By
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com
| abu-ubaidallah@fugusau.edu.ng
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334
| WhatsApp: +2348133529736
Shimfiɗa
A yau ne ɗaukacin al'ummar Hausawa da suke cikin gida
Nijeriya da Nijar da sauran sassan duniya suke taruwa domin gudanar da bikin Ranar
Hausa Ta Duniya ta shekarar 2026. Rana ce ta musamman da aka ware
domin karrama harshen Hausa, al'ada, tarihi, da kuma adana kimar da kakanninmu
suka bar mana.
Daga fada mai
tarihi ta Masarautar Daura da take Jihar Katsina, har zuwa al'ummomin Hausawa
da suke birnin London, New York, da Dubai, wannan biki yana ci gaba da bunƙasa a matsayin wata babbar dama ta
nuna kishin al'ada da mutuncin Bahaushe.
Mene ce Ranar
Hausa Ta Duniya? An ƙaddamar
da bikin Ranar Hausa Ta Duniya a karon farko ne a ranar 26 ga Agusta,
2015. Wani ma’aikacin jarida ɗan
Nijeriya mai suna Abdulbaki Aliyu Jari, shi ne ya kawo wannan tunani ta
hanyar kafofin sadarwa na zamani, da nufin ƙarfafa
amfani da harshen Hausa a yanar gizo da kuma fahimtar muhimmancin al'adu.
Manufar
Abdulbaki Jari ta kasance mai sauƙi
amma mai zurfin tasiri. Ta mayar da hankali kan ƙarfafa
wa masu jin Hausa guiwar domin amfani da harshensu wajen sadarwar zamani da ƙirƙirar sababbin kalmomin Hausa da
za su dace da fasahar zamani, gami da wallafa hotunan tufafi da abincin
gargajiya da sauran hotuna masu alaƙa
da harshe da adabi da al’adun Hausawa. Wannan fafutuka da ta soma a
kafar sadarwa ta koma wata babba kuma gagurumin bikin al'ada da take kewaye
duniya baki ɗaya.
Yadda Bikin Yake
Bunkasa a Faɗin
Duniya
Duk da cewa Ranar
Hausa Ta Duniya ba ta samu karɓuwa
a hukumance daga Majalisar Dinkin Duniya (UN) ba tukuna, ƙwarjininta da karɓuwarta a tsakanin mutane yana
ci gaba da ƙaruwa. Yanzu haka
ana gudanar da bukukuwa da dama kamar:
a. Bukukuwar
nuna murna da farin ciki
b. Karanta waƙoƙin
hikima
c. Nunawa da
baje kolin ayyukan fasaha da kayan al'ada
d. Tarukan mawaƙa da marubuta
e. Gabatar da maƙalu game da matsayin
harshen Hausawa a yau da matakan buƙasa shi
f. Nuna girke-girke da sauran nau’ukan
Wannan rana tana
tattara sarakuna da malamai da marubuta da masu kishin al'ada waje guda domin
karrama harshen da faɗakarwa
da kuma ƙara wayar da kan al'ummar Hausa. Manufar ita ci ƙara haska musu ƙima da mutuncin harshensu
da al’adunsu.
Hausa:
Harshen Kasuwanci Da Samar Da Haɗin
Kai
Harshen Hausa
yana ɗaya daga cikin
mafi tarin masu amfani da shi a nahiyar Afirka da ma duniya baki ɗaya. Miliyoyin mutane ne suke
magana da shi a ƙasashen
Nijeriya, Nijar, Gana, Kamaru, Chadi, Sudan, da sauran sassa na duniya.
Tasirinsa ya wuce batun ƙabila mai daɗaɗɗen
tarihi kawai, ya kai bunƙasasshe mai matuƙar bunƙasa da yaɗuwa.
Kare Harshen
Hausa a Zamanin Bunƙasar Fasaha
Da Na’urori Da Intanet
A yayin da
duniya take ƙara fuskantar bunƙasar zamani ta fuskokin da suka haɗa da
kwamfuta da intanet, adanawa da bunƙasa
Hausa a kafafen intanet ya zama wajibi. Shafuka irinsu amsoshi.com suna kan
gaba wajen samar da rubuce-rubuce, fassarar kalmomi, da yaɗa labarai masu alaƙa da al'adu da harshe da adabin
Hausa ga duniya baki ɗaya.
Kamar Amsoshi.com
tana ɗaya daga cikin kafafe
ƙalilan a kan intanet da ƙwararrun da suka karanta harshen
Hausa suke tafiyar da su, tare da tabbatar da ingancin saƙwanni da adana tsantsar al'ada.
Shafin yana gudanar da ayyuka kamar fassara, gyaran rubutu, da ba da shawarwari
game da sha'anin al'adu.
Taken Wannan
Shekara: "Al'adunmu, Futurarmu"
Taken bikin na
shekarar 2026 shi ne "Al'adunmu, Futurarmu" (Our Culture, Our
Future). Wannan taken yana jawo hankali ne kan muhimmancin kiyaye harshe da
gado yayin da ake rungumar zamani.
Yana da kyau mu
tuna cewa Hausa ba kawai yare ko harshen magana ce ba, rumbu ne na tarihi,
hikima, fikira, da azancin kakanninmu. Ta hanyar yin magana, rubutu, da koya wa
na baya, muna miƙa wannan
fitila ga na gaba.
Hanyoyin
Kasancewa a Cikin Bikin
Ko da kuna Kano,
Kaduna, Lagos, Landan, Amurka - ko ma ina ne a faɗin
duniya, za ku iya sa hannu wajen gudanar da bikin ta hanyoyin da suka haɗa da:
1. Yaɗa saƙon taya murna cikin harshen Hausa a kafofin sada
zumunta
2. Wallafa
hotunan kayan sawa, abinci, ko fasahar Hausawa
3. Koya wa wani gaisuwa
ko kalmar Hausa ko wani furucin azanci
4. Halartar
taruka kai tsaye ko a kan intanet
5. Bibiya da ƙarfafa guiwa ga shafukan da suke ƙoƙarin
bunƙasa harshen Hausa
Barka Da Ranar
Hausa Ta Duniya 2026!
Muna taya duk
Hausawan ƙwarai masu kishin Hausa a faɗin duniya murnar zagayowar ranar Hausa Ta
Duniya 2026!
Wannan saƙon gaisuwa ne daga dukkan ma'aikata na www.amsoshi.com. Muna nan tsaye tsayin daka wajen ciyar da harshe da al'adu da adabin Hausa gaba a kafafen intanet da ma sauran fannonin yaɗa ilimi da tarihi da al’adu.











0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.