Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Ta'aziyyar Farfesa Bello Sa'id

Rubutawa:
Ibrahim Garba Nayaya,
NTI, Kaduna.

Komai na dosa dole zan sa Rabbana,
Sannan salati gun Rasulu a nan gaba,
Har ma sahabban nan da alayen gaba,

Wayyo fa zuci a yau ta yo ƙonewa,
Kaina ya yo nauyin da bai yayewa,
Ƙwalwa ta tsaya fa cak ba motsawa.

Laka ta bar fa jiki gare ni ficewa,
Ruɗu ya nemi ya sa na yo zaucewa,
Ƙunci a rai ƙwalla idanu zowa.

Kun san dalilin wanga duk rikicewa?
Har ma na ɗimauce na gasa ganowa?
Ga nan bayani nan ina jerowa.

Ran Litinin zaune ina hutawa,
Can Central Centre da ke digirewa,
Har mu huɗu mun kulle tattaunawa.

Nan dai na hau Facebook fa don na ganowa,
Me ke gudana har da kai komowa,
Tsak nat tsaya domin da ganowa.

Dakta Nabil ɗan Bello ke fa sanarwa,
Rai ya gushe gun Baba Bello ficewa,
Kaina ya yo nauyi na yo rikicewa.

Ƙaramar waya ni kam na yo ɗaukowa,
Mannir na doka kiran sa ban mantawa,
Nan take babu musu ya ƙara sanarwa.

Har ma ya ce Markaz a nan sallewa,
Sannan a kai shi gidan da ba dawowa,
Bayan Asar aka sa ka sake kulawa.

Wayyo tunani ne ya sake fitowa,
Loton da ke bitar rubutu nawa,
Kan ƙa'ida, tushe da nai jerawa.

Nan kam ya yo shi yabo gare ni zubowa,
Sannan ya ce aikin ga ka yi rufewa,
Don ka sako komai cikinsa kwatsawa.

Can baya sai na tuno batu da jimawa,
Loton fa taron Hausa ban mantawa,
Mambayya House can gidan ajiyewa.

Shi ya fito domin ya je sallewa,
Sai ga ni nan haɗuwa mukai ganawa,
Har ma ya ban lambarsa don gaisawa.

Wataran fa na je Jami'a ta Kanawa,
Nan dai na je Centre wurin sa jimawa,
Har ma ya ce nan dai nake zaunawa.

Sallar Zuhur muka yo da shi fa tunawa,
Sannan na ɗauki jaka na yo juyawa,
Yai min du'a'i mai yawa fa nusarwa.

Centre fa ta yi rashin abin dubawa,
Mu ma fa mun yi rashin uban zantawa,
Kai Hausa ta yi rashin tudun dafawa.

Masani a fannin Hausa ne na bugawa,
Nazari na waƙen Hausa kar ka rabawa,
Dokar rubutu ƙa'idarsa rufewa.

Masanin Adibi ne na nunnunawa,
Masanin rubutun Hausa kar ka ragewa,
Masani da bitar ayyukan kurtawa.

Ya yo kutub duk musu kyan dubawa,
Ya yo maƙalu dan nazar tsarawa,
Har ma a waƙe dole sai sarawa.

Shi kam karimi ne na ƙin ƙarawa,
Kunya da dattako gare shi haɗawa,
Ga son zumunci babu mai kushewa.

Ban manta kalmar Dakta Sani faɗawa,
Kan Baba Bello a gun nazar bitawa,
Haka Dr. B. Usman ya yo kurtawa.

Allah ya kai haske gare ka kushewa,
Ni'ima Ya sa kabarin ka yo hutawa,
Aljanna ba shi fa ya Ilahu daɗawa.

Har ma Ubana wanda yai fa tsirarwa,
Ƙaro shi peace gun Umma Mama tawa,
Haƙuri Ka bai 'ya'yansa ba su kulawa.

Dakta Nabil wannan masoyin nawa,
Ga ta'aziyya ta riƙe ta kulawa,
Allah ya gafarta wa Baba kulawa.

Ni ne Nayaya na yo fa jerantawa,
Ran Lahadi mota ina tafiyawa,
Zan je Nguru daga can Damaturu tawa.

Ƙarfe biyu kafin ta kai na haɗawa,
Fa alif ɗaya da huɗu-huɗu da takwaswa,
Biyu can dubu da biyu ka sa sistawa.

Ibrahim Garba Nayaya,
National Teacher's Institute,
23 Lahadi, 2026.
Farfesa Bello Sa'id

Post a Comment

0 Comments