Ticker

6/recent/ticker-posts

Wane Ne Farfesa a Farfesance? (Hannunka Mai Sanda Ga Magabata, Hayya! Ga Mabukata, Kashedi Ga ‘Yan Kallo)

Article Citation: Aliyu Muhammadu Bunza (2020). Wane Ne Farfesa A Farfesance? (Hannunka Mai Sanda Ga Magabata, Hayya! Ga Mabuƙata, Kashedi Ga ‘Yan Kallo). DEGEL: The Journal of the Faculty of Arts and Islamic Studies, Vol. 18, No. 2. ISSN 0794-9316

WANE NE FARFESA A FARFESANCE? (HANNUNKA MAI SANDA GA MAGABATA, HAYYA! GA MABUƘATA, KASHEDI GA ‘YAN KALLO)

Na

Aliyu Muhammadu Bunza

Tsakure

Muƙamin Farfesa shi ne, mataki na ƙarshe da ɗalibin ilmi zai kai ya yi fice cikin fagensa. Muƙami ne da sai an ratsi farfajiyar duniyar karatu mai tsawo gabanin a same shi. Wannan takarda ta yi yunƙurin lalubo fassarar kalmar ita kanta daga harshen da aka samo mata sunan “Ingilishi”. An ɗan yi bayanin daɗa juna sani da masana Hausa suka yi gabanin su tsayar da kalmar “Farfesa” a Hausance. An mayar da hankali gadan-gadan a kan yadda Bahaushe ke son ya ga Farfesa, ya ji Farfesa. Haka kuma, an kalli Farfesanci a matsayin ire-iren abubuwan da ya kyautu a ce, Farfesa ya sa ƙwazo a kansu domin tabbatar da martabar kujerar Farfesa. Aka sake ɗauraye takardar da ɗan ƙaramin fasalin da ya yi daddage sosai a kan tabbatar da muƙamin kujerar ita kanta. A yunƙurin kafa hujjoji da tabbatar da su, an gayyato fitattun mawaƙan baka 7, marubuci 1, an sarrafa ɗiyan waƙa 11, an narka ƙissoshi 10, kirari 1, da ƙaƙale 1, domin nagartar da hujjojin da aka sussuka. Haƙiƙa, yadda aka san kujerar Farfesa a da, a yanzu, kama da wane ba wane ba ne. Matsalar durƙusawar ilmi ruwan dare game duniya ne, kowa na da hannu a ciki, sai an taru a gyara. Da dai za a kafa wasu mujalloli na tarayya da za a keɓe wa Farfesoshi kawai, kuma a tilasta ganin shawagin kowa a ciki da dole nakiya ta yi zaƙi. Idan aka ƙara da keɓe wa farfesoshi rana ɗaya kowace shekara, da za su gabatar da gagarumar lacca da za ta fito da ɗan wani abu sabo da suka hango, da abu ya yi. Matuƙar hukuma ba ta tuba da yi wa ilmi ta’addanci a kasafin kuɗi ba, manyan kujerin ilmi ba za su kafu da ƙafafunsa ba. Ga alama, rashin hasken fitar ba laifin gwalab ba ne, laifin batir ne.

Gabatarwa

Buƙatar kowace rayuwa ta kai matuƙa ga muradin sha’awarta. Labudda kowane mutum akwai abin da ya gada, ko abin da ya yi haye, ko abin da ya koya. Gurin ɗalibin Alƙur’ani ya kai ga “dogon alif maƙarar basin”. Kowane uba fatarsa ɗansa ya gaje shi. Matuƙar ba a ce wa ɗan galadima “sarki” ba, buƙata ba ta biya ba. Babu wani ɗan sana’a da ba ya burin ya yi wa tsara fintinkau ya sarauce su. Lallai yin nasarar kai buri ke sa a tattaro ‘yan’uwa da abokan arziki a yi bukin mun gode. Shekarar da Narambaɗa ya samu muƙamin malamin waƙa (wato kamar Farfesan Waƙa) ya ƙago bakamdamiyarsa ga yadda ya yi walimarsa:

Jagora: Ko waz zaka kallo ya karkaɗe kunnenai,

Yara: Ga makandamiya za ni yi cikin manyan waƙoƙi

Jagora: Na jiya Jankiɗi

Yara: Ya yi tai uwar waƙa sai nai tau

Jagora: Na jiya Zamau

Yara: Ya yi tai uwar waƙa sai nai tau

Jagora: Na jiya Gurso

Yara: Ya yi tai uwar waƙa sai nai tau

Jagora: Na jiya Akwara

Yara: Ya yi tai uwar waƙa sai nai tau

Jagora: Na jiya Ɗandawo

Yara: Ya yi tai uwar waƙa sai nai tau

Jagora: Na jiya Nagaya

Yara: Ya yi tai uwar waƙa sai nai tau

Jagora: Dodo malamin waƙa kundumin magajin Ɗanɓaidu

Yara: Ya yi tai uwar waƙa sai nai tau

Jagora: Kullum ji nikai azanci na hudo min

Yara: In wani ya hi ni martaba ni kau na hi wani

Jagora: Ai kyan mafarauci

Yara: Ya ɗau kare ya kiyaye yah hi

Jagora: Shi dillali

Yara: Da an saya ya hwaɗi ad daidai

Jagora: Shi ko arne

Yara: Ya kama noma daidai an nan

Jagora: A sai mai kwando

Yara: Ya barbaɗe taki ad daidai

Jagora: Shi makaɗi kau

Yara: Shi gyara turu daidai an nan

Jagora: Ni kan kun gane ni

Yara: Na gyare turuna

Jagora: Sai zuba waƙa nikai

Yara: Kama da ta Alfa Zaazin[1]

Gindin Waƙa: Gwarzon shamaki na Malam toron giwa

: Baban Dodo ba a tamma da batun banza.

A ma’aunin malaman addinin Musulunci na Afirka ta Yamma, duk wani yabo baya ga na Annabi Muhammadu (SAW) yake. A fagen yabon Annabi (SAW) “Ishiriniyar” Alfa Zaazi ta cancanci kujerar Farfesa. Don haka, kowane mawaƙin Hausa ke burin zama Alfa Zaazi.

Zubin Karatun Allo Da Boko A Ƙasar Hausa

Karatun boko a ƙasar Hausa cikon sunna ne makaho da waiwaya, domin ko da iska ya zo ya tarar da kaba na rawa. Boko ya tarar da mu da iliminmu na addini da duniya da littattafai da fasahar karatu da rubutu da bincike cikin harsunanmu. A tsarin karatun addininmu, idan yaro ya iya Fatiha zuwa “Alam Tara” a baki da ƙidan baƙi, sai a dafa wake a yi walima. Idan ya turza ya kai “Sabbi” sai a yi masa walima da tuwo. Idan yana fara wa kansa rubutu kowane hizo za a yi masa walima da tuwo. Da ya kai “Ƙuluhiya” sai a yanka bunsuru. Idan likkafa ta ci gaba ya kai “Ƙaala” rabin Alƙur’ani sai a yi babbar walima ta cikin gida. Da ya soma dafa “Bara’atu” sai babban bunsuru na a zo a gani. Idan ya kai dogon “Alif” sai zayyana da gangamin bukin babbar sauka muradi ya samu, ya samu lasisi karatun Alƙur’ani sai a naɗa masa babban rawani, digiri ya samu[2]. In ya hardace ya zama “Alaramma”.In ya rubuta da hannusa ya zama “Gwani”. In ya goge ya kai matsayin gyara wa Gwani rubutu ya kai “Gangaram”, kwatankwacin Farfesa ke nan a karatun biɗar tuwo. Na so a ce wa Gangaram “Shakundun” da Hausa ya zamo shi ne ƙarshen mukamin karatu na addini da na boko.

Da gaba ta koma baya, boko ya yi wa karatun addini idon marurugiya, e-bi-ci-di ta yi wa a-ba-ja-da wayo da sunan gurgusa in zauna abu ya koma gurguza ba ni wuri. Da yaro ya kai shekara bakwai za a kai shi aji ɗaya har shekara bakwai. A yi bukin ba shi takardar iya karatu da rubutu. Daga nan sai makaranta ta gaba, a shekara biyar, a ba shi takardar shaidar sanin gari da ƙara karatu. Daga sanin gari yana da zaɓi uku: in dai ya je Jami’a, ko Kwalejin Koyan Koyarwa, ko Kwalejin Kimiyya da Ƙere-Ƙere. Ɗayan biyun ƙarshe duk ya je zai share shekara uku gabanin a yaye shi. Idan Jami’a ya je kai tsaye tsakanin shekara (4-5) a ba shi digirin farko. Komai saurinsa sai ya shekara (1-2) ya je digirin ƙwarewa (Masters). A al’adance za a yi shekara (1-3) a samu digirin. Daga nan in a yi zagege (ta Ɗanfulani) in ko a tsaya a huta. Duk yadda aka yi sai an shekara (3-5) za a samu digiri na uku (PhD). Da samun digirin PhD komai ƙwazo ana share shekara (6-10) gabanin a hau kujerar Farfesa.[3] Matuƙar kowace tasha ana tsayi a huta, sai an share shekara (40-45) ana wasan kura da takardun boko gabanin a hau kujerar Farfesa.

Ma’anar Farfesa

Malamanmu sun yi kai da kawo wajen fassara wannan kalma cikin Hausa. Na tabbata ɗan share fagen da ya gabata ya ɗan ba mu haske yadda wahalan noma gandun yake. Wasu masana suna fassara kalmar da “Shaihin Malami”. Masu taka tsan-tsan ga shiga cikin kadadar addini su fassara ta da “Shehin Masani” . Da baya-bayan nan wasu masana suka hausantar da ita zuwa “Farfesa” kawai. Rashin kalmar a ƙamusoshinnmu na Hausa ba zai rasa alaƙa da cewa baƙuwa ce ba.

A Turanci asalin kalmar daga “Profess” yake wadda ke da harshen damo a fassara. Tana ɗaukar ma’anar bayyanar da wani abu (da ya shafi mai bayyanarwa) shi kansa, ko iƙirarin samun wani horo ko koyo ga wata sana’a ko abin sha’awar mutum. A fassarar fannu sun ce:

Ingilishi: “A teacher of the higher grade in a University or College, or in an institution where professionals or technical studies are persued; usually an officer holding a chair in some particuler branch of higher institution”. (The New International Webster’s Comprehensive Dictionary of the English Language)

Hausa: “Malami mai gawurtaccen matsayi a Jami’a ko kwaleji ko wata Cibiya (-r karatu) da ake horar da ƙwararru ko karatun fasahohin hannu;musamman (ana fassara shi) ma’aikaci mai riƙe da wata kujerar alfarma a wani sashe na musamman a manyan cibiyoyin zurfafa karatu”.

A bisa bayanin masu abu Farfesa shi ne, fitaccen malami, sananne, gawurtacce wanda ke saman kujerar shakundum a farfajiyar da ya yi artabon karatu da bincike. In ya kai babin murabus ba ya da abokin gwada tsawo, daga ɗa sai jika, sai kama kunne, bai fasa ba, bai kasa ba, sai a ƙara wa kujerarsa ƙwari zuwa “Emeritus”. Masu abu cewa suka yi:

Ingilishi: Emeritus[4]: Retired from active service (as an account of age), but retain in an honorary position, postor Emeritus. (Webster’s Comprehensive Dictionary of the English Language)

Hausa: Kartagi shi ne wanda ya yi murabus don rage nauyin aiki (musamman idan shekaru sun fara karɓar shara) amma aka ci gaba da riƙe shi bisa ga martaba shi, kartagin Pasto.

Ga alama kujerar Farfesa ba a son gara ya ci ta, matuƙar yana raye, ko da idanu da ƙafafu sun yi masa tawaye, muddin yana ji ana jinsa, da shi da hankali ba su fara hararar juna ba, kujerarsa na nan daram! Mannanu ƙuda ya faɗa ƙwaryar alewa.

Farfesa A Farfesance

Hausawa na cewa, kowa ya ci zomo ya ci gudu. Don haka wasu ke ƙara wa batun gishiri da faɗar zomo ba ya kamuwa daga kwance. Duk Bahaushen da ya ji irin shekarun da ake sharewa ana kokuwa da boko kafin a zama farfesa, dole ya ce, ba a wane bakin banza. Matuƙar ƙwazon ya dace da sunan to za mu ce, Farfesa:

i. Soja ne tsakanin mazaje, namiji ne a ko’ina ake zancen maza, su ma mazan da kansu za ka ji sun ce: “Soja maza”. Ga yadda wani soja ya fassara batun:

Sannun ku soja maza tsakanin mazaje,

Sannunku masu kashi da wawan gidaje,

Ku ɗai ka kwanci kan ƙasa ba gadaje,

Sauro shi ciza ga kiyashi, ƙudaje,

Manya wajen ladabi, wajen bin umurni.

(Kaftin U.D. Suru: Nijeriya Ina Muka Dosa (1986) b+24)

ii. A fagen suna da fice, Farfesa kwatancin “Shago” ne a fagen fama. Da an gilma sunan “Shago” babu namijin da za ya sake kirari. Yadda duk Shago ya zama:

Jagora: Samji irin hakin da ka ramno,

: Burundumi abin zuba shara,

: Kutuɓi abin aza ma ruhewa,

: Lahira a kai maki gawa.

(Ɗan’anace: waƙar Shago)

A fassara Bahaushe haka farfesa yake, kuma haka yake son ya ga ya kasance. Da ya zo a wuri gardama ta ƙare.

iii. A fassarar Bahaushe farfesa uban ‘yan boko ne, da ya zo al’amari ya kai ƙarshe, kamar yadda Ɗanƙwairo yake ce wa, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato:

Jagora: Namiji uban ‘yan boko,

: Amadun Amadu mai tawakkali gun Allah,

: Baban mai saje,

Gindi : In ba ka nan maza suka ƙarya su ce, “maza ne”,

: In ka taho uban Ajiya kowa bai motsawa,

Gindi : Mai dubun nasara tarnaƙaƙi Sardauna,

: Ba a kai maka wargi....

(Musa Ɗanƙwairo: Waƙar Sardauna)

iv. Na tabbata Bahaushe abin da yake kallo farfesa a farfesance shi ne, wata “aya” ta ƙarshe ga boko. Haka kuma, yana kallon ta wata irin kadada ga ilimin boko da an kai gare shi an tuƙe, idan ganɗon ya fashe kuwa sai kowa ya yi ta kansa. Na kwatanta shi da irin hangen da Narambaɗa ke yi wa sarkin Gobir Amadu yana cewa:

Jagora: Ganɗo kake ran da kaf fashe,

: Rannan sai ka iske kowa na dawara,

: Ruwa sun cika karkara,

Gindi: Na rabu da ganin amali yau na zaka in ganai

: Daɗin Tudu ya kamata daɗin Tudu hanƙuri.

Babu wai, irin yadda Bahaushe ke kallon farfesa kamar yadda ya ke kallon limamin garinsu ne ko unguwarsu. A boko, yana ganin farfesa liman ne domin shi ne ƙarshen e-bi-ci-di. Na tuna, wata shekara, mun je garin Ƙaurar Namoda ɗaurin auren ‘ya’yan Khalifa Maahi. Liman na zuwa tare da jama’arsa kowa na a bayansa sai maba/sanƙira ya hau baki da yi wa liman kirari:

“Dudduƙe Maguzawan Allah,

Azumi babbar gayya,

Komi girman mutum guda yaka ɗauka,

Allahu akbar! Haka muƙamin Farfesa yake, komi tsufan mutum guda aka bashi.

A Ji Farfesa A Ga Farfesa

A wajenmu ɗalibai koyaushe muna son mu ga mai suna irin na karatu da ɗalibta ya karɓi sunansa da muƙamin da aka ba shi. Ba dole ne sai ya gamsar da kowa ba, amma ko da ba a samu gamsuwa daga gare shi ba, ba za a yi wa maganarsa turbuɗar mushen jaki ba. An so Farfesa ya ɗan siffantu da waɗannan siffofi da ake zaton a samu a wajensa.

i. Ya san da cewa, muƙamin Farfesa fara karatu ne aka yi, yanzu aka sa ƙafa, ka ce dai manomi ne ya haɗa babban gona ga taki da iri da sungumi na shuka yana jiran a samu ruwa a yi shuka. An ce, wani malami ya ce, ya zama farfesan sanin halin mata, ya kwashe shekara (40) yana bincike ga sakamakon da ya samu:

Bayan ya kwashe shekara arba’ain yana binciken sharrin mata ya rubuta kundaye manya-manya. Ya zo wani ƙauye, ya je rijiya ya sha ruwa. Ya tarar da wata ‘yar yarinya ko budurci ba ta fara ba. Ya nemi ta ba shi ruwa, ta yi masa kallon raini. Malam ya husata ya ce: “Ke tun ba a haifi uwarki ba nake binciken makircin mata, karɓi kundayen nan ki kai wa kakanki ya fassara miki”. Ta ce: “In gani baba!” Ya miƙo mata gafakar tana gefe ɗaya na rijiyar. Yana sakar mata ta jaye hannu kundayen suka yi alkafura cikin rijiya tsundum! Ta ce, wayyo! Baba ka iya wannan[5]? To, Farfesa a lura. Ashe dai cika baki da bugun gaba da karatu bai hana jahili ya ribace ka ya dabirta karatunka. In mun san da haka ga kowa muna koyo kuma ba mu ce wa kowa mun iya.

ii. Yarda da cewa, ga kowa ana koyo. Kana koyo ga ɗanka da abokinka da yayanka da ƙanenka da ɗalibinka da ɗalibin ɗalibinka. Samun kujerar ba hujja ba ce ta rufe karatu ba da cewa an fi kowa. Dubi ka-ce-na-ce tsakanin yaran Firamare da ƙwararrun injiniyoyin hanya:

An ce, wasu injiniyoyi suka je wani gari da motar cire itace. Ƙofar ganuwar garin ta hana su shiga domin motar ta yi tsawo. Suka share wuni suna tunanin yadda za su yi, can suka yanke shawarar a fashe ƙofar ganuwar motar ta wuce, in an ƙare aiki a gyara. Lebarori na batun fara aiki sai ga yara ‘yan Firamare sun taso ƙwallo, suka ce: “Ah!Ga mota ba wurin wucewa”, sai wani ya ce: “In ni ne, zan fasa ƙofar”, wani ya ce: “Ni ɗaga motar zan sa a yi”. Can sai wani ya dube ta da kyau ya ce. “In ni ne zan sace tayoyinta ta huce (sace), a nemo mai faci ya sa iska”[6]. Ƙwararrun injiniyoyin na jin haka suka bi shawarar yaro suka ci nasara. Farfesa a kula. Ashe Farfesa matakin sanin yadda ake bincike ne, da ɗurkusa wa wada a tashi da cikakken tsawo. Kushe abokan aiki da hana wa ɗalibai bin fassarar kowa sai taka alamun rashin sani ne.

iii. Farfesa ya sani cewa, saninsa ba hujja ce ta ƙaryata wani ko wasu ko da a kan kuskure suke. Abin sani ga Farfesa shi ne, amfani da saninsa ya gyara kuren wani cikin nishaɗi da annashawa da tawali’u. Dubi yadda Sarkin Wawan Sarkin Katsina ya yi da telansa:

Wawan Sarkin ya ba tela ɗinki an sha yi masa ƙarya, ya zo ya karɓa in ya zo ba a ƙare ba. Da aka yi masa alƙawalin ƙarshe ya dako sabko, tela na hangensa sai ya shige cikin kayan da aka kawo ɗinki aka jibga masa su aka lulluɓe shi. Ashe an manta ba a rufe yatsun ƙafarsa ba. Da Wawan Sarki ya shiga ɗakin ɗinki suka ce: “Baba tela ya je kasuwa ya nemo zaren da zai yi maka aiki ka je an jima ka dawo”. Ya tsaya ya dubi kayan ɗinki ya ga ƙafar tela a waje ya ce: “To babu laifi, a dai cika alƙawali, kuma in ya dawo ku gaya masa ba ya da kyau dattijo na tafiya da ƙafa ɗaya a kasuwa, ya dinga zuwa da ƙafafunsa biyu mana”[7]. A gaida Farfesa Wawan Sarki. Ta tabbata gani a ƙi gani, ji a ƙi ji, wata babbar sifa ce ta ma’ilmantan duniya, Ƙure mutum a tozarta shi, ba karatu ba ne tashanci ne a dai bi a hankali, da wasa aka gaya wa wawa gaskiya.

iv. Dole Farfesa ya san, ana dafa kafaɗarsa a fi shi tsawo. Wanda ka koyar ya zo da wata basira cikin basirar da ka koyar da shi, kai Allah bai ba ka ba. Godiya ya kamata ka yi ba ɓata rai da kuka za ka yi ba. Dubi ƙissar malami da matarsa da almajirinsa ka ƙara karatu:

Malami ne ya fita zuwa zauren karatu bai ci abinci ba. Ya bayar a gasa masa zakara. Zakara ya gasu, ga jama’a sun taru, ga malam na jin yunwa. Matarsa ta ce wa ɗalibansa: “Wa zai yi dabarar gaya wa maigida zakara ya nuna”? Ɗaya daga ciki ya ce, zai yi. Ya je zaure ya tarar jama’a tinjim, kuma duk irinmu ne almajirai masu tambaya. Sai yaro ya durƙusa ya aje allo a gaban malam ya ce:

Yaro: Malam Zakarutu ya nun naam!

Malam: To, a sarkafe shi ga tankallazii,

: Hatta jama’atu Watseem![8]

Farfesa a nan wane ne malam? Wane ne ɗalibi? Haka ake son mu kasance, ba mu dinga tunzuri idan ɗalibi ya zo da hazaƙa ba. Ai da riga da abinda ke aljihun riga, duk na mai riga ne. Da kara da dagumi duk albarkar farautar kura ce.

v. Zuga da kirari da yabo ba su sa Farfesa ya wuce saninsa. Duk abin da ba ya iyawa zai yi tsaye ya zama ɗalibi sai ya san shi. Da yabo da kushewa duk ba su sa ya ci mutunci martabar ilimi. Karatun malam Gambo da Farfesa Manu Dahin Gumbire abin lura ne. Manu ya shahara ga sata. Ga abin da suka yi da Gambo:

Jagora: Ɗan Dahi Manu,

:Wanga da ag Gumbire dauri,

: Ko bataliyas soja tas shiga daji,

: In gaya maka Manu Dahi na ɗan taya ta,

: Yac ce min:“Mis samu Gambo?”

: Nac ce, “Tudu Tsoho yat taɓa ni,

: yac ce: “Maganar banza da yohi”,

: In akwai ta da daɗi ka je da kanka

: Ai ba mu tsar ma tambaya ba”.[9]

Farfesa Manu ya yarda gaba da gabanta ya rufa wa kansa asiri, yau ga mu muna amfana da fatawarsu. Haba Farfesa! Duk mai ganin iliminsa ya kai yana gwada tsawo da kowa ba Farfesa ba ne farfesu ne. Hattara da kayan Allah! Da zarar ka ga abin da ya zarce ɗan abin da ka sani, tsaya nan ka sauke kayanka ka ɗalibce shi sai ka iya shi ka yi magana kansa.

vi. Ya kasance mai hankalin amfani da ilimi wajen gyaran matsalar ilimi, ba da cin fuska da cin zarafi da muƙabala da bugun gaban wa mutum nan. Ya kyautu Farfesa ya san tunatar da ɗalibi da mai ilimi cikin ilimi, wani haske ne na karatu da ke amfanar mai gyara da mai kuskure.

An ce, wani cikakken malami a Masar ya je aikin Hajji da ɗalibansa. Ba su taɓa ganin Ka’aba ba. Da ka’aba sai suka rungume ta suna kuka. Suna shafarta suna sumbata. Abin ya koma bautar ɗakin ba bautar Allah ba. Da wani ƙwararren shaihin malamin tauhidi ya gan su sai ya ɗauki Alƙur’ani, ya je gun shaihin neman a koya masa karatu da fassara; ya ce: “Allah Ya taimaki malam, a taimake ni da fassara wannan aya”: “Fal ya’abuduu Rabbu haazal baiti.” Shehi ya fassara masa da cewa: “Ku Bauta wa Ubangijin wannan ɗaki”. Sai Shehin ya ahumo ya kira ɗalibansa ya ce: “Ku zo mu gyara” “Rabbu haazal baiti” aka ce, ba “haazal baiti ba”. Daga nan suka daina abin da suke, suka ci gaba da ɗawafi yadda shari’a ta tanada[10]. Tabbas! Muna da aiki baya. Fatar Farfesa koyaushe a gane, a gyara, a ci gaba, ba a tabka muƙabala da gardandami ba. Wanda duk ya ce, kowa bai iya ba, shi ne bai iya ba.

vii. Ƙwararren Farfesa shi ne mai yarda da fassararsa da ta waninsa, matuƙar ba su ci karo da sawaba ba. Wanda ya yarda duk abin da ya sani wani ya san saɓaninsa ya huta da ɗirkaniya, mota cikin randa. Wani Shehi ya yi wa jama’a nasiha da su riƙa kyauta da sadaka. Ya gaya masu cewa: “Ku sani rubuce yake, in ka ci ya ƙare, in ka ba wani ya ƙare, in ba ka ba wani ba ya ƙare”. Jama’a kowa ya gamsu sai Ɗankama ya ce: “Akwai gyara ga hadisin malam, fassarar nan ba ta lugudu ba”. Malam ya so ya yarda sai jama’a suka yi caa kamar su cinye Ɗankama. Sarkin gari ya ce: “To, kai kawo taka fassara mu jiya” Ɗankama ya ce: “In ka ci ya ƙare, in ka ba wani ya ƙare, in ba ka ba kowa ba ka daɗe kana cin abinka”[11]. Me za ka ce da wannan Farfesa? Matuƙar da hankali za a yi aiki, Farfesa a taka sannu.

viii. An so Farfesa ya kasance mai cikakken wayo da ƙoshin ilimin tunkarar kowane ilimi ya bijiro masa. Da iliminsa zai yi amfani ya kuɓutar da kansa da wani ya ceci al’umma. Labarin ɓarawon maƙullin mota da direba abin lura ne:

Wani fitaccen ɓarawo ne ya dami mutanen Arkilla Federal low coast, Sokoto. Ya sha sace wa direbobi maƙullan mota da dare ya je ya buɗe ya sace abin da ke ciki. Wata rana ya ɗauki maƙulli wani yaron Alwasa. Yaron mai wayo ne, da ya tabbata yaron ne ya sace maƙulli, kuma ya gan shi cikin aljihunsa. Idan aka ta da rigima zai iya jefa shi wani wuri ya ɓace. Tsoro haka ya sa ya kira ɓarawon gefe ɗaya. Ya zaro naira hamsi ya ba ɓarawon ya nuna masa wata kwana ta unguwar mai nisa ya ce: “Ga yaron da ya sace min maƙullin motata can ya shiga kwanar can, je ka ƙwato min abina ka ci goron naira hamsin”. Da jin haka sai ɓarawon ya ruga da gudu ya shiga kwanar ya dawo da maƙulan a hannunsa ya ce: “Ga su, su ne waɗannan? Abdullahi Alwasa ya ce: “Su ne na gode”[12].

Da ƙasar Turai ne aka yi haka, ba abin mamaki ba ne a kira direban a ba shi kyauta ko wata jami’a ta ba shi digirin girmamawa. Madalla! Ashe a tasha ma akwai masana da manyan Farfesoshi. A kowane lokaci Farfesa ya shiga wata matsala ya nemo masu hannu a abin, ya nemi ilmi wurinsu kana iya sa tasa basira abu ya je tangam.

ix. Koyaushe a dinga tsantseni wajen yanke hukuncin ilimi. Wannan wata dama ce da za su daina nuna wa mutane sun iya ko da sun sani. A al’adance gwani ko ya san abu yana so ya ji ta bakin abokin tattaunawa. Domin Hausawa cewa, suka yi.“Ko ɓata ƙara sanin daji ne”. Ƙissar wani malami da ya bugi ƙirjin cewa, in yana raye ba a ƙara musun kwanan wata wani babban darasi ne:

Musu ya kaure a masallaci kan kwanan wata domin a tantance tsayuwar Ramalana. Da musu ya tsananta, sai wani malami ya tashi ya gaya wa jama’a cewa, in yana raye ya ɗauke wa kowa ganin wata da tantance kwanakinsa. Bayan an yi ittifaƙin yau ɗaya ga wata, ya je gida ya ɗauko burgamensa ya rataya shi a rumfar ƙofar ɗakinsa. Kowace rana ta Allah sai ya ɗauko tsakuwa ɗaya ya jefa a ciki. Ashe ɗiyarsa ta lura da cewa, kowace asuba malam in ya dawo da salla sai ya jefa tsakuwa ɗaya burgame. Halinka da yaro, sai ta dinga taya shi, a koyaushe ta lura ya jefa sai ta laɓaɓo da nata cike da ɗan hannunta ta jefa. A kwana a tashi gardama ta sake tashi kan tsayuwar wata. Malam ya ce: “Ku bari in zo an gama”. Ya je gida ya sauke burgami ya ƙyarga ya ga wajen (80-100), ya sake rairayewa ya tsame (50-60) ya sake ɗebe wasu ya fitar da (30-40) ya zo masallaci ya ce wa jama’a:“Yau kwanan wata (35)”, aka bushe da dariya. Ya ce:“Da na gaya maku abin da burgamina ya faɗa ai za ku sha mamaki[13].

Danƙari! Ashe gaskiyar Bahaushe da ya ce: “Kowa ya ce, ya ce, sai ya ce, bai ce ba”. Idan haka karatu da bincike suke, don me ba za mu rage doro da taƙama ba? Da duk aka yi bugun gaba da ilmi sai ya ba mai shi ruwa.

x. Farfesa ilimi amana ce ka daina ɓoye wa mai koyo shi, kada ka yaudare shi da shi. Duk abin da za a koyar ga ɗalibai ka tabbatar da gaskiya ce, a gaban kowa ya ambace shi ba za a muzanta shi ba balle a yi masa dariya. Na tuna da labarin wani Resdan Bature da yaronsa mai kula masa da dokinsa:

A kowace rana Resdan na cire kuɗi ya bayar domin a kula masa da dokin da yake hawa. Yaro yakan je ya ce: “A kawo kuɗin ciyawa, a kawo na gyaran linzami, ko ƙaimi ko na gyaran turke da na tur!” Duk Bature ya bayar. Da Bature ya ji Hausa sosai sai ya je fadar sarki ana cikin taɗi ya ce, yana son a gaya masa abin da ake ce wa tur!” Kowa ya kasa, ya gaya wa sarki cewa, a kira masa yaron da ke kula da dokinsa ya san kalmar, aka kira shi a fada. Ya faɗi ma’anar kalmar “tur!” Sai turu-turu da idanu[14]. Da aka gano yaudara ce sai aka dinga yi masa kirari, “Adaɗe ana yi” sai ya ce: “Sai gaskiya”. Dukkanin abin da ya koyar da Resdan a nan ya zuba saboda samun cin amanar ilmi ɗaya na kalmar “tr” da ba ta a Hausa. A kula duk abin da aka koyar da yara girma zai zo musu kuma za su tuna da shi. In gaskiya ce a koyaushe girmanka na a zuciyarsu. Idan kuwa na akasin ta ne, kai ka zubar da girmanka da kanka.

xi. Farfesa masani ne mai ilimin hangen nesa tare da kiyaye karatun yau a tunkari na gobe. Wannan ce ta sa a koyaushe ba a girshinsa a fagen karatu, domin da tambaya yake tunkarar mai tambaya, har sai tambaya ta fito da amsar wata tambaya a kasa wata tambaya ta gaba. Saƙon Yakubu Gawon zuwa ga Sarkin Musulmi Abubakar III da tambayar sarkin Gwandu Haruna wani babban kundin karatu ne.

A zamanin mulkin Yakubu Gawon ya samu labarin ana son a yi masa tashintashina a hamɓare gwamnatinsa. Ya aika wa Sarkin Musulmi Abubakar III cewa, a tara sarakuna su shirya talakawa a yi zanga-zangar goyon bayan gwamnati domin a samu damar kama masu son su yi ba-mu-so a hukunta su. Sarkin Musulmi ya kira taron sarakuna, wakilan gwamnatin tarayya suka hallara a taron, da sarki ya karanto saƙon shugaban ƙasa, sai ya ce: “Abdullahin Gwandu (cewa da sarkin Gwandu Haruna) me kuka gani?” Sarkin Gwandu Haruna ya ce: “A gaya wa shugaban ƙasa cewa, Mai Martaba Sarkin Musulmi ya ce:“In suka sa talakawa zanga-zangar ‘muna so’ idan wata rana talakawa suka yi masu zanga-zangar ‘ba mu so’,. Wa zai kwantar da tarzomar?[15]

Wannan tambaya har yau gwamnatin Yakubu Gawon ba ta ba da amsar ta ba. Haka malamanmu suka ce, a koyaushe Farfesa ya yi magana a ji ta a yi tangam, mai zuwa hajji ya gamu da Annabi (SAW).

Ba Fankam – Fankam ne Kilishi ba, Tsomi

Hausawa sun ce, “Maza tamkar gyaɗa ne sai an ɓare, za a san mai ƙwaya”. A al’adance, ba kowane mutum ke cin sunansa ba. Babbar buƙata ga kowane mutum ita ce, idan aka ga mutum sunansa na ɗaukaka, a ga ayyukansa da halayensa na ɗaukaka. Ba abin mamaki ba ne a irin ƙarshen zamaninmu a tarar da Farfesa bai cika mudun da ya kamata a ce ya cika ba a fannin karatu. Wanda duk Allah Ya nufi aka naɗa wa wannan rawani, ya sani cewa:

1. Rawanin karatu ne na har abada babu ranar hutu har sai an kwanta kushewa. Sunanka da rawanin da aka ba ka ba su yi wa jahili barazana sai dai a yi taho- mu-gama. Ba a wa ilimi kwalo-kwalo da dabarar da wayon sanin gari na shekaru. In an san abu, an san shi, in ba a san shi ba, ba a san shi ba. A zage dantsen neman a san shi. Na yarda da hangen Marigayi Ɗantalata Maiduma Bunza, makaɗin tauri da yake cewa:

Jagora: Ba wayo aka wa yuƙa ba,

: Ba ta da ban magana sai tauri.

Gindi : Gara da kaz zaka baban Idi,

: Dajin namu da zabbin gumbi.

Wane wayo za a yi wa kujerar Farfesa in babu karatu kuma ba a yi shi ba? Ai sai dai karatun Baru uwa uba ga maraye, wa in bari bari, wa in kasada kasada”.

Kama da Wane ba Wane ba ne

Kujerar Farfesa ba ita ce ilimi ba, sannan kuma Farfesa ba shi ne ilimi ba. Zama Farfesa ba ita ce hujjar gogewa da ƙwarewa ba. Babbar hujjar da babu makawa a kan ta ita ce, “Karatu” a tabbata an yi shi, an san shi, an saba da shi, karatun ya zama tobashin zuciya abokin baki. Ina amfani a ce wane ya kai, a zo da ɗan ma’auni a tarar bai kai ba. A sake bitar tunanin Narambaɗa:

Jagora: Ai An wa wani Alƙalin ƙasa,

Yara : Da babu sani taw walwale,

Jagora: Bai san amma ba, bai san sabbi ba,

Yara : Shi dai shi tsare “min nun guda,

Jagora: Can gaba ko “ra baguje”[16],

: Iya kas sanin an nan.

Gindi: Ya san girma ya san yabo,

: Mu zo mu ga Alƙali Abu.

Ba Sunan Ba Aikin

Malaman ƙasar Hausa idan aka ce wane ya sauke Alƙur’ani sukan ce, “ Allah ya ba da karatun tsoron Allah”. Abin da suke nufi shi ne, ba karatun za a yi wa hisabi ranar Alƙiyama ba, mai karatun za a yi wa. Idan an hau kujerar Farfesa ana son a ga ayyuka na ɗa’a da biyayya ga gabaci da rahama a magana da rubutu da ƙauna da soyayya ga wanda aka sani da wanda ba a sani ba. Da muƙamin da sunan Farfesa ke ɗaukaka mutum ba za a jin suna wani a bangon ƙasa ba face Farfesa. Aiki mai sunan shi ke ɗagar da sunan da aiki a ji su a duniyar zamaninsa. Wani mawaƙin mashaya giya ya yi wa wani Shaihin malami wa’azi lokacin da Shaihi ya ce masu: “Yan wuta masu saɓo”. Shi kuwa ya mayar da raddi da cewa:

Jagora: Dan nan sai nak kada baki,

: Nac ce malam ka yi saɓo,

: Ɗan laifinmu na shan giya na,

: Wansu da sata, wansu maita,

: Wansu had da biɗar matan maƙwabta,

: Ba allo ka ganin Ma’aiki ba,

: In allo ka ganin Ma’aiki?

: Shekarar bana danya ba ta toho,

: Dud da ni sai na yi bakwai ba.[17]

(Kwara Mairuwa: Waƙar ‘yan Birni ku yi tamataila, 1975)

Wai in don ta alluna ne kawai ke sa a ga Annabi (SAW) ba a yi aiki nagartacce ba, to shi zai sassare itatuwan danya gaba ɗaya, (da ita ake yin allo) ya yi wa kansa bakwai ya ga mai hana masa ganin Manzon rahama (SAW).

Farfesanci

Farfesanci wata babbar daraja ce da ɗaukaka wadda ke tabbata wa duniya cewa, lallai kujerar da jami’a ta ba mutum bisa cancanta aka ba shi. Daga lokacin da aka saka ƙafa a jami’a, har lokacin da aka samu hawa kujerar Farfesa, duk nema ake yi. Duk wani aiki da ake yi don a kai ga kujerar nan ne. Hausawa cewa suka yi, “Ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare”. Idan an hau kujerar ana buƙatar a ga :

1. Wani sabon ƙwazonka na bincike da rubuce-rubuce da za su tabbatar da cewa, lallai ƙwazonka ne ba kirarin matsoraci ba. Duk wata takarda ko littafi ko bincike ya fito daga gare ka a tabbata ƙwazonka ne sabo ba ɗaurayar baya ba ce, ba damben wada ba ne.

2. Farfesanci shi ne a samu fannin da aka ce ka cancanta, hatta da Mala’iku su shaida Allah Ya hore maka shi. Jami’arka ba ta fargaban sa ka gaba, ka wakilce ta domin ta san ko an daka cikin turmi da ku cikin masu fita. Ƙasarku da jiharku ba su fargaba wajen neman taimakonka a fanninka saboda an san zancenka, nashin ƙasa ne babu kure.

3. Duk yadda zamani ya juya, in dai kana raye, ba a tababan tura ku gaba wajen saka wa jahilci takumkumi da yi wa ilimi talala na sai baba ta gani. Kuna zaune gida a nemo wasu ƙwararru waje kunya ne a kanku. Ku yi tsari ya kasa karɓuwa zance ne. Ku yi nuni a kasa ganin haske labari ne.Ku sa hannu a ce a dakata shirme ne. Ai ku ne igiya maɗaura kaya, kowa ya yi ba da ku ba ta tsinke.

4. Hankali ba zai yarda da a ba ka tsani/kwaranga ka hau rumbu ka ɗebo abinci ka ci, kai da iyalanka, da ‘yan uwanka, da masoyanka, sai kun ƙoshi ka ɗauke tsanin ka ɓoye wai kar a sake amfani da shi. Ɗalibbai nawa ka yaye kuna tare ana fafatawa? Nawa ka yi wa mafarin samun kujera irin taka? Nawa an nan kana raino da kake son su hau munzalinka gabanin ka yi murabus ko duniya ta kore ka da aiki? Me ka rubuta ka ajiye wa na baya domin su karanta su shahara kamar yadda ka yi? A ɗan namu gani na ɗalibbai, Furofesanci ya fi Farfesa wuya, domin Farfesa nawa aka fesa wa turare har suka kai ga kujerar sai sun haye su fesa wa ɗalibai barkonon tsohuwa?

Hankali ka Gani ba Ido ba

Amfani ilimin ya saka wa mai shi hankalin da zai iya zama da kowa, a yi hulɗar arziki da mutunci. Da yawa, hankali na koya wa ilimi karatu, sai dai idan ilimi ya yi tambaya a raba ‘yan kallo. Da magabatnmu da mabuƙatanmu da mu ɗalibbai da ‘yan kallo mu kiyaye sosai da sanin:

· Kujerar Farfesa ba ta tsira hasada ba ce da abokan gwagwarmaya. Tir! Da hassadar ka a ke ana barin ta kai gareta? Don me za ka yi hasadar wani?

· Ba ta girman kai ba ce, na ganin dole sai an duƙa maka

· Ba ta sauke karatu ba ce a dangane allo, wai an kai walawaladaina, walam malam na ƙiya.

· Ba ta soke ƙwazon magabata ba ce, ka fito da naka salo da sanin gari.

· Ba kujerar neman muƙamai ba ce, kujera ce ta nema wa masu neman kujerun girma girma, mai ita sai gyashin Alhamdulillah.

· Ba kujerar kafa wata sabuwar mazhaba ba ce, don duniya ta ji kai ma ka kai. Assha! Babu ƙira me ya ci gawai?

· Ba kujerar kirari ba ce, wai girma ya kawo tsoro ya ɗebe. Kash! Da wa ka yi kokuwa ka ƙwato ta.

Sakamakon Bincike da Shawara

Kowane ilimi na duniya yana da tsarin da aka hau aka same shi. Muƙamin Farfesa da a Arewacin ƙasarmu sai ƙwara-ƙwara. A yau, saboda yawaitar jami’o’i a yankinmu sun fara yawaita. Ina ɗan hasashen taɓarɓarewar ilimi a ƙasarmu da mummunar aƙidar nan ta cin hanci da rashawa da maguɗi babu fannin da ya tsira ciki a ƙasarmu. Babu laifi a samo wani tsanin da zai riƙa zaburar da Farfesoshi su ƙara amfanin ƙasa da jama’a. A fafutukar rubuta wannan takarda na gano cewa:

· Mafi yawan farfesoshin ƙasar nan sun manyanta shekaru na yi masu barazana. Wane lokaci ne suka samu na kulawa da lafiyar jikinsu da farfesanci?

· Jingar da aka biya ba ta taka kara ta karya ba, kuɗaɗen bincike da ake bayarwa ko kuɗin rangadin bincike ba su biya, balle a tsaya a yi aiki a wallafa shi.

· Yawan ɗalibban da ake bai wa masanan masu digirin B.A da M.A da PhD sun yi yawa. Abin takaici an daina biyan tallafi ga masu duba ɗalibai da yawa. Wannan kisan mummuƙe ta’addanci ne ga ilimi.

· Siyasa ta shiga jami’o’i haiƙan musamman jami’o’in jihohi da sababbi, in ba a kula ba za su ragaita kujerar Farfesa ta koma ƙarƙashin ofishin gwamna ko ofishin Pati

· A fito da wasu gawurtattun mujallu na ƙasa da za su riƙa wallafa ayyukan farfesoshi kawai. A yi tsaye ganin dole kowane farfesa sai an ji muryarsa a ciki. A fito da matakan ladabi ga masu daƙilewa.

· Bayan laccar shimfiɗa Buzun karatu (Inaugural lacca) a fito da laccar shekara-shekara ta manyan masana da kowane masani zai baje kolin wani sabon abu da ya hango a shekara.

· Hukuma ta sa hannu ga wallafa ayyukan farfesoshi da tallafa musu da biyansu na goro, in ana ta ciki da wane hankali za a yi bincike.

Naɗewa

Haƙiƙa ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare. Ga kowane ɗalibin sani mai ƙwazo da naci da kishin kai, samun kujerar farfesa gare shi da al’ummarsa babbar nasara ce. Hawan kujera da rashin cancanta wani tonon silili ne, da zubar da mutunci ga ɗan ƙuƙe-na-ƙuƙe. Ilimin da ladabi da biyayya da hankali maƙwabtan juna ne, amfanin sani aiki da shi. Daga cikin sirrin ilmi akwai riƙon gaskiya da fake amana da gode wa ga wanda ya azurta ka da shi. Narambaɗa ya ce a gaya muna:

Jagora: Duk ɗan malamin,

: Da yaƙ ƙi biyan Allah,

: yak kiɗe baƙi,

Yara : To, Allah yana watse kayanai.

Jagora: Ya kama yawo,

Yara : Yannan gidan har ya zan kango.

Gindi : Gagarau mai buge kangara Ali ‘Yandoto,

: Ba shi son wargi ba a kai mai batun banza.

Manazarta

Bunza, A. M. (1996). Baki Abin Magana, ANLAT Publishers.

Bunza, A. M. (2009). Narambaɗa: Jerin Littatafan Cibiyar Nazarin Al’adun Hausawa, Sahen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato. Lagos: Ibrash Islamic Publication Center Limited.

Ɗangambo, A. (1981). Ɗaurayar Gadon Feɗe waƙa, Kano.

Ɗangambo, A. (1984). Rabe-raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa, Kano: Triumph Publishing Company.

Ɗangambo, A. (2007). Ɗaurayar Gadon Feɗe waƙa, (Sabon Tsari) Zariya: Amana Publishers Limited.

Ɗangambo, A. (2011). “Waƙa da Rawar da Take Takawa A Rayuwar Hausawa” (Domin tunawa da cikar shekara gomasha biyu da rasuwa Alhaji Mamman Shata yana da shekara 76), Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Kasina ta Shirya.

Ɗanjuma, S. (1982). Rabe-raben Waƙoƙin Hausa da Tasirinsu ga Rayuwar Hausawa: Kano: Triumph Publishing Company.

Ɗanjuma, S. (1982). Rabe-raben waƙoƙin Hausa da Tasirinsu ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph Publishing Company. The New International Webster’s Comprehensive Dictionary, of the English Language.

Suru, K. U. D. (1986). Najeriya Ina Muka Dosa? Rubutacciyar Waƙa da ya rera a Garmaho.




[1] Fitattun waƙoƙin Madahun Manzon Rahama (SAW) da suka samu karɓuwa sosai a ƙasar Hausa su ne: Alburda da Ishiriniyya. Alburda Balarabe ya rubuta ta Shehu. Ita kuwa Ishiriniya baƙar fata ya rubuta ta ɗan Afirka da aka fi sani Albuusiirii mutumin Masar da Alfaa Zaazi. Kalmar ‘alfa’ Yarbawa da Zabarmawa na amfani da ita a madadin ‘malam’. Suna ‘Zaazii’ ya fi kusa da Zabarmanci, don haka ake kirdadon cewa, Alfa Zaazii Bazabarme ne. Allah masani.

[2] . Tattaunawa ta musamman da Malam Usmanu Birnin Kabi asali Malam Usman haifaffen garin “Buma” ne ta wajen garin Gulumbe. Karatu da karantarwa ya kawo shi Birnin Kabi tare da ƙanensa Malam Aliyu. Na yi hirar da shi a wajen shekarar 1993.

[3] . A wasu lokuta na musamman, ana zama Farfesa da digiri ɗaya kacal ko ma babu digirin idan mutum ya gawurta. Waɗanda na san an ba kujerar ba su da digiri akwai: Farfesa Neil Skinner na Jami’ar Wisconsin Amerika, ya rasu 2016, da Farfesa Haliru Binji a Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Sashen Shari’a. Masu digiri ɗaya akwai: Farfesa Abdullahi Smith a Jami’ar Ahmadu Bello, da Farfesa A.M.H. Kirk-Green, na Jami’ar Oxford, London; da Farfesa Na’ibi Swaid na Sashen Larabci Jami’ar Bayero, Kano; da Farfesa Wole Soyinka na Jami’ar Legas, waɗannan masana gudunmuwar da suka bayar ta keta hazon duniyar ilmi sosai, ko cancnta ta san sun cancanta.

[4] . Ni na fara kiran sa da suna “Kartagi” a garin Yakawada ta ƙasar Zazzau. Gogaggen ɗan caca idan ya manyanta ba ya da abokin wasa, za a naɗa masa rawanin “Kartagi uban ‘yan caca”. Wani muƙami ne na nuna an manyanta cikin abu, an yi murabus, amma an ƙi rabuwa da shi domin da tsohuwar zuma ake magani. Ban ce, sunan shi ya fi dacewa ba, ɗan yunƙuri ne na ɗalibai, ina son masana su taya ni gyara mu fito da sunan da zai fi dacewa.

[5] . Na saurari wannan ƙissa ga marigayi Sheikh Sidi Ibrahim Attahiru Sokoto, a tafsirin Alƙur’ani da yake yi a masalacin jumu’ar da ke gidansa, a shekarar 1982.

[6] . Ina godiya ta musamman ga Dr. Nasiru Aminu Kalgo na Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Sakkwato. Na samu wannan bayani a yayin tattaunawarmu da shi a wajajen shekarar 2012/2013 a ofishina.

[7] . Hira da ɗaliban makarantar malamin da na ambata a lamba ta 2.

[8] . Na ƙaru da wannan bayani a wajen wani ɗalibina Bakatsine da ya yi kundin digirinsa na B.A. kan Wawan Sarkin Katsina.

[9] . Da Manu bai kai matsayin Farfesa ba a sana’arsa, zai hau tulin ƙasar da makaɗa Gambo ya tara masa, a ƙarshe ta rutsa da shi.

[10] . Tattaunawa da wasu ɗaliban ilmi a masalacin jumu’a na garin Bunza, Masalacin Jumu’a na 2, a shekarar 1990.

[11] . Hira da Liman Khidir bin Saleh, Limamin Unguwar Malamai Bunza shekarar 2015.

[12] . Tattaunawa da Abdullahi Alwasa ma’aikaci a Asibitin Masu Taɓuwar Hankali, Kware, a gidan Alhaji Suleiman Umar Tunga Arkilla Federal Lowcost, Sokoto.

[13] . Ina godiya ta musamman da roƙon gafara ga marigayi Malam Yusuf Kantu Isa da ya ba ni wannan labarin a garin Argungu, 1982.

[14] . Na samu wannan labari a fadar mai martaba Sarkin Musulmi ga wani Yaro daga cikin yaran da ke yi wa gidan hidima, 1990.

[15] . Na yi matuƙar godiya ga Farfesa Ibrahim Mukoshy na sashen Nazarin Harsunan Nijeirya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto, ya ba ni labarin a ofishinsa, 2015.

[16] . Idan aka haɗa harufan “min” da “nun” da “raa” da “baa” za a sami “min rabbi”. Haka, marigayi Alhaji Garba Gwandu Bazza ya fassara mini baitin a gidansa, 1980. Sun shaidi waƙoƙin Narambaɗa kuma sun sha zama da shi da tambayarsa ma’anonin wasu kalamai na cikin waƙoƙinsa.

[17] . Wannan fasahar ce makaɗa Gambo mai ɓarayi ya ara ciki waƙoƙin hululuwa, Gambo fice ya fi su. Kwara mutanen ƙasar Geza ne, a garin Geza, ƙaramar Hukumar Dandi, Jahar Kebbi, gundumar Argungu.

 Degel Journal

The official website of the DEGEL Jounal is https://www.degeljournal.com

Post a Comment

0 Comments