Ticker

6/recent/ticker-posts

Wasu Matsalolin Kasuwanci a Tsohuwar Kasuwar Sakkwato Jiya zuwa Yau

Citation: Gado, I. A. (2026). “Wasu Matsalolin Kasuwanci a Tsohuwar Kasuwar Sakkwato Jiya zuwa Yau.” In Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies, Vol. 04, No. 01, Pp. 117 – 124. www.doi.org/10.36349/djhs.2026.v04v01.015.

WASU MATSALOLIN KASUWANCI A TSOHUWAR KASUWAR SAKKWATO JIYA ZUWA YAU

Na

Ibrahim Alhaji Gado

Ɗalibin Ph.D., Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato

1.0 Gabatarwa

Kasuwanci daɗaɗɗen abu ne da ya sha faɗi-tashi tun farkon fara shi shekaru aru-aru zuwa yau a Sakkwato. Kamar kowane yanki a ƙasar Hausa, al’amari ne da ake yi tun yana ƙarami har ya girma, tare da samun sauyi na juyawar zamani da ya kawo shigowar wasu baƙin abubuwa. Lamarin kasuwanci wanda ya zama sila ta cigaban al’umma ko kuma koma baya na tattalin arziki. Kasuwanci hada-hada ce ta saye da sayarwa, da yawa akan fita neman da ake ganin zai iya zama cigaba, sai a yi karo da wasu abubuwa na ba zata da za su zama sila ta faɗuwar ‘yan kasuwa da kasuwanci da tattalin arziki da al’umma baki ɗaya.

Wannan muƙala ta fito da wasu muhimman abubuwa da suka haifar da matsaloli ga kasuwancin tsohuwar kasuwar Sakkwato, tun farkonta har zuwa lokacin da ake ciki. Abubuwa ne masu dangantaka da bala’o’i da tsarin tattalin arziki da haka ya sanya wasu suka rasa dukiyoyinsu da kariyar tattalin arziki, sanadiyar tsarin kasuwanci da ko ohon hukuma da makamantansu. Maƙalar ta kawo bayanai na yadda matsalolin da suka faru suka jawo koma baya na kasuwanci a tsohuwar kasuwar Sakkwato. An gudanar da wannan aiki ne ta hanyar tattaro bayanai daga dattawa da tsofaffi da sababbin ‘yan kasuwa na garin Sakkwato da jami’an gwamnati. Muhimmancin wannan bincike shi ne domin jama’a da masana tarihi da yara matasa masu tasowa su fahimci irin matsalolin da kasuwanci ya fuskanta da kuma ba da shawarwari. An kasa wannan maƙala zuwa abubuwa kamar haka.

2.1 Kasuwanci

Kalmar kasuwanci kamar yadda masana suka tabbatar an aro ta ne daga harshen Kanuri, wato ‘kasuk’ sai Hausawa suka mayar da ita kasuwanci. Ta ɓangaren ma’ana kuwa masana da manazarta da ɗaliban al’ada da dama sun tofa albarkacin bakinsu game da ma’anar kasuwanci, kamar Alhassan (1987:28) ya kawo cewa “A saye a sayar shi ne kasuwanci. Wato a nan mutum ya fitar da kuɗinsa ya sayi kadara ko wani abu ko haja. Sannan wani lokaci ya fitar da wannan kadara ya sayar shi ne kasuwanci”.

Ƙamusun CNHN (2OO6:238), cewa ya yi “Kasuwanci,sana’ar saye da sayarwa a kasuwa”.

A ra’ayin Ibrahim (1987) ya bayyana kasuwanci da cewa “musayar wani abu, a kai shi kasuwa domin a musanya shi da wani abin. Ta wannan hanya ce aka sami yanayin ciniki, na bani gishiri in ba ka manda”.

Daga ra’ayoyin da waɗannan masana suka bayar, wannan muƙala ta aminta da cewa, kasuwanci yana nufin duk wata dabarar sarrafa wani abin amfnai da za a iya samun wani abu daban don samun biyan wata buƙata ta hanyar saye da sayarwa ko ciniki ko musaya.

3.1 Taƙaitaccen Tarihin Tsohuwar Kasuwar Sakkwato

Birnin Sakkwato yanki ne da aka daɗe ana hulɗar kasuwanci a wurin tun kafin zuwan Larabawa da Turawa, inda ake baje kolin kayan da Hausawa suke sarrafawa na gargajiya. Hulɗar ta ci gaba da wanzuwa har zuwa lokacin da suka haɗu da Larabawa ‘yan kasuwa da suke zuwa daga ƙasashe daban-daban. To, daga wannan lokacin aka ci gaba da samun baƙi, inda suke shigowa da sababbin abubuwa na kasuwanci wanda ya sanya dole aka samar wa wurin kasuwancin bagire wanda ake kira kasuwa inda ake zuba haja a ciki da wajen ƙasar nan don Tarawa da saye da sayarwa. Wurin ya bunƙasa har aka kira shi da kasuwa ‘yar gabas. Bayan da wurin ya bunƙasa, sai aka ga wurin ya yi wa ‘yan kasuwar ƙaranci, sai aka yi tunanin samun wani wuri inda zai wadaci ‘yan kasuwar. Ta haka aka samar da kasuwar da ake kira ‘yar dole. Muhallin kasuwar ya taso daga Masallacin Shehu zuwa titin ƙofar Aliyu Joɗi da titin Ahmadu Bello da Marafa Ɗanbaba zuwa shagon goro da runjin ragga da kuma titin ƙofar Atiku zuwa rukunin shagunan Ɗanjabalu da bayan wurin tukanen gargajiya. Bayan bunƙasar kasuwar, daga nan aka samar da sabuwar kasuwa.

4.1 Matsalolin Kasuwanci a Tsohuwar Kasuwar Sakkwato

Tsohuwar kasuwar Sakkwato ta fuskanci matsaloli da dama tun kafuwarta har zuwa yau. Waɗannan matsalolin sun sa ‘yan kasuwa barin kasuwar na wani lokaci, wasu kuma suka ka bar ta gaba ɗaya, sanadiyyar wani bala’i da ya faru a kasuwar binciken ya gano cewa an sami matsaloli da dama a kasuwar da suka zama sanadi na karewar tattalin arzikin ‘yan kasuwar da dama. Babbar matsala mafi girma da kasuwar ta fuskanta ita ce wuta (gobara) da ambaliyar ruwa da sauransu[1].

4.1.1 Gobara

Gobara ko tashin wuta wani al’amari ne da yake faruwa a cikin dukiya ko wani abin amfani da ke salwantar da wannan abin da ta faɗawa ko rauna ta shi. Tashin wuta yana daga cikin matsalolin da tsohuwar kasuwa ta yi fama da su, da suka yi ta gurgunta cigaban kasuwanci a kasuwar, Ga bayanan wannan tashin da kasuwar ta samu daban-dabah a lokutta daban=daban. Da yake ba a samu bayanai na wasu ayukka da aka yi game da kasuwar ba, duka bayanan an samosu ne ta hanyar hira da waɗanda abubuwan suka wakana a gaban idanunsu,

i. Gobarar Ƙofar Sarauniya

Tashin wuta kamar bayanan da aka samu daga wani dattijo kuma tsohon Ɗansuwa mai suna Ɗanmamuda, cewa tashin gobara a wasu wurare na tsohuwar kasuwar ya jawo babbar matsala ga kasuwanci, wani lokaci sai ta durƙushe gaba ɗaya daga baya ta sake farfaɗowa. Gobara ta farko da aka fara yi a tsohuwar kasuwar Sakkwato ita ce ta ƙofar Sarauniya a shekarar 1970, wutar ta tashi ne da yamma lokacin da ‘yan kasuwa suka tashi da ga kasuwanci, suka koma gida, wutar ta yi mummunar ɓarna, inda daga nan wasu ‘yan kasuwa na wannan lokaci suka kare, domin jarinsu ya ƙone gaba ɗaya. Wani shago ne da ke kusa ga ƙofar wutar ta tashi, amma sai da ta ƙona kasuwar kasuwar gaba ɗaya. Babu wani abu da wutar ta raga baya ga abin da ‘yan kasuwar suka fita da su a hannunsu. Gobarar ta sanya damuwa ga ‘yan kasuwar ta hanyar rasa abubuwan kasuwancin su da taɓa hankalinsu, domin an nuna cewa akwai waɗanda suka sami taɓuwa ta rashin hankali sakamakon ganin irin hasarar da ta shafi dukiyoyinsu. Wasu kuma sun guje wa kasuwar. Masu sayar da kayan buhuhuwan abinci da masu sayar da atamfa da zannan gargajiya na saƙi da birgima, su ne suka fi hasarar dukiya mai tarin yawa a kasuwar. Lumo wanda yake matsayin alƙalin kasuwar ya yi kira ga gwamnati ta taimaka wa. To waɗannan ‘yan kasuwar, da wannan matsalar ta shafa, amma ba a sami taimakon komi ba, sai dai daga baya wasu ‘yan kasuwar sun sayar da wasu kadarorinsu suka sake gina wuraren su. Wasu kuma, suka ciyo bashi suka sake dawo da kasuwancinsu. Daga baya gwamnati ta zo da wasu buhuhuwan abinci don taimaka wa ‘yan kasuwar abin da ya fusata su, har suka ɗauki matakin rashin biyan haraji da suke biya a baya. Wannan gobara ta haifar da matsaloli sosai ga ‘yan kasuwa ta hanyar salwatar jarinsu.[2].

ii. Gobarar Wurin ‘Yanmanja

Baya ga waccan wutar da aka yi ta farko, kuma kasuwanci ya sake bunƙasa a kasuwar, hada-hada ta sake buɗuwa. Bayanan da aka samu daga AlhajiAbu mai Ilmi wanda tsonhon Ɗankasuwa ne, kuma a gabansa abin ya faru cewa. A shekara 1972 aka sake yin wata gobara a nan cikin tsohwuar kasuwar Sakkwato. Wutar masu sana’ar mai ne ta fi yi wa ɓarna, kuma ba ta yi mummunar ɓarna kamar ta farko ba, domin wurin ‘yan manja kawai ta ƙona. Dalilin faruwar wannan wutar shi ne ijimin lantarki ne aka tada yana aiki sai wutar ta tashi, kasan cewar mai yana da masƙi ya sa wutar ta riƙa ruruwa har ta yi ɓarna a wurin. Kasancewar wutar ba ta yi mummunar ɓarna ba ya sa ‘yan kasuwa ba su shiga damuwa sosai ba, kuma sun sami taimako daga manyan ‘yan kasuwa masu safarar daga wurare daban-daban, suka sake ba su kaya domin farfaɗo da kaswancin su. Wannan wurin yana a cikin tashar lemu. Mutane sun shiga damuwa sabo da hayaƙi da nason mai da turɗa, wannan ya sa wasu ‘yan kasuwa suka ƙaurace wa kasuwar.

iii. Gobarar da ‘Yan Ta’adda Suka Haddasa

A shekarar 1989 an sami wata hasara ta yin gobara wadda ta ƙona dukkanin shagunan da suke cikin tsohuwar kasuwar Sakkwato. Dalilin wannan gobarar kuma kamar yadda binciken ya samo, daga Alhaji Zaki mai sugar shi ne, wasu daga cikin ‘yan kasuwa ne suka amshi kaya da kuɗi bashi ga hannun wasu manyan ‘yan kasuwa suka halakar da kuɗaɗen da jarin gaba ɗaya, ganin ba su da mafitar da za su mayar da kuɗin da kayan da suka ansa, kawai sai suka yanke shawarar ƙona kasuwar, domin su ɗauke hankalin ‘yan kasuwar, a manta da wannan dukiya da take hannun su. Daga nan suka cillawa wasu shagunan kasuwar wuta sai da kasuwar ta ƙone ga ba ɗaya. Wutar sun sanya ta ne da yamma bayan ‘yan kasuwar sun tashi daga kasuwancin su sun koma gida. ‘Yan kasuwa a wannan lokaci sun sami kan su cikin yanayi na damuwa, na ta’addancin da ba su taɓa samun kan su a ciki ba. Wutar ta yi mummunar ɓarnar domin an kasa kashe ta, sai da aka sami taimakon motocin da ake amfani da su a filin jirgin saman ƙasa da ke Sakkwato, aka sami nasarar kashe wutar. A wannan lokaci an sami taimako daga mutane daban-daban, inda Sarkin musulmi na wannan lokaci ya ba da kashi ɗaya bisa biyar ga kowane ɗan kasuwa da shagon sa ya ƙone. Haka kuma gwamnatin jaha ta ba da kashi ukku bisa biyar na hasarar da ‘Yan kasuwar su ka samu. Wannan ya sa ‘Yan kasuwar su ka sami natsuwa da cire fargaba a zukatansu. Wannan ya sa ‘Yan kasuwar su ka yi godiya ga gwamnati da waɗan da suka ba da taimako su, Daga nan kasuwanci ya sake farfaɗowa, aka cigaba da hada-hadar kasuwanci.

iv. Gobarar Rukunin Shagunan Ɗanjabalu

Bayanan da aka samo daga Malam Hakimi tsohon Ɗankasuwa a tsohuwar kasuwar Sakkwato cewa. An yi gobara a tsohuwar kasuwar Sakkwato a shekarar 2019, a wurin da ake kira da suna kasuwar Ɗanjabalu, wurin sayarda kayan suturar mata, wurin wani ɓangare ne da yake a cikin tsohuwar kasuwar Sakkwato da aka gina mallakin iyalan gidan Alhaji mu’azu Danjabalu majidaɗin Sarkin Musulmi. Wutar ta tashi ne a wurin sayar wa da ɗinka kayan mata da ke cikin kasuwar. An nuna cewa wani injimi ne na lantarki da ake aiki da shi ya kama da wuta daga nan sai abubuwan da suke wurin suka kama da wutar ta yi ta yaduwa har ta ƙona wurin gaba ɗaya. ‘Yan kasuwar da suka fi hasara a wurin su ne masu ɗinka kayan mata kamar hijabai da masu sayar da kayan bulawus na mata da suturarsu kamar takalma da sarƙa da kalolin kayan shafe-shafe na mata da kayan suturar yara da jarirai da masu haɗa kayan buki da na lefe da makamantansu. ‘Yan kasuwar sun sami taimako daga gwamnati da wasu manyan ‘Yan kasuwa da suke hulɗada su, kamar tawagar ‘Yan kasuwa daga ƙasar Dubai da suka zo domin ganin irin ɓarnar da wutar ta yi. Sun kuma ba da taimako mai yawa ga ‘Yan kasuwar. Baya ga waɗannan munanan asara da babbar kasuwar ta fuskanta, an nuna cewa an sami wasu tashin wuta a wurare daban-daban waɗanda sakamakon gine-gine na zamani da ake yi wa aiki da kankare na siminti ya sa ba su yi tasiri sosai ba, sukan ƙona iya shagon da ta tashi ne sai a sami nasara a kashe ta.

4.1.2 Ambaliya Ruwa

Ambaliya ta ruwa a lokacin damina na ɗaya daga cikin matsalolin da tsohuwar kasuwar Sakkwato take fuskanta tun lokaci mai tsawo.

Alhaji Bello Ƙofar Atiku cewa yayi. A shekarar 2019 an sami ambaliyar ruwa mafi muni. Ranar jamu’a lokacin da jama’a da ‘Yan kasuwa suka tafi wurin sallar jumu’a, ruwan sama ya sauka kama da bakin ƙwarya wanda sakamakon haka kasuwar ta cika da ruwa, duk shaguna suka cika da ruwa kaya suka taso saman ruwa. Wannan ya tada hankalin ‘yan kasuwar sosai, wanda ya tilasta aka nemi taimakon jama’a domin kwashe ruwa daga shaguna da tsamo kaya domin shanya wa, wasu suka lalace wasu kuma ruwa ya tafi da su. An nuna cewa tun ranar jumu’a ake aikin kwashe ruwan har ranar lahadi, duk da haka ba a iya kwashe ruwa a wasu shaguna ba. Gwamnati ta jajanta wa ‘Yan kasuwar, sai dai ba wani taimako da suka samu a hukumance. ‘Yan kasuwar ne suka sake farfaɗo da wurarensu na kasuwanci a dalilin wannan matsala. An shiga damuwa ta tsayawar kasuwanci a tsohuwar kasuwar Sakkwato. To tun daga wannan lokacin har zuwa yanzu duk shekara aka sami saukar ruwan sama mai yawa, kasuwar takan cika da ruwa inda wasu shaguna sukan cika da ruwa, hanyoyin ruwa su toshe tituna su cika da ruwa, wannan ke sa kasuwanci ya tsaya, wasu kaya kuma su lalace motoci da abubuwan ɗaukar kaya kan tsaya na wani lokaci, har sai lokacin da ruwan ya gama tsiyayewa. Wannan yana faruwa ne sakamakon yawan manyan gine-gine na zamani ba tare da fitar da hanyoyin ruwa ba kamar yadda ya kamata.

4.1.3 Cinkoson Abubuwan Hawa

Alhaji Cika Sarkin Gishiri mai riƙe da muƙamin shugaban ‘yan kasuwar Sakkwato, a hirar da aka yi da shi ya bayyana cewa. Cinkoson abubuwan hawa da na dakon kaya yana daga cikin matsalolin tsohuwar kasuwar Sakkwato, yayin da manyan motoci da ƙanana kan taru a saman titi su rufe hanya ta yadda wasu kayan ‘yan kasuwa ba za a iya sauke su cikin lokaci ba. Haka ma abubuwan dokon kaya kamar kura da baro, inda sukan ɗora kaya fiye da kima su biyo mayan tituna da motoci da Babura suke wucewa, wannan yakan kawo tsaiko da faɗuwar kayan da suka ɗauko, wasu su lalace wasu motoci su take su wasu su zube a kasa kwashe su, wasu kuma kamar gishiri da suga da madara da sauran wasu abubuwa da indan sun zuba a ƙasa sun lalace da fashewar taya ta mota ko ta baro ko ta kura da kan sanadiyar faɗuwar su kayan su lalace, wannan yakan jawo hasara sosai ga ‘yan kasuwa. Baya ga wannan kuma akwai cinkoson mutane,da suke haddasa yawan satar kayan ‘yan kasuwa, ta hanyar aza wa mai baro ko kura kaya ya ɓace ya sulale da su, ko a aji ye kayan wani ya zo ya ɗauke[3].

4.1.5 Tsaro

Tsaro wani babban fage ne da ya daɗe yana ciwa ‘yan kasuwa tuwo a ƙwarya. Samar da tsaro na buƙatar abubuwa da dama kamar haɗin kan ‘yankasuwa da sa hannun gwamnati da cire son rai da kuma hukunta masu laifi idan an kama su da laifin, don a samu tsaron kasuwar da kayan ‘yankasuwa. Samar da tsaro ana iya kallon sa ta hanyoyi daban-daban, inda ake samun hanyoyi na yaudarar ‘yan kasuwa mabambanta.

A tattaunawar mu da Baba Ɗanmamuda ya nuna cewa sata tana daga cikin waɗannan hanyoyi. Ya bayyana sata da cewa, wata yaudara ce da ke gudana a cikin al’umma wadda ke jawo hasara ka ga dukiyoyin jama’a wasu ɓarayi ne da ake tare da su a cikin kasuwa sukan yi shiga ta yadda ba za a gan su a ce su ɓarayi ne ba. Sukan yi tsame na wayar hannu da kuɗaɗen da ‘yan kasuwa suka sata a aljihunsu ko su biyo wurin mai kaya ko inda ake loɗi su zare wani abu su tafi da shi su sayar. Suna yin haka ne ta hanyar wannan ya ɗauko yaba wancan, wancan yaba wancan ko da mai kaya yake kula da wurin kayan sun yi nisa. Haka kuma akan sami ma su kasuwancin kayan da ɓarayi suke satowa wanda shi ma ƙalubale ne ga kasuwancin tsohuwar kasuwar Sakkwato.

4.1.6 Shugabanci da Siyasa

Shugabanci wani tsari ne na tafiyar da jagorancin al’umma domin sama musu cigaba na rayuwa. A tsohuwar kasuwar Sakkwato akwai tsari na shugabancin kasuwar, inda ‘yan kasuwar sukan zaɓi wanda zai shugabance su na tsawon shekaru (5) wato suna gudanar da zaɓen su cikin shekaru biyar. Da zarar lokacin ya cika za a sake sabon zaɓe. Wanda yake kai zai sauka ya ba wani wanda ya ci zaɓen da aka gudanar. A lokacin da siyasa ta zo a shekarar 1999 sai tsarin shugabancin ƙungiyoyin ‘yan kasuwa ya sauya, sai gwamnati ta karɓe harakar shugabanci sai wanda gwamnati mai ci ta zaɓa zai zama shugaban ‘yan kasuwa. A lokacin gwamnatin farar hula ta farko daga 1999 zuwa 2007 sun zaɓi Alhaji Ladan Unguwar mallamai a matsayin shugaban ‘yan kasuwar jahar Sakkwato sai daga shekarar 2007 zuwa 2015 a lokacin suka zaɓi Alhaji Yaro Gobirawa a matsayin shugaban ‘yan kasuwa, sai daga shekarar 2015 zuwa 2023. A lokacin aka zaɓi Alhaji Chika Sarkin Gishiri a matsayin shugaban ‘yan kasuwar wanda bayan faɗuwar gwamnatinsu a 2023 ya sauya sheƙa ya koma jam’iya mai ci, sai aka bar masa jagorancin har zuwa wannan lokaci.

Wannan tsari na shugabanci yana jawo matsala ga ‘yan kaswa, ta hanyar tauye ‘yancin da suke da shi na zaɓen wanda suke so, kuma yakan jawo rabuwar kawunan ‘yan kasuwa. Domin wasu ba za suyi biyayya ga wani tsari da aka ɗora musu ba.[4]

4.1.7 Tsare-Tsaren Tattalin Arziki

Alhaji Cika Sarkin Gishiri ya bayyana cewa. Tsarin tattalin arziki da ‘yan kasuwar tsohuwar kasuwa suke amfani da shi yana da matukar muhimmanci ga bunƙasa tsohuwar kasuwar Sakkwato, musamman idan aka dubi yadda suke yin haɗaka a wajen sayen kaya daga kamfanoni daban-daban, inda masu ƙaramin ƙarfi kan haɗa jarinsu, su sayi kaya daga kamfani ta hanyar waƙilan da suke yi wa kamfunan waƙilci a tsohuwar kasuwar Sakkwato. Su sayo kaya, su raba, su fitar da kyautar kamfani da ake kira (Promo) sai su riƙa sayarwa ga sauran ‘yan kasuwa a bisa farashi mai sauƙi, kafin waɗannan kayan su ƙare sun sake haɗa kuɗin da za su sake turawa ga kamfani a turo musu da wasu kaya. Haka, kuma akwai tsarin tattalin arziki na zamani wanda yake da ban sha’awa na saka adadin kayan da aka yo odar su daga kamfani a cikin na’urar rubutu (Computer) inda ake cire adadin abin da aka sayar a jikin computer har kayan su ƙare. Haka kuma, akan yi amfani da irin wannan hanyar a tura wa ɗan kasuwa adadin kaya da kuɗinsu ya turo kuɗin a tura masa kayan ba tare da ya zo wurin ba, ta amfani da wayar hannu da P.O.S domin sauƙaƙa kasuwancinsu.

Matsalolin da wannan tsari yake fuskanta ita ce, Waƙilan kamfunan da ake tura wa, kuɗi su tura wa kamfani wani lokaci sukan riƙe kuɗin su yi wani kasuwanci da su wanda ya ke haifar da tsaiko wajen isowar kayan a cikin lokaci. Haka kuma, akan sami yanayi na ɗaukewar sabis (Network) wanda yake haddasa maƙalewar kuɗin da aka tura. Baya ga wannan akan sami matsaloli na rashin son cigaba daga wasu ‘yan kasuwa, don kada kasuwancin wani ya bunƙasa bisa ga na ɗan uwan kasuwancinsa, wanda yake sanya hasada da ƙeta da cutar wa ga wasu ‘yan kasuwa[5].

 

5.1 Sakamakon Bincike

Wannan ya yi ƙoƙarin fito da wasu muhimman abubuwa da suka kawo wa tsohuwar kasuwar Sakkwato ƙalubale da matsalolin kasuwanci da suke bibiyar ta tun lokaci mai tsawo. Daga cikin sakamakon da maƙalar ta gano akwai:

i. Kasuwancin tsohuwar kasuwar Sakkwato ya fara samun matsala ne tun lokacin da kasuwar ta fara samun haɗari na ƙonewar dukiyar ‘yan kasuwa a wurare daban-daban.

ii. Ta’adanci ya taka muhimmiyar rawa wajan kawo cikas ga kasuwancin tsohuwar kasuwar Sakkwato.

iii. Gine-gine ba bisa ƙa’ida ba ya sa akan sami ambaliyya ta ruwan sama da ke kawo hasarar kayan kasuwanci ga ‘yan kasuwa.

iv. Son rai da masu gudanar da harakar kasuwanci suke nunawa na daga cikin matsalolin da kasuwar take fuskanta.

v. Zamani ya yi tasiri sosai wajen rage samun wasu matsaloli ga kasuwancin tsohuwar kasuwar Sakkwato.

6.1 Shawarwari

i. Samar da tsaro ta hanyar haɗin guiwar ‘yan kasuwa da gwamnati don kamawa da hukunta waɗanda suka yi laifi.

ii. Gwamnati ta sa ido ga manyan ‘yan kasuwa da suke manyan gine-ginen su ba bisa bin dokokin da tsarin yin gini ya tanadar musu ba kafin su fara yin gini a wurin.

iii. Cire son rai ga harkar kasuwanci wanna zai taimaka wajen fahimtar juna da samun mafita ga kasuwancinsu.

iv. Ƙungiyoyin ‘yan kasuwa su samar da tsari na bai-ɗaya wanda za a riƙa lura da yadda shigowar abubuwa na zamani da yadda rungumarsu yake haɓɓaka kasuwancinsu.

v. Inganta hanyoyin shiga wuraren kasuwanci, domin lokacin damina shiga wasu wuraren yana da matuƙar wahala sakamakon ruwan sama da toshewar hanyoyinsu.

vi. Tsare gaskiya a yayin gudanar da hada hadar kasuwanci.

7.1 Kammalawa

Wannan maƙala ta tattauna kan wasu muhimman abubuwa da suka zama manya-manyan matsaloli da aka samu wajen gudanar da kasuwanci a tsohuwar kasuwar Sakkwato. Baya ga gabatarwar, an yi ƙoƙarin kawo ma’anar kasuwanci da bayanin yadda gobara, tashin wuta suka jawo matsaloli da hasara ga ‘yan kasuwa da amballiyar ruwa da toshewar magudanun ruwa da fashewar gadoji na tituna da sata da fasa shaguna suka kawo cikas ga cigaban kasuwanci a tsohuwar kasuwar Sakkwato.

Manazarta

Abdullahi, K. (1978). “Exchange and the Origins of Market in West Africa: A Case Study of Kasuwar ‘Yar Dole in okoto”. B.A History, Sokoto: Department of History, Usmanu Danfodiyo University.

Abubakar, J. (2017). “A History of Shinkafi Market.” M.A. Dissertation, Sokoto: Department of History, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

Abubakar, M. (2012). “Unguwannin Sakkwatoi da al’adunsu,” Kundin Digiri na Biyu (M.A). Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Abubakar, M. (2017). “Tasirin Ƙungiyoyin Zaɓi-Sonka Ga Al’ummar Hausawa, Keɓaɓɓen Nazari a Jihar Kaduna”. Kundin Digiri na Farko, Sashen Nazarin Harsunan da Kimiyya, Kaduna: Jami’ar Jaha.

Abubakar, S. (1982). “Birnin Shehu the City of Sokoto: A Social and Economic History. C. 1809-1903”.

Adamu, G. (2012). “Ire-Iren Huluna da Tasirin Kasuwancinsu a Garin Maiduguri”. A cikin Languages, Literature, & Culture, a Festcrift in Honour of Professor Abdulhamid Abubakar, Department of Languages and Linguistics. Maiduguri: University of Maiduguri.

Adamu, H. (1985). “Colonialism, Capitalism, and Crafts in Northern Nigeria, State an Articulation in Sokoto Province 1903-1960”. PhD. Thesis, Department of History “Sokoto: Usmanu Danfodiyo University.

Adamu, M.U. (1999). Confluence and Influence: The Emergence of Kano as a City State. Kano: Munawar Books Foundation.

Ado, A. (2017). Ra’o’in Bincike Kan Al’adun Hausawa. Katsina: Classical Media Enterprises.

Alhassan, B. S. da Abubakar, A. da Zarru}, R. M. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa, Littafi Na Biyu. Iba da n: University Press Limited.

Attahiru, M.K. (2015). “Hanya Mai Gamin Zumuntar Dole: Cuɗeɗeniyar Al’adun Hausawa da Fulani,” Kundin Digiri na Uku. Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeirya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Auta, A.L. (2006). “Tattalin Arzikin Al’umma: Nazarin Sana’o’i Da Kasuwancin Hausawa”. A cikin Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies No.4, Vol. 1. Kano: Benchamark Publisher Limited.

Bagudo, F.A. (2010). “Gudunmawar Mata Ga Bunƙasar Sana’o’i a Garin Sakkwato.” Kundin Digiri na Biyu. Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeirya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Bargery, G.P. (1934). A Hausa-English Dictionary-Hausa Vocabulary. Zaria: ABU Press, Ltd.

Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero: Zaria : Ahmadu Bello University Press.

Collins, U.O. (2011). A History of Onitsha Main Market. M.A Dissertation, Sokoto.

Ibrahim, A. (2023). “Jima da Dukanci a Ƙasar Hausa Jiya da Yau. Kundin Digiri na Uku Sakkwato: Jami’ar UsmanuƊanfodiyo.

Ibrahim, M. S. (1987). “Gudunmawar Sana’o’in Gargajiya na Hausa Wajen Farfaɗo da Tattalin Arzikin Nijeriya.” Takardar da Aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sani. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Imam, A.H. (2023). “Tallafin Kasuwanci Daga Wasu Jama’a ko Gwamnati”. Takardar da aka gabatar a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, Sakkwato.

Sallau, B.A.S. (2009). “Sana’ar Wanzanci da Sauye-Sauyen Zamani”. Kundin Digiri na Uku. Kano”. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero.

Umar,G.G. (2009). Bukukuwan Hausawa. Gusau: Al-fath Prnts. 

Waɗanda aka yi Hira da Su

 

Suna

Shekara

Rana

Adireshi

  1.  

Malam Hakimi

75

12/10/2025

Tudun Hausare

  1.  

Malam Yusuf Giɗaɗawa

67

10/11/2025

Giɗaɗawa

  1.  

Baba Ɗanmamuda

65

23/9/2025

Tsohuwar kasuwa

  1.  

Aminu na Alun Bacaka

38

25/9/2025

Tsohuwar kasuwa

  1.  

Alhaji Chika Sarkin Gishiri

51

18/12/2025

Sabon Titri

  1.  

Alhaji Bello Ƙofar Atiku

42

7/1/2026

Ƙofar Atiku

  1.  

Alhaji Abu Mai Ilmi

85

12/5/2025

Faru

  1.  

Alhaji Zaki Mai Sugar

79

20/5/2025

Sakkwato Rawun

  1.  

Ladan Ciyama

78

2/6/2025

Unguwar Malammai




[1] Hira da Malam Hakimi tsohon ɗan kasuwar Sakkwato 12/10/2025.

[2] Hira da Baba Dan Mamuda tsoho Dankasuwa dake kasuwanci a tsohon kasuwa Sakkwato 1/11/2025.

[3] Hira da Alhaji Cika Sarkin Gishiri a shagonsa da ke tsohuwar kasuwar Sakkwato ranar 18/12/2025.

[4] Hira da Alhaji Cika Sarkin Gishiri shugaban ‘yan kasuwar jahar Sakkwato ranar 18/12/2025

[5] Hira da Dan Mamuda wani tsohon Dan kasuwa a Tsohuwar kasuwar Sakkwato a ranar 23/9/2025. da Aminu na Alhaji Alun Bachaka Dankasuwa a tsohuwar kasuwar Sakkwatoi 25/9/2025 da Alhaji Fodiyon Lawali Bachaka a ranar 25/9/2025.

Dundaye

Post a Comment

0 Comments