Ticker

6/recent/ticker-posts

Mai Son Abin Ka Ya Fi Ka Dabara: Kore a Sana’ar Sata

Citation: Lawali, B. (2026). “Mai Son Abin Ka ya fi Ka Dabara: Kore a Sana’ar Sata” In Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies, Vol. 04, No. 01, Pp. 93 – 98. www.doi.org/10.36349/djhs.2026.v04v01.012.

MAI SON ABIN KA YA FI KA DABARA: KORE A SANA’AR SATA

Na

Buhari Lawali

Sashen Hausa, Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, Sakkwato 

Tsakure:

Wannan maƙala ta mayar da hankali ne a kan nazarin kore a sana’ar sata. Ɓarayi suna amfani da wasu dabaru su daburta hankalin mai wayo, su yi masa sata mai ban mamaki. Suna kuma yi wa kansu ɓulo, su kuɓuta idan rana ta so ta ɓatar musu. Wannan tunani ya jawo hankalin mai bincike ya gabatar da wannan maƙala. Binciken yana da manufar fito da yadda ɓarayi suke amfani da dabarar kore a wajen sata. A fito da shi ga fili jama’a su fahimce shi. Idan ɓarawo ya zo da wannan dabara, a tunatar da shi karin maganar Hausawa sa suke cewa: “Kifi yana ganinka mai jar koma.” A ƙoƙarin gabatar da wannan bincike, an yi amfani da wasu hanyoyi da suka ƙunshi tattaunawa da wasu mutane. An nazarci ayyukan masana da manazarta masu alaƙa da wannan bincike. An kuma yi amfani da hanyar ɗora aiki ta karin maganar Hausawa da suke cewa: “Mai son abin ka ya fi ka dabara.” Wannan karin magana tana nuna duk dabarun da mai kaya ya yi amfani da su domin ya kare dukiyarsa ko wata kadara tasa, ɓarawo yana da tasa dabarar da ta wuce ta mai kaya. Sakamakon binciken ya gano ɓarayi ba ƙarfi kawai suke amfani da shi ba, suna amfani da dabarar kore su dabirta hankalin mai wayo su yi masa sata.

1.0 Gabatarwa

Sata sana’a ce da Hausawa suke ƙyama. kamar yadda Maiyama (2013:223) yake cewa: “A al’adar Bahaushe sata wata abu ce wadda babu mai ƙaunarta, balle ƙaunar mai yin ta. Ɓarawo ba ya da wata ƙima a idon Bahaushe.” Duk da wannan ƙyama da Bahaushe yake yi wa sata, ya yarda sata sana’a ce da ta ƙumshi ƙarfin tuwo da dabara da wayo da kaifin basira. Bunza (2014:212) ya tabbatar da cewa: “A al’adar Bahaushe, sata aiki ne da ya haɗa da ƙarfi da dabara da wayo da ƙwarewa domin a mallaki wata dukiya ko wani abu mallakar wani ba da saninsa ko yardarsa ba. Idan aka yi amfani da ƙarfi ido na ganin ido aka rinjayi mai abu aka karɓe ana ce da shi “ƙwace”. Mai irin wannan dabarar sunansa “Ɗan ƙwace” Idan aka sa makami tare da ƙarfin tuwo aka tare hanya a daji aka karɓi dukiyar masu dukiya sunansa “Fashi da makami”. Idan dabara aka yi amfani da ita aka yaga aljihu ko aka cire kuɗin da ke ciki sunansa “sane”. Idan da ƙarfin wayo aka nuna wa mutum sannan aka karɓe na hannunsa ya yi biyu babu, sunan abin “Damfara”. Wannan ne ya sa wani lokaci satar ba ta yi wa sai an haɗa da kore. Bunza (2014:243) ya ce: “Ba ɓarawo zai yi kore ba. Abin da ake nufi da kore shi ne, taimaka wa ɓarawo yayin da yake son ya yi sata, ko yayin da yake sata, ko bayan ya yi sata yana son ya tsere.”

2.0 Bitar Muhimman Batutuwa

Fayyace ma’anonin kalmomin da suka gina wannan batu yana da matuƙar muhimmanci. Kore a sana’ar sata shi ne batun bincike. A wannan gaɓa, sanin ma’anar kore da sana’a da sata, tamkar jagora suke wajen sanin inda maƙalar ta dosa.

2.1 Kore da Ɗan Kore

Kore hanya ce ta dabara da wayo a ɓatar da hankalin mai wayo domin a samu sauƙin cim ma biyan wata buƙata. A fahimtar Bunza (1999:2-3) ya ce: “Kore shi ne dabarun taimaka wa mai siddabaru ko boka ko malami ko makaɗi ko duk wanda ya bayyana a bainar jama’a cikin wayo domin tabbatar da abin da yake da’awa”.

Ɗan kore kuma kamar yadda Bunza (1990: 274) ya bayyana shi ne: “Wani mutum babba ko yaro, mace ko namiji, ɗan gida ko baƙo wanda zai dinga taimaka wa ɗan siddabaru”.

2.2 Sana’a

Masana da manazarta sun tofa albarkacin bakinsu dangane da ma’anar sana’a. Yakas ai (2020:118) yana da fahimtar cewa: “Sana’a hanya ce ta neman ɗan abin dogaro da kai.” Shi kuma (2023:15) ya ce: “Sana’a ita ce amfani da duk wata baiwa da ɗan’Adam yake da ita, ta gaɓoɓin jiki da kaifin basira da azanci domin samar wa kai abin dogaro don biyan buƙatunsa na rayuwa.

2.3 Sata

 Sata ita ce mallakar abin da ba na ka ba, ba tare da sani ko amincewar mai abu ba. Maiyama (2001:12) ya nuna sata da cewa: Sata hanya ce da wani ko wasu ke bi, wajen mallakar abin da ke mallakar wani ko wasu ba tare da sanin mamallakin ba. Wannan abu na iya zama mai rai ko maras rai.”

3.0 Kore a Sana’ar Sata

 Sata suna ta tara. Kowane ɓarawo da satar da ya fi ƙwarewa. Daga cikin ɓarayi akwai masu shiga ɗaki, akwai masu fashi da makami, akwai masu ƙwace, akwai kuma ‘yansane (masu riƙa reza). Duk waɗannan ɓarayi suna amfani da kore idan za su yi sata, domin su ɓatar da hankalin mai wayo, kuma su nema wa kansu mafita idan rana tana shirin ɓatar musu.

3.1 Masu Shiga Gida ko Ɗaki

Wannan sata wasu rukunin ɓarayi ne suke aiwatar da ita. Idan aka yi sata aka zo wurin ƙuncin ɓarayi, abu na farko da zai tambaya shi ne, wace irin sata ce, waɗanne kaya ne aka ɗauka? Da an ce cikin gida aka ƙetaro aka ɗauka, zai ce su wane ne. Yanzu za a kira su kawo kayan, kai kuma sai ka ba da na goro. Irin wannan sata tana buƙatar ɗankore, saboda zamani ya sa ana amfani da gambu mai ƙwari, da katanga mai tsawo a gida. Wannan yana yi wa ɓarayi wahalar ƙetara gida su yi sata.

Canzawar kiɗin da zamani ya yi, ya sa su ma ɓarayin suka canza rawa. Tun da marece suke samun wani ƙaramin yaro da yake da ƙwarewa da wayo da sanin abin da ya zo yi, ya shiga cikin gida ya ɓoye a wani wuri da ke da wuyar a gane shi. Idan dare ya yi ya buɗe wa ɓarayi gida domin su shigo su yi sata. Idan safiya ta waye aka ga an yi sata, sai a kama mamakin ta ina ɓarawo ya shigo, ba a san cewa da ɗan koren ɓarayin aka rufe gida ba.

Wani nau’in kore a cikin irin wannan sata shi ne, idan unguwa ta kasance ba ta da yawan jama’a ɓarayi sukan zo da rana ido-na-ganin-ido su yi sata. Ita ma wannan sata tana amfani da ɗankore. Lokacin da ɓarawo ya shiga cikin gida domin ya yi sata, ɗan korensa zai tsaya waje yana duba masa abin da zai je ya komo. Idan ɗan koren ya hangi mutane suna zuwa, zai yi masu sallama da ƙarfi, ko kuma ya tambaye su wurin da ake sayar da wani abu daga nesa. Da ɓarawon ya ji haka ya san akwai mutane kusa da inda yake yin sata. Duk wannan dabara ce ta sanar da ɓarawo halin da ake ciki.[1]

Wani lokaci kuma, idan ɗan koren ya ga alamar rana za ta ɓace, mutane sun fahimci akwai ɓarawo a cikin gida, kafin jama’a su taru ɗan kore zai zo ya ce mi yake faruwa? Da an ce masa ɓarawo ne, zai yi farat ya keta kuwwa. Jama’a ɓarawo, wai don ya tsere. Idan ranar ta ɓaci har aka biyo ɓarawon, ɗan koren shi ma zai shigo cikin tawagar masu biyar sa tare da nuna bai san ɓarawon ba. Ɗuk wanda ya kusan cim ma ɓarawon ɗan koren zai sa ƙullin hannunsa ko wani makami ya buge shi domin ya tsere. Jama’a su ɗauka cewa wannan da ɗan kore ya buge shi ne ɓarawon, a bi shi da bugu sai daga baya a gano ba shi ne ɓarawon ba.”[2]

3.2 Fashi da Makami

Wannan wata sata ce da ake amfani da makami domin a ƙwace dukiyar mutum. Galibi masu wannan sata sun fi tare hanya. Daga cikin dabarun da suke amfani da su, su tare mutane, akwai amfani da kore. Ɗan kore zai zo bakin hanya ya tsaya kamar yana neman taimako. Da zarar an tsaya a taimaka masa, sai ɓarayi su fito da makamai su karɓe dukiyar mutum. Wani lokaci yakan shiga kasuwa ya ga waɗanda suke da kuɗi. Idan sun gama cin kasuwa ya shiga mota guda tare da su. Kafin ya shiga motar ya kira ɓarayi ta waya ya sanar da su cewa, yana cikin mota mai kala kaza da lamba kaza. Idan aka zo daidai wurin da ɓarayin suke sai ya ce a aje shi, ko kuma ya faɗi wata lalura. Ana tsayawa sai ɓarayi su fito, shi kuma ya ranta cikin na kare. Wani lokaci ‘yan fashi za su tare motar a game har da ɗan koren a yi masu fashi. Wai don a ɓatar da hankalin mai wayo.”[3]

Wata dabara da masu fashin da makami suke amfani da ita, ita ce, amfani da ƙananan yara a matsayin ‘yan kore. Za su baza ƙananan yara a gonakin da suke kusa da hanya, ko titin da za su yi fashi. Ganin waɗannan yaran suna aikin roron wake ko aikin gona, ba za a yi zaton akwai ‘yan fashi a wurin ba. Duk motar da ta zo a tarbe a yi wa mutanen cikinta fashi. Yaran kuma ba za su fasa yin aikinsu na roron wake ba. Waɗannan yara ‘yan koren ɓarayi ne.”[4]

3.3 ‘Yansane (masu riƙa reza)

A tunanin mai bincike, masu wannan satar ne suka bunƙasa suke satar waya a aljihu, ko a sa hannu a zare kuɗi maimakon a yi amfani da reza. Ba ana nufin an daina amfani da reza ba ne, sai dai zamani ya ƙara haifar masu da wata hanya ta yadda wasunsu za su hutar da reza a lokacin sana’arsu ta sane. Irin wannan sata da ɗan kore ta fi sauƙi.

Yadda kore yake kasancewa a cikin wannan sata shi ne, idan ɓarawo ya zo kasuwa da niyar yin aikinsa, zai tsaya ya natsu ya ga waye yake ɗauke da kuɗi. Idan ya samu wanda yake ɗauke da kuɗi sai ya bi shi tare da ɗan korensa. Ɗan koren zai turi mai kuɗin, sannan ya ce da kaza uba ba ka gani ka ture ni? Idan mai kuɗin ya tanka masa sai ya kai masa duka. A nan ɓarawon zai zo da niyar raba faɗa, kuma a nan zai yi halinsa, ya tsame kuɗin ya wuce.[5]

Wani nau’in kore da masu sane suke yi shi ne, shagaltuwa da ciniki na banza da wofi ga wanda za a yi wa sata idan an taɓa aljihunsa ya so ya gane. Daga cikin mutanen Gambo mai waƙar ɓarayi akwai waɗanda suka shahara da amfani ga wannan kore ya yi musu garkuwa idan rana tana shirin ɓatar musu. Waɗanda suka fi shahara da wannan kore su ne Ɗanzabarma da Mai’arakke na Makirin. Bunza (2014:247) ya bayyana cewa: “Ɗanzabarma a koyaushe ya je kasuwa yin sane yana riƙe da littafi da biro, ɗaya a hannu, ɗaya a ka, ya soka cikin gashin kai, wai shi ɗan boko, malamin kasuwa. Idan ba kaifin hankali mutum ya cika ba, da wuya ya gano wannan dabarar. A nan, ɓarawon ya shagaltu da wani aiki, da ya ga an fahimce shi. Haka Mai’arakke na Makirin ke Shirin cuta kamar yadda Gambo ya tofa:

Jagora: Ban taɓa kwana Makirin ba,

:Sai zuwanmu gidan Mai’arakke wasa,

:Mai’arakke ɗan ƙaramin yaro matashi,

:Mai kama da ɗan makaranta mai aji uku,

:Kana aza komi bai sani ba.

Abu ne mawuyaci a wannan zamani da muke ciki a ga ɗan makaranta da kayan makaranta da bokiti dole a yi zaton makaranta zai je ko aikinsa aka yi. Idan ya taɓa aljihu ya ga an gane sai ya karkace kai da ɗan bokitinsa da cefane ciki yana cewa, “Baba ka da ka zubar mini da cefanenmu.” Wa zai kula da ganin yaro da cefane a bokiti ya yi naɗa (ɗana) ya yi zaton ƙwaro ne? Nan kuwa, in ji Gambo, yana riƙe da rezarsa a hannu ta cuta. Da Mai’arakke da Ɗanzabarma duk da ilmi suka yi kore da shi a matsayin garkuwa da mutum zai gani ya daina yi musu mugun zato.”

Dan sane ya san kashinsa zai bushe idan rana ta ɓatar masa, kasancewar cikin taro ya fi gudanar da harƙallarsa. Yakan nemi jami’an hukuma su yi masa kore ya yi sata, ko su ba shi kariya domin ya tsira da rayuwarsa. Idan ɗan sane ya kwararo mai dukiya ruɓaɓɓun ‘yan sandar da ya haɗa baki da su za su biyo shi. Idan mai dukiya ya waigo ya ga hukuma zai saki jiki, shi kuwa ɓarawo ya ci karensa babu babbaka. Wa zai yi zaton a haɗa baki da hukuma a yi sata? Idan kuma ɗan sane ya taɓa aljihu aka gane, aka bi shi da duka, ‘yan korensa daga cikin ‘yan sanda za su yi sauri su kai masa ɗauki kar mutane su halaka shi.[6]

3.4 Ƙwace

Ƙwace sata ce mai haɗari domin ita gaba da gaba ɓarawo zai yi da mai abu ya ƙwace ya ruga a guje, ido na ganin ido. Irin wannan sata tana buƙatar ɗan kore. Aikin ɗan kore a wannan sata shi ne ya taimaka wa ɓarawo ya tsere yayin da ya yi sata. Wata mata da wannan bincike ya tattauna da ita ta bayyana cewa: “Wata rana tana tafiya sai wani ya ƙwace mata waya, ta yi kuwwa ta ce jama’a ɓarawo. Tana rufe baki sai wani ya sharara mata mari wai ta ce masa ɓarawo, alhali ba da shi take ba. Haka suka ta rigima har ɓarawon ya tsere ba tare da an kama shi ba, sai daga baya aka fahimci ɗan kore ne, tare da ɓarawon yake.”[7]

Masu ƙwacen mashin su ma suna amfani da ɗankore. Yadda suke yi shi ne, wani zai tarbi ɗan kabu-kabu ya ce a kai shi waje kaza. Da sun isa wurin da ɓarayi suke sai ya ce a aje shi. Wani lokaci yakan ce sai an zo zai karɓi kuɗi ya biya, kafin ya biya kuɗin sai ɓarayi su fito a inda suke ɓoye su ƙwace mashin su tsere”. Wani lokaci kuma ɗan kabu-kabun ne zai yi wa ɓarayi kore idan ya ɗauko wanda yake zaton akwai manyan kuɗi tare da shi. Kafin ya isa wurin da za a ƙwace dukiyar mutum zai yi ƙoƙari ya kashe man mashin yadda zai mutu da zarar an zo wurin. Da isar su ɓarayi za su fito su ƙwace musu kuɗi tare da ɗan kabu-kabun, wai don kar a ɗauka ɗan korensu ne.[8]

3.5 Sata ta Musamman

A wannan sata, ɓarayi suna amfani da kaifin basira tare da taimakon ɗan kore su daburta tunanin mai abu, su sace dukiyarsa a bar shi da mamaki. Wasu ɓarayin sukan yi shigar malamai da rawani a aminta da su, sai su yi kore da wannan shiga tasu su yi sata. Ɓarayin motoci da babura su ma suna irin wannan sata ta ban mamaki. Sukan yi shigar masu kuɗi, su saka sutura mai tsada tare da ‘yan korensu su rinƙa girmama ɗaya daga cikinsu a matsayin shi ne mai gidansu. Wau kuma su nemo ɗan sanda su yi dodon-gona da shi, daga ƙarshe a sace mota a bar dan sanda da masu dukiya suna sallallami. Masu sata babur su ma suna irin wannan sata ta ban mamaki.[9]

4.1 Sakamakon Bincike

Daga cikin sakamakon da wannan maƙala ta gano, sun haɗa da:

1. Ƙara samun tabbacin ɓarayi suna amfani da ‘yan kore a lokacin da suke aiwatar da sana’arsu ta sata.

2. Ɓarayi suna amfani da basirarsu da dabara da wayo su yi sata, ba sai sun yi amfani da ƙarfin tuwo ba.

3. Satar da aka yi amfani da kore ta fi ciwo, domin sai an yi wasa da hankalin mai abu kafin a sace dukiyarsa.

4. Sakamakon maƙalar ya tabbatar da ba ɓarayin ne suke yin kore ba, aikin ɗan kore shi ne ɗauke hankalin mai dukiya a lokacin da ɓarawo yake son ya yi sata ko yake yin sata ko bayan ya yi sata domin ya tsere.

5. Maƙalar ta gano akwai bambanci tsakanin ɗan kore da imfoma.

5.1 Shawarwari

Masu hikimar magana suna cewa: “Shawara ɗaukar ɗaki.” Wannan maƙala tana da wasu shawarwari da za su taimaka a kauce faɗa wa tarkon ɗan kore a sana’ar sata. Ga su kamar haka:

1. Kafin a rufe gida a tabbatar an duba kowane lungu da saƙo na gidan, don kar a rufe gida da ɗan koren ɓarayi.

2. Kar a saki jiki da duk wata baƙuwar fuskar da ba a gamsu da ita ba a cikin unguwa.

3. A yi taka-tsantsan wajen yin jinƙai a hanya. Sau da yawa jinƙai yake komawa jiƙƙice.

4. Idan aka shigo kasuwa a kula da aljihu, kar a biye wa duk wanda ya ja mai dukiya faɗa don kauce wa tarkon ɗan kore.

5. A yi hattara da mutane, ba kowane mutum ake aminta da shi ba wai don an gan shi da sifar mutanen kirki. Masu hikimar magana suna cewa: “Kama da wane ba ta wane.”

6.1 Kammalawa

Sata sana’a ce mai haɗari da tafi karfin matsoraci ko wawa. Koda yake al’ada tana kallon ɓarayi a matsayin masu mutuwar zuciya, ba jarumai ba. Jarumai shi ne wanda ya fito neman na kansa, ba neman na wanda ya nemo ba. Duk kaifin basira da dabara da wayo da ɓarawo yake da su, ba abin yabo ba ne. Kasancewar ɗan kore b ashi yake yin sata ba, bai hana al’umma su yi masa kallon ɓarawo ba. Hausawa suna cewa: “Abokin ɓarawo, shi ma ɓarawo ne.” Wannan maƙala ta fito da yadda ɓarayi suke amfani da ‘yan kore su ɓatar da hankalin mai wayo a yi masa sata. Idan an samu ɓacin rana kuma a yi musu kore su tsere. Hausawa suna cewa: “In an bi ta ɓarawo, a bi ta mai biyar sawu.”

Manazarta

Bunza, A. M. (1990). “Hayaƙi Fid da Na Kogo: Nazarin Siddabarun Hausawa.” Kano: Kundin Digiri na Biyu. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Bunza, A. M. (2014). In Ba Ka San Gari Ba Saurari Daka: Muryar Nazari Cikin Tafashen Gambo. Cairo: Elkods Printing House.

Garba, C. Y. (1991). Sana’o’in Gargajiya a Ƙasar Hausa. Ibadan: Baraka Press and Publishers

Lawali. B. (2023). “Gurbin Kore a Sana’o’in Bahaushe.” Sakkwato: Kundin Digiri na Biyu. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Lawali, B. da Aminu, N. (2024). “Jirwaye Mai Kama da Wanka: Ɓirɓishin Kore a cikin Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru na Sarkin Kudun Skkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo”. In: Bakura, A. R., Gummi, M. F., Sani, A. U., Bashir, A., Umar, M. A. (Eds). Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceeding from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Faru. In Honor of 19th Sultan of Sokoto, Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar na Uku. Department of Languages and Culture Federal University, Gusau, Zamfara State.

Maiyama, U. H. (2001) “Jigon Sata Cikin Wasu Rubutattun Ƙagaggun Labaran Hausa.” Sakkwato: Kundin Digiri na Biyu. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Maiyama, U. H. (2013). “Sata a Idon Bahaushe: Ma’auninta da Ƙimarti a Bakin Malaminta Muhammadu Gambo.” Makaɗi a Mahangar Manazarta: Jerin Takardun da aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sani Kan Tubar Muhammadu Gambo Mai Kalangu, a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo. Kano:Gidan Dabino Publishers.

Muhammad, M. S. (2019). Sana’a Sa’a: Nazari a kan Sana’o’in Hausawa. Kaduna: Gado da Masu Communications.

Yakasai, A. S. (2020). Jagoran Ilimin Walwalar Harshe. Kaduna: Amal Printing Press..


[1] Ɗan kore ba imfoma ba ne. aikin imfoma ya kawo bayani, amma ba da shi ake yin sata ba. Ɗan kore da shi ake zuwa sata. Aikinsa shi ne ya sa ido, ya ɗauke hankalin mutane, sannan ya yi wa ɓarawo ishara idan ya hangi matsala.

[2] Tattaunawa da Malam Sa’adu Mai Bulala Bakin-Kusu. Kwamanda a Hukumar Banga reshen Wamakko, Sakkwato. A ranar Attanin 02/01/2026. A gidansa da yake Bakin-kusu.

[3] Tattaunawa da Malam Umar Altine. Jami’in Tsaro, a ranar Attanin 02/01/2026, a sakatariyar Usman Faruk, Sakkwato.

[4] Tattaunawa da Farfesa Bashir Aliyu Sallau a ranar Attanin 21 ga watan Nuwanba 2023, a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

[5] Tattaunawa da Yahuza Zubairu Muhammad, 04/11/2025, a gidansa da yake Guiwa bayan katangar kwalejin ilimi ta Sahehu Shagari, Sakkwato.

[6] An ce, wata rana wani ɓarawo ɗan sane ya yanke wa wani mutum aljihu ya cire kuɗin da ke ciki. Da maaikacin da ke tare da shi ya zo, ya ce a ba shi rabonsa. Aka ɗiba aka ba shi, ya ce bai yarda ba sun yi kaɗan a ƙara. Da ɓarawo ya ƙara, ya ce, sai ya ƙara. |arawo a ƙarshe dai sabbene ya tashi ya tashi da kashi uku na kuɗin ya bar ɓarawo da kashi ɗaya da nauyin sata. Rayuwar ɓarawon ta ɓaci ƙwarai, sai ya kira mai kuɗi ya ba shi ragowar kuɗin ya ce, je gun mutumen can ya nuna maaikacin da aka yi kasha-mu-raba da shi, ka ba shi kuɗin nan, ka gaya masa cewa, An fasa sata. Da aka kai wa mai kuɗi kuɗinsa ya lalubo aljihu ya ji babban rame, ya je wajen sabbene ya ce masa, ga wani mutum can ya ce a gaya maka, an fasa sata. Ɗan kore ya rasa abin da zai yi, dole ya ba da kuɗin ga mai abu (Bunza 2014: 2444).

[7] Tattaunawa da malama Balkisu Bello, 17/10/2025, a gidan aurenta da yake shiyar Arkilla, Sakkwato.

[8] Tattaunawa da Malam Sa’idu Rabi’u, 15/10/2025. A ofishin ƙungiyar abokai maabuta sauraren tashar Rima FM (RILFAS), Sakkwato.

[9] An ce wata rana soja ya je banki da mashin, sai ya sa kwaɗo ya kulle tayar gaba. Da shigarsa banki sai ɓarawo ya zo ya kulle tayar baya. Soja yana dawowa ya buɗe kwaɗon da ya kulle tayar gaba ya ja mashin, sai mashin ya ƙi tafiya. Da ya duba sai ya ga an kulle tayar baya. Sai wani yaro ya ce yanzu wani ya sa wannan kwaɗon ya shiga banki yana saye da tufafi masu kalar ja. Cikin fushi, Soja ya juya ya nufi banki domin ya ga wanda ya kulle masa mashin. Yana shiga ɓarawo ya kwance tayar baya suka tsere tare da yaro. Ko da soja ya dawo ba mashin ba yaro sun tsere. Wannan yaro shi ne ɗan kore.

 Dundaye

Post a Comment

0 Comments