Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Adama Yarima Balla

Umma ban manta da ke ba,
Mama ba gajiya na yo ba,
Ɗa ba zan gaji da uwa ba.

Ɗan halak bai manta khairi,
Ɗan halak bai mai da sharri,
Baki yo sharri ga ni ba.

Kin riƙe ni riƙon amana,
Kin ciyar ni dare da rana,
Kuma ba gajiya ki kai ba.

Sha-biki laƙabin uwar mu,
Na ji yo daga Malaminmu,
Dr. Kabura ba kawai ba.

Jaruma ce babu shakka,
Shugaba ce kam haƙiƙa,
Inna ba raguwa bace ba.

Ko a mata ke daban ce,
Kin fi dubbai a rubuce,
Ba kawai zance nake ba.

Duk da ba tafiya kike ba,
Kuma ba tsayuwa kike ba,
Ba ki yarda ki shantake ba.

Wanda duk ya san ki Balla,
To a Keke ya gan ki Allah,
Na Guragu ba hawa ba.

Tun tana 'yar ƙaramar ta,
Wanga cuta ta riƙe ta,
Ba ta girma da tafiya ba.

Ba ta ɗauki hakan naƙas ba,
Ba ta yarda da naƙasa ba,
Zuciyar ba ta naƙashe ba.

Da ta tashi tayo karatu,
Kuma ga ta uwar rubutu,
Ba iya nan ta tsaya ba.

Sai ta ƙirƙiri ƙungiyar ta,
Ta naƙas duka 'yan uwanta,
Ba naƙas ɗin zuciya ba.

Ba ta yarda su yo bara ba,
Naƙasa ba ta zam gaza ba,
Mai naƙas ba zai gaza ba.

Ƙarfafa su take haƙiƙa,
Don su rayu kawai su haska,
Ba su zam mara galihu ba.

Babu mai naƙasa a zahir,
Sai fa wanda ya saki dahir,
Bai zamo mai fa'ida ba.

Naƙasasshe shi ya kasa,
Babu kasasshe kamar sa,
Ita ba a jiki take ba.

Dole ne nayi yo yabonki,
Don a guna kin fi Sarki,
Ba kurum waƙa nake ba.

Emeritus ya yabe ki,
Shehu Umaru ya kira ki,
Jaruma ba mai naƙas ba.

Rabbi ja mana kwanakin ta,
Rabbi kyautata lafiyarta,
Ba ta zam mara lafiya ba.

Rabbi ba ta abin biɗar ta,
Rabbi ƙarfafi zuciyarta,
Rabbi ba don baitukan ba.

Rabbana kare ta Allah,
Rabbi ɗauke mata jalalah,
Rabbi domin ɗan Suwaiba.

Rabbi duk daraja ka ba ta,
Don akwai haƙuri gare ta,
Hikima ba ƙanƙani ba.

Rabbi ninka dubun Salati,
Gun Habibu da nai wafati,
Ahlu Baiti ba zan shika ba.

Mai yabon dai Ɗanbala ne,
Mara shin hikima ku gane,
Za ku shaida hakan a gabba.

Baituka Ashirin na tsara,
Da biyar ga uwar su Zahra,
Mama Adama ba ta yau ba.

©
Mohamed Bala Garba.
5:07pm
22 August, 2026.
Adama Yarima Balla

Post a Comment

0 Comments