Kurtun rai kai kurtu-bam-bam,
Mai sa wa rai karkiya,
Ga sukukum bakaka jigatau,
Cacuma boƙara yamutsattsa,
Ƙwaƙuma Jibgau duniya.
A yau baiti na yin hawaye,
Ɗango na yin magiya.
A kan na fito in saƙa waƙa,
In yo alhini ta'aziya.
Ga Farfesa Bello Sa’id yau,
Ka tashi ka ƙero Marsiya.
Farfesan Harshen mu Hausa,
Kushewatai yau ya maya.
Duk maujudi hadisi,
Labudda lahu an yafniya.
Duk mai rai tuni mun sani ai,
Dole ya ƙaura a duniya.
Dole ya amsa kiran Ta'ala,
Akwai ko ma ba lafiya.
Yau mutuwa ta zo ga babban,
Bangon Hausa na duniya.
Ta ɗauke ilimi da haske,
Ta ƙyale duhu nan duniya.
Tai diɗiɗim dinkim diɗim yau,
Ta koma fa sakaliya.
Tana tafiya salalo salau,
Sam babu kuzari ko ɗaya.
Ta susuce ta ɗimauce,
Ta koma ya baha’iya.
An yi rashin mai haskaka ta,
Bello Sa'id a daren jiya.
Hatta buzaci na teku,
Lashakka yau ya tsaya.
Ya yi rashin mai karkaɗa shi,
Mai motsa shi da safiya.
Farfesa ya bada himma,
Yai hidima ga bahaushiya.
Yai baiko ya ƙulla aure,
Balarabe da Bahaushiya.
Ya ƙwaƙwace ya fa tsanfe,
Zumuncin Hausa da Arbiya.
Mun yo shuka ga shi tsuntsa,
Ye sun tone woh niya.
Babu iri balle mu koma,
Mu sake ƙwafi don mui maya.
Ga shi ruwa har ya yi nisa,
Marka ta kai har wuya.
Ga bartai nan na ta zarya,
Ƙasa ta ƙone dukiya.
Ya Allahu Buwayi gyara,
Kawo sauƙi duniya.
Mun yi rashin gwarzo masoyi,
Magaga asirin duniya.
Na so in kawo shi Malam,
Ya sha kuka bahaɗejiya.
Du dai da na san ɗan Kano ne,
Su sun fi gane jar miya.
Rabbi gifirhu ka haskaka mai,
Ƙaburi Jalla Ilahiya.
Ya Allah Ka jiƙan Galadan,
Chi har Bello Sa'idu ya.
Sun yi dashe har ya yi reshe,
A waƙa sun kafa tushiya.
Allah gafarta wa Bello,
Ɗa ga Sa'id har ma niya.
Har Maulana Shaikh Ƙani,
Ar-rathy mai yin marsiya.
Rabbi haɗa har ma musulmai,
Kulluhumu kaf duniya.
Ni USMAN NAGADO na writo,
Sai ku karanta kitabiya.
Na ƙare tas babu roho,
Sam ba na yin fariya.
Ran ashirin da guda Agusta,
Twenty-six miladiya.
Wa attahiyatu ga Ɗaha Manzo,
Wa Alu da Sahabi da Auliya.
Tilas in gode wa Allah,
Alhamdul Lahi Ilahiya.
Daga taskar:
USMAN IBRAHIM BULANGU
09064862386
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.