𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum mal. Khamis da fatan kana cikin koshin lafiya. Tambaya ta ita ce; Mene ne falalar sahun farko?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuh.
Falalar sahun farko a
cikin sallah ta jam'i tana da babban matsayi a Musulunci, inda Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya nuna cewa ladanta da kima a wajen Allah sun yi
yawa matuka har ma mutane da sun san abin da ke ciki da sun yi riga-ka-fi ko
sun jefa ƙuri'a don samun damar tsayawa a ciki.
Sahun farko yana da
matuƙar falala, musamman ga maza, saboda shi ne mafi alherin
sahu, kuma yana daga cikin abubuwan da ake ƙarfafa musulmi ya yi
gaggawar zuwa masallaci domin ya samu.
Daga cikin falalar
gaggauta zuwa sahun farko akwai abin da Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya
ce:
«لَوْ
يَعْلَمُ النَّاسُ مَا فِي النِّدَاءِ وَالصَّفِّ الأَوَّلِ، ثُمَّ لَمْ يَجِدُوا
إِلَّا أَنْ يَسْتَهِمُوا عَلَيْهِ لَاسْتَهَمُوا»
Ma'ana: “Da mutane
sun san falalar da ke cikin kiran sallah (adhaan) da sahun farko, sannan ba su
samu wata hanya ba sai sun yi kuri'a a kansu, da sun yi kuri'a.” (Bukhari da
Muslim).
Daga Abi Hurairata
R.A Ya ce: Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: Mafi alkhairi sahun maza shi
ne sahun farko, kuma mafi sharrin sahun maza, shi ne sahun karshe kuma mafi
alkhairin sahun mata na karshe, mafi shirrin sahun mata na farko) (رواه
مسلم).
A wani hadisi Aisha
R.A tana cewa: Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: Lallai Allah da
mala'ikunsa suna yin Salati ga wadanda suke sadar da sahu, kuma wanda yacike
wani gurbi acikin sahu, Allah zai daukaka darajarsa. (حسنه الألباني)
Daga Anas R.A ya ce
Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: Ku daidaita Sahunku domin daidaita
sahu yana cikin cikar sallah (متفق عليه)
Daga Ibn Umar R.A
lallai Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: Ku tsayar da sahunku domin kuna
yin sahune da Sahun mala'iku, ku daidaita tsakanin kafadunku, ku daidaita
tsakaninku, ku hade tsakaninku, kada ku barwa Shaidan, duk wanda ya sadar da
sahu, Allah zai sadar dashi, kuma wanda ya yake sahu Allah ya yanke sa (صححه
الألباني).
Daga cikin neman
samun falalar sahun farko, bai kamata mutum ya bar sahun farko ba, sai ya yi ƙoƙarin samun
matsayinsa. Amma kada ya matsa wa wani ko ya cutar da shi saboda neman sahun
farko, domin hakan na iya jefa shi cikin abin da bai dace ba.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.