Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Matar Aure Da Ta Zubar Da Ciki

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam khamis ga tambaya game da zubar da ciki, ni ce muke tare da mijina muna zaman lafiya amma ya ce mun ba ya son haihuwa, in na samu ciki sai ya sani dole na zubar, meye hukuncina a wurin Ubangijina? Kuma Macen da ta ke da ƙaramin goyo sai kuma ta samu wanin cikin. Ko za ta iya zubar da shi saboda neman lafiyar jaririnta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

A asali bai halatta a zubar da ciki ba kome ƙanƙantansa, sai in akwai wata larura ƙaƙƙarfa. Kamar idan an samu tabbaci ko marinjayin zaton cewa haihuwar za ta saka rayuwar mahaifiyar ko na abin haihuwar ko kuma na su duka a cikin matsanancin hali. Misali idan mace tanada ciki kuma likitoci suka tabbatar dacewa bazata iya haihuwa ba za ta mutu to koda cikin yakai wata nawa idan akwai yanda za ayi azubar dashi aceci rayuwarta to ya halatta domin rayuwarta tafi muhimmanci fiyada wanda yake ciki domin shi baizo duniyarba.

Zubar da ciki don tsoron talauci yana daga cikin manyan zunubai domin shima kisan kai ne. In dai cikin yakai wata huɗu zuwa sama. Idan cikin yakai wata huɗu to sannan an riga an busa masa rai. Idan an zubar dashi da gangan, sai an biya diya yiah zuwa ga Waliya yian jaririn (wato dangin Ubansa). Diya yiar jariri shi ne kwatankwacin Rakuma guda biyar. Wato Ushurin diya yiar Mace ke nan. Kuma bayan haka za a 'yantar da Kuyanga guda, idan babu kuyangar sai ayi azumi Sittin amatsayin kaffara.

Manyan malamai (Rahimahumul Laah) sun sha bamban a kan haka. Dubi tattaunawa a kan mas’alar a cikin littafin Al-Mausuu’atul Fiƙhiya yiatul Muyassarah (6/256) na As-Shaikh Husayn Bn Audah Al-Awaayishah (Hafizahul Laah). Amma abin da fatawar Shaikhul-Islaam Ibn Taymiyah (Rahimahul Laah) ta nuna shi ne:

1. Wajibi ne su bayar da cikakken bawa ko baiwa ko kuma farashinsa na ushurin (1/10) diya yia ga sauran dangin wannan jaririn ban da su. Domin a ƙaida wanda ya kashe wani ba kuma zai ci gadonsa ba.

2. Ushurin diya yia shi ne dinare hamsin idan cikakkiyar diya yiar ita ce dinare ɗari biyar (500). Amma idan dinare dubu (1, 000) ne kamar yadda hadisin Amr Bn Shu’aib ya nuna, ushurinsa zai zama dinare ɗari ɗaya (100) ke nan a yau.

3. Sannan kuma a wurin yawancin malamai akwai kaffara a kansu na ’yanta bawa ko baiwa. Idan kuma ba su samu ba sai su yi azumin watanni biyu a jere. Idan kuma ba su iya yi ba sai su ciyar da miskinai guda sittin. (Majmuu’ul Fataawaa: 34/161).

Duk wanda suke da hannu cikin kashe jaririn duk za su haɗu su biya diya yiar. Kuma kowannensu sai ya 'Yanta Kunyanga ko kuma ya yi azumi Sittin. Hujjah a nan ita ce Hadisin nan na 6910 acikin Sahihul Bukhariy, kuma na 1681 acikin Sahihu Muslim. Duk sun ruwaito Hukuncin da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yanke ma matar data kwada ma wata Mai juna biyu dutse wanda ya yi sanadiya yiar mutuwarta da kuma jaririnta. Amma idan cikin bai kai wata huɗu da samuwa ba, To babu diya yia ko kaffara amma duk da haka dai Zunubi ne mai girma. Don Ƙarin bayani aduba cikin MATALIBU ULIN NUHAA (juzu'i na 6 shafi na 50).

Duk wani laifi da aka tilasta wa mutum ya yi shi, to idan ya yi wannan laifi saboda an fi ƙarfinsa, to Allah ba zai kama shi da laifin wannan aiki ba, saboda hadisin da Abu Zharril Gifáriy ya ruwaito cewa: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: "Lallai Allah ya share wa al'ummata abin da suka yi da kuskure, da abin da suka yi da mantuwa, da abin da aka tilasta masu yin sa". Ibn Majah 2043. Lallai shi mijin ne za a ɗora wa laifin idan ya tilasta miki zubar da ciki, musamman ma idan cikin ya kai watanni huɗu an hura masa rai.

Allaah Maɗaukakin Sarki Ya ce:

وَلَا تَقْتُلُوا أَوْلَادَكُمْ مِنْ إِمْلَاقٍ نَحْنُ نَرْزُقُكُمْ وَإِيَّاهُم

Kuma kar ku kashe ’ya’yanku domin talauci (wanda kuke cikinsa), mu muke azurta ku da su kansu. (Surah Al-An’am: 151).

Sannan kuma ya ce:

وَلَا تَقْتُلُوا أَوْلَادَكُمْ خَشْيَةَ إِمْلَاقٍ نَحْنُ نَرْزُقُهُمْ وَإِيَّاكُم

Kuma kar ku kashe ’ya’yanku domin tsoron talauci (a gare su), mu muke azurta su da ku kanku. (Surah Al-Israa’: 31).

Don haka, bai halatta a kashe abin da ke cikin ciki ba domin tsoron talaucin da ake fama da shi yanzu, ko wanda ake tsoron aukuwarsa nan gaba. Haka ma ko ba domin tsoron talauci ba ne bai halatta a kashe jariri ba, matuƙar dai ya kai girman da aka hura masa rai wato watanni huɗu. Kuma ko da bai kai watanni huɗun ba ma, malamai ba su yarda a dakatar da tsarin halittar ɗan ta yin da ke cikin ciki haka nan siddan, ba tare da wani dalili ƙwaƙƙwara ba.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments