Ticker

6/recent/ticker-posts

Sunaye Na Mata Sahabbai

Daga

Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng

Da

Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736

Daga cikin mata ma akwai Sahabbai da suka taka muhimmiyar rawa wajen yaɗa addinin Musulunci ta fuskoki da dama. Masana sun yi ƙoƙarin kawo jerin sunayensu domin al’ummar Hausawa da suka rabauta da karɓar Musulunci su raɗa wa ‘ya’yansu mata. Waɗannan mata Sahabbai su ne:

1. Asma’ bint Abu Bakr As-Siddiƙ

2. Asma’ bint Umais bin Ma’d

3. Asma’ bint Yazid

4. Fatimah bint Al-Khattab

5. Fatimah bint Ƙais bin Khalid

6. Hamna bint Jahsh

7. Hind bint Utbah

8. Khansa’ bint Amr Tamadir

9. Khaulahbint Hakim

10. Rubayyi bint Mu’awwidh bin Afra, da sauransu

(Hareeri & Tahir, 2009 p. 104)

Haka kuma, akwai sahabbai mata da suka hardace Alƙur’ani Maitsarki, waɗanda suka haɗa da: A’ishah Siddiƙah, Hafsa, Umm Salamah, da kuma Umm Warƙah. Wasu Sahabban mata sun koyi wani ɓangare ne na Alƙur’anin. Irin waɗannan matan sun haɗa da:

1. Hind bint Usaid

2. Ra’itahbint Hayyan

3. Umm Hisham bint Harithah

4. Umm Sa’d bint Sa’d bin Ar-Rabi

(Hareeri & Tahir, 2009 p. 106-7).

Haka kuma, sun yi ƙoƙarin kawo matan da suka mallaki ilimin tafsiri. Misali, A’ishah Siddiƙa, tana kuma ɗaya daga cikin waɗanda Allah Ya yi wa baiwa da sanin hadisan Annabi S. A. W. Haka kuma, akwai ‘yar’uwarta Asma bint Abu Bakar, da Fatimah bint Ƙais, da Umm Atiyyah Al-Ansariyah, da Umm Hani Al-Ansariyyah da kuma Umm Salamah (Hareeri & Tahir, 2009 p. 106-7).

Sahabbai mata kuwa da Allah Ya hore musu fahimtar ilimin fiƙihu sun haɗa da:

1. A’ishah Siddiƙa

2. Asma bint Abubakar

3. Fatimah Az-Zahra’

4. Fatimah bint Ƙais

5. Hafsah bint Umar

6. Haula bint Tuwait

7. Laila bint Ƙanif

8. Maimunah, da Safiyyah

9. Sahlah bint Suhail

10. Umm Ad-Darda’ Khairah bint Abu Hadrad Al-Aslami

11. Umm Aiman

12. Umm Atiyyah

13. Umm Habibah

14. Umm Salalah

15. Umm Sharik

16. Zainab bint Abu Salamah

(Hareeri & Tahir, 2009 p, 107-8)

Akwai wasu keɓaɓɓantu fannonin da Allah Ya yi wa waɗannan mata Sahabbai baiwa da su. Misali, Aishah Assaddiƙa ta shahara wajen naƙaltar fasaha. Ita kuwa Ummu Salamah an yi mata baiwa da naƙaltar ciki da wajen Shara’a. Yayin da Asma’ bint Yazid bin Sakan aka yi mata baiwa da fasahar magana. A ɓangaren fassarar mafarki kuwa babu kamar Asma bint Umais bin Ma’ad (Hareeri & Tahir, 2009 p. 108).

Shahararru a fannin magani da aikin tiyata a tsakanin Sahabbai mata, babu kamar waɗannan:

1. Hamnah bint Jahsh

2. Laila Al-Ghifariyah

3. Mu’adhah Al-Ghifariyah

4. Rubayyi bint Mu’awwidh

5. Rufaidah Aslamiyyah (har ta mallaki asibiti)

6. Umaimah bint Ƙais

7. Umm Atiyya

8. Umm Kabashah Al-Ƙuda’iyyah

9. Umm Muta Al-Aslamiyah

10. Umm Sulaim

(Hareeri & Tahir, 2009 p. 109).

An kawo waɗannan sunaye ne domin Hausawan da suka karɓi Musulunci su yi amfani da su a madadin sunayen gargajiya da sukan raɗa wa ‘ya’yansu. Saɓanin a baya da sukan ba wa ‘ya’yansu laƙabi akan ƙudurin sunayen abubuwan da sukan yi tasiri ga wanda aka ba.

Ta fuskar addinin Musulunci kuwa, maƙasudin amfani da suna shi ne, domin wanda aka ba sunan ya kasance mai halaye da ɗabi’u da tsoron Allah tare da bin dokokin Mahalicci sau-da-kafa, tamkar mai shi na asali. Wannan ne Ya sa akan sanya wa mutane sunayen Ma’iku, saboda su ba sa saɓa umarnin Ubangijinsu. Kodayake dai al’umomi da dama sun fi raɗa wa ‘ya’yansu suna kamar:

1. Jibrilu

2. Rilwanu

3. Maliki

Sukan saka waɗannan sunaye ne kasancewar su Mala’iku ne da sukan zo da abubuwan rahama ga al’umma. Don haka ne ake kwaɗayin mai bin sunan ya kasance kamar yadda halayensu da ayyukansu suke. An guji sanya sunayen Mala’iku kamar Azara’ilu da Raƙibi da Atidu, domin kauce wa tasirin ayyukansu ga mai sunan. Hasali ma Hausawa sukan ce: “Suna linzami” domin sanin yadda yakan yi tasiri ga mai shi.

Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083

Post a Comment

0 Comments