Ticker

6/recent/ticker-posts

Tasirin Zamani a Neman Kudin Hausawa

Daga

Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Damfara a Duniyar Intanet

Cuɗanyar Hausawa da baƙin al’ummu musamman Larabawa da Turawa da kuma sauyawar zamani sun samar da sauye-sauye da dama a fannin neman kuɗin Hausawa. Duk da haka, za a fahimci cewa, ko da Hausawa ba su yi cuɗanya da kowace al’umma ba, za su samu sauye-sauye da cigaban zamani a harkokin rayuwarsu. A har kullum, halin rayuwa na tilasta wa ɗan’adam amfani da fikira wajen samar wa kansa sauƙi da mafita daga ƙalubalen da yake dabaibaiye da matakan rayuwarsa. Saboda haka, yadda kullum yanayin duniya yake sauyawa tare da ɓullo da sababbin ƙalubale da ɗan’adam bai taɓa cin karo da su ba, haka shi ɗan’adam yake ƙara ƙirƙiro hanyoyin fuskantar matsalolin. Waɗannan su suke haɗuwa su samar da cigaban zamani. Cropley, (2019) ya kawo cikakken bayani a kan wannan falsafa.

A kullum Hausawa suna ƙara samun wayewa ta fuskar kasuwanci tare da faɗaɗawa da bunƙasa sana’o’insu. Ana iya kallon tasirin zamani kan neman kuɗin Hausawa ta fuskoki daban-daban kamar haka:

i. Ƙare-ƙare: Wannan ya shafi fito da wasu sababbin dabarun bunƙasa hanyoyin neman kuɗi da ake da su. Ya haɗa da sauƙaƙa samar da abubuwa ta yadda idan kuɗin da ake kashewa wajen samar da su ya ragu, to ribarsu za ta ƙaru. Bugu da ƙari, ya shafi yi wa kayan da ake samarwa kwaskwarima ko wani ƙari domin ya dace da buƙatun al’umma a zamanance.

ii. Ƙirƙire-ƙirƙire: Wannan ya shafi ƙirƙirowa ko ƙago sababbin abubuwa da za su dace da zamani tare da biyan buƙatar da ake da ita a lokacin.

iii. Hulɗayya: Ƙulla hulɗa da sababbin abokan kasuwanci wani babban sauyi ne a harkar neman kuɗi. Wannan ya fi faruwa a yanzu da intanet yake bayar da damar hulɗa da kwastomomin da suke wata uwa duniya.

Kamar yadda masu iya magana suke cewa “ruwa ba ya tsami banza,” akwai dalilai daban-daban da suke haifar da waɗannan sauye-sauye a sha’anin neman kuɗin Hausawa. Idan aka ce “tasirin zamani,” dunƙulallen zance ne da yake tattare da abubuwa mabambanta. Yayin da aka fasa cikinsa, za a tarar da ɗaiɗaikun sabubban da suka haɗa da:

a. Ɗaukar hannu

b. Yanayi/tilas

c. Yayi

A- Ɗaukar Hannu

Wannan ya shafi kwaikwayo daga fasahohin waɗansu al’ummu na daban. Misali, a yau teloli a ƙasar Hausa sukan koyi nau’o’in ɗinkuna irin na tufafin al’ummomin ƙasashen ƙetare (kamar kwat da sauransu). Wani misali shi ne yadda maƙeran Hausawa suke samar da kayayyaki daban-daban ta hanyar ɗaukar hannu daga ƙere-ƙeren ƙasashen ƙetare. Haka ma kafintoci Hausawa suke ƙera abubuwa ta hanyar ɗaukar hannu. Babban misali shi ne bodin babbar mota (roka) da ake amfani da kataki[1] da ƙarafa wajen ƙerawa.

B - Yanayi/Tilasci

Sauyin yanayi da ya shafi rayuwa ko muhalli yana kaiwa ga an samar da sababbin hanyoyin neman kuɗi tare da sauye-sauye a waɗanda ake da su. Kasuwancin sayar da datar intanet da ta POS waɗanda Hausawa suka runguma a yau, duk misalai ne na sababbin nau’o’in kasuwanci da suka samu a sakamakon tasirin yanayi. Haka kuma, sana’ar sayar da awara/wara/ƙwai-da-ƙwai da take ƙara mamaye ƙasar Hausa tana da alaƙa da yanayin yunwa da talauci da Hausawa suke ciki. A lokacin annobar korona kuwa (2019-2022), Hausawa da dama sun tara kuɗi ta hanyar kasuwancin takunkumin fuska (face mask).

C - Yayi

Akan samu lokutan da yayi yake sauyawa wanda sauyin nasa kuma zai samar da sababbin hanyoyin samun kuɗi. Sannu a hankali akan saki wani abu da aka yi riƙo da shi na tsawon lokaci domin a koma wani daban. Irin wannan sauyi yana kasancewa cikin yanayin da abu ne mai wuya a iya bayanin mene ne haƙiƙanin dalilin da ya sa aka saki al’adar baya. Sau da dama sai dai a ce “wayewa.”

Babban misalin wannan shi ne yadda matasan Hausawa suka riƙi babban wando (fantalo) a matsayin kwalliya (tsukakken wando kuma ya kasance ƙauyanci), har zuwa wajajen shekarar 2008. Daga baya kuma sai yayi ya sauya inda aka ɗauki fantalo a matsayin ƙauyanci, shi kuwa tsukakken wando ya koma wayewa. Duk lokacin da irin haka ya faru, masu kasuwancin wandunan dole su sauya domin samar da abubuwan da mutane za su saya ba waɗanda za su yi kwantai ba.



[1] Jam’in “katako”

Manazarta: 

Sani, A-U.,  Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307

Post a Comment

0 Comments