Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsoron Tunkarar Mace Da Soyayya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, Mallam Khamis. Ni namiji ne mai tsoron in ma mace magana ina son ta kuma ga shi ina son na yi Aure, yaya zan yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Tsoron tunkarar mace da soyayya abu ne na halitta kuma mafi yawan maza suna fuskantarsa, musamman idan mutum yana da tsananin kunya. Kunya tana da kyau, amma idan ta wuce kima har ta hana ka cimma burinka na rayuwa, to lallai kana bukatar ka canza takun takawa.

Ka sani cewa mata ma mutane ne kamar kowa, kuma suna da tasu kunyar, kuma mafi yawancinsu suna mutunta namiji mai kunya da tsoron Allah. Macen da take da tarbiya yia ba za ta taɓa wulakanta namiji da ya nuna yana son ta da aure ba, koda ba ta ra'ayinsa.

An karɓo hadisi daga Anas dan Malik (Allah Ya ƙara yarda da shi) cewa wani mutum yana tare da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) sai wani mutum ya wuce ta wajen sai ɗayan ya ce: Ya Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ina son wannan mutumin. Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce masa: “Shin ka gaya masa?” sai Ya ce: A’a. Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce: “Faɗa masa.” Don haka ya same shi ya ce: Ina son ka don Allah. Shi kuma Ya ce: wanda ka so ni saboda shi, shi ma ya ƙaunace ka. Abu Dawuud Ya ruwaito shi (no. 5125) da Imamul Nawawi a cikin Riyadh Saliheen (183) kuma Albaani ya ruwaito shi a cikin Saheeh Abi Dawud.

An karbo daga ‘Ali ibn al-Husayn bin’ Ali dan Abi Taalib (Allah Ya yarda da shi) ya ce: Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Idan dayanku ya kasance yana son dan’uwansa Saboda Allah, to ya fada masa, domin yana da kyau kuma yana sanya soyaya yia ta daɗe.”

Sannan Uwar Muminai, Uwar gidan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Nana Khadija ita ce Tace tana son Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam). Sabida Kyawawan Halayensa. Kuma ya Aureta, daga baya Allah ya Sanya Musu Albarka. Wanda bai Taɓa Haihuwa da wata Mata ba, in banda Nana Khadija. Ita ce Uwar Ya'yansa, ita ce wadda ta Taimaka Masa da Kuɗinta da Lokacin ta, tin a Farkon Musulunci.

Sobada haka idan mace ko namiji yana son mace to ya sanar da ita, yana sonta ko ta hanyar kira ta waya ko ta tezt Massage ko ta hanyar social media, kamar WhatsApp ko Facebook da sakon zai kai gare ta, ko ya nuna Mata wata Alama da za ta iya gane hakan.

Anan, za a samu saurayi ko budurwa suna son junansu, amma sai su kasa faɗawa junansu saboda kunya ko tsoron wani abu. A rashin faɗawar kuma, sai ka ga soyayya ta dakushe a hankali, ko kuma su shiga wani yana yi na tunani daban.

Manzon Allah (Sallallahu Alaihin Wasallam) Ya ce hakika idan ɗayan ku ya ga wata mace sai ta kayatar da shi toh ya tafi wajan iyalin sa, hakika yin hakan zai mayar da abin da ya ji a zuciyar sa. Muslim ne ya ruwaito shi (hasanun sahihun).

Kada ka damu idan ba za ka iya yi wa mace magana kai tsaye ba saboda tsoro ko fargaba. A al'adance da kuma a Musulunci, ba lallai sai kai da kanka ka tunkari mace ka baya yiana mata soyaya yia ba. Idan akwai macen da kake so, za ka iya tura magabata ko amfani da dangi ko wani babban abokinka wanda ka yarda da shi, Su yi maka magana. Za su iya tunkarar yarinyar ko iyayenta don baya yiana musu niya yiarka ta gari ta son yin aure.

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce; "Idan wanda kuka yarda da addinsa da dabi'unsa yazo neman aure wajenku ku aura masa. Idan baku yi hakan ba, to ɓarna mai yawa za ta kasance a bayan kasa. Tirmizi ya ruwaito shi.

Ka yawaita yin addu'ar neman zaɓin Allah (Istikhara) da kuma addu'ar neman buɗe baki kamar yadda Annabi Musa (A.S) ya yi:

رَبِّ اشْرَحْ لِي صَدْرِي وَيَسِّرْ لِي أَمْرِي وَاحْلُلْ عُقْدَةً مِّن لِّسَانِي يَفْقَهُوا قَوْلِي

"Ubangijina! Ka buɗe mini ƙirjina. Ka sauƙaƙe mini al'amarina. Ka kwance kulli daga harshena, domin su fahimci maganata."

Wannan ita ce addu'ar da Annabi Musa (A.S) ya yi lokacin da Allah ya umarce shi da ya tafi wajen Fir'auna. Addu'ar tana cikin Suratul Taha, aya ta 25 zuwa 28.

Wannan addu'a neman ƙarfin gwiwa ce, tana sanya natsuwa da cire fargaba a zuciya. Tana sa Allah ya sauƙaƙe maka duk wani abu mai tsanani. Tana taimakawa wajen yin magana mai fita daddala wadda mutane za su fahimta da wuri. Ya dace a karanta ta kafin yin jawabi, jarabawa, ko wata tattaunawa mai muhimmanci.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments