Daga
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
Tsohuwar Gida
Akan samu dattawa mata da suke rayuwa a wasu gidaje. Yawanci akan ware musu balbalinsu (yankinsu/ƙofarsu) na musamman sannan a riƙa kai musu abinci a duk lokacin da aka ƙare. Ire-irensu suna kan gaba musamman fannin aiwatar da tatsuniyoyi musamman a da. Tara yara domin yi musu tatsuniya yana sa yaran su taya su hira tare da ɗebe musu kewa. Ga misalin tsokacin karin magana game da tsohuwar gida:
1. Tsohuwar Gida hana Walwalar Iyali
Wannan karin magana (kirari) na bayyana irin yadda wasu tsofaffin gida suke yin
kane-kane ga lamuran gidan ‘ya’yansu, su hana surukansu da jikokinsu da sauran
mutanen gida rawar gaban-hantsi saboda matsi da faɗace- faɗacensu. Shi ya sa sau da yawa
matan zamani ba su faye
son su auri mijin da yake zaune da iyayensa a gida guda ba. Saboda haka, irin
wannan zamantakewa
na buƙatar gyara domin samun
kyakkyawar zamantakewa ta girmama juna.
Ana amfani da ita ne domin a yi shaguɓe ga wani mutum da yake amfani da matsayinsa wajen takura wa
na ƙasansa.
Kakar
Wajen Uba
Kakar wajen uba ita ce mahaifiyar mahaifi – wato kamar yadda
mahaifiyar mahaifiya take matsayin kakar wajen uwa. Akwai karin maganar da take
ɗauke da amon kakar wajen uba,
kamar haka:
1. Ta fi babu kakar wajen uba
Wannan karin maganar tana nuna irin yadda mafi yawancin
kakanni na wajen uba ba su cika shagwaɓa jikansu, ko nuna masa
matsananciyar ƙauna, ta
hanyar yi masa duk abin da yake so ba, kamar yadda dangin uwa suke nuna masa
tausayi da kulawa.
Ana amfani da wannan karin magana ne a bayyana cewa mutum yana da wani abu mai matuƙar amfani a gare sa, amma amfanin da yake samu daga gare sa ya yi kaɗan kwarai.
Manazarta
Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.