Article Citation: Sani, A.-U., & Suleiman, M. (2026). Tauraron mawaka: Aminu Ladan Abubakar a faifan daukaka. Njinga & Sepé: Revista Internacional de Culturas, Línguas Africanas e Brasileiras, 6(Special II), 292–312. UNILAB, Brazil https://revistas.unilab.edu.br/njingaesape/article/view/2923
Tauraron Mawaƙa: Aminu Ladan Abubakar a Faifan Ɗaukaka
Na
Abu-Ubaida
SANI, Ph.D.
Department
of Languages and Cultures,
Federal
University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | abu-ubaidallah@fugusau.edu.ng
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Da
Musa Suleiman
Department of Hausa, Aminu Kano College of
Islamic and Legal Studies, Kano
Email: musasuleiman424@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0009-0004-9860-0473
Phone: +1238061256096
Tsakure
Manufar wannan bincike ita ce nazartar fice da shahara da
mawaƙi Aminu Ladan Abubakar (ALA) ya yi a tsakanin mawaƙa a ƙasar Hausa. Domin tattara
bayanai, an bibiyi ɗakunan adana bayanan ilimi,
don bitar littattafai da kundaye da mujallu; musamman waɗanda suke da alaƙa da ALAn Waƙa. An ɗora aikin a kan Ra’in
Tasirin Taurari a Kan Al’ada (Celebrity Theory of Culture). Ra’in ya jagoranci
aikin bisa mahangar cewa, lallai ficen ALA a matsayin tauraro ya kai ya yi
tasiri a al’adun Hausawa. Binciken ya gano cewa mawaƙin ya ɗamfaru da wasu siffofi
nagartattu da suka zamar da shi fitacce kuma na daban a duniyar waƙa. Haka kuma, an fahimci
cewa mawaƙin ya kasance tauraro da yake da nagartattun
halaye da ɗabi’u da al’adu. Alaƙarsa da masu sarauta da
attajirai da malamai ta sanya tauraron mawaƙin haskawa har ya zama
sha-kundum kuma gagara-gasa a tsakanin takwarorinsa. Daga ƙarshe, takardar ta bayar da
shawarwari da suka haɗa da kira ga yin wani
gagarumin taron ƙara wa juna sani domin nazartar ɗaukacin rayuwa da waƙoƙin tauraron.
Fitattun Kalmomi: Tauraro, Ɗaukaka, Waƙa, Mawaƙa, Waƙoƙin Hausa
Abstract
This study examines the rise, prominence, and cultural
influence of Aminu Ladan Abubakar (ALA), one of the most recognizable and
celebrated figures in contemporary Hausa music. The research is based on an
extensive review of academic works (including books, theses, and journal
articles) particularly those that discuss ALA’s artistic contributions. The
Celebrity Theory of Culture provides the analytical framework, offering insight
into how ALA’s public visibility and artistic presence have shaped modern Hausa
musical expression. The findings show that ALA’s talent, artistic discipline, and
commitment to moral and cultural values have played central roles in elevating
his status. His strong relationships with traditional leaders, wealthy patrons,
and scholars have further enhanced his visibility, helping to position him as a
distinguished and influential cultural figure within the Hausa entertainment
industry. The paper concludes with recommendations, including the need for a
major symposium to further examine ALA’s life, body of work, and enduring
impact on Hausa music and culture.
Keywords: Celebrity, Fame, Music, Hausa Singer, Hausa Music
1.0 Gabatarwa
Aminu ALA ɗaya ne daga cikin fitattun mawaƙan Hausa na zamani da suka
yi fice wajen yaɗa al’adu da ilimintarwa da
nishaɗantar da al’umma ta hanyar
waƙa. ALA ya shahara ne saboda irin hikima da fasaha da
yake ɗora wa baitocin waƙarsa, wanda ya bambanta shi
da sauran mawaƙan Hausa. Waƙoƙinsa ba wai nishaɗi kaɗai suke bayarwa ba, har ma
suna ɗauke da darussa masu zurfi
da suke ƙarfafa tunani da zaburarwa ta fuskar neman ilimi da kuma
gina kyawawan ɗabi’u a cikin al’umma.
Wannan ne ya sa ake kallon sa a matsayin tauraron mawaƙa, wanda ya yi zarra a
tsakanin takwarorinsa. ALA ya bambanta da takwarorinsa saboda salon waƙoƙinsa masu ɗauke da karin magana da hikima da kuma amfani
da harshen Hausa cikin tsari mai sauƙi da jan-hankali.
Kasancewar ba a rasa nono a ruga, akan samu wasu mawaƙa da suka yi fice ta wasu
fuskoki daban kamar waƙoƙin soyayya da siyasa da yabo da na fada da kuma faɗakarwa. Duk da cewa sun shahara a ire-iren waɗannan ɓangarrori da suka keɓanta da su; ba sa iya taɓuka abin a-zo-a-gani a sarauran fannonin waƙa. Shi kuwa ALA, ya shiga
dukkan waɗannan fannoni - ya ba da
tasa gudummawa. Wannan dalili ne ya sanya tauraruwarsa ta haska har ya zama
zakaran gwajin dafi, sha-kundum kuma garara-gasa a tsakanin takwarorinsa. Waƙoƙinsa suna ɗauke da zurfin ma’ana da ke sa mai sauraro ko
mai karatu yin tunani mai zurfi. Wannan salon ne ya sa waƙoƙinsa suka shahara.
A taƙaice dai, an gina wannan bincike ne da manufar nazartar
fice da shaharar da mawaƙi Aminu Ladan Abubakar (ALA) ya yi a tsakanin mawaƙa a ƙasar Hausa. An dubi irin
rawar da ya taka wajen gina waƙa a matsayin hanyar sadarwa da raya al’adu da nishaɗi da faɗakarwa da wayar da kai da soyayya da kuma
ilimintarwa. Kai tsaye, binciken ya mayar da hankali a kan muhimman
abubuwan da suka haɗa da:
a. Tantance tasirin shahara da ficen da ALA ya
yi a tsakanin mawaƙa da kuma al’umma.
b. Fito da alaƙar da take tsakaninsa da
wasu rukunnonin al’umma.
c. Nuna ɗaukakarsa a matsayin tauraro kuma gagara-gasa.
2.1 “Tauraro” da “Ɗaukaka” a Bahaushiyar
Al’ada
A ma’ana ta lugga, kalmar “tauraro” (tàuraaròo, sn., nj.,
mc., tàuraarùwaa; jam., tàuràarii ko tàuràaruu) tana ɗaukar ma’anoni kamar haka: (i) halittar da ke
bayyana a sararin sama da daddare tana haske, daidai da tamraro,
(ii) shahararren mutum ko wata halitta, musamman cikin labaru, (iii) alama ta
farin gashi a girar doki, (iv) sa’a. (Sa'id da wasu (editoci) (2006, sh. 433)
A al’adance, Hausawa suna kallon kalmomin “tauraro” da “ɗaukaka” a wata mahanga wadda ta saɓa da ma’anarsu ta zahiri. A wajen Bahaushe
idan aka ce “tauraro” ana nufin wani mutum wanda ya yi suna, ya shahara a
wani ɓangare na rayuwa. Bugu
da ƙari, Hausawa suna kallon tauraro a matsayin mutum mai
basira da hikima da ƙwarewa da fice ta fuskar abubuwan da al’adu da kuma
addinin da wannan al’ummar suka aminta da shi. Hakan ya sa ake samun wasu
al’umma suke tasirantuwa da shi, saboda shararsa da ficensa.[1]
Ita kuwa “ɗaukaka” a wajen Hausawa
tana nufin daraja da girma da samun matsayi na yabo. Hausawa suna amfani da
kalmar wajen nuna nasara ko fice da mutum ya samu ta hanyar aiki tuƙuru da fasaha da
kyawawan ɗabi’u.[2] A
al’adance, kalmomin suna da tasiri wajen gina kyawawan ɗabi’u, domin suna ƙarfafa wa al’ummar Hausawa
guiwa su yi aiki tuƙuru don su zama taurari su kuma ɗaukaka. Wannan ne ya sa mawaƙa da marubuta suke amfani
da kalmomin a waƙoƙinsu da rubuce-rubucensu domin nuna yadda fice da shahara
suke da tagomashi ga jama’a.
2.2.
Waiwayen Tarihin Aminu Ladan Abubakar
Tarihin Aminu Ladan Abubakar (ALA) ba ɓoyayye ba ne a ƙasar Hausa. Wannan ya samo
asali daga ficen da ya yi bayan watsuwar waƙoƙinsa da suka karaɗe ƙasar Hausa. Daga nan aka samu rubuce-rubuce
da dama da aka gudanar a matakan ilimi daban-daban game da tarihinsa da kuma waƙoƙinsa. Daga cikinsu akwai
Faragai, (2008) da Imran (2008) da Malami (2010) da Hamza (2011)A da
Hamza (2011)B da Lawan (2011) da Umar (2011) da Mohammed (2014)
da Lawal (2015) da Ahmad (2017) da Sulaiman (2017) da Yakasai da Sani (2021) da
kuma Sani da Suleiman (2022). A bisa wannan, kawo tarihinsa tiryan-tiryan zai
zama maimaici ne kawai a kan abin da aka riga aka kundace a rubuce-rubucen da
suka gabaci wannan. Sakamakon haka, wannan takarda ta mayar da hankali a kan
kawo waɗansu muhimman al’amura da
suka shafi rayuwarsa kawai.
Aminu Ladan Abubakar da kan sa ya yi tsokaci game da
haihuwarsa a inda yake cewa:
Shekararrun
haihuwata,
Hijira
ta alif dubu ɗai,
Ma’anar
manufar ɗugunna,
A Municipal Kanawa,
Nan ne
aka haihuwa ta,
Dangane da karatunsa na boko da na Islamiya kuwa, yana
cewa:
Nai
ilmin Islama,
Nai
ilmi zamanina,
Gwargwado
dai diploma,
Nai
kan Art and design,
2.3
Dabarun gudanar da bincike
Wannan takarda ta tattara bayanan da aka nazarta kai
tsaye daga bibiyar ɗakunan adana bayanan ilimi.
An gudanar da bitar littattafai da kundaye da mujallu; musamman waɗanda suke da alaƙa da ALAn Waƙa. Waɗannan bayanan da aka samu daga rubuce-rubucen masana
sun yi ƙarin haske da jagoranci ga wannan bincike.
An ɗora wannan bincike a kan,
Ra’in Tasirin Taurari a kan Al’ada (Celebrity Theory of Culture),
wanda Richard Dyer (1970 da 1990) da Chris Rojek (2001) suka samar da shi.
Ra’in ya samo asali ne a ƙarshe ƙarni na 20 yayin da masanan suka fara nazarin tasirin
shahararun mutane mashahurai a kan ɗabi’u, halaye da al’adun al’umma. Wannan ra’i ya nuna
cewa, mashahurai ba kawai masu samar da nishaɗi ba ne, har ma suna da tasiri mai ƙarfi wanda yake tsara
yanayin zamani, ra’ayoyin jama’a da ayyukan al’umma.
Ra’in ya samu karɓuwa musamman ta bunƙasar kafofin yaɗa labarai na talabijin da mujallu. Daga bisani kafafen
sada zumunta sun ƙara bayyana shi, yayin da aka samu mashahuran mutane da
suka yi fice a cikinsu. Masanan sun nuna cewa, yayin da mutane da yawa suke bi
ko girmama mashahuran mutane, ɗabi’unsu da salon suturarsu da ra’ayoyinsu (na fitattun
mutanen) suna yin tasiri a cikin al’umma. Hakan ne kuma yake ƙara ƙarfafa ikon mashahurai a
kan al’adu.
Ra’in ya samu tagomashin ayyukan masana waɗanda suka haɗa da: Dyer (1986) da Street (2004) da Rojek
(2001) da Rojek (2012) da Gamson (1994) da Turner (2004) da Turner
(2013) da Marshall, (1997) da Marshall (ed.) (2006). Manufar
wannan ra’in ta nuna tasirin mashahuran mutane a cikin al’umma ta yi canjaras
da ta wannan bincike. Wannan dalilin ne ya sa aka ɗauki ra’in domin ya jagoranci aikin bisa mahangar cewa,
lallai ficen ALA a matsayin tauraro ya kai ya yi tasiri a al’adun Hausawa.
4.0
ALA a Matsayin Tauraro Gagara-Gasa
A wannan bagire, binciken ya kawo wasu matakai da aka yi
amfani da su domin tabbatar da iƙirarin ALA a matsayin tauraro gagara-gasa. Waɗannan matakai su ne suka tabbatar da
matsayinsa na nagarta, fice, da tasiri - kuma abin alfahari a tsakanin mawaƙan Hausa. Daga cikin waɗannan matakai akwai:
4.1
Shakundum a Fagen Waƙoƙi
Aminu ALA yana da matsayi na musamman sakamakon irin
ficen da ya yi a tsakanin mawaƙan Hausa. Shaharsa ta samo asali ne daga fasaha da
nagarta da kuma irin tasirin da yake da shi a cikin al’ummar Hausawa. Zamansa a
matsayin tauraro kuma gagara-gasa ba ya rasa nasaba da ƙwarewa da yake da ita a waƙoƙin Hausa.
Su kansu takwarorinsa suna kallon sa a matsayin jagora
kuma abin koyi. Dalilin faɗin haka shi ne, duk
wani fage na waƙa da ake ginawa a kan wani jigo, ALA ya taɓa wannan ɓangare. Misali, idan aka ɗauki ɓangaren waƙoƙin sarauta, ALA sha-kudum
ne a wannan fannin kasancewar ya yi waƙoƙi da dama a cikinsa.[4] A
fagen waƙoƙin siyasa, nan ma ba a bar shi a baya ba.[5] Idan
aka dubi waƙoƙin baƙar addu’a, shi ma ba daga nan ba.[6] Haka
kuma, ya yi waƙoƙin yabo da faɗakarwa da wa’azi da soyayya da kuma nishaɗi. Wani abin sha’awa da birgewa shi ne, ALA
ya kasance mawaƙi guda ɗaya tilo da ya yi “Alfiyya”
a wannan zamani. A wannan lokacin da ake ciki, babu wani mawaƙi da aka yi
wa “Diwani” sai Aminu ALA. Ire-iren waɗannan siffofi suna daga cikin abubuwan da suka bambanta
ALA da sauran mawaƙan Hausa, har ya zaman shakundum kuma gagara-gasa.
4.2
Alaƙarsa da Sarakuna
Aminu ALA ya kasance mawaƙi da yake da kyakkyawar
dangantaka da masu sarauta a ciki da wajen ƙasar Hausa. Masu sarauta su
ne fitulu da suke haska al’umma wajen rayawa da adana al’adu. Wannan ya sa
al’umma suke koyi daga gare su a matsayin jagorori. Alaƙar da take tsakanin ALA da
sarakuna ba ta waƙa ba ce kaɗai. Shi kansa Basarake ne
jinin gidan sarautar Gobir daga cikin zuri’ar Gwankawa.[7] Wannan
yana daga cikin abubuwan da suka ƙara ƙulla kyakkyawar alaƙa tsakaninsa da sarakuna;
wanda hakan ya sa ake ba shi girma da ganin darajarsa. A wasu lokuta akan
karrama shi kamar yadda ake yi wa sarakuna.
Wani babban tagomashi da ALA ya samu a rayuwarsa shi ne, karrama shi da sarautun gargajiya daban-daban. Hakan ta faru ne sakamakon kyakkyawar alaƙa da yake da ita da sarakuna a ƙasar Hausa. Wannan ya ƙara masa fice tare da ɗaukaka sama da mawaƙan Hausa da dama. Sarautun da yake riƙe da su sun haɗa da:
a. Sarkin Waƙar Dutse (Sahibul-Hikima), a masarautar Dutse da ke Jahar Jigawa
b. Ɗan Amanar Bichi, a masarautar Bichi da ke Jahar Kano[8]
c. Dujimin Ƙaraye, a masarautar Ƙaraye da ke Jahar Kano
d. Ɗanburan Gobir, a masarautar Gobir/Sabon Birni da ke Jahar Sakkwato
e. Sarkin Ɗiyan Gobir, a masarautar Maraɗi da ke Jamhuriyar Nijar
f. Fasihin Hausawan Duniya[9]
4.3
Alaƙar ALA da Attajirai
Aminu ALA yana da kykkyawar alaƙa da Attajirai a matsayinsa
na tauraro kuma mai tasiri a cikin al’umma. Alaƙarsa da Attajirai ba ta
rasa nasaba da yadda ya riƙe al’adu da addini da kuma zalaƙar harshe da yake da ita
wajen isar da saƙo a cikin waƙoƙinsa. Wannan dalilin ya sa wasu attajirai suke jan sa a
jiki tare da ba shi tallafi domin ci gaban ayyukansa. Wannan tallafi da ALA
yake samu, shi ne ya ba shi ƙwarin guiwar gina gidauniya mai suna, “ALAn Waƙa Foundation.”[10]
Mawaƙin ya yi amfani da wannan gidauniya wajen tallafa wa
gidajen marayu da na masu lalurar ƙwaƙwalwa.[11] Gidauniyar
ta ci gaba da ayyukan da ta saba na tallafa wa marasa galihu, musamman bayar da
kayan abinci da kiwon lafiya da kuma taimakon gaggawa ga al’umma. Haka kuma,
gidauniyar tana tallafa wa ayyukan raya al’adu da shirye-shiryen waƙoƙi da tarukan da suke da alaƙa da bunƙasar harshen Hausa.
Ire-iren waɗannan ayyukan da ALA yake
gudanarwa a sakamakon alaƙasa da attajira ta sanya ya zama tauraro gagara-gasa a
cikin mawaƙan zamani. Waɗannan kyawawan ɗabi’u, sun taimaka wajen zamar da shi zakaran–gwajin-dafi
a tsakanin mawaƙan zamaninsa.
4.4
Alaƙar ALA da Malamai
Aminu ALA mutum ne da ya tashi a gidan malanta kuma yake
da sha’awar neman ilimi.[12] Wannan
yana daga cikin abubuwan da suak ƙara ƙulla alaƙarsa da Malamai.[13] A
wajen neman ilimi, a nan ne ya samu tarbiyya tun daga Islamiyya. ALA ya samu
tagomashin naƙaltar hikima da fasaha ta hanyar ƙirƙirar waƙa cikin tsari.[14] Waƙoƙin da ya gudanar sun nuna
cewa ALA yana ɗauke da ilimi da fahimtar
darussa na addinin Musulunci. Hakan ya nuna cewa, malaman addinin Musulunci sun
taka muhimmiyar rawa wajen gina halayensa da fasaharsa da kuma tasirantuwa da
ya yi da ɗabi’unsu a rayuwarsa.
Dalilin haka ya sa mafiyawancin waƙoƙinsa suke ɗauke da jigogin addini da suka haɗa da wa’azi da faɗakarwa da gargaɗi da tarbiyya da wayar da kai da kuma yabo.
A ɓangare ilimin zamani (boko)
kuwa, ALA ya yi firamare da sakandare da difiloma (diploma), sannan ya yi
mu’amula da malaman zamani da dama. A sakamokon haka ya samu ilimin zamani da
ya ƙara bunƙasa basirarsa a duniyar adabin Hausa. Aminu ALA ya yi waƙoƙi da dama da suke ƙunshe da yabon malamai tare
da nuna matsayinsu na jagororin al’umma masu ba da ilimi da kuma tarbiyya. Waɗannan waƙoƙin sun ƙara tabbatar da kyakkyawar
alaƙarsa da Malamai. Wasu daga cikin waɗannan waƙoƙi sun haɗa da:
A- Na Malaman Boko na Zamani
1. Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau
2. Farfesa Ɗandatti Abdulƙadir
3. Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo
4. Farfesa Ahmad Bello Zaria (A.B.Z.)
5. Farfesa Abdullah Uba Adamu
6. Farfesa Yusuf Adamu
7. Farfesa Salisu Ahmad Yakasai
8. Farfesa Aliyu Muhammad Bunza
9. Farfesa Ibrahim Aliyu Malumfashi
10. Farfesa Isah Muktar
11. Farfesa Magaji Tsoho Yakawada
12. Dr. Gaji Ɗantata
13. Dr. Hauwa’u Muhammad Bugaje
14. Dr. Ahmadu Bello
B - Na Malaman Addinin Musulunci na Zamani
1. Sheikh Muhammad Sambo Rigacikum
2. Sheikh Ɗahiru Usmanu Bauchi
3. Sheikh Abdul Wududi Ghana
4. Sheikh Ibrahim Khalil
5. Sheikh Sanin Ba
4.5
ALA a Duniyar Ilimi
Tauraron Aminu ALA ya haska ƙwarai a duniyar ilimi.[15] Wannan
ya haɗa da ilimin addinin
Musulunci da kuma na zamani kamar yadda wannan bincike ya bayyana a baya. Ta
fuskar ilimin addinin Musulunci, malamai suna kallon sa a matsayin malami,
kasancewar a cikin waƙoƙinsa ana samun tsattsafin ayoyin Alƙur’ani da hadisai da kuma
amfani da kalmomin Larabci. Waƙarsa ta “Hasbunallah wa ni’imal wakilu” tana nuni ga irin
ilimin addinin Musulunci da yake da shi na sanin muhimmanci addu’a.
A ɓangaren ilimin boko kuwa,
sai dai a ce san barka, domin duk mai sauraren waƙoƙinsa ya san cewa ya yi
karatun zamani. Akan ji ya yi tsattsafin kalmomin da suka shafi ɓangarorin kimiyya da fasaha da kiwon lafiya a
cikin Turancin Ingilishi. Waƙarsa ta “Jami’a” kaɗai ta isa hujjar da za ta nuna cewa ALA yana da ilimin
zamani. Idan aka dubi yadda ya bayyana yanayin jami’a, abin sai dai a ce san
barka. Haka abin yake a waƙarsa ta “Baba ina za ka ne” wadda take nuni
da sanin siyasa da ya yi. A kalli waƙarsa ta, “Na zama ɗan jarida”, ita ma tana nuni da cewa
yana da wata masaniya a kan aikin jarida.
Malaman addinin Musulunci suna kallon waƙoƙin ALA a matsayin wata kafa
ta isar da saƙo cikin sauƙi ga al’umma da wayar da kai da wa’azantarwa da kuma faɗakarwa. Wannan ya sa wasu malaman addini suke
misali da wasu daga cikin waƙoƙinsa a lokutan wa’azinsu.
A zamanance kuwa, malamai suna kallon ALA a matsayin wani
madubi a fagen nazari. Wannan dalili ya sa akan nazarci waƙoƙin ALA a matakan kwalejoji
da kuma na jami’o’i. Zarrar da ya yi a wannan fage, ta nuna cewa babu wani mawaƙin zamani da aka gudanar da
bincike na ilimi masu ɗimbin yawa a jami’o’in da
suke ciki da wajen ƙasar nan kamar Aminu Ladan Abubakar (ALA). An gudanar da
bincike a kan waƙoƙinsa a matakai daban-daban da suka haɗa da, digiri na farko (B.A.), na biyu (M.A.)
da na uku (Ph.D.) waɗanda suka shafi harshe,
adabi da al’ada. Haka kuma, an yi rubuce-rubuce da dama a kan waƙoƙinsa a takardun ilimi tare
da gabatar da su a tarukan ƙara wa juna sani na ciki da wajen ƙasar nan. Kaɗan daga cikin misalan ayyukan da aka gudanar
game da shi da kuma waƙoƙinsa sun haɗa da:
A - Matakin Digiri na Farko (B.A.)
A nan an kawo ayyukan digiri na farko da aka gudanar a kan wasu waƙoƙin ALA. Wasu an gudanar da su a fannin adabi, wasu na al’ada, yayin da wasu kuma aka gudanar da su a ɓangaren nazarin harshe. Daga cikin waɗannan ayyuka akwai:
a. Jami’a Gidan Ban Kashi: Nazarin Matsayi da Ƙimar Jami’a ga Cigaba da Bunƙasa Al’ummar Hausawa (Malami, 2010)
b. Jigo da Salo a Waƙoƙin Aminu ALA (Imran, 2008)
c. Kiɗa da Waƙar Hausa Jiya da Yau: Kamance da Bambanci Tsakanin Waƙar Jami’ar Ahmadu Bello Zariya ta Alhaji Mamman Shata Katsina da ta Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Rogo, 2013)
d. Matsayin Uwa a Bahaushiyar Al’ada: Nazarin Waƙar “Ummina” ta Aminu Ladan Abubakar (Umar, 2011)
e. Nazarin Salon Sarrafa Harshe a Waƙoƙin Aminuddeed Ladan Abubakar (ALA) (Hamza, 2011)
f. Salo da Sarrafa Harshe a Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (Hamza, 2011)
g. Tasirin Zamananci kan Al’adun Hausawa: Nazarin Mu’amalar Aure Tsakanin Mata da Miji Cikin Waƙar Gizo-gizo ta Ala da Fati Nijar (Giɗaɗo, 2012)
h. Uwa a Bahaushiyar Al’ada: Nazarin Mu’amalar Uwa da Ɗa Cikin Waƙar Ummina ta Aminu Ala (Dikko, 2010)
B - Matakin Digiri na Biyu (M.A.)
A matakin digiri na biyu kuwa, an gudanar da bincike a cikin wasu waƙoƙin ALA. Nazarce-nazarcen da aka gudanar an aiwatar da su a fannonin harshe da adabi da kuma al’ada. Daga cikin waɗannan ayyuka akwai:
a. Nazarin Salo da Sarrafa Harshe a Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Faragai, 2008)
b. Kwatanta Salon Wasu Waƙoƙin Aminu ALA da na Fati Nijar (Mohammed, 2014)
c. Yabon Sarakuna a Waƙoƙin ALA: Nazari Daga Waƙar Bakan Dabo da Waƙar Farar Aniya Farar Atafa (Lawal, 2015)
C - Maƙalu da Mujallu
Masana da manazarta sun rubuta maƙalu da mujallu da dama a kan waƙoƙin ALA. Ga ‘yan misalai daga cikinsu:
a. Aminu Alan Waƙa a fagen rubutattun ƙagaggun labarai na Hausa (Mujaheed, 2021)
b. Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa) a tsakanin sha’irci da ƙagaggen labari (Shehu, 2011)
c. Bitar Littafin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALAN WAƘA) (Gusau, 2009)
d. Bugun gaba a waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa) (Mujaheed, 2019)
e. Hausa and the Green Environment: An Examination of Selected ALA’s Song (Ayuba, 2018)
f. HAWAN SARKI a MASARAUTAR KANO: Wani Ɗigo a Cikin Waƙar Mai Martaba Magajin Dabo (Suleiman, 2025)
g. Jiga-jigan Hausa a bakin mawaƙin Hausa: Waiwaye kan waƙoƙin ALA na Farfesa Abdulqadir Ɗangambo da Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau (Isah, 2014)
h. Nazarin harshen farfaganda cikin siyasar Kudanci da Arewacin Nijeriya cikin waƙar ALA ta Rajista (Yakasai, 2014)
i. Salon Hoton Zuci: Nazari a Waƙar Ta’aziyar Yahaya Mahmud da ta Ado Bayero na Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa) (Sulaiman, 2017)
j. Some Major Themes of Hausa Responsorial Songs in Aminu ALA’s Performance (Yakasai, 2012)
k. SURKIN HARSHE: Wani Ɗigo a Cikin Gulbin Waƙoƙin Aminu Alan Waƙa (Suleiman, 2025)
l. Tasirin Waƙa a Cikin Al’ummar Hausawa: Tsokaci Daga Wasu Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa) (Ahmad, 2017)
m. Tsattafin Haliya: Wani Ɗigo Cikin Tafashen Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Sani, 2022)
D - Bugaggun Littattafai
Littattafai da aka rubuta game da ALA sun haɗa da:
a. Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar ALAn Waƙa, Littafi na Ɗaya (Lawan, 2011)
b. Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Yakasai & Sani, 2021)
c. Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar Alan Waƙa: Littafi na Ɗaya (Barista, 2011)
Wani abin birgewa da wannan mawaƙi shi ne, babu mawaƙin zamani guda ɗaya tilo da aka yi wa “Diwani” sai shi.
Wannan kaɗai ya isa ya nuna shaharasa
da fice da zarra a tsakanin mawaƙa. Haka abin yake a ɓangare rubutun zube. Kafin Aminu ALA ya fara waƙoƙin zamani, sai da ya soma
rubuta littattafai na ƙagaggun labaran soyayya.[16] Littafi
na farko da ya rubuta shi ne, Jirgi Ɗaya. Ya rubuta shi a
shekarar 1992, amma sai a 1999 aka buga shi. Littafin ya yaɗu sosai a cikin jama’a. Bayan wannan littafin
ya samu damar ƙara wallafa wasu littattafai guda bakwai a wannan fanni.
Ga su kamar haka:
Jadawali Na 1: Wasu Littattafan Aminu Ladan Abubakar (ALA)
|
|
Littafi |
Shekarar Bugawa |
|
1. |
Baƙar Aniya |
2000 |
|
2. |
Cin Zarafi |
2001 |
|
3. |
Ƙawazuci |
2003 |
|
4. |
Tarzoma |
2003 |
|
5. |
Sawaba |
2003 |
|
6. |
Jirwaye |
2003 |
|
7. |
Jagoranci |
2004 |
Madogara: Yakasan da Sani (2021 sh. 16)
Tabbas! Aminu ALA tauraro ne kuma gagara-gasa a tsakanin
abokan waƙarsa na zamani. Sakamakon babu wani mawaƙi da ya haɗa hikimar waƙa da rubutun zube kamarsa a
wannan lokaci. Iya wannan ya isa ya bayyana shi a matsayin tauraro, kuma
gagara-gasa a tsakanin takwarorinsa mawaƙan zamani.
4.6 Riƙon Al’ada da Addinin
Musulunci
Riƙo da addini da al’ada ya zamar wa wannan mawaƙin tamkar hanta da jini. Ko
a cikin bidiyonsa, abu ne mai wahala a isko shi yana rawa irin wadda wasu mawaƙan zamani sukan yi.[17] Ta
fuskar tufafi kuwa, mawaƙin ba ya saka tufafi wanda ba na Hausawa ba. Hasali ma
wani lokaci yakan yi shigar sarauta ta al’ada, wanda hakan yake nuna
kasancewarsa cikakken Bahaushe. Waɗannan suna daga cikin
abubuwan da suka tasirantu a gare shi har ya samu waɗancan sarautu da binciken ya ambata a baya. Ke nan
haka yana nuna ɗaukakarsa har a fadojin ƙasar Hausa.
Aminu ALA duk da ɗaya ne daga cikin mambobi na Kannywood, shi ba ya nanaye
ba ya gala. Wannan ya sa mawaƙa abokansa suke mutuƙar ganin girmansa. Wasu
daga cikinsu suna kiran sa da suna “Malamin Waƙa”. Wannan suna ba a ƙasa ya ɗauka ba, kasancewarsa ma’abocin neman ilimin
addini. Hakan yana daga cikin dalilan da suka sa ya kafa makarantar da
suke ɗaukar karatun addinin
Musulunci.[18] Ke
nan za a ga cewa riƙon ALA da addini da al’ada shi ma wata hujja ce da ta
sanya ya zama wani mutum na musamman a tsakanin mawaƙan zamani. Ko da kuwa an fi
shi suna ko kuɗi, tabbas yana da wasu
siffofi da ya sha bambam da sauran mawaƙan zamani. Waɗannan siffofi nasa su ne suka ƙara jawo masa ƙima da daraja a wurin
al’ummar Hausawa.
4.7
Tasirin ALA ga Al’umma
Aminu ALA mawaƙi ne da ya samu ɗaukaka kuma ya yi shura a cikin al’ummar Hausawa. Wannan
bunƙasa da ALA ya yi a wannan fage na waƙoƙin zamani ta sanya ya zamo
wani madubi ga al’umma, saboda tasirin da yake da shi a gare su. Misali: Aminu
ALA jakadan zaman lafiya ne a al’adance.
Idan aka dubi labarin wata tsohuwa da ta zo gidansu a
galabaice, tana zuwa ta gan shi sai ta fashe da kuka. A nan ya taushe ta har ta
samu nutsuwa. Bayan da hankalinta ya dawo jikinta, sai ta fara ba shi labarin
abin da yake tafe da ita.Ta ce ‘yarta ta yi wa aure, an yi, an yi ta zauna,
amma ta ce ba za ta zauna ba, sai an kawo mata kaset ɗin ALA da ya yi waƙar “Ummi Momina”. Haka ya ɗauko kaset ɗin a wannan lokacin ba shiri ya ba ta. Ya yi haka ne don
a samu yarinyar ta zauna a gidan mijnta.” ALA da kansa ya kawo wannan a cikin
wannan labari a cikin “Shahara” inda yake cewa:
Wataran
a watan Nuwamba,
Wata
tsohuwa ta zo ta,
Rauni
linkif jikinta,
In
tana tafe sai ta huta,
Da kaɗan da kaɗan ta zo ta,
Da
shiga ta fashe da kuka,
Ko da
ta nutse ko ta huta,
‘Yar ɗiyata ce na wanke,
Mun yi
mun yi ta zauna,
Sai an
kawo mata kaset,
Kuma
an ce ba a sai da,
In
gidan radiyo ta kunna,
Ban
shirya fitar da shi ba,
Sai na
ba ta gami da ƙari,
Tsohuwa
ta rugume ni,
Ta
kirayi Ubangijinmu,
Makamancin irin wannan ya taɓa faruwa da wata tsohuwa da ta taso daga garin Illela
a ƙasar Sakkwato. Ta zo Kano don ta ga ALA har sau biyu.
Haka ta sha wahala kafin su haɗu da juna. Ranar da suka haɗu kuwa, tana ganin sa sai ta kama hawaye. Ta
bayyana masa irin soyayyar da take masa abin har yana neman ya cutar da ita.
ALA ya bayyana hakan a cikin Shahara da cewa:
Wata
tsohuwar Illela,
Tai maya biyu don mu gana.
Ni ko
saɓani gare ni,
Tai
maya biyu uku guna,
Da mu
kai arba da juna,
Sai ta
ce ko yanzu Allah,
Ka
cikan buri muradun,
Ta riƙe ni ta hau jawabi,
Lafazinka
idan na ji shi,
Boɓelle gari da nisa,
Illela
kusa da boda,
Na
taho domin biɗar ka,
Nan take Tsohuwa Illela ta yi wa Allah godiya saboda
burinta ya cika ta haɗu da ALA. Haka ALA ya karɓi tsohuwa hannu biyu ya sauke ta a gidansu ya
kuma karrama ta, ya yi mata kyautuka, ya ba ta hotunansa. A Shahara ALA
ya bayyana cewa:
Na yi
kalmomi gare ta,
Nai
kyautuka gare ta,
Da
atamfofi na sawa,
Daga ƙarshe, ya yi mata alƙawarin shi da kansa zai
kawo mata ziyara har garinsu kamar yadda ta kawo masa. Cikin ikon Allah haka ya
tashi mota da yaransa suka tafi ƙasar Sakkwato har garin Illela. Ya kai wa
tsohuwa ziyara.[19] Bugu
da ƙari, ya yi mata waƙa mai suna “Tsohuwa ta Illela.” ALA ya bayyana a
cikin Shahara cewa:
Muka
kwana gidan Khadija,
Nai waƙoƙin yabawa,
Aka
min tarbar bajinta,
Sai na ce ni gun Khadija,
Cikin runkar Khadija,
A
cikin runkar Khadija
Ko bayan waɗannan, an samu makamancin
wannan tsakanin ALA da wata yarinya ‘yar shekara bakwai (7) jikar Sarkin Kano
mai suna “Sa’adatu”.[20] A
taƙaice dai iri wannan tasiri na ALA a zamantakewa da
al’ummar Hausawa har sai da ta kai iskoki suna shafar masu sauraren waƙoƙinsa. Akwai mai gidansa,
ma’aikacin gidan radiyon Kano ne, mai suna “Malam Abdullahi Sani.” Iskoki sun
shiga jikin ‘ya’yansa. Da aka zo ana yi musu ruƙiyya, sai iskokin suka
bayyana inda suka ce yaranka kullum da safe da rana da yamma waƙoƙin ALA suke ji. Kuma ALA
gwaninsu ne, suna son sa. Mutuƙar za su kunna waƙarsa, to har abada suna tare da su. Da aka
tambaye su mene ne laifin ALA a wajensu, sun tabbatar da ba shi da laifin
komai. Soyayya ce kawai a tsakanisu.[21]
Aminu ALA yana tasiri a cikin al’umma ta fuskar siyasa,
sakamakon al’umma suna kallon sa a matsayin mutum mai ƙima da daraja. Wannan ne ya
sa suke ganin ba zai bi alƙiblar siyasar da za ta cutar da talakawa ba. Shi ne ya sa
idan ya fahimci tafiyar da yake bi ba mai kyau ba ce yake barin ta sannan ya
fito a cikin waƙa ya faɗa wa jagororin tafiyar
gaskiya. Wannan ta faru a zamanin mulkin shugabata Muhammadu Buhari. Ya goyi
bayansa a yaƙin neman zaɓe. Da ya ga matsala kuma ya
fito ya faɗa masa gaskiya.
Tasirin da ALA yake da shi a cikin zamantakewar Hausawa, ya sa har wasu mutane suke jingina sunansa da nasu. Misali:
a. Zayyanu ALA
b. Shafi’u Zakin ALA
c. Sanin ALA
d. Musan ALA da sauransu da dama.
Mutane suna yin haka ne saboda kasancewarsa mai
kyawawan ɗabi’u da halaye nagari da
riƙo da addini da kuma al’ada. Wani abin birgewa kuma, duk
wanda za ka ga ya jingina sunansa da na ALA sai a ga cewa sun yi canjaras ta
fuskar ɗabi’u da halaye da riƙon addini da al’ada. Ya yi
daidai da furucin masu iya magana cewa: “Ba a zama inuwa ɗaya sai hali ya zama ɗaya”.
4.8 Ɗaukakar ALA a Cikin
Zuri’arsa
A tsarin al’adun Hausawa, ɗaya daga cikin abubuwan da suke nuna ɗaukakar mutum shi ne yawan zuri’arsa, wato
adadin matansa da ‘ya’yansa. A tsarin al’adar Hausawa, ko sarki aka naɗa mutum yana da mata ɗaya, nan da nan za a auro masa ragowar guda
ukun su cike huɗu. Yawan mata da ‘ya’ya a
wajen Bahaushe wata ɗaukaka ce ta musamman a
cikin al’umma. Irin wannan ɗaukaka Allah ya albarkaci
Aminu ALA da ita, wadda hakan ya ƙara nuna fice da zarrar da mawaƙin ya yi a tsakanin mawaƙan zamani. Gusau, (2016 sh.
234) da kuma Yakasai da Sani (2021 sh. 7) sun kawo bayanai game da iyalan ALA.
Tun a shekarar 2021, yana da mata huɗu (4) da ‘ya’ya goma sha huɗu (14).
4.9 Yawan Waƙoƙinsa da Nau’o’insu
Dangane da yawan waƙoƙi kuwa, har zuwa yanzu ba a iya tantance
adadin waƙoƙin ALA ba. Duk da haka, a wata tattaunawa da binciken ya
yi da hadiminsa Shafi’u Zakin ALA ya bayyana cewa: “A yanzu haka akwai album ɗin waƙoƙin ALA guda arba’in da suke cikin kasuwa.
Kowane album ba zai rasa waƙoƙin aƙalla guda goma ba.” Ke nan
a iya album ɗaya yana da waƙoƙi kimanin ɗari huɗu da suka shiga kasuwa.[22]
Dangane da yanayin waƙoƙinsa kuwa, Yakasai da Sani (2021) sun raba nau’o’in waƙoƙin ta fuskar jigoginsu zuwa kashi goma sha ɗaya (11). Ga sukamar haka:
1. Waƙoƙin ilimintarwa da wa’azantarwa da faɗakarwa
2. Waƙoƙin siyasa
3. Waƙoƙin soyayya
4. Waƙoƙin sarauta
5. Waƙoƙin yabo/jinjina
6. Waƙoƙin ganin dama/sha’awa
7. Waƙoƙin talla
8. Waƙoƙin aure
9. Waƙoƙin zagin kasuwa
10. Waƙoƙin ta’aziyya
11. Waƙoƙin ɗaukaka
Idan aka dubi yadda aka raba waƙoƙin ALA bisa jigoginsu, za a
ga cewa ɗaukakarsa ta karaɗe duniyar waƙoƙin zamani. Duk wani babban
jigo na waƙa ALA bai gaza a kansa ba, sai da alƙalaminsa ya ɗiga tawada a kansa. Irin waɗannan dalilai su ne suka sanya ake ganin ALA
a matsayin tauraro kuma gagara-gasa a tsakanin takwarorinsa mawaƙan zamani.
5.0
Kammalawa
Lallai Aminu Ladan Abubakar (ALAn Waƙa) ya kasance babban
tauraro a fagen waƙoƙin Hausa na zamani. Ya samu ɗaukaka ta fuskoki masu yawa. Sun haɗa da sarautu da yake riƙe da su da tasirinsa ga
al’umma da ɗimbin waƙoƙinsa waɗanda jigonsu suka ƙunshi mamaye da dama.
Sirrukan wannan ɗaukaka sun samo asali daga
yadda yake mu’amala da mutane a matakai daban-daban, kamar sarakuna da malaman
addini da na boko da sauran rukunonin al’umma. Haka kuma, riƙon da ya yi da addini da
kyawawan al’adu da jajircewa bisa gaskiya da amana sun ƙara masa kwarjini da farin
jini a cikin takwarorinsa.
Akwai buƙatar a yi taron ƙara wa juna sani na
musamman domin faɗaɗa tattaunawa a kan rayuwa da waƙoƙin ALA. Bugu da ƙari, akwai buƙatar ci gaba da bincike a
matakan ilimi daban-daban game da falsafar rayuwarsa da waƙoƙinsa domin sake fito da su
fili tare da kundace su. A ɓangare ɗaya kuwa, yunƙurin ayyuka game da ALA zai
taimaka wajen jawo hankali wasu mawaƙan Hausa domin koyi da tafarkinsa na riƙo da addini da kyawawan
al’adu.
Manazarta
Adewale, E. O. (1984). An introduction
to social anthropology. Agbo Areo Publishers.
Ahmad, S. B. (2017). Tasirin waƙa a cikin al’ummar Hausawa: Tsokaci daga wasu waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa). Takardar da aka gabatar a taron Masoya Aminu Ladan Abubakar Alan
Waƙa, Kano.
Aliyu, S. B. (1986). Alhaji Isah Mai
Kukuma Mina da waƙoƙinsa (Kundin digiri na farko). Jami’ar Jihar Sakkwato.
Ayuba, A. (2018). Hausa and the green
environment: An examination of selected ALA’s song. Yobe Journal of
Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), 6. Yobe State University.
Barista, M. L. (2011). Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar Alan Waƙa: Littafi na ɗaya. Iya
Ruwa Publishers.
Bunza, A. M. (2009). Narambaɗa. Ibrash
Islamic Publication Center Limited.
Ɗangambo, A. (2007). Ɗaurayar gadon feɗe waƙa. Amana Publishers.
Dikko, S. S. (2010). Uwa a Bahaushiyar
al’ada: Nazarin mu’amalar uwa da ɗa cikin
waƙar Ummina
ta Aminu Ala (Unpublished
undergraduate thesis). Usmanu Danfodiyo University.
Dyer, R. (1979). Stars. BFI.
Dyer, R. (1986). Heavenly bodies: Film
stars and society. British Film Institute.
Dyer, R. (1986). Heavenly bodies: Film
stars and society. Macmillan.
Dyer, R. (1990). Now you see it: Studies on
lesbian and gay film. Routledge.
Faragai, N. A. (2008). Nazarin salo da
sarrafa harshe a waƙoƙin Aminu
Ladan Abubakar (ALA) (Kundin
digiri na farko). Bayero University.
Gamson, J. (1994). Claims to fame.
University of California Press.
Gamson, J. (1994). Claims to fame: Celebrity in
contemporary America. University of California Press.
Giɗaɗo, H. A. (2012). Tasirin zamananci kan al’adun Hausawa:
Nazarin mu’amalar aure tsakanin mata da miji cikin waƙar Gizo-gizo ta Ala da Fati Nijar (Unpublished undergraduate thesis). Kaduna
State University.
Gobir, Y. A., & Sani, A.-U. (2021). Waƙoƙin Hausa na gargajiya. Amal Printing and Publishing.
https://www.amsoshi.com/2026/05/wakokin-hausa-na-gargajiya.html
Gusau, S. M. (2009). Bitar littafin waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa). Takardar taro, Bayero University.
Gusau,
S. M. (2015). Mazhabobin ra’i da tarƙe a adabi da al’adu na Hausa. Century Research and Publishing.
Gwammaja,
K. D. (2018). Jagoran nazarin karin magana. KDG Publishing Limited.
Hamza, M. K. (2011a). Nazarin
salon sarrafa harshe a waƙoƙin Aminuddeen Ladan Abubakar (ALA) (Kundin
digiri na farko). Usmanu Danfodiyo University.
Hamza,
M. K. (2011b). Salo da sarrafa harshe a waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (Kundin
digiri na farko). Usmanu Danfodiyo University.
Imran,
A. L. (2008). Jigo da salo a waƙoƙin Aminu ALA (Kundin digiri na
farko). Ahmadu Bello University.
Isah,
Z. (2014). Jiga-jigan Hausa a bakin mawaƙin
Hausa: Waiwaye kan waƙoƙin ALA na Farfesa Abdulqadir Ɗangambo da Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau. In S. M. Gusau et al. (Eds.), Garkuwan
adabin Hausa: A festschrift in tribute to Abdulqadir Ɗangambo. Ahmadu Bello University Press.
Lawal, M. (2015). Yabon sarakuna a waƙoƙin ALA (Kundin digiri na biyu). Kaduna State University.
Lawan, M. B. (2011). Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar Alan Waƙa: Littafi na ɗaya. Iya
Ruwa Publishers.
Magaji, B. (2009). Nazarin aron kalmomi
a waƙoƙin Muhammadu Sambo Wali Giɗaɗawa (Kundin digiri na farko). Usmanu Danfodiyo University.
Malami, U. (2010). Jami’a gidan
ban ƙashi (Kundin digiri na farko). Usmanu Danfodiyo
University.
Marshall, P. D. (1997). Celebrity and
power. University of Minnesota Press.
Marshall, P. D. (1997). Celebrity and power:
Fame in contemporary culture. University of Minnesota Press.
Marshall, P. D. (Ed.). (2006). The
celebrity culture reader. Routledge.
Marshall, P. D. (Ed.). (2006). The celebrity
culture reader. Routledge.
Mohammed, Y. (2014). Kwatanta salon wasu
waƙoƙin Aminu ALA da na Fati Nijar (Kundin digiri na biyu). Bayero
University.
Muhammad, D. (1980). Waƙa Bahaushiya. In Studies in Hausa
language, literature and culture. Bayero University.
Mujaheed, A. (2019). Bugun gaba a waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa). In B. Zulyadaini (Ed.), Yobe Journal
of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), 7. Yobe State University.
Mujaheed, A. (2021). Aminu Alan Waƙa a fagen rubutattun ƙagaggun labarai na Hausa. Algaita:
Journal of Current Research in Hausa Studies, 14(1), 173–188.
Omar, S. (2013). Fasahar mazan jiya.
Garkuwa Media Service Limited.
Rogo, M. S. (2013). Kiɗa da waƙar Hausa jiya da yau (Unpublished undergraduate thesis). Kaduna State University.
Rojek, C. (2001). Celebrity.
Reaktion Books.
Rojek, C. (2001). Celebrity. Reaktion Books.
Rojek, C. (2012). Fame attack.
Bloomsbury.
Rojek, C. (2012). Fame attack: The inflation of
celebrity and its consequences. Bloomsbury Academic.
Sa’id, B., et al. (Eds.). (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Ahmadu Bello University Press.
Sani, A.-U., & Suleiman, M. (2022).
Tsattsafin haliya: Wani ɗigo cikin tafashen Aminu Ladan Abubakar
(ALA). South Asian Research Journal of Arts, Languages and Literature,
4(2), 70–77.
https://www.amsoshi.com/2022/04/tsattsafin-haliya-wani-igo-cikin.html
Shehu, I. (2011). Aminu Ladan Abubakar
(Alan Waƙa) a
tsakanin sha’irci da ƙagaggen labari (Departmental seminar paper). Kaduna State University.
Street, J. (2004). Celebrity politicians. British
Journal of Politics and International Relations, 6(4), 435–452.
Street, J. (2004). Celebrity politicians:
Popular culture and political representation. British Journal of Politics and
International Relations, 6(4), 435–452.
Suleiman, M. (2025). Hawan sarki a
masarautar Kano. Unpublished manuscript.
Suleiman, M. (2025). Surkin harshe.
Unpublished manuscript.
Turner, G. (2004). Understanding celebrity. Sage
Publications.
Turner, G. (2004). Understanding
celebrity. Sage.
Turner, G. (2013). Celebrity culture.
Sage.
Turner, G. (2013). Understanding celebrity (2nd
ed.). Sage Publications.
Yahya,
A. B. (1997). Jigon nazarin waƙa. Fisbas Media Services.
Yahya,
A. B. (1999). Salo asirin waƙa. Fisbas Media Services.
Yahya,
A. B. (2004). Tsattsafin raha cikin waƙoƙin Alƙali Haliru Wurno. Takardar taro, Usmanu
Danfodiyo University.
Yahya,
A. B. (2013). Tsattsafi: Wani ɗigo
cikin nazarin salon waƙoƙin Hausa. Takardar taro, Usmanu
Danfodiyo University.
https://www.amsoshi.com/2023/04/tsattsafi-wani-igo-cikin-gulbin-nazarin.html
Yakasai, S. A. (2012). Some major themes
of Hausa responsorial songs in Aminu ALA’s performance. Conference paper,
Bayero University.
Yakasai, S. A. (2014). Nazarin harshen
farfaganda cikin siyasar Kudanci da Arewacin Nijeriya cikin waƙar ALA ta Rajista. In S. M. Gusau et al.
(Eds.), Garkuwan adabin Hausa: A festschrift in tribute to
Abdulqadir Ɗangambo. Ahmadu Bello University Press.
Yakasai,
S. A., & Sani, A.-U. (2021). Diwanin waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Amal
Printing Press.
https://www.amsoshi.com/2026/05/diwanin-wakokin-aminu-ladan-abubakar-ala.html
Brief
About the Authors
Dr.
Abu-Ubaida Sani
Dr. Abu-Ubaida Sani is a Nigerian
scholar, researcher, author, and academic specializing in Hausa culture and
modernity. He is a lecturer in the Department of Languages and Cultures at
Federal University Gusau, Nigeria. He has authored and edited numerous books
and published over one hundred scholarly articles and book chapters in
reputable national and international journals and conference proceedings. He
has presented papers at academic conferences within and outside Nigeria and
serves on the editorial boards of several scholarly journals across Africa,
Asia, the Middle East, and North America. Dr. Sani is the founder of Amsoshi
(amsoshi.com), one of the leading online platforms dedicated to Hausa language
scholarship and research.
Musa Suleiman
Musa Suleiman is a Nigerian
scholar, researcher, author, and academic specialising in Hausa language,
literature, culture, and media studies. He is a Lecturer in the Department of
Hausa at Aminu Kano College of Islamic and Legal Studies, Kano, where he
teaches in the affiliated degree programme of Federal University Dutsin-Ma, and
also serves as an External Facilitator at the National Open University of
Nigeria. He previously held academic appointments at Kano State College of
Education and Preliminary Studies and Dala College of Education, Kano. Musa
Suleiman has published numerous scholarly articles in reputable national and
international journals and conference proceedings and has presented papers at
academic conferences across Nigeria.
[1] Misali: Akwai taurari daban-daban da suka yi
fice a ƙasar Hausa. Ta fuskar siyasa, akwai Sir
Ahmadu Bello Sardauna. Ta furkar waƙar
baka ga (Dr.) Mamman Shata. Haka abin yake a fagen adabi, domin tarihin ba zai
manta da (Dr.) Abubakar Imam ba.
[2] Aminu
ALA ya kawo hoton ɗaukaka da fice a cikin waƙarsa ta Ɗanmazari
wadda ya yi ta naɗin
Sararutar Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa, Dauda Adamu Abdullah Kahutu (Rarara). Inda
yake cewa:
Idan na bi hujjoji,
A matakin kai Sarki,
Samunka da malanta,
Abin ka Furofesa,
Ko ka zama mai baiwa,
A gan ka da nairori,
Siyasar mai mulki,
Koko ka ɗare Gwamna,
A ina ka baro Rara?
A ina ka baro ALA?
[3]A
baitocin da ke sama, za a ga cewa, ALA ya bayyana ranar haihuwarsa da wurin da
aka haife shi.
[4] Ya
yi waƙoƙin
sarauta masu tarin yawa.
[5] Ya
taka muhimmiyar rawa a wannan fage. A shekarar (2015) waƙarsa ta “Baƙar
Malafa” ta yi tasiri sosai wajen jan hankalin al’ummar ƙasar Nijeriya a zaɓen shugaban ƙasa.
[6] Waƙoƙinsa na “Hasbunallahu” da
”Gilasai” sun yi suna sosai a ƙasar
Hausa.
[7] Domin ƙarfafa wannan zance, ga abin da ya bayyana a cikin waƙarsa ta shahara:
Ɗan
malam Sani ALA,
Sani Ladan Habu ne,
Shi ko Bakar ko ɗa ne,
Mijiyawa Kura Jarmai,
Ɗan
Sarki Dambuwa ne,
Ɗanbuwa ɗa ne ga Gwanki,
[8] Bayan
Sarkin Bichi ya dawo Kano, ya sake ɗaga darajar Sarautar tasa zuwa Ɗan’amanar Kano.
[9] An
yi masa wannan naɗi ne a
taron ranar Hausa ta Duniya a Jahar Gwambe.
[10] Akwai
takwarar wannan ƙungiya mai
suna “Dangin Juna Masoya ALA Foundation.”
[11] A
sakamakon ziyarar tallafi da ALA yake kai wa waɗannan gidaje da halin da ya
tarar suke ciki, ya sa shi ya yi waƙar
“Gidan Marayu” da ta “Gidan Mahaukata”. Ga abin da ya faɗa a cikin waƙarsa ta Shahara:
Wani loton sai a gan ni,
Ni da fagal za mu zauna,
Inda ‘yan canji a guna,
Nakasassu ma ku ji ni,
Da makafi har guragu,
Wata ran in kai ziyara,
Ko ni je ni gidan marayu,
[12] Domin tabbatar da wannan iƙirari ga bin da yake cewa da bakinsa a cikin waƙarsa ta shahara:
Nai ilmin Islama,
Matayassara gwargwado na.
Nai ilmi zamanina,
Boko dan zamanina.
Haka kuma, ya ƙara ƙarfafa
wannan iƙirari a wani baiti, inda yake cewa:
[13] Dubi
waƙarsa ta shahara inda ya tabbatar da wannan
batu. Yana mai cewa:
Sannu-sannu a kwan a tashi,
Sai ga ni ga malamina.
Sani Makarantar Lingu,
Shi ya zam tsani a guna.
Gunsa nai ilimi na waƙa,
Na rabe adabin baka na.
Nan na san wa ab Bahaushe,
Da al’adar garina.
Adabin gargajiyarmu,
Adabin ga na zamanina.
[14] ALA
ya bayyana haka a cikin waƙarsa
ta shahara inda yake cewa:
Babu wanda ya san da ALA,
Tun ina Islamiyyarmu,
Na yi waƙoƙi da kaina.
[15] Mutum
ne da yake da ilimin addinin Musulunci da kuma na zamani. Ilimin addininsa ya
bayyan a cikin waƙoƙinsa,
musamman aka yi la’akari da jigogin wa’azi da faɗakarwa da makamantansu.
Haka a ɓangaren
ilimin zamani ma ba a bar shi ya ba. Ya yi ilimin zamani daidai gwargwado kamar
yadda ya bayyana a cikin waƙarsa
ta shahara. Wannan dama da ya samu ta ba shi zarafin ƙirƙirar
abubuwa da dama a rayuwarsa. Daga cikin akwai zane a cikin littattafai da
sana’ar ban ruwa da leburanci da kuma mesin (Gusau, 2016:231). Haka kuma, ALA
yana da ilimin zamantakewa, baya ga tafiye-tafiye da ya yi a ciki da
wajen ƙasar nan.
[16] Ga abin da yake cewa a cikin Shahara:
Na zo alkatimin nan,
Ba domin ban iya ba,
[17] Sai dai ba za
a rasa inda ya yi rangaji na shauƙi ba.
Duk da haka, ba ya zagewa ya saki jiki yana rawa.
[18] Wannan makaranta tana nan a bakin offishin
Taskar ALA Global da ke Titin Gidan Zoo a cikin Birnin Kano.
[19] A
Shahara ya fito da wannan inda ya ce:
Muka ɗau hoto a tare,
Da busharar ni da kaina.
Za na yo ramko gare ta,
In ziyarce ta da kaina.
Haka ko a kai umarni,
Bisa yardar Kaliƙina.
Na ziyarci Illela haka,
Ni da yarana da rana.
[20] ALA da kansa ya kawo wannan labari a cikin
alfiyarsa ta Shahara.
[21] Don
tabbatar da wannan iƙirari a saurari tafashen
tauraron mawaƙan zamani a cikin Shahara, inda
yake cewa:
Wani jami’i na aikin,
Radiyo ta Kano garina.
Malam Abdullah Sani,
Sunansa uban gidana.
Ya ishe ni ina a zaune,
Muka gaisa sai ya zauna.
Sai ya ce ALA na waƙa,
Lamuranka azan wurina.
Girman al’amarinka,
Ya gaji da sani na kaina.
Yarana aka yi wa,
Ruƙiyyar
ahlusunna.
Aljani ya fito jikinsu,
Sai ya ɗora faɗin bayana.
Aka ce masa meye dalili,
Na shigar ka jikin ɗiyana?
Sai ya ce kullum ɗiyanka,
Ko marai dare da rana.
Waƙar ALA
gwaninmu,
Suka ji a dare da rana.
Mu ko in har za su kunna,
Da’iman kuma za mu zauna.
Mutum yat tambaye su,
Laifin ALA su tona.
Suka ce masa ba shi laifi,
A gare shi da so da ƙauna.
Sai ya dube ni da shakka,
Rantsuwa yai da gwanina.
[22] A nan ban da waɗanda ba su shiga kasuwa a
Album ba, da kuma waɗanda ba a sake su ba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.