Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Annabawa Kafin Annabi Muhammad (SAW) Suna Yin Sallah?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Aassalamu alaikum mln ftn kn lpy Allah ya ke mln lpy da nisan kwana. Mln tambayata kafin zuwan Annabi S A W Annabawa sun gabache shi toh mln shin lkcn Daman Ansaukar Da sallah ko sai da Annabi S A W yazo Aka saukar masa da sallah Kafin lkc Ana yin sallah koh saida bayyanar Annabi S A W Aka fr yin sallah

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Atakaice ba Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) ne ya fara kawo sallah ba. Annabawa da suka gabace shi ma sun kasance suna yin ibada da sallah bisa umarnin Allah, kodayake yadda ake yin sallarsu da lokutanta ba lallai su kasance daidai da tsarin sallolinmu biyar ba. Misali, Allah Ya ambaci Annabi Ibrahim عليه السلام yana addu’a cewa:

رَبِّ اجْعَلْنِي مُقِيمَ الصَّلَاةِ وَمِن ذُرِّيَّتِي ۖ رَبَّنَا وَتَقَبَّلْ دُعَاءِ

Ya Ubangijina, Ka sanya ni mai tsayar da sallah, da kuma daga zuriyata.Ya Ubangijinmu Kuma ka karɓi addu'ata." (Suratul Ibrahim ayata 40).

Haka kuma Allah Ya ce wa Annabi Musa (عليه السلام):

إِنَّنِي أَنَا اللَّهُ لَا إِلَٰهَ إِلَّا أَنَا فَاعْبُدْنِي وَأَقِمِ الصَّلَاةَ لِذِكْرِي

Lalle ni, Ni ne Allah, babu abin bautawa da gaskiya face Ni, sai ka bauta mini, kuma ka tsai da salla domin tuna Ni (Suratul Taha ayata 14).

Haka Annabi Isma’il عليه السلام da sauran annabawa sun kasance suna umartar iyalansu da sallah.

Sbda haka, sallah ta kasance tun kafin zuwan Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam), ba a fara yin sallah ne sai bayan bayyanarsa ba. Abin da ya kebanta da al’ummar Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) shi ne cewa a daren Mi’iraji Allah Ya wajabta salloli biyar na yini da dare a kan wannan al’umma, bayan da aka fara wajabta su hamsin sannan aka rage su zuwa biyar, amma lada ta kasance kamar hamsin. Don haka, idan aka ce “yaushe aka saukar da sallah?” sai a bambanta: asalin sallah da ibadarta sun kasance tun zamanin annabawa kafin Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam), amma sallolin farilla guda biyar da tsarin da muka sani a yau Asuba, Azahar, La’asar, Magariba da Isha’i an wajabta su ga al’ummar Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) a daren Isra’i da Mi’iraji kafin hijira.

WALLAHU A’ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments