𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Limamin masallacin da yake zuwa sallah baya natsuwa a cikin sallar, shi kuma gidansa yana da nisa daga masallacin, kuma yana fama da matsalar ƙafa. To wai ko waɗannan matsalolin sun isa hujja a kan ya riƙa yin sallah a gida?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam
Wa Ramatul Laah:
A gaskiya saboda
Allaah! Ba su isa ba, saboda dalilai kamar haka:
1. Sallah a cikin
jama’a wajiba ce a kan kowane musulmi namiji baligi mai lafiya, wanda kuma ya
ji kiran sallar. Wannan ita ce mazhabar Hanaabilah kuma ita ce daidai, in
shaa’al Laah. Saɓanin Hanafiya yiah da
Maalikiya yiah da suke ganin ita Sunnah ce mu’akkadah kawai, ko kuma Shaafi’iya
yiah da suke ganin ita farali ce ta kifaayah kaɗai, ko kuma Zaahiriya yiah da suka zaƙe har suka ɗauke ta a matsayin
sharaɗi ga ingancin sallar!
2. Sallar Tsoro da Allaah
ya wajabta wa musulmin da suka fita jihadi domin kare addini cewa su yi ta a
cikin jama’a, duk kuwa da tsananin da suke ciki. (Surah An-Nisaa’: 102).
وَاِذَا
كُنۡتَ فِيۡهِمۡ فَاَقَمۡتَ لَهُمُ الصَّلٰوةَ فَلۡتَقُمۡ طَآٮِٕفَةٌ مِّنۡهُمۡ
مَّعَكَ وَلۡيَاۡخُذُوۡۤا اَسۡلِحَتَهُمۡ فَاِذَا
سَجَدُوۡا فَلۡيَكُوۡنُوۡا مِنۡ وَّرَآٮِٕكُمۡ وَلۡتَاۡتِ
طَآٮِٕفَةٌ اُخۡرٰى لَمۡ يُصَلُّوۡا فَلۡيُصَلُّوۡا مَعَكَ وَلۡيَاۡخُذُوۡا
حِذۡرَهُمۡ وَاَسۡلِحَتَهُمۡ ۚ وَدَّ الَّذِيۡنَ كَفَرُوۡا لَوۡ تَغۡفُلُوۡنَ عَنۡ
اَسۡلِحَتِكُمۡ وَاَمۡتِعَتِكُمۡ فَيَمِيۡلُوۡنَ عَلَيۡكُمۡ مَّيۡلَةً وَّاحِدَةً
ؕ وَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ اِنۡ كَانَ بِكُمۡ اَ ذًى مِّنۡ مَّطَرٍ اَوۡ
كُنۡـتُمۡ مَّرۡضٰۤى اَنۡ تَضَعُوۡۤا اَسۡلِحَتَكُمۡ ۚ وَ خُذُوۡا حِذۡرَكُمۡ ؕ
اِنَّ اللّٰهَ اَعَدَّ لِلۡكٰفِرِيۡنَ عَذَابًا مُّهِيۡنًا
Kuma idan ka kasance
a cikinsu, sai ka tsayar musu da salla, to, wata ƙungiya daga gare su
ta tsaya tare da kai, kuma sai su riƙe makamansu.
Sa'an nan idan sun yi salla, to, sai su kasance daga bayanku.
Kuma wata ƙungiya ta dabam (ta) waɗanda ba su yi sallar ba, ta zo, sa'an
nan su yi sallar tare da kai. Kuma su riƙi shirinsu da makamansu.
Waɗanda suka kafirta sun
yi gũrin da dai kuna shagala daga makamanku da kayanku domin su karkata a kanku,
karkata guda. Kuma babu laifi, a kanku idan wata cũta daga ruwan sama ta
kasance a gare ku, ko kuwa kun kasance masu jinya ga ku ajiye makamanku kuma
dai ku riƙi shirinku. Lalle ne, Allah Ya
yi tattali, ga kafirai, azaba mai walakantarwa.
(Surah: An-Nisaa, Ayat: 102).
Wannan shi ne babban
dalili a kan wajibcin jam’in a kan duk wanda yake zaune a cikin gari lafiya
lau. Sannan idan da sallar jam’in Sunnah ce kawai da bai farlanta wa mujahidai
da suke cikin halin firgici da rashin natsuwa ba. Kuma in da farilla ta kifaya
ce kaɗai da bai wajabta ta
a kan jama’a ta biyu a cikin sallar tsoron ba.
3. Hadisin makahon da
ya nemi Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya sama masa sassaucin
yin sallah a gida. (Sahih Muslim: 653). Idan dai har makaho mara ɗan-jagora zai rasa
samun sassaucin yin sallah a gida daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam), to ina kuma ga mai matsala a ƙafa kawai a irin waɗannan za munnan na ƙarshen zamani?!
4. Babu ranar da
Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya taɓa zama bai yi sallah
a cikin jama’a ba, har a lokacin rashin lafiyarsa na ajali! (Sahih
Al-Bukhaariy: 687). Shiyasa manyan malamai daga cikin Sahabbai irinsu Ibn
Mas’ud (Radiyal Laahu Anhu) yake cewa:
مَنْ
سَرَّهُ أَنْ يَلْقَى اللَّهَ غَدًا مُسْلِمًا فَلْيُحَافِظْ عَلَى هَؤُلاَءِ
الصَّلَوَاتِ حَيْثُ يُنَادَى بِهِنَّ فَإِنَّ اللَّهَ شَرَعَ لِنَبِيِّكُمْ -صلى
الله عليه وسلم- سُنَنَ الْهُدَى وَإِنَّهُنَّ مِنْ سُنَنِ الْهُدَى وَلَوْ
أَنَّكُمْ صَلَّيْتُمْ فِى بُيُوتِكُمْ كَمَا يُصَلِّى هَذَا الْمُتَخَلِّفُ فِى
بَيْتِهِ لَتَرَكْتُمْ سُنَّةَ نَبِيِّكُمْ وَلَوْ تَرَكْتُمْ سُنَّةَ نَبِيِّكُمْ
لَضَلَلْتُمْ وَمَا مِنْ رَجُلٍ يَتَطَهَّرُ فَيُحْسِنُ الطُّهُورَ ثُمَّ يَعْمِدُ
إِلَى مَسْجِدٍ مِنْ هَذِهِ الْمَسَاجِدِ إِلاَّ كَتَبَ اللَّهُ لَهُ بِكُلِّ
خَطْوَةٍ يَخْطُوهَا حَسَنَةً وَيَرْفَعُهُ بِهَا دَرَجَةً وَيَحُطُّ عَنْهُ بِهَا
سَيِّئَةً وَلَقَدْ رَأَيْتُنَا وَمَا يَتَخَلَّفُ عَنْهَا إِلاَّ مُنَافِقٌ
مَعْلُومُ النِّفَاقِ وَلَقَدْ كَانَ الرَّجُلُ يُؤْتَى بِهِ يُهَادَى بَيْنَ
الرَّجُلَيْنِ حَتَّى يُقَامَ فِى الصَّفِّ.
Duk wanda yake
sha’awar ya haɗu da Allaah gobe a
halin yana musulmi, to ya kiyaye a kan waɗannan sallolin a duk inda aka yi kiran
sallarsu. Domin Allaah Ta’aala ya shar’anta wa Annabinku (Sallal Laahu Alaihi
Wa Alihi Wa Sallam) Sunnonin Shiriya, kuma su ɗin suna daga cikin Sunnonin Shiriya.
To idan da kun tsaya yin sallah a cikin gidajenku kamar yadda wannan da yake ƙin zuwa jam’in
yake yin sallar a cikin gidansa, to da kuwa kun bar Sunnar Annabinku. Idan kuma
da kun bar Sunnar Annabinku, to da kuwa kun ɓace. Babu wanda zai yi tsarki, kuma ya
kyautata tsarkin sannan ya taka da nufin zuwa ɗaya daga cikin waɗannan masallatan, face
Allaah ya rubuta masa lada da kowace takawa da yake yi, ya ɗaga masa daraja da
ita, kuma ya kankare masasa laifi da ita. Haƙiƙa! Na gan mu (a
zamanin Sahabbai), babu mai ƙin zuwa sallar jam’i
sai dai munafukin da kowa ya san munafuncinsa. Kuma haƙiƙa! Ya kasance ana
rungumo mutum (mara lafiya) a tsakanin mazaje biyu, har sai an tsayar da shi a
cikin sahu. (Sahih Muslim: 654).
A cikin riwaya
sahihiya da ke cikin Sunan Abi-Daawud: 550, ya ce:
وَلَوْ
تَرَكْتُمْ سُنَّةَ نَبِيِّكُمْ -صلى الله عليه وسلم- لَكَفَرْتُمْ
Idan kuma da kun bar
Sunnar Annabinku (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) to da kuwa kun
kafirce! Wannan kuwa shi ya fi tsananin wurin razanarwa.
5. Rashin natsuwar
liman shi ta shafa, saboda hadisin Abu-Hurairah wanda Annabi (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya faɗa a cikinsa cewa:
« يُصَلُّونَ
لَكُمْ ، فَإِنْ أَصَابُوا فَلَكُمْ ، وَإِنْ أَخْطَئُوا فَلَكُمْ وَعَلَيْهِمْ »
Limamai suna yi muku
sallah, to idan suka dace da daidai kun haye. Idan kuwa suka kuskure wa daidai,
to kun haye su kuma sun nutse. (Sahih Al-Bukhaariy: 694).
A ƙarshe dai abubuwan da
malamai suka ambaci cewa yana iya hana mutum zuwa jam’in
sallah a masallaci sun haɗa da:
1. Rashin jin kiran
Sallah saboda nisan inda ya ke daga masallaci.
2. Idan ladan ya ce:
‘Ku yi sallah a gida’, saboda sanyi ko ruwan sama.
3. Larura mai tsanani,
kamar ta rashin lafiya ko rashin kyawun hanya domin ruwa.
4. Samuwar abincin da
yake sha’awarsa.
5. Matsuwa ta buƙatar kewayawa.
(Mausuu’atul Fiƙhiya yiah:
2/217-220).
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad
Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.