𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu. Malam, Mene ne Hukuncin Luwadi (Homo) A Musulunci? Kuma Mene ne Illolinsa Da Abin Da Ya Kamata Mutum Ya Yi Idan Ya Fada Cikinsa?
HUKUNCIN
LUWAƊI
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa
Alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarakatuhu.
Hakika
A Cikin Nau’o’in Zina Da Dangoginta, Luwaɗi Shine Mafi Muni Kuma Mafi Ƙazanta. Kamar
Yadda Allah Yake Gaya Mana A Cikin Al-Ƙur’ani:
وَلُوۡطًا اِذۡ قَالَ لِقَوۡمِهٖۤ اَتَاۡتُوۡنَ الۡفَاحِشَةَ مَا
سَبَقَكُمۡ بِهَا مِنۡ اَحَدٍ مِّنَ الۡعٰلَمِيۡنَ اِنَّكُمۡ لَـتَاۡتُوۡنَ
الرِّجَالَ شَهۡوَةً مِّنۡ دُوۡنِ النِّسَآءِ ؕ بَلۡ اَنۡـتُمۡ قَوۡمٌ
مُّسۡرِفُوۡنَ
“Ka
Tuna Annabi Luut Lokacin Da Ya ce Ma Mutanensa: Me Ya sa Kuke Yin (Irin Wannan)
Alfasha? Babu Wani Wanda Ya Rigaku (Aikatawa) Daga Cikin Talikai (Halittu Baki
Daya). Ku Kuna Zuwa Ma Mazaje Ta Fannin Sha’awarku Maimakon Mata, Bari Dai Ku
Mutane Ne Masu Mutukar Barna.” (Suratul A’araf, Aya Ta 80–81).
Kuma
Saboda Munin Laifinsu, Allah Ya yi Musu Azabar Da Bai Taɓa Yima Kowa Kafinsu Ba. Allah Ya Aiko Da Mala’iku
Suka Kifar Da Garinsu, Sannan Aka Yi Musu Ruwan Duwatsun Azaba. Acikin Suratu
Huud, Allah Ya ce:
فَلَمَّا جَآءَ اَمۡرُنَا جَعَلۡنَا عَالِيَهَا سَافِلَهَا
وَاَمۡطَرۡنَا عَلَيۡهَا حِجَارَةً مِّنۡ سِجِّيۡلٍۙ مَّنۡضُوۡدٍۙ
“Ya
yin Da Al’amarinmu Ya Zo, Sai Muka Sanya Saman Birnin Ya Zama Kasantansa,
Sannan Muka Yi Musu Ruwan Duwatsun Wuta Na Sijjeel.” (Surah: Hud, Ayat: 82).
Kamar
Yadda Allah Yake Cewa:
وَاَمۡطَرۡنَا عَلَيۡهِمۡ مَّطَرًاۚ فَسَآءَ مَطَرُ
الۡمُنۡذَرِيۡنَ
“Sai
Muka Yi Ruwan (Duwatsun Azaba) Akansu, Lallai Ruwan Duwatsun Azabar Nan Ta
Wadanda Aka Yi Musu Gargadi Ya Yi Muni Kwarai.” (Suratun Namli, Aya Ta 58).
Saboda
Tsananin Bala’in Da Yake Cikin Wannan Aika-Aikar, Manzon Allah (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Ya ce: “Mafi Girman Abin Da Nake Tsorace Ma Al’ummata, Shine
Irin Aikin Mutanen Annabi Luut.” (Tirmizy, Hadisi Na 1457; Ibn Maajah, Hadisi
Na 2563).
A wani hadisi kuma Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa: “Tsinanne ne duk wanda ya yi jima’i da dabba, kuma tsinanne ne duk wanda ya aikata irin aikin mutanen Annabi Luut.” (Ahmad, Musnad, Hadisi na 1878).
Acikin
Wani Hadisin Kuma, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya Fadi Irin
Hukuncin Da Shari’ar Musulunci Ta Tanadar Ma Masu Luwadi: “Duk Wanda Kuka Tarar
Dashi Yana Aikata Irin Aikin Mutanen Annabi Luut, To Ku Kashe Mai Aikatawar Da
Kuma Wanda Ake Aikata Masa.” (Tirmizy, Hadisi Na 1456; Abu Dawud, Hadisi Na
4462; Ibn Maajah, Hadisi Na 2561).
Luwadi
Da Madigo Mummunar Annoba Ce Wacce Ta Kauce Ma Fitrar Da Allah Ya Halicci
Dukkan Halittunsa Akai. Shi Ya sa Annabi Luut عليه
السلام Ya ce Ma Mutanensa: “Kun Zo Da Alfasha Wacce Babu
Wani Daga Cikin Halittu Wanda Ya Rigaku Aikatawa.”
Imam Ibnul Ƙayyim Al-Jawziyyah Yana Cewa: “Dukkansu Guda Biyu, Wato Zina Da Luwaɗi, Suna Ƙunshe Da Mummunar Alfasha Wacce Ta Kauce Daga Fitrar Allah.”
Kuma
Luwadi Yana Kunshe Da Bala’o’i Masu Yawa.
Ka
Tuba Zuwa Ga Allah, Ka Sani Cewa Rahamar Allah Tana Da Yalwa, Kuma Allah Yana
Son Bayinsa Masu Tuba.
قُلۡ يٰعِبَادِىَ الَّذِيۡنَ اَسۡرَفُوۡا عَلٰٓى اَنۡفُسِهِمۡ لَا
تَقۡنَطُوۡا مِنۡ رَّحۡمَةِ اللّٰهِ ؕ اِنَّ اللّٰهَ يَغۡفِرُ الذُّنُوۡبَ
جَمِيۡعًا ؕ اِنَّهٗ هُوَ الۡغَفُوۡرُ الرَّحِيۡمُ
“Kace
Musu: Ya Ku Bayina Wadanda Suka Yi Wa Kansu Barna! Kada Ku Fidda Tsammani Daga
Rahamar Allah. Hakika Allah Yana Gafarta Dukkan Zunubai Baki Ɗaya, Shi
Shine Mai Gafara Kuma Mai Jin-Ƙai.” (Suratuz-Zumar, Aya Ta 53).
Ka
Nisanci Miyagun Abokai. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yana Cewa:
“Mutum Yana Bin Addinin Abokinsa Ne. Don Haka Kowanenkun Ya Kula Da Wanda Zai
Yi Abota.” (Sunanut Tirmizy, Hadisi Na 2378).
Ka
Rika Zama Cikin Mutanen Kirki, Kuma Ka Kula Da Sallolinka Na Farillah Da
Nafilfili. Ka Yawaita Zikirin Allah A Ko Yaushe.
Ka
Nisanci Kalle-Kallen Haramun A Zahiri Ko A Cikin Wayar Salularka. Ka Sani Cewa
Allah Ya Baka Amanar Dukkan Gabobin Jikinka Ne, Kuma Akwai Ranar Da Zai
Tambayeka.
WALLAHU
A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.