Ana walƙiya can ga hadari,
Guguwa iwa dodon gori,
Ga duhun dare kuma ga ɗari,
Kuma jim kaɗan sai ga maɗari,
Mai ya sa ki kuka waƙata,
Ki yi min bayani na fahimta,
Sai ta ce a yau ba ni da gata,
An dakushe min muryata,
Wa za ya ji ni ka dudduba.
Wa za shi karɓi jawabina,
Da idon basira zan magana,
Zan yo batu yau with manner,
Da za ku gane bayanina,
Koyaushe ba zan koka ba.
Ina ma da mai jin muryata,
Ina ma Aku fa ya maimaita,
Ina ma Kahuhu ya yayata,
Ina ma ku karɓi nasihata,
Sai na ce faɗo ta fa ma karɓa.
In kana biɗar yin ƙasaita,
Kan arziƙi ko kan bauta,
Siyasa da mulki na sarauta,
Fannin sani ko malinta,
Riƙi gaskiya sai kai galaba.
Zo ga madubi nan duba,
Ita gaskiya ita ce a gaba,
Mai bin ta ba zai taɓe ba,
Ita ce da tasiri babba,
Ba mai musu ko tababa.
Ita gaskiya ba ta tsufa,
Saurinta ya fi na gaggafa,
Nagartarta ta fi a lissafa,
Ba a sanin ta cikin harufa,
Gaskiya da ƙarya kwai gaba.
Mu kiyaye harshe fa guba ne,
In za mu furzar mui taune,
Domin muna nan fa a zaune,
Harshen mu zai sa fa mu ƙone,
In mun bari ya yo galaba.
Harshe fa shi linzami ne,
Maganar mu tamkar doki ne,
Zuciyar mu ƙaimi ce aune,
Filin sukwar shi ne kunne,
Dabba mutum hankali maraba.
Mai yaɗa ƙage a labarai,
Ai yai kama da ɗiyan birrai,
Don zuciyarsa da injury,
In kun gane shi ku mai quiry,
Hujjarsa ba zai amsa ba.
Ku ƴan siyasa ga magana,
Ku bar zambo ko gugar zana,
Habaici da zagi ko tsokana,
Tabbas suna jawo fitina,
Su hana ƙasata tac ci gaba.
Ku mu daina ɓatanci ƙazafi,
Ƙauli na zur ko cin zarafi,
Ƙyashi da ƙi-juna yarfi,
Ɗora wa juna ma laifi,
Ba za ya sa kui nasara ba.
Kar mui adawa mai muni,
Domin fa ba ta da amfani,
Mai zai hana mui yo nuni,
Kuskure na juna ba raini,
Domin ƙasar nan tai yi gaba.
Na sanya full stop zan huta,
Na kammala ta a Agusta,
Rana ta sha tara ne ga wata,
Twenty twenty-six nai ta,
Baiti twenty-two duba.
Allah daɗe ni da ilhama,
Da niƙi-niƙin rumbun kalma,
Allah ina daɗa gode ma,
Da ka sa na zamto mai hikima,
Alhamdu na gode Rabba.
USMAN NAGADO (II)
19 ga Agusta, 2026.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.