Daga
Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Sunayen addini tsantsa, su ne sunayen da suka zo ƙasar Hausa sakamakon zuwan Larabawa ‘yankasuwa da masu yaɗa addinin Musulunci. Akan yi wa wasu sunayen laƙabi a sakamakon wasu halaye ko ɗabi’u da masu su na asali suka nuna. Irin waɗannan laƙubban ba a al’ummar Hausawa kaɗai ake aiwatar da su ba. Hasali ma Ubangijin talikai ne da kanSa Ya yi wa zaɓaɓɓun bayinSa. Kodayake Hausawa suna gudanar da wasu sauye-sauye ga irin waɗannan laƙubban addini domin su dace da tsarin ginin kalmominsu. Misali:
Jad. na 5: Samar da Sunayen Hausawa Daga Laƙubban Addini
|
|
Suna |
Laƙabi |
|
1. |
Muhammadu |
Allah
ne da kanSa ya kira Annabi
S. A. W da laƙubba da suka haɗa da, Al’amin, Hausawa suka mayar
da shi Aminu. Haka Ya kira shi Haris, sai suka mayar
da shi Harisu. Ya kuma kira shi Mubasshir, su kuma suka mayar
da shi
Mubasshiru. Ya ambace shi da Mudaththir, suka mayar
da shi Mudassiru. An kuma ambace shi
da Nadhir su kuma suka mayar
da shi Naziru. An kuma kira shi Siraju suka mayar
da shi Surajo. Haka kuma akan haɗa sunan Muhammadu da wani suna
da yake ishara da tsarin jerin adadin yaran iyali,
Kamar: Auwalu, Sani, Salisu, Rabi’u, Hamisu, Sadisu, Sabi’u, Saminu, Tasi’u, da
kuma Ashiru. |
|
2. |
Musa |
Kallamu |
|
3. |
Ibrahim |
a.
Halilu b.
Badaɗe c.
Aboki makusanci |
|
4. |
Khadijatu |
Kubura |
|
5. |
Abubakar |
Kubura |
|
6. |
Umar |
Faruk |
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.