Citation: Gado, I. A. (2026). “Samuwa da Bunƙasar Tsohuwar Kasuwar Sakkwato.” In Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies, Vol. 04, No. 01, Pp. 99 – 105. www.doi.org/10.36349/djhs.2026.v04v01.013.
SAMUWA DA BUNƘASAR TSOHUWAR KASUWAR SAKKWATO
Na
Ibrahim Alhaji Gado
Ɗalibin
Ph.D., Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
Tsakure:
Wannan takarda ta yi magana
ne a kan yadda aka samuwar da tsohuwar kasuwar Sakkwato, yadda aka fara
hada-hadar saye da sayarwa, da yadda kasuwar ta bunƙasa. Dalilin gudanar da wannan takarda shi ne tunanin da take da
na cewa har zuwa yau jama’a da dama ba su san yadda aka samu tsohuwar kasuwar
Sakkwato ba a matsayin wurin da ya ba ‘yan kasuwa damar haɗuwa domin gudanar da
kasuwancinsu. Manufar wannan takarda shi ne yin bincike domin fito da wasu
muhimman abubuwa da suka faru suka zama tushen samun tsohuwar kasuwar Sakkwato.
Sakamakon da takardar ta samar shi ne lokaci mai tsawo an samu wasu ƙananan muhallai da wasu jama’a da suka daɗe suna kasuwancin wasu
hajjoji da suka shafi buƙatun al’umma na gida da na
waje. Domin cimma wannan manufa an samu bayanai kan muhimman wuraren kasuwanci
da irin tasirinsu da yadda aka fara hada-hadar kasuwanci a wurin, da kuma irin
sauyin da aka yi ta samu na kasuwanci a waɗannan wurare. An yi amfani da hanya hira da masana, tsofaffiin
mutanen da suka yi kasuwanci a tsohuwar kasuwar Sakkwato. An yi amfani da Ra’in
sauyin al’adu(Social Change theory). Ta haka aka samu bayanan da aka gudanarda
wannan takarda.
1.0
Gabatarwa
Al’amurran kasuwanci a Sakkwato kamar kowane yanki na
al’umma ne a ƙasar Hausa da aka daɗe ana cin gajiyarsa, wanda ya kai babu wata hanya mai
saurin bunƙasa al’umma da tattalin arziki kamar sana’a da kasuwanci.
Wannan ya sa duk lokacin da al’umma ta fara yaɗuwa sai ta fara tunanin samun sauye-sauye na rayuwarsu ta
hanyar samun wani abu da za su yi sana’a. Sakkwatawa sun fara da sana’ar noma
har suka shiga wasu sana’o’i. Sannun a hankali suka fara ware wasu wurare domin
ajiye wasu kayayyakin biyan buƙatunsu na rayuwa. Daga nan ne aka fara samun wuri wanda
ake kira wurin kasuwanci wato saye da sayarwa. Sakkwatawa sun daɗe suna amfana da irin wannan hanya, kusan
kowace unguwa akwai wani muhalli ko fili da aka ware domin ajiye wani abu na
sayarwa ko da abinci ne, wanda za a kira wurin da suna wurin sayar da abinci.
Da haka aka yi ta samun wuraren kasuwanci mabanbanta.
Wannan maƙala ta fito da wasu muhimman wurare da ake aiwatar da
kasuwanci da suka zama tushen samun tsohuwar kasuwar Sakkwato, ta kuma kawo
bayanin su dalla-dalla, muhimmancin yin haka zai taimaka wurin tattaro bayanai
domin haɗa bayanan al’adun kasuwanci
na asali da suka zama jagora ga kafa tsohuwar kasuwar Sakkwato. Wannan takarda
ta yi ƙoƙarin kawo yadda muhalli da wasu jama’a da buƙatun rayuwa suka agaza
wajen kasuwanci (saye da sayarwa) an gudanar da aikin ne ta hanya tattaro
bayanai daga dattawa da tsofafin ‘yan kasuwa na garin Sakkwato.
2.1 Kasuwanci
Sanin asalin kalmar yana iya taimakawa wajen bayar da
ma’anarta a ilmance. Kalmar kasuwanci ga dukkan alamu masana sun nuna cewa ba
Bahaushiyar kalma ce ba. An aro ta ne daga harshen Kanurii, wato ‘kasuk’ sai
Bahaushe ya yi mata gyaran fuska zuwa kasuwanci. Ta ɓangaren ma’ana kuwa. Masana da manazarta da ɗaliban al’ada da dama sun tofa albarkacin
bakinsu game da ma’anar kasuwanci, kamar Alhassan da wasu (1987:28) suna cewa,
a saya a sayar shi ne kasuwanci. Wato anan mutum ya fitar da kuɗinsa ya sayi ƙadara ko wani abu ko haja.
Sannan wani lokaci ya fitar da wannan ƙadara ya sayar shi ne
kasuwanci.
Shi kuma Ibrahim (1987) ya yi hasashen cewa, an samo
kalmar kasuwa ne daga Barebari wadda ake ce mata ”kasuk” ya nuna cewa bayan an
kafa kasuwanni da zarar ana son a yi musayar wani abu sai a kai shi kasuwa
domin a musanya shi da wani abin. Ta wannan hanya ce aka sami yanayin ciniki,
na bani gishiri in baka manda.
CNHN (2006:238) cewa ya yi:“Kasuwanci, sana’ar saye da
sayarwa a kasuwa.”
Umar (2009:9) a nasa ra’ayin cewa ya yi:“Kasuwanci wata
hanyar hulɗa ce, ta saye da sayarwa
tsakanin jama’a.”
Kamar yadda aka gani a waɗannan ma’anoni da suka gabata, tabbas haka abin yake,
domin al’amarin kasuwanci da jama’a ake yi. Ba zai taɓa yiwuwa a yi kasuwanci ba tare da jama’a ba domin kuwa
abu ne da ya shafi saye da sayarwa tsakanin mutane. Idan aka yi la’akari
da ƙunshiyar waɗannan ma’anoni da magabata
suka bayar kan kasuwanci, wannan takardar ta aminta da cewa, kasuwanci yana
nufin duk wata dabarar sarrafa wani abin amfani da za a iya samun wani abu
daban don samun biyan wata buƙata don cigaban rayuwa.
3.1 Tsohuwar Kasuwar Sakkwato
Birnin Sakkwato yanki ne da aka daɗe ana hulɗar kasuwanci a ciki tun
kafin zuwan Larabawa da Turawa, inda ake baje kolin kayan da Hausawa suke
sarrafawa na gargajiya. Hulɗar ta ci gaba da wanzuwa
har zuwa lokacin da suka haɗu da Larabawa ‘yan kasuwa
da suke zuwa daga ƙasashe daban-daban. To, daga wannan lokacin aka ci gaba
da samun baƙi, inda suke shigowa da sababbin abubuwa na kasuwanci
wanda ya sanya dole aka samar wa wurin kasuwancin bagire wanda ake kira kasuwa
inda ake zuwa da haja a ciki da wajen ƙasar nan don tarawa da saye
da sayarwa. Wurin ya bunƙasa har aka kira shi da kasuwar ‘yar gabas. Bayan da
wurin ya bunƙasa, sai aka ga wurin ya yi wa ‘yan kasuwar ƙaranci, sai aka yi tunanin
samun wani wuri inda zai wadaci ‘yan kasuwar. Ta haka aka samar da kasuwar da
ake kira ‘yar dole, wacce take daga gabas, wurinda a yanzu ya zama rukunin
shagunan ajiye kaya ( Store) kuma ita ce ‘yar gabas. Tsohuwar kasuwa ta yanzu
ta ƙunshi ɓangaren Masallacin Shehu
zuwa ƙofar Aliyu Joɗi da titin Ahmadu Bello da shagon goro da Marafa Ɗanbaba da Runjin Ragga da
yankin rukunin gidajen Ɗanjabalu.[1]
4.1 Bunƙasar Tsohuwar Kasuwar
Sakkwato
Kasuwar ta fara samun haɓaka da bunƙasa ne a shekarar 1960, inda ta zama cibiya ta manyan
‘yan kasuwa wato (Central Market) kuma a wannan lokacin, ana samun manyan ‘yan
kasuwa da suka mallaki manyan shaguna a wannan kasuwar da ake kira ‘yar dole.
Irin waɗannan manyan ‘yan kasuwa
sun haɗa da: Alhaji Atu da
Alhaji Ɗanjibo Ƙwanni da Alhaji Mamman mai ‘yar ganga da Aliyu Joɗi da Na’allah Buda Ƙofar Rini da Alhaji Mamman
na Ussu da Amadi Wulli Rijiyar Ɗorawa da kuma Abdu Kayama Marmaro. Haka kuma,
akwai Alhaji Ibrahim Dan’utte Zarumawa da Malami Ɗanmaraya Faru da Alhaji
Sodagi Unguwar Rogo da Alhaji Abdun Inga Nufawa da Kadi Mai katifa Ƙofar Kware da Alhaji Baƙon Dare Assara. Sauran su
ne, Malam Daɗi Wangarawa da Alhaji Ɗan Kabo Tambuwal da Ali
Rami Kware da Alhaji Yusuf Dayi Kware da Ladan Mai wake Kware da Alhaji
Muhammad Sarkin magani Gwadabawa da Sarkin Gobir Adiya da Jafar mai ruwa Gabas
da Alhaji Dan Tabukka Cimola da kuma Ba’are Dogon Daji ‘yar Sakke. Har wayau, akwai
mutane irin su, Alhaji Aji Adarawa da Sarkin Atttajirai Dasuki Assarakawa da
Amadu Citta Illela da Alhaji Ladan Mai turare Rumbukawa da Alhaji Mamman na mai
Kosai Shuni da Alhaji Arzika Sarkin Giribshi da Altine Tarke da Alhaji Sayidi
Tarke da Alhaji Abarshi Goronyo da Abdun Ƙofar Aliyu Joɗi da Alhaji Sabo Shuni da Alhaji Maidamma
Shuni da Alfa da Alhaji Baƙon Dare Katangar Ɗunɗi da Alhaji Turawa Ɗan Atte da Alhaji Maiturare
Dogon Daji da kuma Alhaji Mamman Ɗansakola Dancaɗi. Waɗannan ‘yan kasuwa sun
taimaka wajan samun bunƙasar tsohuwar kasuwar Sakkwato, domin wasu wurare da aka
samar an samar da su ne hanyar sunayen waɗannan ‘yan kasuwar a wancan lokaci.[2].
4.1.2 Samar da Hanyoyin Zirga-Zirga
Wata hanyar kuma da ta ƙara bunƙasa kasuwanci a tsohuwar
kasuwar Sakkwato kuma ita ce, samar da hanyoyin zirga-zirga inda aka samar da
manyan godabbu guda uku da suka haɗa tsohuwar kasuwa da wasu
muhimman wurare na shigo da kaya. Waɗan da aka yi wa suna da, Godaben
Sultan Bello (Sultan Bello Road) da Godaben Firin Alezandi
(Prince Alexander Road) da kuma Godaben Gusau (Gusau Road).
Haka kuma a 1951 aka samar da filin sauka da
tashin jiragen sama a Sakkwato wanda ya ke a
kan titin Gusau, wanda a 1977 aka mayar da shi Ƙasarawa da
ke kan hanyar zuwa Birnin Kebbi. Waɗannan hanyoyi sun taimaka wajan sauƙaƙawa ‘yan kasuwa wajan
shigowa da fitar da kaya zuwa wurare daban-daban, ba tare da samun tsaiko ba.
4.1.3 Samun Tashar Ajiye Kaya
Baba Ɗanmamuda a hira da akayi da shi ya bayyan cewa, wani abu
da ya ƙara bunƙasa kasuwanci a tsohuwar kasuwa shi ne samar da tashar
ajiye kaya (wurin ɗauka da sauke kaya), inda
manyan motocin dakon kaya suke saukar da kaya, guda uku da suke kusa da kasuwar
da ake kira ‘yar dole. Waɗan nan wurare su ne Ƙwarni lorry park da wurin
fakin na G.T. Bank da yake kan titin Ahmadu Bello da kuma wurin da ake kira
Savanna Bank. Babbar mahaɗar waɗannan motocin shi ne Union Bank da ke hanyar shiga
tsohuwar kasuwa ta farkon da wannan da ake kira ‘yar dole.
4.1.4 Samun Hanyoyin Saka Jari
Alhaji Cika Sarkin Gishiri ya bayyana cewa, samar da
hanyar saka hannun jarin ‘yan kasuwa da manyan kamfanonin da ke buga kaya
daban-daban ya ƙara bunƙasa kasuwanci a tsohuwar kasuwar Sakkwato. Wanda ya
haifar da samun wakilci na kamfuna da za su tallata hajar su ga ‘yan kasuwa da
samar da hanyar da za a yi sufurin kayan zuwa ga ‘yan kasuwar, cikin sauƙi ba tare da sun tafi
kamfunnan da kan su ba.
4.1.5 Samun Fito da Takardar Shedar Ciniki (Invoice)
Baya ga wannan kuma, akwai maganar (invoice)[3] da manyan ‘yan kasuwa
suke amfani da shi wanda za a rubuta kaya da farashin su a tura wa abokan hulɗar kasuwanci su turo da kuɗi a tura masu kaya. Wannan shi ma ya bunƙasa harkar kasuwanci sosai
a tsohuwar kasuwar Sakkwato. Wayar hannu da akwatin cire kuɗi na P.O.S, sun taimaka sosai wajan bunƙasar kasuwanci a tsohuwar
kasuwar Sakkwato ta hanyar tura kuɗaɗe ga abokan kasuwanci.[4]
5.1 Samar da muhimman Wurare Kasuwanci A Tsohuwar Kasuwar
Sakkwato
A tsohuwar kasuwar Sakkwato akwai wuraren kasuwanci
daban-daban waɗanda duk safiya ana gudanar
da hada-hada kasuwanci a cikinsu, kuma kowane bagire yana da sunan da ake kiran
sa da shi, kuma kowane wurin da irin hajar da ake sayar wa a wurin. Ga bayanin
su kamar haka:
i. Shagon Goro
Shagon-goro wuri ne mai cikakken suna da tasiri da tarihi
a tsohuwar kasuwar Sakkwato tun lokacin da aka baro ‘yar gabas aka dawo ‘yar
dole, wanda ba yadda za a yi a yi maganar tarihin tsohuwar kasuwar da ake kira
‘yar dole ba a yi maganar shagon- goro ba wanda shi ne wurin da ya fara suna da
shahara wajen shigowa da saukar da kayan da ake shigowa da su da ga kudu da
kuma sauran wurare daban-daban a faɗin jahar Sakkwato. Shagon- goro wani bagire ne da ke kudu
da tsohuwar kasuwa inda ake shigowa da kaya daga kudu. Asalin wurin wuri ne da
Yarbawa daga kudancin Najeriya ke kawo kayan da suka zo da su daga
yankunansu.Tun lokacin da ake zuwa Kurmi (Legas) da Gwanja (Ghana) ana sufurin
kaya ta hanyar dabbobi da ɗaukar su a saman kai zuwa
arewacin Najeriya. Shagon goro nan ne babban wurin da suke sauka su raba kayan
ga ‘yan kasuwa masu fataucin su daga wurare daban-daban.
Babban
abin da suka fi kawowa a wurin shi ne goro shi ya sa aka san ya wa wurin suna shagon goro. Haka
kuma suna kawo lemu da gwaiba da ayaba da gade da mangoro da ake kira ɗan odoba da
abarba da oro da gorar yaji da ɗiyan miya da ayoyo wanda ake yin miya da shi. da kwakwa da
takalman roba da gishiri da kanwa da man ja da roba da sauran abubuwan da babu su a Arewa. Su kuma suna sayen kaya daga nan Arewa su tafi da su kudu, kamar ƙirgi da walki da wake da suren soɓo (soɓorodo) da gyaɗa da kwaruru da riɗi da waken suya da miyar yoɗo da goriba da mazari
na kaɗin zaren gargajiya da saƙi da zannuwan da Hausawa ke sarrafawa, kamar birgima
da Bakurɗe da allura huda. Wadda ake saƙa da ita da albasa da tanka
tarugu da tatasai da kaji da dabbobi daban-daban kamar, tumaki
da awaki da shanu da tantabaru da agwagwa. Shagon goro wani ɓangare ne na gonar sarkin Musulmi Tambari da aka bayar domin a yi
kasuwa.
ii. Gidan Ƙyame
Alhaji Abu Mai Ilmi ya bayyan cewa. Ƙyame wani nau’in abinci na
tsutsa ne da ake samu daga ɗiyan kuka da akan
fasa ɗiyan a samar da wasu ƙananan diya farare
masu ƙarammin saye a ciknsu. Bagiren da ake kira gidan ƙyame a tsohuwar kasuwar
Sakkwato wuri ne mai cikakken tarihi tun lokaci mai tsawo. Asalin sa wuri ne da
ake sayar da ƙyame wanda mafi yawa Kabawa ne suke kawo shi daga Kabi,
suna hada-hadar saye da sayar da shi a tsakanin ‘yan kasuwa masu sayensa daga
wurare daban-daban a faɗin jahar Sakkwato. kamar
Illela da Sabon Birni da Gada da Gwadabawa da Kware da Wamakko da Binji da
Dogon Dutse da ƙwanni a jamhuriyar Nijar da ma ƙasashe daban-daban. Mutanen
jahar kabi, su aka fi sani da aikin sarrafa shi da shigo da shi daga wurare
daban-daban zuwa wannan tasha da ake kira gidan ƙyama. Ta hanyar jiragen
ruwa kwale-kwale da raƙuma da jakuna. Wannan wuri yana bisa titin Ahmadu Bello
Yamma ga Shagon goro, wanda ya zama wani sansani na fatake ‘yan kasuwa masu
shigowa daga kudanci da yammancin Sakkwato. a tarihin gidan ƙyame kamar yadda binciken
ya tabbatar ƙyame kawai ake sayarwa a wurin, sai hada-hadar mutane
fatake masu tafiya. Domin wurin yana kusa da tashar Bodinga, inda nan ne
matattara da wurin zirga-zirgar ‘yan kasuwa da ke shigowa daga kudu da yammacin
Sakkwato. Gidan Ƙyame wuri ne mai tasiri da tarihi a tsohuwar Sakkwato,
wanda in an yi maganar bunƙasar tsohuwar kasuwar Sakkwato sai an yi magana akansa.
iii. Marafa Dan Baba
Asalin sunan Marafa Dan Baba surukin Sardauna Ahmadu ne
yana auren ɗiyar Sardauna wadda ake
kira Luba kuma ɗan kasuwa ne yana sana’ar
hatsi da abinci, zuwa wannan wurin da ake kira Marafa Dan Baba. Da siyasar su
Sardauna ta ci sai aka ba shi wannan sarauta ta marafa Dan Baba, aka kuma ba
shi kwangiloli a cikin gwamnatinsu wannan ya sa ya yi suna, kuma ya yi karfi a
cikin jahar Sakkwato. kuma Dansa Hassan ya yi sarautar magajin garin Sakkwato,
wannan wurin yana nan a cikin tsakiyar tsohuwar kasuwa. A farkon buɗa wurin ana sayar da kayan da Hausawa ke nomawa na lambu. Kamar tumatur da albasa da
tanka da alaiyahu da sure da yakuwa da zogala da rama. Daga baya aka fara kawo
kayan wanki kamar toka soda da omo da ake fitowa da su daga Lagas zuwa wannan
wurin domin sayarwa. Haka kuma an yi sayar da alawar likko wadda ake kira
alewar likko babba da ake zuwa da ita daga Gusau kuma ana ce mata alewa mai
kifi. Ahalin yanzu wurin an mayar da shi gini na zamani da falaza-falaza na zamani.[5]
iv. Ɗan Jabalu
Asalin wurin da ake kira Ɗanjabalu a halin yanzu wuri
ne da ke a ƙofar da ake kira Ƙofar Sarauniya a wancan
lokacin. Ɗanjabalu shi ne ke rike da sarautar da ake kira Majidaɗin Sarkin Musulmi, Ubansa kuma ɗan Galadiman Sarkin Musulmi ne Abubakar na Ukku. Bayan da
aka raba wurare a tsohuwar kasuwa sai sarkin Musulmi ya ba da wurin ga
Majidaɗin Sarkin Musulmi Alh. Mu’azu Ɗanjabalu.
v. Wurin Abdun Zagi
Abdun Zagi sunan mutum ne sunansa Abdullahi Ubansa shi ne
Zagi wato Zagin Sarkin Musulmi wanda ya ke shiga gaban dokin sarki ya rataya
bargo da buta yana jaye da dokin Sarki, shi ne muƙamin Ubansa. Abdun Zagi
asalinsa baduku ne mai gyaran takalma saboda tsare gaskiyarsa Sarkin Musulmi
Abubakar na Ukku ya zaɓe shi domin ya yi wa Turawa
dillacin fata domin su fita da ita zuwa ƙasashensu. Wurin fili ne
babba da aka ware domin gudanar da hada-hadar fata da auduga da gyaɗa inda ake tara su a ɗaka zuwa Kano daga nan a fita da su ƙasashen waje. Turawan sukan
yi amfani da sikeli ma’auni na zamani domin awon fata da auduga da gyaɗa a wurin, inda daga baya ana kawo takwala da
kayan rini da na saƙa. wurin a yanzu ‘yan atamfa ne suka mamaye shi da masu
sana’o’ln da suke bazawa a hanya
vi. Wurin Bazzazage
Malam Hakimi ya bayyana cewa. Bazazzage suna ne na laƙabi wanda kane ne ga Abdun
Zagi kuma kusan wuri ɗaya ne domin kuwa da aiki
ya yi wa Abdun Zagi yawa sai ya ware wani fili ya ba Bazazzage a cikin wurin.
Kuma duk suna gudanar da sana’a iri ɗaya. Idan ana buƙatar ganin Abdun Zagi, ko wani yana buƙatar yin hulɗa da shi ta kasuwanci to Bazazzage ya kan yi
jagoranci zuwa ga Abdun Zagi.
vii. Tudun Zabarmawa
A hirar da aka yi da shi Baba Ɗanmamuda ya bayyana cewa.
Tudun Zabarmawa yana bisa titin Marafa Ɗan Baba daga sama kuma haɗe da unguwar Hausare. Asalin wurin Zabarmawa
ne suke zuwa daga ƙasar Nijar musamman Dogon Dutse, inda Hausawa ke yi wa
wurin kirari da “Dogon Dutse lahira Bazabarme” Zabarmawa kan zo da kayansu, su
baje kolinsu a wurin irin kayan da suke zuwa da su kayan miya ne kamar batso da
balma da jar kanwa da ‘ya’yan itace kamar aduwa da gwaddar masar da kurna da
magarya da gawasa da bagaruwar ƙasa da kayan shimfiɗa kamar wundi ɗan asala da malfa da fayafai da ƙananan wundaye na sallah da
makuru wanda mata ke ɗaurawa da jiran tsada wanda
ake yin turare da shi da turaren jawul wanda ake yi da jirai da turaren jibda
wanda suke zuwa da shi cikin ƙumba da kitsen zaki da sauran wasu magunguna gargajiya.[6]
6.1 Sakamakon Bincike
Maƙalar ta yi ƙoƙarin fito da wasu muhimman wurare da suka yi
tasiri sosai wajen samar da wuraren kasuwanci a tsohuwar kasuwar Sakkwato, waɗanda su ne suka fara samuwa. An samar da waɗannan wurare ne ta hanyar sunayen fitattun
‘yan kasuwa da suka yi suna a wurin. Daga cikin sakamakon da maƙalar ta samar, akwai:
i. Kasuwanci wani fage ne da ba shi da babba, kuma ba shi da
yaro. Kusan duk wanda ya sa kansa da shi yake tafiya
ii. Bunƙasar wurin kasuwanci yana yin tasiri sosai wajen samar da
sunan bagiren kasuwanci a kasuwa da duk wurin wata hada-hada.
iii. Lallai samuwar wuraren kasuwanci a tsohuwar
kasuwar Sakkwato ya sauƙaƙa wa ‘yan kasuwa wajen sauka da ɗaukar kaya zuwa ɓangarorinsu daban-daban.
iv. Wuraren kasuwanci da aka samar sun kasance
wata mahanga da ke jagorantar mai sayen kaya zuwa ga abin da yake son saye ko
sayarwa.
v. Wasu jama’a da suka sadaukar da kai a kasuwanci tsohon
kasuwa Sakkwato.
vi. Zamanin ya yi tasiri ga kafuwa da cigaba
tsohuwar kasuwar Sakkwto.
6.2 Shawarwari
Matuƙar ana son gyara a harkar kasuwancin tsohuwar kasuwa da
kuma samun bunƙasar tattalin arziki, to dole ne al’umma su rungumi
abubuwa kamar haka:
i. Cire son rai ga harkar kasuwanci wanna zai taimaka wajen
fahimtar juna da samun mafita ga kasuwancinsu.
ii. Ƙungiyoyin ‘yan kasuwa su samar da tsari na bai ɗaya wanda za a riƙa lura da yadda shigowar
abubuwa na zamani da rungumarsu ke haɓɓaka kasuwanci.
iii. Inganta hanyoyin shiga wuraren kasuwanci,
domin lokacin damina shiga wasu wuraren yana da matuƙar wahala sakamakon ruwan
sama da toshewa hanyoyinsu.
iv. Tsare gaskiya a yayin gudanar da hada-hadar
kasuwanci.
7.1 Kammalawa
Wannan maƙala ta tattauna kan wasu muhimman wuraren da ake gabatar
da kasuwanci a cikinsu waɗanda suka shafi wani ɓangare na tsohuwar kasuwa Waɗan da dasu ne tsohuwar kasuwa ta fara ginuwa.
Bayan gabatarwa, an yi ƙoƙarin ma’anar kasuwanci daga bakin masana daban-daban. An
yi bayanin tsohuwar kasuwa da hanyoyin da ke sada mutun zuwa tsohuwar kasuwa da
yadda aka sama wa wuraren kasuwanci suna ta hanyar manyan ‘Yankasuwa da suka
fara harakar kasuwanci a wurin, wanda duk da sauye-sauyen zamani da aka samu
har yanzu wasu wurare na nan riƙe da sunansu.
Manazarta
Abdullahi, K. (1978). “Exchange and the Origins of Market in West
Africa: A Case Study of Kasuwar ‘Yar Dole in Sokoto”. B.A History, Sokoto:
Department of History, Usmanu Danfodiyo University.
Abubakar, J. (2017). “A History of Shinkafi Market.” M.A.
Dissertation, Sokoto: Department of History, Usmanu Danfodiyo University,
Sokoto.
Abubakar, M. (2012). “Unguwannin Sakkwato da Al’adunsu,” Kundin
Digiri na Biyu (M.A). Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar
Usmanu Ɗanfodiyo.
Abubakar, M. (2017). “Tasirin Ƙungiyoyin Zaɓi-Sonka Ga Al’ummar Hausawa, Keɓaɓɓen Nazari a Jihar Kaduna”. Kundin Digiri na Farko, Sashen Nazarin
Harsunan da Kimiyya, Kaduna: Jami’ar Jaha.
Abubakar, S. (1982). “Birnin Shehu the City of Sokoto: A Social
and Economic History. C. 1809-1903”.
Adamu, G. (2012). “Ire-iren Huluna da Tasirin Kasuwancinsu a Garin
Maiduguri”. A cikin Languages, Literature, & Culture: A Festcrift in Honour of Professor Abdulhamid Abubakar, Department of Languages and Linguistics. Maiduguri: University
of Maiduguri.
Adamu, M. U. (1999). Confluence and Influence: The
Emergence of Kano as a City State. Kano: Munawar Books Foundation.
Ado, A. (2017). Ra’o’in Bincike Kan Al’adun Hausawa. Katsina:
Classical Media Enterprises.
Alhassan, B. S. da
Abubakar, A. Da Zarruƙ, R. M. ( 1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa,
Littafi Na Biyu. Ibadan: University Press Limited.
Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero: Zaria :
Ahmadu Bello University Press.
Ibrahim, M. S. (1987),
“Gudunmawar Sana’o’in Gargajiya na Hausa Wajen Farfaɗo da Tattalin Arzikin Nijeriya,” Takardar da Aka Gabatar
a Taron Ƙara wa Juna Sani. Kano: Sashen Harsunan Najeriya ,
Jami’ar Bayaro.
Umar, ( 2009). Bukukuwan
Hausawa. Gusau: Al-faith Prints.
Usman, I. (2010) History of
Gross and Development of Metropolotant, Sokoto 1900-2007. Ph.D Thesis. Sokoto;
Department of History, Usmanu Danfodiyo University.
Waɗanda aka yi Hira da Su
|
|
Suna |
Shekara |
Rana |
Adireshi |
|
1. |
Malam
Hakimi |
75 |
12/10/2025 |
Tudun
Hausare |
|
2. |
Malam
Yusuf Giɗaɗawa |
67 |
10/11/2025 |
Giɗaɗawa |
|
3. |
Baba Ɗanmamuda |
65 |
23/9/2025 |
Tsohuwar kasuwa |
|
4. |
Aminu na Alun Bacaka |
38 |
25/9/2025 |
Tsohuwar kasuwa |
|
5. |
Alhaji Chika Sarkin Gishir |
51 |
18/12/2025 |
Sabon Titri |
|
6. |
Alhaji Bello Ƙofar Atiku |
42 |
7/1/2026 |
Ƙofar Atiku |
|
7. |
Alhaji Abu Mai Ilmi |
85 |
12/5/2025 |
Faru |
|
8. |
Alhaji Zaki Mai Sugar |
79 |
20/5/2025 |
Sakkwato Rawun |
|
9. |
Ladan Ciyama |
78 |
2/6/2025 |
Unguwar Malammai |
[1] Usman
I. 2010 ya kawo kwatankwancin irin wannan bayani
a cikin aikinsa mai taken History Growth and Development of Metropolitan Sokoto
1900-2007, sh. na 137.
[2] Muhammad A.J. 2017
A cikin kudinsa mai taken “A History of Donkey Trade in Sokoto State.”
[3] Wani
kundi ne da ‘yan kasuwa ke amfani da shi mai ɗauke da suna da wurin kasuwanci ,
wanda ake rubuta adadin kaya da farashinsu, ko kuma a yi amfani da kwamfuta
wajan tsarawa da fitarwa.
[4] Hira da Alhaji Aminu mai P.O.S Ranar
25/5/2025.
[5] Hira da Alhaji Bello Ƙofar Atiku Ranar
7/1/2026.
[6] Hira
da Baba Ɗanmamuda wani dattijo wanda ya daɗe yana harkar kasuwanci a tsohuwar
Kasuwar Sakkwato, da kuma Alhaji Cika Sarkin Gishiri, Shugaban Gamayyar
Ƙungiyoyin ‘Yan Kasuwar Sakkwato da Alhaji Bashar na Alhaji Adamu ɗan kasuwa a
Tsohuwar Kasuwar Sakkwato.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.