𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum Mallam Shin ya halatta namiji mai mata biyu ya sadu da su a lokaci guda a daki guda?
SHIN YA HALATTA MIJI
YA SADU DA MATANSA BIYU A LOKACI GUDA A ƊAKI GUDA?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuh.
Mafi yawan malamai
daga mazhabobin Hanafiya yia, Malikiya yia, Shafi'iya yia da Hanbaliya yia sun
baya yiana cewa wannan bai hallata ba, saboda ya saɓa wa kunya (hayaa), mutunci,
da kuma hakkin sirrin aure. Allah Madaukakin Sarki ya ce:
وَعَاشِرُوهُنَّ
بِالْمَعْرُوفِ
"Kuma ku zauna
da su cikin kyakkyawar mu'amala." (Suratun Nisa'i Aya ta 19).
Ma'anar
"mu'amala ta alheri" ta hada da kiyaye mutuncin mace da sirrinta, da
kuma guje wa abin da zai cutar da zuciyarta.
Allah kuma Ya ce:
هُنَّ
لِبَاسٌ لَّكُمْ وَأَنتُمْ لِبَاسٌ لَّهُنَّ
"Su tufafi ne a
gare ku, ku ma tufafi ne a gare su." (Suratul Baƙarah Aya ta 187).
Malamai sun ce wannan
aya tana nuna cewa akwai kariya, sutura, sirri da mutunci tsakanin ma'aurata.
Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) ya ce: "Lallai daga cikin mafi munin mutane a wurin Allah
ranar Alkiyama akwai mutumin da yake saduwa da matarsa sannan ya tona
sirrinta." (Sahih Muslim, Hadisi na 1437).
Idan har baya yiana
abin da ya faru bayan an gama yana da wannan tsananin haramci, to ai yin abin a
gaban wata mace ya fi wannan tsanani.
Haka kuma Annabi
(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: "Kada wani namiji ya kalli al'aurar
wani namiji, kada mace ta kalli al'aurar wata mace." (Sahih Muslim, Hadisi
na 338).
Idan mace ba ta
halatta ta ga al'aurar wata mace ba, to yaya za a ce ta zauna tana kallon
mijinta yana saduwa da kishiyarta?
Saboda haka malamai
suka ce wannan aiki ya saɓa wa koyarwar
Musulunci.
A cikin mazhabar
Malikiya yia an yi bayanin cewa wajibi ne miji ya kiyaye mutuncin kowace mace.
Ba ya halatta ya tara su cikin yana yin da kowacce za ta ga abin da ya shafi
sirrin ɗayar.
Imam Malik da malaman
mazhabar sun yi bayanin cewa irin wannan abu yana cikin abin da ya saɓa da muru'a (mutunci)
da husnul mu'ashara.
Wasu suna cewa idan
kowacce ta lullube jikinta ta yadda ba za ta ga tsiraicin ɗaya ba, to ya halatta
miji ya sadu da su a lokaci guda. Shin wannan magana tana da asali?
Babu wata aya ko
hadisi sahihi da ta halatta wannan aiki. Abin da wasu suka kawo shi ne
maganganun wasu malamai a wasu littattafai, amma ba ra'ayin mafi yawan malamai
ba ne. Koda ba su ga tsiraicin juna ba. kowacce tana jin abin da ke faruwa, tana
ganin motsi,.tana sanin abin da ake yi. Wannan ya saɓa da kunya da
mutuncin aure. Saboda haka mafi yawan malaman fikihu sun hana hakan.
Shaikh Ibn Uthaymeen رحمه
الله
ya ce: "Ba ya halatta mutum ya sadu da matarsa a gaban wani, saboda wannan
yana daga cikin abubuwan da suka fi keta sirrin aure."
Shaikh Ibn Baz رحمه
الله
An tambaye shi irin wannan tambaya, sai ya ce: Wannan aiki bai halatta ba, kuma
ya saɓa wa dabi'ar
Musulunci da kunya. Saboda yana keta sirrin aure. Ya saɓawa kunya (hayaa).
Yana iya haddasa hassada da kiyaya yia tsakanin matan. Yana iya jawo cutar
zuciya da rashin adalci. Babu dalili daga Al-Ƙur'ani ko Sunnah da
ya halatta hakan.
Ra'ayin da ya fi
karfi a wajen malamai shi ne: Ba ya halatta miji ya sadu da mata biyu a lokaci
guda a daki guda. Ba ya halatta ko da an ce sun lullube jikinsu har ba sa ganin
tsiraicin juna, domin babu hujja daga Al-Ƙur'ani ko Sunnah da
ta halatta hakan, kuma ya saɓa wa manufar kiyaye sirrin aure da mutuncin ma'aurata.
Abin da ya dace shi
ne miji ya ware kowace mace a lokacin da yake mu'amalar aure da ita, domin
wannan shi ne ya fi dacewa da koyarwar Musulunci da kuma mu'amala ta alheri.
Allah ne Mafi sani.
Wannan shi ne abin da mafi yawan malaman fikihu daga cikin mazhabobi suka tafi
a kai, ciki har da mazhabar Malikiya yia, wadda ta ba da muhimmanci ga kiyaye
mutunci, kunya, da sirrin zaman aure.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.