TAMBAYA❓
Aassalamu alaikum barka da dare malam dan Allah malam ko akwai wata addua da zan yi na jarrabawa mun kusa fara exams, Allah ya karawa malam lafiya da rayuwa mai cike da albarka
AMSA:‼️
Wa alaikumus salam
warahmatullahi wabarakatuh.
Yar'uwa Babu wani
addu'a na musamman da aka ambata sunansa addu'ar jarrabawa a Hadisin Manzon
Allah ﷺ, amma akwai
wasu addu'o'i da suka tabbata daga Alkur'ani da Hadisi wadanda suka dace sosai
da wannan hali - wato neman sauki, karfin hankali, da kara ilimi kafin
fuskantar wani abu mai wahala kamar jarrabawa:
Addu'ar neman sauki:
اللَّهُمَّ
لَا سَهْلَ إِلَّا مَا جَعَلْتَهُ سَهْلًا، وَأَنْتَ تَجْعَلُ الْحَزْنَ إِذَا
شِئْتَ سَهْلًا.
Allahumma la sahla
illa ma ja'altahu sahla, wa Anta taj'alul-hazna idha shi'ta sahla" - wato
"Ya Allah, babu wani abu mai sauki sai abinda Ka sanya shi sauki, kuma Kai
ne kake iya sanya wahala ta zama sauki idan Ka so." Wannan addu'a Manzon
Allah ﷺ ya fadeta, kamar
yadda Ibn Hibban ya ruwaito.
Sannan akwai Addu'ar Annabi
Musa (AS) don neman fadakarwa da karfin hankali:
Allah Ta'ala Ya
ambata a cikin Suratu Taha, aya ta 25-28, addu'ar Musa (AS):
رَبِّ
اشْرَحْ لِي صَدْرِي وَيَسِّرْ لِي أَمْرِي وَاحْلُلْ عُقْدَةً مِنْ لِسَانِي
يَفْقَهُوا قَوْلِي.
"Rabbish rahli
sadri, wa yassirli amri, wahlul 'uƙdatan min lisani, yafƙahu ƙawli" - "Ya
Ubangijina, ka fadada min zuciyata, ka sauwake mini al'amarina, ka warware
kulli daga harshena, don su fahimci maganata." Malamai da yawa suna
karantar da wannan addu'a domin neman fahimta da karfin bayyanawa.
Allah Ta'ala Ya
umarci Annabi ﷺ da ya ce a Suratul Taha, aya ta 114:
رَبِّ
زِدْنِي عِلْمًا
"Rabbi zidni 'ilma" - "Ya
Ubangijina, kara mini ilimi." Wannan addu'a ta dace sosai ga dalibi kafin
jarrabawa.
Sannan akwai wata
Addu'ar da Manzon Allah ﷺ ya kasance yana yi wajen tuna abin daya koya:
Akwai riwaya daga Ali
(RA) inda ya koya wa wani mutum wanda ke fama da mantuwa cewa ya ce:
اللَّهُمَّ
ارْحَمْنِي بِتَرْكِ الْمَعَاصِي أَبَدًا، مَا أَبْقَيْتَنِي، وَارْحَمْنِي أَنْ
أَتَكَلَّفَ مَا لَا يَعْنِينِي، وَارْزُقْنِي حُسْنَ النَّظَرِ فِيمَا يُرْضِيكَ
عَنِّي.
Allahumma-rhamni bitarkil-ma'asi abada, ma abƙaytani, war-hamni an
atakallafa ma la ya'nini, wa razuƙni husna an-nazari
fima yurdika 'anni" - amma wannan riwaya (wanda aka fi sani da "Du'a
Hifz al-Ƙur'an") sanadinta yana da rauni sosai a wurin
malaman Hadisi, don haka bai kamata a danganta shi ga Annabi (SAW) da tabbaci
ba.
Shawaran dazan baki shi
ne: Ka rika karanta addu'o'in da suka tabbata a sama - musamman "Rabbi
zidni 'ilma" da addu'ar sauki - a kowace rana kafin jarrabawa, tare da yin
nazari sosai, domin Musulunci ya koyar da hada dogaro ga Allah tare da yin
kokari na zahiri (tawakkul ma'a al-akhdh bil-asbab). Allah Ya sauwaka maku, Ya
kuma bada nasara ga dukkan daliban da zasu yi jarrabawa.
Wallahu ta'ala aalam
✍️MT
ABDULLAHI
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.