Daga
Adamu Rabi’u Bakura,
Ph.D.
Department of
Languages and Cultures
Federal University
Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI,
Ph.D.
Department of
Languages and Cultures,
Federal University
Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID:
https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
A sakamakon zuwan addinin Musulunci a ƙasar Hausa da yadda suka bayar da gaskiya ga addinin, sun rungumi (karɓi) abubuwan da ya zo da su, ciki kuwa har da tsarin sunayen da ya aminta a yi amfani da su. Duk da haka, sun yi ƙoƙarin kawo wasu abubuwa ga sunayen yanka domin su dace da yanayin ƙirar kalmomin Hausa. Waɗannan abubuwan kuwa sun ƙunshi:
a. Laƙubba na addini
b. Gutsure sunan yanka
c. Yi wa sunan yanka kwaskwarima
d. Ƙirƙirar wa sunan yanka alkunya
Laƙubba
na Addini
Laƙabi dai Balarabiyar kalma ce, wadda aka
samo daga kalmar Larabci, da ake kira LAƘAB. Yayin da Hausawa suka yi mata
kwaskwarima ta hanyar yi mata ɗafa-ƙeya na
ƙwayar
ma’ana na wasalin {-i}
ta koma laƙabi.
Ita wannan kalma tana ɗauke
da ma’anar: “Sunan da ake bayyana mutum bayan sunansa na yanka, kamar yadda
Abubakar (2015 p. 326) ya bayyana.
CNHN, (2006 p. 299) ya bayyana
kalmar laƙabi
da cewa, kalmar suna ce da take cikin jinsin sunaye na maza. Tana nufin sunan
mutum wanda yake bin suna na haƙiƙa. Misali; sunansa Abdu, amma a sa masa “Maikano”.
Daga waɗannan bayanai za a fahimci cewa, laƙabi
wani suna ne da akan laƙaba wa ko akan sa wa wani mutum ko wani abu. Misali: “Mai jan (tuƙin)
mota da ba a san sunansa ba, amma an san sana’arsa, sai aka kira shi Direba. Kuma duk inda ya nufa,
kowa da haka zai kira shi. Wato laƙabin sunan mai tuƙin mota.
Sakamakon haka za a iya cewa, laƙabi
suna ne da ake ba mutum bayan sunansa na yanka ko na gaskiya. A wasu lokutan
akan kira mutum da sunansa na yanka da na laƙabi a haɗe.
Misali, Muhammadu Ashiru ko Umarul Faruk da sauransu.
Kowane suna idan ba sunan yanka
ba ne, to zai zamanto laƙabi. Don haka ana iya samun laƙabi na addini ko dangane da yanayin
lokaci da abubuwa da yawa waɗanda
suke tattare da mutum. Wannan na iya kasancewa wani hali da aka san shi da shi,
kamar rowa ko kyauta ko kuma zamba da ha’inci, ko kuma yi wa mutane ƙeta ko
tausayi. Ko kuma a ɗauki
wani sashen jikin mutum a yi amfani da shi wajen yi masa laƙabin.
Duk irin yadda mutum ya kasance a ƙasar Hausa za a samu yana da laƙabinsa
a tsakanin al’umma
wanda ba dole ne shi kansa ya san da haka ba. Yayin da aka zo maganarsa a
muhallin da ba ya nan sai a ambaci laƙabin.
A al’adar Bahaushe, wasannin da
ke akwai a tsakanin jika da kaka, ko ƙanin miji da matar wa, ko tsakanin
Hausawa da Fulani ko da Barebari da sauransu, su ne matakan tabbatar da laƙubba a
tsakanin al’umma.
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.