Ticker

6/recent/ticker-posts

Baje Haja/Koli a Kan Intanet Domin Samun Kudi

Daga

Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Damfara a Duniyar Intanet

Intanet ya zo da manyan damarmakin tallata kaya zuwa mutane na kusa da na nesa cikin sauƙi. A kullum Hausawa suna ƙara rungumar intanet a matsayin kasuwar baje hajojin da suke sayarwa. Tun a shekarar 2021, Oyekanmi, (2021 p. 1) ya bayyana cewa rahoton National Bureau of Statistics (Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa) ta nuna cewa kashi 22% na masu ƙananan kasuwanci ne suke amfani da intanet wajen gudanar da kasuwancinsu.

Hausawa masu ƙanana da manyan kasuwanci da dama suna amfani da kafafen intanet daban-daban domin tallata kasuwancinsu. Waɗansu suna amfani da kafafen sada zumunta (WhatsApp, Facebook, Instagram, TikTok, da sauransu),[1] waɗansu kuwa suna buɗe kafafensu na kansu ko su haɗa guiwa da waɗansu masu kafafen intanet domin sama musu gurabu. A duba misalai a hotunan da suke ƙasa:

Hoto Na 2.1: Tallan Hajoji a Kan Sitatus Ɗin WhatssApp

Tallan Hajoji a Kan Sitatus Ɗin WhatssApp

Madogara: An ɗauko su daga sitatus ɗin waɗansu Hausawa a WhatssApp.

Hoto na 2.1 da aka kawo a sama, za a tarar da hoton yana ɗauke da haɗakar hotuna huɗu (4) da aka ɗauko daga sitatus ɗin WhatsApp na mutane daban-daban. Uku (3) na farko mata ne da suke sayar da kayan kwalliya. Hoto na 1 yana ɗauke da takalma da jakunkuna. Hoto na 2 da na 3 suna ɗauke da turamen atamfa (zannuwa). Hoto na ƙarshen kuma an ɗauko daga sitatus ɗin namiji da yake sayar da shaddodi da yadi (yaduna). Duk waɗannan kasuwanci ne ƙanana.

Hoto Na 2.2: Shafin Sayar Da Littattafan Hausa Na WikiHausa

Shafin Sayar Da Littattafan Hausa Na WikiHausa

Madogara: https://wikihausa.com.ng/product-category/hausa-novels/

Saɓanin hoto na 2.1, hoto na 2.2 misali ne na kafar intanet ta Hausawa da suke ba da dama ga waɗansu ‘yan kasuwa daban su baje hajojinsu. Yayin da aka yi ciniki, masu kafar za su ɗauki wani kaso daga ribar a matsayin ladan aikinsu.

Hoto Na 2.3: Kasuwancin Katin Waya Da Data Da Katin Lantarki (Da Sauransu) a Kan Intanet

Kasuwancin Katin Waya Da Data Da Katin Lantarki (Da Sauransu) a Kan Intanet

Madogara: https://amlasdata.com.ng

Hoto na 2.3 da yake sama an ɗauko shi ne daga kafar kasuwancin kan intanet ta AMLAS Data. Wannan nau'in kasuwanci ne na kan intanet mallakin Hausawa. A da, dole ne sai mutum ya je ofishi ko shago ko ya kira waya kafin a saka masa katin waya ko datar burawuzin ko katin talabijin ko na wutar lantarki da sauransu. Da fikira irin ta AMLAS Data, yanzu mutum zai iya hawa kafar intanet ko ya yi amfani da manhajar kasuwancin domin ya sayi data ko katin waya ko katin wutan lantarki, da makamantansu.



[1] Da wuya mutum ya karaɗe sitatus ɗinsa na WhatssApp ba tare da cin karo da hajojin da waɗansu suke tallatawa ba, irin su tufafi ko turare ko na’urori da sauransu.

Manazarta: 

Sani, A-U.,  Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307

Post a Comment

0 Comments