Ticker

6/recent/ticker-posts

Addu'ar Magance Firgitar Kananan Yara

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Malam yarona ya kasa bacci saboda yawan firgici, wanda a baya ba ya yi, don girman Allah a taimaka min da maganin hakan na Musulunci (Sunnah). Na gode

ADDU'AR MAGANCE FIRGITAR ƘANANAN YARA

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Akwai hanyoyi da yawa ingantattu da ake bi domin magance irin wannan matsalar. Amma dai abu ne sananne cewa mafiya yawan Ƙananan yaran da Jinnu ke taɓasu, suna yin hakan ne domin alaƙarsu da uwar yaron.

Don haka bisa shawara, duk abinda za a yi wa yaron don nema masa lafiya, arika haɗawa tare da uwarsa. In sha Allah sai anfi saurin ganin waraka.

Idan kuna ganin alamar kamar yana kallon wasu abubuwa ne dake firgitashi acikin dakinku ko atsakar gida ko palor, to ku rika yin kiran sallah awajen. In sha Allah shaidanun za su gudu daga wajen domin su ba su zama aduk wajen da suke yawan jin sautin kiran sallah. Sannan Ku Karanta Ayoyi Uku na karshen Suratul Baƙarah a cikin gida.

Idan yaro yana tashi da dare saboda tsoro ko firgici, Ku rubuta wannan addu'ar ta Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ku rataya wa yaron, kamar yadda yazo acikin Kanzul Ummal da sunanut Tirmidhiy cewa Sahabin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) wato Saya yiiduna Abdullahi bn Amr bn Al-As (radhiyallahu anhuma) yana koyar da yaransa wannan addu'ar. Amma Ƙanana kuma wadanda baza su iya karantawa ba, yana rubutawa atakarda, yana rataya musu:

أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ مِنْ غَضَبِهِ وَعِقَابِهِ، وَشَرِّ عِبَادِهِ، وَمِنْ هَمَزَاتِ الشَّيَاطِينِ وَأَنْ يَحْضُرُونِ

"Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakkun daga fushinsa da azaba da sharrin bayinsa da kuma daga fitintinun shaidanu da kuma kada su halarci wurina."

Wannan ddu'ar neman tsari ce da Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya koya wa jikokinsa Hasan da Husain.

Ga wata addu'ar nan itama ka rika karantawa kana tofa masa, bayan ka tofa masa Ayatul kursiya yii da falaƙi da nasi kafa uku-uku. Gata nan kamar haka :

أَعُوذُ بكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لَا يُجَاوِزُهُنَّ بَرٌّ ولَا فَاجِرٌ مِنْ شّرِّ مَا خَلقَ، وبَرَأَ وَذَرَأَ، ومِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ، وِمنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فِيهَا، ومِنْ شَرِّ مَا ذَرَأَ فِي الأَرْضِ، ومِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا، وَمِنْ شَرِّ فِتَنِ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ، ومِنْ شَرِّ كُلِّ طَارِقٍ إِلَّا طَارِقاً يَطْرُقُ بِخَيْرٍ يَا رَحْمَنُ

"Ina neman tsari da cikakkun kalmomin Allah, wadanda mai bi da wanda ba ya bi (fajiri) ba za su iya wuce su ba, daga sharrin abin da Ya halitta, da abin da Ya yaya yiafa, da abin da Ya kaddara; da sharrin abin da yake saukowa daga sama, da sharrin abin da yake hawa zuwa gare ta; da sharrin abin da Ya halitta a cikin kasa, da sharrin abin da yake fitowa daga gare ta; da sharrin fitintinun dare da rana; da sharrin kowane mai zuwa da dare (ba zaton alheri ba), sai dai mai zuwa da alheri, Ya Mai Rahma!"

أُعِيذُك بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّةِ مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ لَامَّةٍ

"Ina neman tsari a gare ka da kalmomin Allah cikakku, daga dukkan shaidanu da dabba mai dafi, da kuma daga dukkan idanu masu cutarwa (da hassada)."

Sannan ka nemi Muhrikul Jinn ka ba ma uwar yaron ta rika shafawa ajikinta kuma tana shafa wa yaron. In sha Allahu za a samu waraka.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments