Ticker

6/recent/ticker-posts

Neman Saki a Wajen Miji Ba Tare Da Wani Dalili Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Mallam Khamis. Allah ya karɓa wa Malam lafiya, Malam, mene ne ne hukuncin macen ta take neman saki a wajen mijinta ba tare da wani dalili ba? Mace ce ake zaman aure, ba cuta ba cutarwa, amma kullum burinta shi ne Mijinta ya sake ta.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Asali dai a shari'ance a na yin aure ne da nufin sai dai mutuwa ta raba auren ba wai da nufin a rabu ba, shiyasa idan ya kasance Ma'aurata suna irin zamanda a shari'ance babu wata cutuwa a tsakaninsu, to baya halatta ga Mace tanemi saki a wajen Mijinta kamar yadda Mαnzon Allαh (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya faɗa cewa: DUK MATAR DA TA NEMI A SAKE TA BA TARE WANI DALILI BA. BA ZA TA JI KAMSHIN ALJANNAH BA. SHI KUMA KAMSHIN ALJANNAH ANA JIN SA KAFIN A TARAR DA ITA NA TSAWON TAFIYAR SHEKARA ƊARI BAKWAI.

Sabida Haka Hadisin Yana Nuni Akan Idan Mace ta Nemi a sake ta ba tare da Wani dalilin na Shari'ah ba. Ko Kusa da Aljannah ma ba za ta je ba, bare ma ta Shiga Cikin ta. Sabida Haka Wannan Al'amarin Akwai Hadari, Ya Kamata Mata Sudinga Kiyayewa. Musamman Ma Irin Matar da Zaka Samu Kowanne irin Hakki Mijinta yana Fitar Mata. Amma Dan Shedanci Abu Kaɗan Na Kuskure, Wanda Bai Kai ya Kawo ba, Sai ta Ɗora Hannu Akai ta Rufe Idanuwan ta, tace Sai Miji ya Sake ta. Ko kuma ta je ta yi Wa Mijinta Karya a Wajen Iyayenta. Su Kuma Su Ce Sai ya Sake ta. Duk Matar da ta Tirsasa Mijinta ya sake ta haka Kawai Sai ta Haɗu da Jarrabawa a Rayuwarta ta Duniya.

Danhaka asali a shari'ance Mace ba ta da ikon ta nemi saki a wajen Mijinta, to amma idan ya kasance akwai wani sababi ko wata larura da shari'a ta yarda da su to babu laifi idan Mace tanemi saki a wajen Mijinta ba tare da ta biya shi wata fansaba, akwai yanayin ma da yake iya zama wajibi akan Mace ta nemi a sake ta ɗin.

Idan har mace ta takura wa mijinta akan sai ya sake ta ba tare da Wani dalili ba, sai ya a sake ta ɗin amma dole za ta biya kuɗin KUL'I. Ma'ana za ta Biya ka Kuɗin da zaka sake yin wani Auren. Wannan Shi Ake Cewa KUL'I a Musulunci.

Akwai Hadisi daga Abdullahi dan Abbas cewar Matar SABIT IBN ƘAIS ta zo wajen Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ta ce. Ya manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Bana dorawa SABIT Lefin Matsala Akan kula Addininsa ba, haka akan Iya Mu'amular sa ba. Sai dai ina Tsoron bijire Masa. (Ma'ana ba za ta Iya Yimasa Biyayya ba. Sabida ba ta son Shi ) Sai manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce da ita "zaki biya shi gonar sa da ya baki a matsayin gado? Sai ta ce Eh, zan maida masa. sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ba shi umarni akan ya sake ta.

Sabida haka kenan, idan irin wannan ta faru. Wajibi ne zai lisaafa Abinda ya kashe ta Biya shi. Tinda ita ce ta nemi ya sake ta. Sabida Sau da yawa, matan da aka Yiwa Saki Ukku, suna Samu Su Auri Wani daban, daga baya Sai su Tayar Musu Da Fitina Akan sai Sun Sake su. Sabida su sami Dama su Koma Gidan Mazajensu na Baya. Sabida haka Idan Haka ta Faru, za ta Biya ka duk Abinda ka kashe sai ka sake ta. Sai Ta yi tafiyar ta.

Wata Matar Kuma ta Rabu da Mijinta Akan wani Abu da bai Kai ya Kawo ba. sai daga baya idan ta yi wani Sabon Auren. Sai kuma ta ji cewar wannan sabon Mijin Baya Iya gamsar da ita a shimfida kamar Wancan Na baya ɗin. Anan kuma zai Haɗu da Sharrin Mace. Sabida ya Dinga ganin Fitina Kala-kala akan sai ya saketa. Don ta samu ta Koma Gidan Mijinta na Baya. Wasu ma Har waya za ta dinga Yiwa Mijinta na Baya Akan Ita fa ba ta sami wurin zama ba. Wanda kuma ba Mamaki shi ɗin ma ba daɗi bane ya sa ya Rabu da ita ba. Sabida Hankalin ta ya dawo gare shi. Ko kuma Bayan ta Aureka sai take tunanin Yaranta da ta Bari a gidan Mijinta na Baya. A haka sai Tace sai ka sake ta. Ka ga Nan ma za ta biya ka duk Abinda ka kashe mata. Ko ta yi maka wani Auren. Domin zama da ita ba zai yiwu ba.

Sabida haka Mata ku Kiyayewa. Aure ya Wuce Yadda Muke Kallon sa. Domin Shari'ah ne. Ba Wasan Film Bane.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments