Daga
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
Aure dangantaka ce tsakanin namiji da mace, ta hanyar shari’ah. (CNHN, 2006:22). Aure alaƙace ta halattacen zama tsakanin namiji da mace. Aure muhimmin abu ne ga al’umma, saboda tsabtace zuri’a, haka kuma aure zamantakewa ne ta amincewa tsakanin namiji da mace bisa wasu sharuɗɗa da addini da al’ada suka gindaya, shi yasa ake cewa Aure Sunnar Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallam, Tagomashin babba da yaro.
1. A lallaɓa, auren zamani.
2. Abin da kamar wuya, Gurguwa da
auren nesa
3. Alallaɓa, auren dole
4. Allah ya yi abin, inji mafaɗin aurensa
5. Allah ya yi, aure da maras
kwabo
6. An dai yi, auren so babu hatsi
7. Arha, aure bashi
8. Aure ba ka da Malam
9. Aure babu haihuwa wahala ne
10. Aure farin cikin babba da
yaro
11. Aure maganin talauci
12. Aure yaƙin ‘yan mata
13. Auren baya, shi ne sadakin na
gaba
14. Auren karuwa auren wofi ne.
15. Auren mace mai kyau jari.
16. Ba aure ke da wuya ba, biɗar kuɗi.
17. Ba aure ke da wuya ba, shiga
ka fito.
18. Ba ci ba sha, auren
matsiyaci.
19. Ba ji ba gani, auren Kurma da
Makaho.
20. Da auren Karuwa gwamma kiyon
zakara.
21. Daga wajen wa, aure da duka.
22. Dangaga, auren mace da ciki.
23. Fallasa, auren bashi.
24. Haukan kaza, auren mazuru.
25. Idan aure bai kawo shi ba,
saki ya kawo shi.
26. Je ka-na-yi-ka, auren bashi.
27. Kamar gobe aure da wuri.
28. Karuwa ba matar aure ce ba.
29. Kwakwati kwammati aure gidan
mai samu.
30. Lalura, auren namiji da
‘ya’ya.
31. Matar da ba ta da aure mushe
ce.
32. Namijin da ba ya da aure,
mushe ce.
33. Tsautsayin takaba, aure da
mai ƙararren
kwana.
34. Wanda ba shi da aura, ba shi
auren ‘yar dangi.
35. Wanda ya auri mace don
kyawunta, ya auri wahala.
36. Ya kamata auren na gida, ƙauna
da ta ga wanta da kuɗi.
37. Yaro ya so aure, gidansu ba
wuri.
38. Yaro ya so aure, gidansu babu
goɗiya.
A ƙarƙashin wannan gaɓa, an kawo jerin kare-karen maganan Hausawa
guda 37 waɗanda suke
magana a kan aure da yanayinsa, da matsayinsa da kuma yadda al’ada take
kallonsa.
Manazarta
Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.