalilin aikata wannan laifin, ban da fushin da Allah da ma'aikinsa a kan mai aikata wannan mummunan aikin.
Allah
S.A.W. Yana Cewa:
اِنَّكُمۡ لَـتَاۡتُوۡنَ الرِّجَالَ شَهۡوَةً مِّنۡ دُوۡنِ
النِّسَآءِ ؕ بَلۡ اَنۡـتُمۡ قَوۡمٌ مُّسۡرِفُوۡنَ
Shin
Ku Kuna Zuwa Wa Maza Da Sha’awa, Maimakon Mata? A’a, Ku Mutane Ne Masu Ketare
Iyaka. (Suratul A’araf Aya ta 81).
Kuma
Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya Hana Abubuwan Da Suke Kaiwa Ga
Bayyana Al’aura Da Yin Mu’amalar Sha’awa Tsakanin Mata. Ya Ce: Kada Wata Mace
Ta Dubi Al’aurar Wata Mace, Kuma Kada Ta Shafi Jikinta Da Jikin Wata Mace.
(Sahih Muslim).
Indai
Ke Musulma Ce Ya Kamata Kiji Maganar Ma'aikin Allah Akan Kada Ma Mace Ta Duba
Al'aurar Mace Ballantana Su Aikata Wani Abun.
Allah
S.A.W. Ya ce:
وَاَمۡطَرۡنَا عَلَيۡهِمۡ مَّطَرًاۚ فَسَآءَ مَطَرُ
الۡمُنۡذَرِيۡنَ
“Sai
Muka Yi Ruwan (Duwatsun Azaba) Akansu, Lallai Ruwan Duwatsun Azabar Nan Ta
Wadanda Aka Yi Musu Gargadi Ya Yi Muni Kwarai.” (Suratun Namli, Aya Ta 58).
Ka
Dubi Yadda Karshen Miyagun Masu Laifi Ya Kasance.
Duk
Abu Guda Ne Da Luwaɗi
Da Madigo. Kuma Duk Masuyi Azabar Allah Mai Tsanani Na Jiransu.
Saboda
Haka, Bai Kamata Mace Ta Shiga Wannan Aiki Ba, Ya Kamata Ta Nisance Shi Kuma Ta
Kiyaye Kanta Daga Duk Abin Da Zai Kai Ta Zuwa Gare Shi.
Ya
zama wajibi a kan iyaye da dukkan mai nauyin kula da tarbiya ya dinga kula da shige da ficen macen da take ƙarƙashin sa, a dinga dubawa yarsu da kuma kula da waɗanda suke mu'amala da su.
Amma
Duk Wanda Ya Fada Cikin Wannan Laifi, Kada Ya Yanke Kauna Daga Rahamar Allah.
Ya Tuba Ga Allah Ya Bar Laifin, Ya Yi Nadama, Kuma Ya Kuduri Aniyar Ba Zai Koma
Cikinsa Ba. Yabar Dukkanin Mu'amala Ga Wadanda Suke Aikata Laifin Domin Tsira
Daga Azabar Dake Biyo Bayan Laifin.
WALLAHU
A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.